Showing 72001 words to 75000 words out of 133189 words

Chapter 25 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

259

har abada”

Kareem yayi shiru be ce komai ba, domin ya fahimci Daddy ba zai yarda da duk wani zancensa ba.

“Saki nawa ka yi mata?”

“Daya”

Sai a lokacin Daddy ya sassauta muryarsa ya daina yi ma Kareem fada.

“Ka yi hakuri, shi zaman aure dan hakuri ne, duk can talkaminmu suka tsinke, dole sai an kai zuciya nesa, bana son na sake jin wata matsala a tsakaninku, ka maida matarka dakinta ku zauna lafiya dan Allah”

Kareem kamar zai fasa kuka ya ce.

“Daddy mai daki shi ya san inda yake masa yoyo...”

Be rufe baki ba Daddy ya rufe shi da fada yana masa tsawa.

“Get out Kareem, tashi ka dauki matarka ka aje ta gida sannan ka wuce aiki, wato Momy kake tsoro kana gudun zuciyarta mu kuma ka raina mu ko? Toh ka bari har bayan raina sannan ka saketa idan ka ga dama ka hada har da yayanka ka koresu gaba daya”

Da sauri Kareem ya sauko daga kan kujera yana bawa Daddynsa hakuri, domin idan akwai abun da yake gudu da tsoro a rayuwarsa to fushin iyayensa ne.

“Ka yi hakuri Daddy, na maida aurena saboda kai, kuma zan dauke ta mu tafi gida yanzu kamar yadda ka ce ka yafe min dan Allah”

Daddy ya dauke kai ya kai hannu ya dauki gilshinsa ya mike tsaye ya shige bedroom dinsa. Kareem ya dafe kansa ya rumtse ido, ya fi karfin minti talatin a haka sannan ya dago ya fito daga bangaren ya dawo bangaren Hajiya Hassana ya zauna a falon ya kasa yin komai har sai da Step mother dinsa ta fito sannan ya gabatar mata da abun da ya maido da shi bangaren nata.

“Na maida aurena Hajiya, a fada mata ta fito mu tafi”

Hajiya Hassana ta yi murmushin jindadi.

“Haba yanzu na ji magana, ko kai ba haka ake so, kuma dan Allah ayi ta hakuri karka ce zaka biyewa mace ita mai rauni ce, kuma duk matsala da za a samu a daina saurin saki, muna raye idan ya kamata mu ji sai ka sanar mana mu tsawatar mata yafi ayi ta saki ga yara”

“Tohm Hajiya”

Ya amsa irin amsawar nan na wanda ya rasa interes da mafaka da kuma gata a lokaci daya, daman tun farko yayi tsammanin haka shi ya hana shi sakinta a lokacin da Momy bata dade da barin duniya ba, da ace kuma ya sake a lokacin da take raye Allah kadai ya san irin fushin da Momy zata yi da shi. Ya mike tsaye yana jin wani fever na rufe shi ya nufi motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna yana jiranta bakinciki cike fal a zuciyarsa.
Ya bata awa daya a haka sannan Aneesah ta fito ta bude motar ta ce masa.

“Big Bro wai Hajiya tace ka tafi zata kawo ta da kanta”

“Toh ki fadawa Daddy haka idan na wuce”

Cikin tsananin damuwa Kareem yake maganar sannan ya ja motarsa ya fice daga gidan. Wunin ranar aiki kawai yayi dan ya zame masa dole ba dan jikinsa da zuciyarsa suna cikin dadi ba. Bayan ya gama yana kokarin hada kayansa ya wuce wata mate room ta shigo ta kawo masa takardar envelope.

“Maman Khalid miye wannan”

“Wallahi ban sani ba, wata ce ta zo dazun bata same ka tace bari ta ba ni na aje maka dan Allah kar na bawa kowa sai kai hand to hand”

Ta fada cikin hausarta da bata gama kwarewa ba, kasancewarta bayarabiya. Ya karba fuska ba yabo ba fallasa yayi mata godiya ya hada kayan saukinsa ya fice daga office din. Sai da ya shiga motarsa sannan ya bude envelope din wani kamshi mai dadi ya bugi hancinsa, flower ce farkon abun da ya fara cirewa daga takardar sannan wani sexy chocolate da kuma farar takardar mai rubutu red. Be yi tsammanin ganin romantic abu irin wannan ba sai a Safeena kuma ya canka daidai a lokacin da ya fara karanta sakon na karin shekararsa a yau.

“Happy birthday Love, barka da zagayowar ranar haihuwar mutumen da bana son zama da kowa sai shi, barka da zagayowar ranar haihuwar mai bani farinciki a zuciya da jiki, mai kwantar da min da hankali, mutumen da ke nisantarsa ke haukata ni ta hana ni sukuni, barka da karin shekara My future husband, my partner in crime, the father of my future kids, father to be... I know its your birthday today.. I am sure u will give me treat in a big house like we use to be.. so I shall talk to you in person there, because I don't know to express my feelings in paper, i love you duk yadda kake tsammanin za mu iya rabuwa da junanmu ba zamu iya ba Kareem saboda muna son junanmu, ba zan iya kyaleka a irin wannan yanayin da kake da bukatar wani a kusa da kai ba, i know how painful it's to lost a best friend and Mother. Please take good care of yourself for me...”

Ya girgiza after ya gama karantawa, so today is his birthday gaba daya ma ya manta, daman tun kamin su rabu tun tana girlfriend dinsa ita take tunawa da birthday sai kuma Momy, and even after break up bata daina wishing dinsa ba a duk lokacin da ranar zata zo. Wani gurin ya bude a motarsa ya saka takardar ya rufe ya yi ma motarsa key.

Kusan wannan ne karo na farko da yake jin kamar baya sha'awar komawa gidan all his thoughts is Yusura ta koma gidan by that time, hakan ne ya rike shi daga komawa da wuri domin samawa yaransa abun da za su ci da rana wani lokacin daga restaurant yake karbowa ya je musu da shi, wani sa'in kuma da kansa yake girkawa tare da su ko kuma kamin su dawo. He park his car near the entrance ya bude motar ya fito ya shiga falon. To his greatest surprised yaransa suke tarbe shi da wani irin farinciki da murna da ba su taba tarbonsa da shi ba.

“Dady welcome home, Dady Mamy ta dawo”

Ya rage tsawonsa yana kallonsa da murmushin da ya ara ya yaba a fuska saboda yaransa.

“Kun jidadi?”

“Eh sosai”

Babbar ta fada sai ya shafa kanta, ba su taba tambayarsa ina Mamy su tafi ba, yaushe zata dawo me yasa bata gidan, tun da suka dawo daga school ba su same ta ba ba su sake walwala ba, kuma ba su tambaya ina take ba, kai ka ce sun fahimci sakinta aka yi, tun daga lokacin Kareem be sake kai su family house dinsa ba saboda gudun su ganta ko kuma su yi kuka idan zai dawo da su.

“I'm happy too”

Ya fada yana kallonsu cike da alfahari, and he's not lie farincikin yaransa farincikinsa ne, hakan kuma ba yana nufin ya jidadin dawowar Yusura ba, idan har akwai abun da yake nadama a yanzu be wuce aurenta ba, me yasa be fadawa Momynsa gaskiya from first place ko da ba zata jidadin haka ba? Yanzu a wa gari ya waya, waye a matsala sama da shi?

“Kun ci abinci?”

“Eh munci Mamy ta dafa mun ci, naka yana dinning Dady”

“Okay bari na je na yi wanka na shirya sannan na zo na ci, ku je ku yi shirin islamiya”

“Okay Dady”

Karamin ya amsa, babbar kuma sai da ta sumbance shi sannan ta nufi sama da gudu tana murna. Tsaye yayi yana kallonsu har suka haye suka shige dakin Yusura sannan ya sauke ajiyar zuciya ya haura stairs din ya shiga dakinsa. Bayan yayi wanka ya kwanta a dakin yayi bachi awa daya ya farka, bandakin ya shiga yayi alwala ya fito ya saka ya sauya tufafin jikinsa daga kanana zuwa shadda sannan nufi madubi ya dauki dan'uwansa turare ta feshe jikinsa sannan ya dauki wayarsa ya wallet dinsa then car keys ya fice daga gidan gaba daya.

A hanya ya tsaya yayu sallah la'asar sannan ya karasa restaurant dinsa. Yana shigowa reception din Nabil da ya gama dutysa zai fita ya gaishe shi cike da girmamawa. Kareem ya mika masa hannu suka gaisa.

“Ka gama naka eh?”

“Eh na gama ranka ya dade, daman duty safe nake yau, ko akwai abun da zan yi?”

“No aa, ka ce ka daina karatu?”

Ya gosa kansa cikin jin kunya ya amsa domin abun kunya ne wannan zamanin a kalli matashi kamar shi ace baya karatu a .

“Eh Wallahi, amman dai zan koma nan gaba idan Allah ya yarda”

“Me ka taba karanta? Wane course?”

“Mass Com na fara, amman dai ina son nan gaba idan zan koma na canja course”

Kareem ya cigaba da tafiya yana fadin.

“Why baka son aikin jarida ne?”

“Ina son, amman dai yanzu na fi sha'awar Public health”

“Karatun health yanzu yayi yawa, why not ka yi political science? Karatun yana da kyau, kuma idan ka dace da gurin aiki kamin an ankaro ka dauke nauyin gidanku”

“To da har ka kawo wannan shawarar da yardar Allah shi zan yi ranka ya dade”

Kareem yayi murmushi yana jindadin yadda Nabill yake girmamashi.

“Na jidadin haka, ni kuma zan yi kokarin sama maka scholarship, a private ko kuma gov school, ban sani ba ko a samu a nan gida nigeria ko kuma a waje, fatan dai ba zaka ba ni kunya ba”

Nabil ya rasa me zai ce ya rika hannun Kareem yana son masa godiya ya kasa domin be taba kawo wani zai dauki nauyin karatunsa ba, wanin ma kuma Kareem.

“Ranka ya dade, na rasa me zan ce ma”

“Toh ka aje kalamanka sai idan an samu tukuna, sai ka yi godiya”

Cewar Kareem yana dafa kafadarsa sannan ya wuce yana murmushi ya bar Nabil tsaye da mamaki. Be yi taku goma ba ya juyo ya kalli Nabil.

“Nabil ya Noor take?”

Nabil ya hade yawun bakinsa da sauri ya matsa yana amsawa.

“Ta.. Tana lafiya ranka ya dade”

“Ba wata damuwa babu wata matsala?”

“Eh to tana dai cikin damuwa, mutuwarta nan ta dan taba ta gaskiya, domin ta canja gaba daya kamar ba ita ba”

Kareem be ce komai ba, ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Office dinsa ya shiga sai da ya zauna sai kuma ya tashi yake yi yanzu a duk lokacin da ya shigo, da zarar ya kalli kujerar da Hafiz yake zama idan ya shigo office din da yamma sai ya ji babu dadi. Har yanzu ya gagara sabawa da rashin abokinsa wannan kawa zucin yana nan tare da shi, shi ke hana shi walwala a duk lokacin da ya shigo office din.

Be wuce minti ashirin a ciki ba, ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice da kansa ya shiga ya saka aka zuba masa abincin da yake sha'awar ci yaron gurin ya rika masa har gurin motarsa. Front seat ya bude aka zuba abinci sannan ya rufe ya shiga bangaren tuki yaja motar ya fice daga restaurant din gaba daya.

Tuki yake not knowing what to do or to go, shi dai gashi nan duniyar gaba daya ta ki ta yi masa dadi. Be faka ba sai da ya samu wasu itatuwa dake gefen hanya, ta cikin itatuwan ya ratsa ya faka motarsa sannan ya bude ya dauki abinci yana ci, gurin is so fresh ga wani iska mai dadi babu damuwa ko hayaniyar kowa it's just him and himself.




NOOR POV

A kwana a tashi babu wuya ga Allah, kamar jiya na fara wanka duk dai wasu sukance wankan be wajaba a kaina ba, saboda ya sake ni, sai dai zancen da ya fi karfi shi ne na yin zaman takaba domin akwai gyara a auren kuma ban kai ga cika idda ba ne ya rasu. A ranar da na yi wata hudu da kwana goma Mama ta aiko da waina da fanke aka raba sadaka yan'uwanta suka zo tare da yan'uwan Baba aka saka ni na yi wanka na saka sabuwar atamfar, a ranar kuma mutuwar Hafiz ta dawo min sabuwa kai kace mun yi shekara aru aru da shi ba yan watanni ba, sai dai abun da ya daure min kai shi ne na rashin zuwan dangi ko yan'uwansa a gurin tun a ranar da na dawo gida har zuwa yau babu wanda ya leko ni ko ya bincika lafiyata, abincin da ake cewa dangin miji ma suna kawowa matarsa idan tana takama basu kawo min ba. Wata kila Aisha ta shafa min bakin fenti a idonsu domin na lura har bayan mutuwar Hafiz kishi take da ni.

Bayan sallah Isha'i, a lokacin da kowa ya watse, ina zaune ina gyara wake soya Yaya ya shigo cikin gidan da kuzarinsa ya ce.

“Noor oga Kareem ne a waje yace na kira ki”

Na yi shiru na wasu dakiku sannan na mike tsaye kamin na cira kafa na ji Umma ta tabe baki tana fadin.

“Wannan ai ba mutunci ba ne, ace ana maka sallama ka mike kai tsaye ka fice ba tare da tunanin fadawa mahaifi ba, kai ma ai ba ita ya kamata ka samu kai tsaye ka fada mata ba mahaifinku ya kamata ka fadawa”

“Ba kisan waye oga Kareem ba Umma, oganmu ne na gurin aiki kuma abokin mijinta nw Hafiz ya saba zuwa nan akai akai”

Ya Nabil ya bata amsa.

“Tohm Allah ya kyauta, tashi ki tafi, amman gaskiya idan haka mahaifiyarku ta koya muku ba abun kirki ba ne, ai sai uba ya aminta ake fita domin shi yake aurar da yarinya”

A kam ban iya rike kaina ba sai da na mayar mata da martani.

“Baki san komai akan uwarmu ba, karki sake fadin wata mummunar kalma akanta”

Kallona ta yi ta dauke kai bata ce komai ba, ta cigaba da dakan yajin da take. Ni kuma na shiga ciki na dauko hijab dina na saka na fito kofar gidanmu. Sai na same shi a gurin da suka saba tsayuwa shi da Hafiz idan sun zo, ko kuma idan ya zo shi kadai.

Ganinsa ya tuna min da Hafiz sosai sai zuciyata ta yi min babu dadi, shi kuma na lura baya cikin walwala da farinciki, gashi ya rame kamar ni yayi hudu haskensa ya rage. Gambun motar dake bude ya rufe sannan ya jingina da motar yana kallona kamar wanda be taba gani na ba.

“Noor how are you now?”

Tambayar yake ya nake, amman sai na ji kamar yace na fada masa damuwata ta hanyar kukana. Kawai sai na fara hawaye ina kallonsa, i miss him i miss his friend i miss my previous life.

“Kina cikin damuwa ko?”

Na daga mishi kai, sai na ji ya sauke ajiyar zuciya.

“Duk yadda kike tsammanin abun ya wuce nan Noor, na fi ki shiga damuwa yanzu, i loss hope, kawai ina rayuwa da kokarin tsayawa saboda Yayana, a yanzu babu wani daki da zan iya rufe kaina na ji sanyi, duka dakunan zafi ne da su kamar wuta”

Na share hawayena.

“Da zan iya komawa na gyara rayuwata ta a baya...”

Na ji ya fada sai kuma yayi shiru be cigaba ba. Ni kuma na kalleshi na ce.

“Da ka goge shafina a rayuwarka”

Ya girgiza min kai.

“Ba zan iya goge ki a rayuwata ba Noor ko da kuwa ace ina da wannan damar, ba ki min komai ba, babu dalilin da zai saka na natsane ki, you're just innocent, precious soul, and Hafiz was right akan abubuwa da yawa akanki”

“toh me zaka gyara?”

Yayi murmushi ya gyara tsayuwarsa.

“Ba wannan ya kawo ni, na zo nan ne saboda na yi magana da ke da kuma Baba, amman kamin nan fada min ya kike?”

“Ina lafiya, amman mutuwa bata da dadi Kareem, shiyasa lokacin da Hafiz ya fada min mahaifiyarka ta rasu, na yi kuka sosai na tausaya maka yanzu kuma na ji yadda ake ji”

Murmushi yayi ya daga kansa sama sai kuma ya sake kallona.

“Noor... Kamin na manta, na zo nan ne saboda maganar gadonki da kuma kayan dakinki”

Na cigaba da kallonsa ina sauraren abun da yake fada.

“Noor dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen Hafiz akan gado ko wani abu, sun ce baki da gado kanensa ya kira ya fada min kuma na je na same su na yi musu magana na fahimtar da su, amman ba su yarda ba, iyakar hujjarsu wai Hafiz ya sake ki kamin ya rasu, kuma kamin ya sake ki wai be taba tarayya dake ba haka ne?”

A nan na sauke kaina kasa na dan bata rai.

“Aisha ta bata ni a gurin kowa, kuma ita ce silar duk faruwar haka”

“Babu wanda zai iya bata ki a gurina, kuma mutuwar aure abu ne da Allah ya kaddara, kuma ba dan Allah ya rubuta haka ba, na yi magana da Hafiz kuma yayi alkawarin yana dawowa zai zo ya dauke ki ku tafi gidan tare, sai dai kamin ya iso Allah yayi ikonsa”

“Da gaske?”

Ya daga min kai.

“Yes Noor na lura kina cikin damuwa a lokacin kuma kin fada min kina son komawa ai, babu wani abun da zaki roka ban miki shi ba Noor sai idan ba zan iya ba”

“Na dauka ina takura maka ne, na ga har baka son zuwana gurinka, na san ni ina da takura ai”

Yayi murmushi.

“To ki yi hakuri, idan Baba yana ciki shiga ki masa magana”

“Baya nan yana majalisa”

“Shiga ciki zan je can na same shi, ki kwantar da hankalinki Allah zai baki abun da ba su ba ki ba, kayan dakin ma sun ce ba za su baki ba ai saboda shi yayi komai”

“Ni fa ba abun da ya dame ni da wani gado, su je su yi ta riko, amman ka yi magana da Baba shi ne dai na ji yana zancen zai yi kara idan ba a bada ba”

“Okay”

Kallona yake har na shige cikin gidan, ina shigowa Ya Nabil ya fita waje.”Duk wata maganar da zai yi da Baba na san ba zai saurare shi, amman kudi za su iya sakawa ya fahimci komai kuma ya sassauto. Da alaka kuma Kareem yayi amfani da su ne domin babu ya shigo da far'a har da tsarabar nama yayi ma Umma. Cewa yake a yanzu ya hakura zai kyalesu amman saboda Kareem be kawai ba dan haka ba da babu abun da zai hana shi jan min hakkina. Yanka biyu aka ba mu, sai da muka cinye sannan yayi mana albishir

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login