Showing 123001 words to 126000 words out of 133189 words

Chapter 42 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

280

kyau”

Mai gadin ya kalleta da kyau kamar yadda mai gidansa ya ba shi umarni.

“Na ganta ranka ya dade”

“Daga yau karka bari ta sake shigowa cikin gidan nan, idan ka bari ta sake shigowa a bakin aikinka”

“Toh Wallahi ba zata sake ba, ko da kuwa ita din aljanna ce, wuce Hajiya dan Allah ki wuce”

Safeena ya rausayar da kai tana kallon Kareem domin ba da wasa ta zo ba.

“Really?”

Kareem ya daga mishi hannu.

“Ban da yau, bar ni zan yi magana da ita”

“Toh ranka ya dade”

Mai gadin ya juya ya koma, sannan Kareem ya dauke kai ya nufi falon.

“Baki da hurumin shigowa gidana, na baki 2 min to talk your rubbish and go”

Cewar Kareem bayan ya shigo, sannan ya nufi Center table ya dora wayoyin dake hannunsa ya juyo yana kallonta fuska babu annuri. Safeena ta tabe baki.

“Gaskiya ne, hausawa suka ce namiji ba dan goyo ba ne, kuma na gani na tabbatar a yau, har ka manta wacece ni kake fadawa mai gadi kar ya bari na sake shigowa gidanka? Kuma ka ce bana da hurumin shigowa gidan? Saboda me? Ai Yusura bata gidan yanzu, balle ka ce kar ta gani, kuma kana ganin yanke alaka da ni zai sama kama yanci da zaman lafiya ne?”

Ya aika mata da wani kallon kaskanci da tsana.

“i don't want to see your face, kin cutar da ni iyakar cutarwa, sai yanzu nake hango abun da Momy take guje min, na gode Allah da ban aure ki ba”

“Kai ka fara cutar da ni, kai ka fara yaudara da sunan zaka aure ni alhalin kansan mahaifiyarka ba zata bari ba, ina ji ina gani ka aje ni ka auri wata, na yi duk yadda zan iya saboda na cire a zuciya na amman na kasa, bayan na samu mai aurena na yi aure kuma ka sake sabunta min kaunarka har ta kai bana iya gane komai sai naka, na yi sha'awar haihuwa da kai ne saboda ina sonka, amman yanzu na gane na yi babban kuskure domin yaudarata kake a kullum, gashi yanzu na haifi jininka kuma aurena zai lalace bata sigar da nake so ba”

Hawaye na mata zuba ta matsa kusa da shi.

“All my plan was wata rana zaka aureni, saboda ka saba min da kanka, bana da buri sai na zama da kai, bana jin dadin mu'amala da mijina sai kai, a hakan ka budewa wata zuciyarka ta shiga, kuma ka kwashe sirrina duka ka fada mata, gashi yanzu ta yake ni da shi, igiyar aurena haka ya rage ta katse”

Ta muna mishi tazarar dake tsakanin babban yatsanta da mai binsa a yayin da ta kusa hade su. Ta goge hancinta

“Ya dauki yaran duka ya auna jininsu kuma na san ya gani, amman be ce min komai ba ya koma Lagos, the next thing da zai biyo na sani saki ne da tozarci a cikin dangi”

Ta share hawayenta.

“Kanwarsa ta fada min ya fada musu ya Saki Noor amman be fada musu dalilin rabuwar ba, ta dawo gida ta haifi bakwaini, kuma be zo da rai ba, are you planning all this? It's because you love her more then me?”

“I didn't plan this, but yes i love her more then you, i love her so much”

“And think zan tsaya ina kallonku ku auri junanku ne, bayan kun gama lalata tawa rayuwar? Taya? Ka ci amanata Kareem”

Ya daka mata tsawa.

“Babu wanda ya lalata rayuwarki, ke kika lalata rayuwarki da kanki, kuma karki zargi kowa a nan”

“Anyway na zo na na gargade ka, kuma na fada maka, idan har Abdull ya sake ni to ni ce zan maye gurbin Yusura, na san kai ma ba zaka so mutuncinka ya zube ba, ba zaka so a san ka haihu da matar aure ba, kuma na zo na gargade ka ne, ka fadawa Noor ta fita daga rayuwarka, kuma ta yi taka tsantsan da nata rayuwar domin Wallahi ba zan bar wannan ba”

Tsakanin rufe bakinta da kai hannunsa a wuyanta ba za a oya fadar wanda ya riga wani ba, shaketa yayi sosai har sai da idanuwanta suka fito.

“You're hurting me Kareem you're hurting me”

Baya baya take yana binta.

“Karki, taba yarinyar da bata miki komai ba saboda ni, kin cutar da ni that's enough, you have no idea what she's going though, because of your stupid husband, and yanzu kuma ke ki ce zaki saka ta gaba, kuma duk a kaina, ya ishe ki haka”

Ta fara bugun hannunsa da karfinta jin da gaske kokarin kasheta yake, she's fighting for her life. Sai da wayarsa ta fara ringing sannan ya sake ta fuska a hade, ita kanta bata taba ganinsa cikin bacin rai irin na yau ba. Tari ta fara tana hakki kamin ta juya da sauri ta fice daga falon.
Wayarsa dake ringing ya nufa ya dauka number Yusura ce, for the first time take kiransa bayan rabuwarsu, be haddace number duka ba but ya rike karshen numberta tun a lokacin da take gidan.

“Hello”

“Sallamu Alaikum”

“Wa'alaikumussalam, Lafiya?”

“Tine ce bata da lafiya, tun shekaran jiya, an bata magani amman abun be yi ba, jikinta ya tsanani yanzu”

“Ganin nan zuwa”

Ya sauke wayar ya dauki wayoyin duka biyu ya nufi stairs keys dinsa ya dauko ya sauko ya fita daga falon. 30m ya isa family house dinsu be faka ko'ina ba sai a bangaren da Yusura take tare da kanensa da yaransa. A falo ya same su daga Yusura har Tine din da aka yi ma shimfida a falon. Tun da ya shigo Yusura take kallonsa har ya karaso falon da babu kowa sai yarsa da tsohuwar matarsa dake sanye da katon Hijab domin a yanzu shi din ba muharraminta ba ne.
Ya kai hannu ya taba jikin Tine sai ya ji shi da zafi sai dai ba sosai ba, domin bachi ma take.

“Me yake damunta?”

“Zazzabi ne kawai sai ciwon kai da take cewa ta yawan tari da ciwon ciki”

Ya saka hannayensa ya tallafota ya maidata jikinsa yana taba cikin nata, a nan ta bude ido ta kalleshi.

“Dady ka zo?”

“Eh baki da lafiya”

“Eh amman da sauki”

“Fada min abun da kike ji”

Ta nuna masa gun da ke mata ciwo ta fada masa.

“Okay zan siyo miki magani yanzu, idan baki ji sauki ba daga nan zuwa gobe sai mu auna ki mu gani kin ji?”

Ta daga mishi kai tana kwantar da kanta jikinsa.

“Dady i miss you i miss our home, yaushe zamu koma?”

Ya kama hannunta ya rike yana wasa da shi.

“Tine akwai abun da ya kamata ku sani, the thing is...”

“Yara ne ba za su fahimta ba”

Yusura ta tari numfashinsa sai ya daka mata tsawa.

“We have to make them understand...”

“Are you Okay?”

“I'm Not...”

Nan ma ya amsa mata a tsawace, Tine ta dago daga jikinsa ta kalleshi

“Dady why are you shouting?”

“Am... Uhm..”

Ya rasa me zai ce, sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume. Kamin ya kwantar da ita ya mike tsaye ya fice daga falon.




**** **** ****

Ta faka a harabar gidanta misalin karfe goma daidai na dare. Kanta ta jinginar a kujerar dake bayanta tana kuka.

“So cuta ne Allah ka cire min son bawan Allah nan, shi baya ganina ba ni ce a gabansa ba, ina kaunarsa amman baya gani”

Ta fada tana kuka sosai, ta bugi gambun motar.

“Ba zan kyale mutanen ba, taya za su lalata rayuwata su kuma su zauna a free? Ni na rayuwa a bakinciki shi kuma ya auri wacce yake so ya rayuwa cikin farinciki? Na san duk shi ya shirya wannan ai daman yana cire ciki, ta kashe aurenta ta fito yanzu ya aureta ko? Tun fa ya rabu da matarsa, bayan ni tawa rayuwar ta gama lalacewa, shiyasa ya fada mata sirrina, to ba ni kadai zai shafa ba har da kai Kareem, ganin yake idan yayi haka zai wanke kansa zai tsira ko? Okay zamu ga ni ai”

Ta bude motar ta fita sannan ta share hawayenta ta nufi cikin gidan cikin zafin zuciya tana taba wuyanta da dayan hannunta, dayan kuma yana rike da key din mota.Cikin motar ya shiga ya zauna ya lumshe idonta yana maida numfashi a hankali. Be dago ba sai da ya ji ana buga gilashin motar, juyawa yayi a hankali ya duba sai ya ga Areef tsaye rike da ipad. Ya sauke gilashin kasa yana murmushi

“Areef my love”

“Dady na hango ka ta window Hajiya”

Ya bude motar gaba daya ya dauko dansa ya zauna a saman jikinsa ya kwantar da shi jikinsa.

“Ka iya gulma ko Areef?”

Yayi dariya yana boye fuskarsa, Kareem ma murmushin yayi ya shafa bayan dansa. Yaransa na cikin farinciki da Allah ya ba shi domin yana son yara ko ba nasa ba balle kuma jininsa. Slowly ya sauke ajiyar zuciya tunawa da yayi da Noor ta raya abun da ta haifa, shi da yake namiji yake son yara balle kuma ita da haifa da kanta kuma ta yi nagudar abunta, ya lalabo wayarsa ya sake kiran line Noor da wayar yar'uwarta. Ta amsa kiran tana kuka sai har yana jinta.

“What now ta mutu ko?”

“I'm sorry for your lost, Allah ya baki wani mai albarka, and your sister...”

Yayi shiru for a while sannan ya furta.

“She's safe, but tana asibiti saboda ta dan bugu da mota, ba mu san yaushe ba amman haka aka zo mana da ita, amman tana raye”

“Ka rantse ka ce wallahi tana raye tana duniya”

“Me zai saka na yi miki karya?”

“Saboda na jidadi na kwantar da hankalina”

Murmushi mai kyau ya fadada fuskarsa.

“Kin sa ina son kwanciyar hankalinki kenan?”

“Eh na sani fada min gaskiya”

“Wallahi tana da rai tana asibiti”

“Me yasa ba zata yi magana ba? Me yasa kai kake rike da wayarta?”

“Saboda tana bachi, kuma na kira na fara tambayarki ko kin fadawa iyayenki gaskiyar abun da ya faru so that na san ya zan musu bayani”

“Na fadawa Mama ba ka ce na fada ba, amman Baba be sani ba, mama tace kar a fada masa tace ace bata ta yi kawai”

“Okay zan fada musu yanzu an gano ta”

“Zaka kira Mama yanzu?”

“Yeah”

“Zan aje wayar ka kirata sai na tabbatar da gaske kake tana raye”

Yayi murmushi. That's why i love you, ya fada a ransa a zahiri kuma sai ya amsa mata da

“Okay”

Ta katse kiran sai ya aje wayar ya murza key din motar ya fara tukawa tare da dansa ya tafi ya siyo maganin ya rubuta yadda zata sha sannan yayi mata tsarabar gasasshiyar kaza da snack domin ya san tana sonsu sosai, sannan ya dawo gidan Areef ya rika masa leda daya ya shiga ciki wannan karon ya same ta tana kallon tv ne ta lulluba da bargo.

“Tine ya jikin?”

“Na ji sauki”

Ya aje mata tsarabar ya bude maganin da kansa ya bata sannan yayi mata sallama tare da Areef ya fice, Uffan be cewa Yusura ba dake zaune a gafe daya tana kallonsu. Bangaren Hajiya ya shiga ya gaisa da ita da kannensa sannan ya fito ya nufi asibitin...



NOOR POV.


Hankali be kwanta ba har sai da kiran Mama ya shigo wayata ta fada min Kareem ya kira da wayar Hana ya fada mata tana asibiti, rumgume wayar na yi ina jin wani irin kima da mutuncin Kareem a ido na, na yarda wani lokacin Allah ya kan kawawa bawa abun da be yi zato ba, ina jin Allah ya hada ni da Kareem ne domin ya share min hawayen abububuwa da yawa.

Umma na kwalawa kira domin tun dazun take tambaya me ua faru na gagara fada mata saboda kuka, tana shigowa na fada mata cewar kukan da nake Hana ce ta bata daga sunan tafiya makaranta amman an ganta tana asibiti yanzu haka. Tun daga ranar kusan rabi damuwata sai na ji ya gushe, domin yar'uwata yana raye, rabuwa da miji abu ne mai sauki, kamar yadda samun wani dan ko yar yake da sauki a gurin Allah.

Duk yadda na so na tafi ganinta ban samu dama ba, sai waya na yi da ita, shi ma kuma sai washe gari bayan ta farka. Sai da na yi kwana uku sannan Baba ya yarda na tafi na ganta tare da kawata Zainab, da ake ta shirye shiryen aurenta a watan nan. Da dare muka fita saboda gujewa idanuwan mutane, Napep muka hau yana fara tafiya na kira Kareem na fada masa cewar zan zo na duba Hana.

“Bana asibitin yanzu, ba ki san gurin ba?”

Ban san gurin ba, amman Zainab ta sani domin ta je duba ta kamar yadda mutane unguwa da yawa suka je dubata, but i just neet to see him so nake na masa godiya i just miss him.

“Ni ban san gurin ba”

“Okay a me kika zo?”

“Napep”

“Ina family house yanzu nan na shigo, amman zan saka Aaryam ya zo ya tare ki? Ya nuna miki gurin. Kuma ina tunanin akwai wata kanwar mamanku a can ko ki kirata”

Na kashe wayar ba tare da nace masa komai ba. Sai dai ga mamaki ina mai napep na sauke mu a bakin asibitin sai hangon shi na yi ya taho da kafa zuwa inda muke tsaye.

“Ashe ku biyu kuke?”

Ina kallonsa murmushi ya zo min for no reason na sauke kaina kasa kamar mai jin kunya, murmushi ya mayar min ya kalli Zainab.

“Kawarmu ce wannan?”

“Eh sunanta Zainab”

Zainab ta gaishe shi ya amsa, sannan ya juya yana kallon wani mai kama da shi da ya doso inda muke yana fadin.

“Ga key dinka ka shiga da motar ka ciki, sai mu taka na nuna mata gurin”

Kareem ya ce.

“Malam kai zaka ja motar ka shiga da ita ciki”

“Aa Wallahi, ai ba motata ba ce kuma ba asibitina ba ce”

“Amman kai ka nace sai ka biyo ni”

“Da na ji ita ce ba, saboda na ganta mana, malama bismillah ga hanyar nan”

Ya nuna min titi da zamu mike da hannunsa, ni kuma na kalli Kareem irin kallon nan na jiran umarni.

“Karki damu, ni kanensa ne uwa daya uba daya, muje ke kuma kawarta ku je ya sauke ki inda zai faka motar”

Kareem ya karbi keys din hannunsa ya juya ya nufi gurin da motar take fake tare da Zainab. Ni da kanensa kuma muka fara takawa a kafa zuwa cikin asibiti dauriya kawai nake domin ina jin zafin dinkin da aka min har yanzu.

“Sunana Aaryam”

“Nice”

Na fada feeling so nervous.

“Ke fa ya sunanki?”

“Noor”

“Haka ne na tuna, na san baki san ni ba ko?”

“Eh”

“Haka ne, ni ma ina dan jin sunanki gurin big bro ne can sama haka”

Now kuma I'm feeling awkward like Kareem yana hirata ne da mutane? Domin Hafiz ma haka ya taba fada min farkon haduwarmu.

“Ni nake bin Kareem, shi ne babba a dakinmu, muna da kanen mata akwai daya da Momy ta bari sai kuma yaran Hajiya su uku, sai kuma Yusura”

Na kalleshi kamar na yi maganan sai kuma na fasa. Ashe ya lura

“Na san zaki ce Yusura ba matar Kareem ba ce?”

Na daga mishi kai.

“Haka ne, amman a gidanmu take zama a nan ta girma”

Ya ba ni labarin zamanta a gidan yadda aka yi aurenta da Kareem da kuma rashin son junansu da suke.

“Amman a haka Kareem yayi kokari ya bata duka hakokinta, har sai da ta nemi saki so yanzu sakin da yayi mata babu gyara a tsakaninsu”

Mamaki ya kama ni, Kareem be fada min ya saki matarsa, wata kila shiyasa yake cewa ba zata zo ta tararda da mu ba, jin cewar bata sonsa kuma ba sabu abu ba ne na fahimta tun a zuwana na farko gidan, kamin shi kansa Kareem din ya fada min yadda aka yi auren a wacan ranar da ya fada min sirrinsa.

“To yanzu yaran fa?”

“Suna hannunta, idan Kareem yana son ganinsu zai zo ya gansu ne sai ya koma, shi kadai yake rayuwa a gidan yanzu, yana cikin kadaici da ban tausayi sosai, gashi ya rasa yarinyar da ya so ya aura, abun ba dadi, ni ba zan iya biyayyar da Kareem yayi ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, auren kiyayya ba shi da dadi shiyasa Yayana yake matukar ba ni tausayi, yana da zuciya da hallaya masu kyau, amman har yanzu be samu farinciki ba”

Tausayinsa ya kama ni sosai domin na san yadda rayuwa da wanda baka so take, na gwada na san yadda ake ji.

“Kin san me yasa nake baki labarin nan?”

Na amsa masa da alamar ban sani ba.

“I want you to be his best friend, domin yanzu ba shi da abokin shawara ya rasa Hafiz, ya rasa mahaifiya ni kuma tawa safgar nake dabam, na lura da wani abu yayana yana samun farinciki idan kuna tare ko yana zancenki, please idan kin ganshi a cikin damuwa ki yi kokarin cire shi, kuma ki yi iya yadda zaki iya ki ga ya auri wacce yake so take ba shi farinciki yana cikin damuwa sosai...”

Aaryam yana maganar ina kallon Kareem dake tsaye hannayensa zube a aljihu yana jiran karasowarmu.

“Kin min alkawari zaki saka shi ya auri wacce yake so? Shi ma ya samu farinciki kamar kowa? Farincikinsa shi ne na mu, and don't tell anyone mun yi maganar nan”

Ban iya amsa masa da eh ko aa ba har muka isa gurin da Kareem yake shi kadai yana kallonmu. Da dan zargi yake kallon kanensa sai Aaryam ya daga masa hannu ba tare da ya ce komai ba ya wuce cikin asibiti. Sai da na daina hango shi sannan na juyo na kalli Kareem.

“Me ya fada miki?”

“Yadda akan samu Hana”

Na amsa kai tsaye.

“Come on karki wasa da ni mana, na san ki fa”

Na yi murmushi.

“Ba ka ce ba zaka zo ba?”

“Na ji kamar hakan da na fada be miki dadi ba, shiyasa kika yanke wayar maybe you want to see me huh?”

Ya daga min gira sai na yi murmushi

“I miss you, i just wanna say thank you, ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da sanin ya kamata da kawaici da son farinciki ba sai Kareem, ba alakar uwa ba ta uba amman komai nake so kana yi min, people like you a rare, kai mutumen kirki ne, kai mutum ne mai damuwa da damuwar wani, Allah ya faranta maka ya baka abun da kake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login