Showing 30001 words to 33000 words out of 133189 words

Chapter 11 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

253

Hafizun na ji rashin mutuncin da take masa, domin komai aka ce Noor ta yi bana musu yarinya ce da bata da jin magana sam”

“Amman ka bincike me yasa ta zo gida?”

“Bana bukatar ji, ai ita mace baiwa ce namiji ko dukanta yake be kamata ta yi yaji ba ko ta zo gida kawo shedu idan na bata wannan kofar kamin ka ankara kashe auren zata yi”

“Zaman lafiya be tsawaita aure, tashin hankali be gajarta aure, ko ya kashe rai ne da shi ko ana zaune lafiya mutuwa yake, idan lokaci yayi, wani kuma ga tashin hankali amman auren ya ki mutuwa saboda lokacin rabuwar be yi ba, da dadi da ba dadi as long as auren yana raye za a zauna”

“Haka ne, amman Noor ba a nuna mata wannan, yarinya da bata da tunani babu natsuwa a tare da ita”

“Amman ko minene ya kamata ka saurari damuwarta, ka aura mata wanda bata so at her young age kuma ta yarda ta aureshi, yanxu kuma ta zo da matsala ya kamata ka aurareta, mace bata da gidan da ya wuce na uba a duniya idan aka cire gidan mijin, wani bangaren ma gidan uban ya kan fi na mijin, domin yanzu da ya korota gidan ubanta ta doso, da namiji ne shi zai yi korar ko kuma ya nemi wani gurin ya fake, irin haka yana saka rayuwar mace ta lalace”

“Wato duk abun da za a fada maka ba zaka gane ba, ita Noor dabam take ta sauran yaya, kuma ka duba yadda abokin ka yayi hidima da mu, ace wai Noor ta kwaso jiki ta zo gida ai be kamata ma na saurareta ba”

“Ina ganin ku kuka haifi Noor a hannunku ta girma ta yi wayo, amman ko ku din ba ku fi ni fahimtarta ba, ban sani ba ko dan ina kallonta a wani yanayi ne da ku ba a baka kuke kallonta ba”

“Ni fa na haifi noor na san halinta gaba da baya”

Kareem ya aje numfashi da karfi.

“Ko ma dai minene yanzu, Baba ina son ka karbi wannan kaddarar, dan Allah ka yi hakuri ya karbi Noor, ni kuma zan shiga na fita na ga na yi abun da ya dace”

“To wai sakinta yayi ne ko kuma me?”

“Sakinta yayi, ni kaina ban san abun da ya hada su ba, amman dai yanzu haka Noor din tana asibiti saboda buga mata abu da aka yi a kai ta ji ciwo sosai”

“Yayi daidai ai kara da yayi mata duka, daman Noor bata san arziki ba, wato ni zata watsawa kasa a ido ko? Aure ko wata daya be yi ba ta an sakota ta dawo? Oh Allah na gode maka da ka yi min wannan kyautar, yarinyar nan ban da bakinciki babu abun da take saka min tun da aka haife ta, yanzu ina murna na aurar da ita na huta ita ma ta huta, sai kuma yanzu na ji wani labarin na dabam? So take fita sallah cikin jaama'a ma ya gagareni?”

Kareem yayi shiru ba tare da fada masa dalilin dukan ba, ko fayyace masa cewar ba Hafiz ne yayi ba matarsa ce ta yi mata duka a rashin fahimta. Sai kawai ya dora da

“Hakuri zaka yi Baba, komai zai wuce”

Baba yayi baya baya ya jingina da ginin gidansa, gaba daya furucin saki da Kareem ya furta ya fi jefa Baba cikin damuwa, duk wani buri da hangen dafgen da Baba yake a auren Hafiz da Noor ta yi ya sha ruwa.

“To wai saki har nawa yayi mata ne?”

“Daya ne ina zaton ba zai wuce haka ba, ni dai abun da nake so daga gurinku shi ne hakuri ku karbeta, zan binka komai kuma da yardar Allah zata koma dakinta amman dole sai ka yi hakuri Baba”

Kareem ya fada ne kawai saboda ya samawa Noor matsuguni a gidansu ba wai dan yana da niyar yin wani abun akan auren ba. Be ji zai iya sake tuntubar Hafiz ma da maganar ba balle har yayi ruwa da tsaki Noor ta koma gurinsa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, wannan yarinya ba zata tana canja hali ba, to sai ta zo ta zauna ai ta ji idan zaman gidan dadi ne da shi, sakarya kawai marar hankali”

Kareem be ce komai ba ya bude motarsa ya dauko 50k ya mikawa Baba.

“Baba ga wannan ayi chefa ne, ina mai kara baka hakuri akan abubuwan da suka faru, kowa baya wuce kaddararsa. Ka yi hakuri dan Allah yanzu haka Noor tana asibiti, ita kanta tana cikin tashin hankali na abun da ya faru”

Baba ya saka hannu biyu ya karbe kudin ya jefa alJihu sai dai har lokacin damuwar bata bar fuskarsa ba.

“Toh dole ai zai hakuri, yaran zamani ne duk yadda zaka fada musu abu ta bayan kunnensu yake bi”

“Allah ya kyauta, zan tafi zan samu abokin nawa sai mu tattauna”

“Toh an gode, ka ba shi hakuri dan Allah, na san halin Noor zata iya komai, ka ba shi hakuri ita kuma In Shaa Allahu za mu gargadeta”

“Tohm”

Kareem ya shiga motarsa yayi mata key ya juya ya fice daga unguwar.




NOOR POV.

Duk yadda na yi kokarin tafiya sai matar ta sha gabana da kalamai ta hana ni fita. Ina zaune har kusan sha daya na rana ina ta tunanin mafita, na sake kiran Kareem na masa magana ne ko kuma dai idan na samu damar fita na tafi kai tsaye gurin Hafiz na ba shi hakuri. Karar turo kofar dakin ne ya saka na daga kai na kalli kofar arba da na yi da fuskar Aisha ya saka ni jin kamar an kara min ciwon dake jiki even though ba ni da tabbacin tana tare da Hafiz ne ko akasin haka. Cooler abinci ce a hannunta Ina zaune ta karaso ta aje kayan abinci cikin tausayin da yanzu na tabbatar na makirci ne Aisha ta zauna a kujera tana kallona kamar zata fasa kuka.

“Noor ya jikin na ki?”

Na dauke kai na kawarta da fuska ba tare da na amsa ba.

“Noor rai ne ya bace haka? Ki yi hakuri da abin da ya faru, ni kaina ban jidadi ba, Wallahi be fada min ba sai yanzu da zai fita, shiyasa na yo rushing na zo dubaki ya jikin”

“Bana bukatar dubiyarki, dan Allah ki tashi ki tafi”

“Ikon Allah ni miye nawa a ciki Noor? Dalilin zuwana fa so nake a gyara abun nan kamin ma familynsa su sani”

Na juyo na kalleta.

“Duk halin da na shiga a yau ke ce sila, gaba daya kin rikita min tunani kin dasa min abubuwan da babu a zuciyata, daga baya kuma kike daure ni da su kina cutar da ni, bana son ganinki Aisha”

“Hmmm Allah sarki, an hure miki kunne ko? Ke yarinya ce baki san miye duniya ba, amman ni kauna nake nuna miki saboda na rike ki ne tsakani da Allah”

“Karya kike yi, kina munafurci ne kawai kina ke din ta kwarai ce alhalin ba haka ba ne, to yanzu ya sake ni hakan be wadatar dake ba sai kin biyo ni har nan?”

“Alheri ne ya kawo ni ba sheri ba, ban jidadin yadda kike jefata da zargina da abun da ba hali na ba, wata rana zaki gane gaskiya”

Ta mike tsayeta fice daga dakin. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko min, na sani ko da zan fadi kasa na yi birgima na roki ta ce Hafiz ya maida aurensa da ni ba zata yi hakan ba, domin ita ce silar lalacewarsa, aikata hakan kuma raina kai ne a gurinta da janyowa kai gori. Ban saka tsamanin zuwa kowa ba domin ba zan iya tunkarar mahaifina da takardar Saki ba, kamar yadda na san Mama ba zata saurare ni ba, babu wanda zai duba ni, babu wanda zai yarda da ni ko da kuwa ina da gaskiya.
Sai dai abun da ya fi komai yi min ciwo shi ne, me yasa Hafiz zai aureni alhalin ya san yana son matarsa kuma ya san ba zai iya adalci a tsakanina da shi ba, ba zai iya tausaya min ba. Misalin karfe daya ina zaune a dakin shiru Gwaggo Saude tare da kanwarta suna shigowa bata duba halin da nake ciki ba ta rufe ni da fada kamar wadda bata da gata, sai kanwarta ce take dan tare min tana cewa ba a bincika ba wata kila ni ce mai gaskiya. Ban san waya fada musu ba ban san ta ina suka ji ba maganar sakin ba domin ban yi maganar da kowa ba bayan Kareem. Haka na yi kwana biyu a asibitin a duk tsawon zaman da na yi Hafiz be leko ba, daman me zai saka ya leko ni bayan ya datse igiyar data hada, mahaifiyata kam ina jin bata da labarin komai sai dai abun da ya daure min kai shi ne rashin zuwa Ya Nabil da Hana duba ni, haka ma Baba be zo ba, Kareem din ma da matarsa ta yi min illa be leko ba ko sau daya be taba shigowa ya duba ni ba. A zaton su raunin da na samu Hafiz ne yayi min duka ni kuma ban damu na fada ba domin ni na kai kaina fadar zai kara janyo min karin wani tsanar ne ko fadan. Idan suka tambaye me ya faru tsakaninmu sai na ce babu komai ban masa komai ba, na samu kaina da nauyin fadar dalilin asalin fada na samun robar c**mdom da maganin planning a jakata, a lura da na yi ne da hakan babban abu ne da zai iya sakawa wasu ma su zarge ni kamar yadda Hafiz ma ya kasa yarda da ni shi da yake mijina. Ranar da aka sallamoni daga asibitin tare da Gwaggo na dawo gida, gaba daya tsoron irin tarbon da Baba zai yi min ya gama firgita ni ya saka na fita hayyacina a take, tsoronsa da nake ji a yanzu ya ninka wanda nake ji a lokacin da ban yi aurenba.

Ban gane dawowa gidan na zauna kuskure ba ne har sai da gari ya waye, na leka daki na gaishe da Baba ya ki ya amsa min, daman tun da muka shigo be sake min fuska ba. Haka Ya Nabil ma be ce min komai ba, hana ma ta kasa sake min kamar ba ita ba. Within a week na lalace kamar ba ni ba, labarin sakin da aka yi ma ya cika unguwa wasu na tambayar yaushe ma aka yi auren har na dawo gidan, daman sun san ba zan yi zaman aure ba, haka Zainab take fada min yadda ake yawo da ni a unguwa. Ga shi cikin zaman babu dadi domin sun hade min kai, Yaya baya min magana, Hana bata hira da ni iyakacinta idan ta girka abinci ta zuba min ta koma gefe ta zauna, Baba kuma idan ya shigo ba yi masa sannu baya amsa min, idan zai fita ko da safe idan na gaishe shi baya amsa kuma be taba tambayata me ya faru ba!! Haka Mama bata kira ta tambaye ni me ya faru ba, na san kuma ba zata rasa sani ba, domin Ya Nabil yana yawan waya da ita, Hana kuma ta tafi gurinta sau biyu a zuwan da ta yi na karshe take fadawa Yaya jumma'ar ne aka daura mata aure.
A tunanina suna min horo ne da wannan saboda a gaba idan na koma kar na sake marmarin dawowa gidan, Sai dai abun da suka kasa fahimta shi ne mace bata sakin kanta, ni kaina na zan iya cewa ga abun da na yi masa ba da har ya saka ya sake ni, saboda suna ganin bana jin magana tun asali ne shiyasa babu wanda zai yarda da ni. Hakan kuma ya saka na ji kamar a gidan yari nake rayuwa saboda kunci da takura, a kowace Sallah sai na roki Allah ya daidaita ni da mijina, sannan na daukarwa kaina alkawari ko da Hafiz sai yanka ni ya ci ko kuma yayi min horo da wuta ba zan taba daga ido na kalleshi ba balle har na yi wani kuskuren da sai saka ya sake sakina. Tsegumin mutane kadai ya ashe ni, wasu har fadar suke wai amanar Zafeer, ba mamaki kuma ta kan iya zaman amanarsa ce ta hana ni zama cikin amincin a gidan Hafiz, domin na cutar da Zafeer na raba kaina da shi da na yi, sanadin Baba wata ila da gaske amanarsa ce Allah kadai ya san halin da ya shiga a sanadin haka.










#KhadeejaCandyPAID PAGE 1️⃣2️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______


Ina ta tsammanin zuwan Hafiz ko Kareem da sunan gyara amman ban ga ko dayansu, hakan kuma ba karamin Mamaki ya ba ni ba, sai na ke ganin kamar daman can Hafiz ba sona yake ba, ya aure ni ne kawai saboda yana son raba ni da wanda ke tsananin kaunata. Sai dai Kareem ya fi ba ni mamaki domin sanadinsa na san Hafiz ko kuma nace Hafiz ya san ni, kuma na kai masa kukana ba sau daya ba amman har yanzu be yi komai ba.

Idan na zauna ina tunani sai na ji zuciyata kamar zata fashe, gaba daya na rasa tudun dafawa na rasa ina zan saka kaina na ji sanyi, Mijin da ya dauke ni ya saki ni be waiwayo ba, abokinsa da shi ne sanadin auren be yi wani yunkuri ba, a gidanmu kuma Baba baya min magana saboda yana ganin laifina, Kanwata bata hira da ni, yayana baya kulani na rasa, hakan ya saka na dauki laifin na dorawa kaina. Kullum burina taya zan bullowa lamarin na samu komawa dakin mijina. Da yammancin wata labara na saka hijabina na saka talkamina na fito tsakar gidan. A lokacin Hana ce kadai zaune tana karatun biology, sau daya ta kalleni ta maida kanta bata ce min uffan ba duk kuwa da ta san fita nake da niyar ni.

“Hana”

Ta juyo ta kalleni ba tare da ta amsa ba.

“Abun da kuke min ya dace kenan? Kun maida ni bare a gidan nan?”

“Toh ya kike son ayi miki Noor, idan fa ba ki canja hali ba, zaman rayuwar duniya zai miki wuya”

“Amman babu wanda ya tambaye waye mai gaskiya me ya faru?”

“Baba be son jin uzurinki, saboda ya ci buri a aurenki, na san Baba be kyauta miki ba aura miki wanda baki so, amman be kamata ki ce ba zaki zauna ba, da zarra an daura aure kin tashi daga budurwa Noor, Mama farko bata farinciki da auren amman bayan aurenki nan tana ta jindadin yadda mutane suke yaba gidanki, kuma idan ta duba yadda zaman gidan yake babu dadi sai ta ce kara ma da aka miki auren yanzu ta huta sauran ni, to miye kuma na zuwa ki fito Noor auren da ba a dade da yi ba?”

Na share hawayen da suka zubo min.

“Ganin kike laifina ne?”

“Tohm laifin waye? Mutumen dai yana sonki, ke ce baki son shi, kuma Noor kowa ya san halinki na rashin jin magana sanadin haka kika je kika hadu da wannan mutumen sai kuma yanzu ki dawo kina kame kamen ba zaki zauna ba”

“Hannatu ke ma fa mace ce, baki san ya rayuwa zata kasance miki ba, na tabbatar da kin san yadda zafi da bakincikin auren wanda baka so yake da baki fadi haka ba”

“Na sani ni mace ce, amman tun yanzu ai ba irin rayuwarki nake ba, kuma bana fatan na yi kalar rayuwarki Noor, ke ce kin son makaranta ke ce jawo ki ce rashin jin magana ke ce saka Mama kuka bakinciki komai dai ke yanzu kuma ana murna an miki aure sai kuma ki kashe auren ki dawo? Yanzu ai sai ki ji idan zaman gidan dadi ne da shi”

Bana jin akwai sauran abun da zan fada da zai gamsar da yar'uwata a yanzu, ko kuma ya wanke ni daga mummunan kallon da suke min, gaskiya ta fada da ace ni din kamar ita nake mai jin magana wata kila da yanzu ban samu matsala kamar haka ba. Fita na yi daga gidan ina tafiya jikin ba dadi as well as zuciyata bana iya daga kai na kalli ko'ina har na isa titi, Napep din da ta faka kusa da ni na nufa. Ban tana sanin ina tsananin kaunar Zafeer sai a yau da na yi arba da shi ya fito daga Napep din da nufa zan shiga, ya rame kamar dai he is the only person da na kalla daga fitowa ta gida zuwa nan, shi ma kallona yake kamin ya dauke idonsa ya saka hannunsa aljihu ya dubu daya ya mikawa mai napep din.

“Canjin ka kai wannan inda zata je”

Wannan karon muna hada ido hawaye suka zubo min. Ya dauke kai ya matsa baya ni kuma na shiga na zauna ina kallonsa har mai napep din ya fara tafiya...

“Ina zamu je Hajiya?”

A take hankalina ya dawo jikina, kunya da damuwa da bakinciki nadama da kuma dana sani suka rufe ni. Yaushe Zafeer ya dawo garin? Ko dai be tafi ba? Har yanzu yana so na? Ko ya daina? Ya yake kallona? Wata kila ya ji labarin mutuwar aurena amanarshi ta kamani. Ina Son ka Zafeer ina sonka sosai ina son Zafeer Allah ka sani, shi ne abun da nake ta fada a zuciyata, ban hakaro da inda nake ba har sai da Mai napep din ya sake tambayar ina zai kaini. Toh ina zan je kuwa bayan restaurant din Kareem by this time na san Hafiz yana gurinsa, zan fi jindadin tunkararsa a can na bashi hakuri kuma na fada masa ba zan sake aikata kuskure ba, duk kuwa da na san ni din ba ma'asumiya ba ce. Rokonsa a can zai fi min rufin asiri fiye da rokonsa a gidansa kuma a gaban muguwar matarsa wadda ita ce silar faruwar komai.

A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login