Showing 69001 words to 72000 words out of 133189 words
Chapter 24 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete
karara a fuskata, tunanin yadda rayuwa zata zame min nake, hankali ko tunanin da suke ganin kamar ba ni da shi ina da shi, ni na san ina da shi, idan ma babu a da to yanzu yana tare da ni. Rayuwar gidance nake jin kamar ba zata min dadin zama ba, gashi kuma ba ni da wani gurin rabawa da zan zauna na ji sanyi.
Yunkurawa na yi na tashi na nufi gurin da kayan wanke wankemu suke na wanke komai tass Hana kuma ta dora girki ta girka mana shimkafa da miya, duk da kasancewa white rice and stew are my favorite amman ban iya cin wani abun kirki ba, daman abinci ya daina burge ni. Kamar wani zanenen al'amari a daren da muka yi haka da Baba sai ga kanen margayi ya zo gidanmu, ban san ya aka yi ya gane gidan ba, kusan ni dai zan iya cewa ban taba ganinsa ba, idan ma na ganshi ba zan iya shaidar fuskarsa ba, domin ban jima a gidan ba balle na san duka yan'uwansa balle kuma mazan da be gabatar min da su ba. A zauren gidanmu ya shigo bayan yayi sallama Hana ta yi masa izinin shigowa. Dogon hijab ne a jikina har kasa kaina kuma a kasa na kasa kallonsa ganin nake kowa kallona yake a wani muhalli da Aisha ta saka ni a idonsu.
Bayan mun gaisa ya gyara tsayuwarsa ya ce.
“Ya Hakuri Noor?”
“Alhamdullahi”
“Haka Allah ya so sai hakuri, shi kuma Allah yayi masa rahama”
“Ameen”
Na amsa ina jin idanuwa suna cika da kwalla.
“Na san babu dadi, musamman ma ke da kike farkon shiga gidansa ba ki jima ba mutuwa ta yi muku gaggawa, amman duk da haka ki yi hakuri yana cikin jarabawa ne”
“Haka ne, na gode”
“Na san ba ki san ni sosai ba, ni kane ne a gurin Margayi uwa daya uba daya, ni ne kanensa na biyu, makasodin zuwa na a nan shi ne... Abubuwa marasa dadi sun shiga kuma za su biyo baya na sani, amman dan Allah ina son ku kawar da kanku musamman ma ke, ki yi hakuri da abubuwan da zaki ji ko ki gani”
Na yi shiru ina ta sauraren bayaninsa da ban fahimci inda ya dosa ba.
“Na ji wasu abubuwan ne da ba su min dadi a gidanmu, na iya yadda zan iya na taushe abun amman ya gagara saboda haihuwarmu aka yi ba mu muka haife su ba, dole sai hakuri, amman na san ke zan iya neman alfarma a gurinki kuma na roke ki duk kuwa da ba ki san ni ba, amman ina rokon alfarmar dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen margayi akan gadonki, ke ba da kike da shi ba balle ace saboda da gaba, kina gama wanka na san In Shaa Allahu zaki yi aurenki, bana son na ji wata matsala ta taso daga gurinki, ni dai ina kyautata miki zato sosai”
“Ni ba zan iya jayaya akan abun da rai ya tara kuma ya tafi ya bari ba, wanda ya tara abun ma ina yake? Toh me zai saka ni yin jayayya? Idan ma ina da hakki abun da za su ba ni ba zai taka kara ya karya ba, ba shi ne gabana ba, kuma na maka alkawari ba zaka taba jin wani abu makamancin wannan daga bangarena ba”
Ya sauke ajiyar zuciya yana kallona.
“Na yi farinciki da jin haka, na jidadi sosai Allah ya saka miki da alheri, ya baki wanda zai maye miki gurbin Ya Hafiz har ma ya fi shi”
Na yi shiru ban iya amsawa da Ameen ba. Daga haka yayi min sallama ya tafi, ni kuma na dawo cikin gidan ina ta mamaki mi ya ji danginsa ana fada har dauko kafafuwansa ya zo ya tari nawa fadan, ni kan idan gado ne ko nawa ne ba zai daga min hankali ba balle ya saka ni yin magana ko daukar wata dokar tsorona duk na Baba ne.
Ban fadawa Baba wani ya zo ba, sai dai na lura hakan be yanke komai daga hanzarinsa na niyar saka iyayen Hafiz a kotu ba, idan har ba su ba da hakkina na wanka ba, na fahinci hakan ne ta dalilin wayar da na ji yana yi da yayansa wai ya bincika ko'ina ance ina da gado, dan haka ba zai saka musu ido su cinye min hakkin ba. Ban ce komai ba daman kuma ban isa na ce ya rufe da fada ba mamaki ma ya kara min duka. Zaman gidan sam baya min dadi kamar ina zaune a kaya haka nake ji. Ba ka kamar lokacin da sabuwar matar da Baba ya aura ta tare a gidan.
Gaba daya sai gidan ya kara fice min a rai, domin na lura ta shigo da wani salo na hana mu walwala ni da Hana da kuma Yaya, gara ma yaya ba a gidan yake wuni ba, sai dare yake dawowa ni da Hana ne muke ganin rayuwa a gidan. Babu kuma wanda ya isa yayi magana domin mun san halin Baba ba zai taba yarda da mu ba.
Umma bata wuce wata biyu ba a gidan ta cigaba da sana'o'inta da take, daman na ji Hana na fadar wai ance tana siyar da kunun waken soya kuma tana wara tana kosai, domin ba yar garin Kano ba ce asalinta yar riɓa ce dake can kusa da zuru ta birnin kebbi amman take zaune a nan Kano gurin Yayarta bayan rasuwar mijinta na farko, tana sana'a har Allah ya kawo mata Baba ya aureta a yanzu.
Bata taba haihuwa ba a wacan auren nata kamar yadda take labarta masa wani lokaci ni da hana, ba wata babbar mace ce be domin Mama ta yi kanwa da ita ta biyu, sai dai tana da irin jikin nan sosai da zata iya daukar Mama da irinta uku ta goya ta gudu, domin ni da Mama jikinmu daya, ita ba kiba ni ma babu kibar, ba mamaki ma kibar ce ta burge Baba ya aurota.
Wani sabon salo da ta kirkira shi ne na dorawa Hana tallar awarar a titi tana siyar mata kullum zata bata 500 naira, ita kuma tana yin kunun waken soyar a gida, ana shigowa ana siya sai dai ba sosai kamar yadda take fada mana ba.
Dole ce ta saka Hana yarda tana soya mana awara a waje ba dan tana so ba, domin ko a lokacin da Mama take gidan kuma muke cikin tsananin shan wahala bata taba gwada dora mana talla ba, amman ita wannan da ba uwarmu ba ta fara dora ma Hana talla daga zuwanta.
Ko da yake ba laifinta babne laifin Baba domin shi ya bata dama Hana kuma bata isa tace ba zata yi ba, duk kuwa da kasancewar bata so ko kadan. Domin fita tallar ya kashe mata tafiya makarantar yamma, ya zama boko kawai take iya tafiya da safe.
Ni kuma aka bar ni da wahalar aikin gidan, shara wanke wanke da hura wuta tun ban iya ba har na iya, girkin ne kawai bata bari na yi domin na gwada girkanwa ta ji be yi mata yadda take ba. Idan zata hada kunun wanken soyan ni nake wanke goruna ni nake mata komai har tacewa, awara kuma ni zan gyara wake da dare da safe taje ta kanta ta kai nika, idan ta dafa a tare zamu natse ni zan yanka idan aka soya be wuce a ba ni da hansin ba ko saba'in.
Wani sabon shafin wahalar rayuwa Umma ta bude mana a idan, ni da Hana saboda sana'ar da take wai ai ba ita zata fita ta yi ba a dole hana zata soya mana wara a waje ni kuma na yi aikin cikin gida. Ta inda nake samun sauki shi ne takaba da nake bana fita, saboda haka duk wani aiki na fita ita zata fita ta yi, da safe kuma Yaya sai ya cika gidan da ruwa sannan yake fita.
Ta inda gurin da ta samu banbancin da Mama a zamanta gidan ita kam Baba yana bata abinci da cefane mai kyau, ba kamar Mama ba da wani lokacin zai ce be da shi ko kuma ya bada abinci ya hana cefane ko ma ya hana gaba daya. Wata kila saboda ita din tana da dan da sauran kurciya ba kamar Mama ba, wata kila kuma dokin amarci ne yake Allah masani.
Idan kuma aka yi girki ba a ba mu wani abun arziki Allah ma ya sa yanzu damuwa bata barina na ci na koshi kamar da, wani lokacin har ragewa nake na bawa Hana a da kam na fi kowa cin abinci a gidan, ranar da Hana ta tafi family house din Mama ta fada musu halin da ake ciki na dora mata talla, washe gari Kawu Garba ya samu Baba yana nuna masa hakan be dace ba, sai Baba yace kar wanda ya sake saka masa baki akan lamarin yaransa shi ya ga damar su yi, kuma babu mai ciyar masa da yara sai su.
A nan yake fadar ai tun kamin auren ya fada mata yaransa za su rika mata wani abun saboda ta fada masa ita fa tana sana'a kuma aure ba zai hana ta yi ba, shi kuma ba zai iya ganin matarsa da aure ta fita waje ta yi sana'ar wara ba, domin haka yarsa zata maye masa gurbi. Ni kam gaba daya na zama kamar ba ni ba duk abun da ake bana iya cewa komai sai ido, wani kalar canji ne ya same ni irin wanda ban yi zato ba.
KAREEM POV.
Da kansa ya shiryawa yaransa abun karyawa ya dauko lunch box dinsu ya raka su har gurin School bus suka shiga sannan ya juyo ya dawo, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito ya shiga motarsa. Family house dinsu ya wuce domin fara gaisawa da iyayensa kamin ya wuce aiki kasancewar yau Monday.
Wani abun da ya sabawa kansa da shi ne, na kin kallon mahaifiyarsa a duk lokacin da ya shiga gidan. Kai tsaye ya wuce bangaren Hajiya Hassana wadda take step mom dinsa. Karyawa ya same ta tana yi tare da Khadija da Aaryam da sauran yaransa Aneesa da Kamla. Kanensa duk suka gaishe shi ya amsa, Yusura dake zaune gefe daya ta mike tsaye ta shige dakin Hajiya Hassana sai a lokacin ma Kareem ya lura da ita. Khadija ta kwashi kayan abincin ta bi bayan Yusura Kamla da Anessa ma haka, sai ya rage daga Step Mom dinsa sai kanensa Aaryam.
“Zaka ci abincin a zuba maka?”
Hajiya ta tambaya.
“Aa”
“Baka cin abinci yanzu, tun da Momynka bata nan, shigowa nan ma sai monday Monday kake yi ka duba mu, idan Momynka bata nan ni da mahaifinka ai muna nan kuma Kanenka suna nan be kamata kana haka ba”
A hankali ya sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya Bana jindadin shigowa ne yana yawan tuna min da Momy kuma ina jin babu dadi”
“Tohm ya za'ayi haka tsarin Allah yake, kai kanka mutuwa zaka yi balle kuma wasu, sai hakuri rayuwa ta gaji haka, ni kaina yanzu gidan ba dadi yake min ba Wallahi, amman a haka nake daurewa saboda Khadija da Aaryam da kuma Aneesah, dole na yi walwala idan ba haka ba dukanmu sai mu taru mu takura mu yi ta bakinciki da kuka”
Yayi shiru be ce komai ba. Hajiya ta dauki tissue ta goge hannunta.
“Likita..”
Ta kira shi sai ya kalleta daman haka take kiransa tun Momy na gidan.
“Ni fa ba zan boye maka ba, ban gane manufar abun da ka yi ba, kuma ban gane inda kuka dosa ba”
“Na miye ba Hajiya?”
“Kai da Yusura mana, ta dawo gida kawai tace mana ka sake ta, saki daya biyu ko uku ba mu sani ba, Daddy ka ma fushi yake da kai shiyasa be maka maganar ba har yau, Khadija da Aaryam ma gashi a zaune kullum haushinka suke ji saboda haka”
Kareem ya juya ya kalli Aaryam kyakkyawan saurayi mai jini a jika, sai yayi murmushi.
“Saboda Yusura?”
“Eh mana, Daddynka cewa yayi ba zai maka magana ba, kuma kar wanda yayi maka a saka maka ido kawai, ita kuma ta so barin gidan ni na hana, saboda na san idan Momynku tana raye Yusura bata da gurin zama sai gidan nan, a nan ta girma nan ta saba yanzu kuma dan Momy bata nan babu wanda zan bari ya dauketa ko kuma ita ta tafi ta bar mu, sai idan na mutu, kai ma dan kana ganin Momy bata nan ya saka kake son ka wulakanta amanar da ta baka, to ka sani Yusura ta fika gata a gidan nan, kuma matukar ina raye ni ce gatanta ba kuma zata wulakanta ba”
Kareem yayi gutun murmushi ya girgiza kai, kana ya sake juyawa ya kalli Saurayin Kanensa ya ce.
“Fushi kuke ta yi da ni akan abun da Baku san komai a kai ba”
Aaryam ya ce.
“Haba Big Bro ko dai minene ai be kamata ace ta kai ga haka ba, kai fa Namiji ne, kuma ga yara tsakaninku, kawai dai ban maka magana ba ne saboda Daddy yace kowa ya saka maka ido, kuma ina kasa da kai be kamata na tsuma baki a irin wannan ba sai idan ka bukata”
“Gaskiya ne”
Kareem ya fada tare da aje numfashi sannan ya mike tsaye ya nufi bangaren mahaifinsu, sai a yanzu ya fahimci dalilin da ya saka har yau da suke wata biyu da sati biyu da rabuwa Daddy be taba kiransa ya tambaye shi miye ya faru ba, kuma be taba yi masa maganar ba a duk shigowar da yake gaishe shi a gidan.
A natse ya shiga bangaren kamar yadda ya saba sai bayan da ya zauna sannan ya gaishe da Daddy dake sanye da gilashi yana duba newspaper.
“Lafiya Kalau, Kareem ya gidan ya yaran?”
“Lafiya kalau Daddy”
“Maa Shaa Allah, yau Monday ko akwai aiki”
“Haka ne Daddy”
“Allah ya taimaka ya bada nasara”
“Ameen”
Kareem ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Daddy. Daddyn ma ya kalleshi
“Allah yasa lafiya, akwai wata matsala ne?”
Kareem ya hade wani abun da ya tsaya masa a makoshi sannan ya ce.
“Daddy, ban ji kace komai akan dawowa Yusura gidan nan ba”
Daddy ya aje newspaper dake hannunsa.
“Oh wai Yusura, Mijinta ne ya sake ta kasan kuma bata da wani gidan da ya wuce nan, bata da gata a duniyar nan sai mu, zamanta a nan ya takura maka ne? So kake a koreta?”
Kareem yayi murmushi jin yadda Daddy yake fadar mijinta ne ya saketa kamar be san Kareem din ne mijinta ba.
“Aa Daddy ai ban isa na ce a koreta ba”
“Good kara dai da kasan haka”
Ya sake yin murmushi, a yanzu ne ya kara tabbatar Daddy fushi yake da shi.
“Kawai dai na yi zaton ko zaka bincike abun da ya faru ne”
“Abun da ya faru, tsohuwar budurwarka tana zuwan nemanka, amaryar abokinka tana zuwan nemanka ta yi magana sai ka mareta ka ce ka saketa”
Dif Kareem ya dauke wuta kamin ya kalli Daddy ya ce.
“Haka ta fada maka?”
“Ba gaskiya ba ne Daddy, Safeena ta zo gaisuwar Momy ne, kuma na gargade kar ta sake zuwa domin babu wata alaka tsakanina da ita, Noor kuma tana zuwa ne saboda tsabanin da suke samu da Hafiz a lokacin”
“Zan yarda da wannan, domin ban san ka da wani aiki na assha ba, shi ma wannan saboda Hassana ta matsa ne ya saka ta fadi wannan dalilin, amman bayan haka bata fada mana komai ba, ni kuma na auna abun a ma'aunin kishi ne, sai dai kai kuma ka yi kuskure na aikata saki a take”
Kareem yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Daddy ya cigaba.
“Shiyasa na yi shiru na zuba maka ido na gani shin kana da hankali kansan ya kamata ko baka sani baKareem ya sauke numfashi mai nauyi.
“Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni”
Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa.
“Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce”
Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce.
“Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba”
“Okay yanzu da bata raye mu ne abokan wasarka? Kai da ita? Ni ba zan ma yarda ba ku son junanku ba. Kareem zan baka shawara karka yarda ka rasa Yusura, na yi aure tun kurciya har yanzu na zauna da mata biyu a lokacin da mahaifiyarka take raye, mu kan samu tsabani mu yi dadi, wani lokacin har iyaye su sani, amman ban taba ganin matar aure da bata taba kuka da mijinta ba sai Yusura, bata fadin sherinka, bata kawo kararka, kai a gurinka ba abun kunya ba ne aji ka saki matarka? Kuna da yara biyu me kake fada musu? Idan aure kake son karawa you're free to do so ba sai ka saki matarka ko ka wulakanta ta ba, idan har kana fadar saboda Mahaifiyarka ka aureta to miye amfanin sakin a lokacin da mahaifiyarka bata raye? Ke nan ganin idonta kake yi ma biyayya ba saboda Allah ba? Yanzu da ban yi magana ba haka zaka zuba ido ta cika idda? Ko saki uku ka yi mata? Domin bata fada mana ko saki nawa ka yi mata ba, kuma ita bata zauna kamar kai ta kalli kwayar idonmu ta fada mana bata son dan mu ba, Kareem idan ka sake ka rasa Yusura ka rasa matar kirki kenan