Showing 1 words to 3000 words out of 75226 words
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
' Wannan labarin kirkiro shi na yi , duk yadda ya yi kama da labarin wata ko wani babu hannu na a ciki , ban yarda ba wani ya sauya min ko da kalma daya ce da ga cikin aiki na , yadda mu ka fara shi cikin Amincin Allah ina fatan mu ida shi a haka '
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
[29/06/2024]
PAGE 1 ❤🔥
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
NIGERIA ( KANO STATE )
Wata kyakyawar yarinya ce ta ke tafiya a hankali saman titi ta na tafe ta
Na wassa , a shekaru ba za ta wuce 14 years ba
Kyakyawar ce gaskia jinin haussa Fulani , skin din ta chocolate , ta na da shape kamar coca cola duk da karancin shekarun ta breast din ta a cike ya ke kuma a tsatsaye ga M
Skuma hips , ta na dara daren idanu barare kal kamar madara , kwayar idanun ta black ce har wani kyali ta ke , ga dogon hanci mai kyau , ga dan karamin bakin ta , lips din ta pink colour yarinyar ta hadu kamar ita ta yi kan ta
Sanye ta ke cikin wando dark brown da riga zuwa guyiwa egg white , ta daura dan karamin hijab zuwa kirji shi ma egg white, ta na rataye da Bag yar karama a baya , ga Dukan allamu da ga school ta ke
Ta na tafe ta na wasu juye² ta na yar waka da ga gani kassan har yanzu ta na dawainiya da yarinta
Sai da ta karasso bakin hanya za ta tsalaka titi ta tsaya ta na dube dube
Cen ta hango wani makaho a daya gefen titin , ya na sanye da bakin glass ya na rike da sandar shi ya na tafiya cikin konciyar hankali
Makahon kyakyawan gaske ne , fari kal da shi me zubin larabawa , ya na sanye da wandon jeans baki da riga fara , kafar shi na sanye cikin boot bakake su ma , ya hadu over , ya na da dogon hanci da dan karamin baki lips din red colour kamar jini na sama ya yi wani shape kamar heart , ga wani kontancen saje a gefe da gefen fuskar shi , gashin kan shi baki kirin da shi so smooth ya zubo mishi bayan keya sai wasu sirarren da su ka zubo mishi a gaban goshi , ya na da tsayi ga murdaden jiki kamar dan dambe , damtsen shi a murde su ke kamar za su fassa hannun rigar , ga wani kyakyawan gashi konce luff saman hannayan shi , idan ka kare face din shi kallo da kyau ya na da wani dan karamin zane baki geffen wuyan shi na dama amma gashin shi ya rufe shi ba a iya ganin shi da kyau , zannen ya fito kamar CROWN an dasa misi wata SWORD a tsakiya
Tun da ta hango shi ta saki wani kyawatencen murmushi
Da sauri ta kali damar ta , ta kali hagun ta , ta ga babu motoci sannan ta fara tafiya da dan sauri ta tsalaka titi
Da gudu ta bi bayan shi
Sai da ta zo dab da shi ta tsaya geffen shi ,cikin wata kyakyawar murya mai dadi ta ce " Yaya Zayd "
Bai ce da ita komai ba su ka ci gaba da tafiya a jere
Sai da su ka yi nisa cikin tafiyar su sannan ta kale shi ta ce " Yaya Zayd gida za ke je ko kuma wajen Abba za ka wuce "
Jinjina mata kai ba tare da ya ce mata komai ba
Haka su ka ci gaba da tafiya ta na zuba mishi surutu shi kuma ya na sauraron ta , sai in ta yi mishi tambaya sai ya girgiza mata kai ko ya jingina mata
Sai da su ka iso bakin kofar wani gida , gida ne madaidaici an mishi shafen siminti da kofar gidan Light green, gida ne irin na ma su hali dan bai yi kama da gidan wadan da ci da sha ke yi musu wuya
Su na isowa kofar gidan su ka tsaya a tare kamar ya san sun iso
Juyo wa ta yi ta kaleshi ta ce " Yaya Zayd ni zan shiga ciki nagode da rakiya " ta kai karchen ta na murmushi
Jinjina mata kai kawai ya yi , ya fara takawa ya yi gaba abun sa
Ya na barin wajen ita ma ta juya ta shiga cikin gidan ta na sallama
Wata mace ce ta zaune tsakiyar gidan saman tabarma , ta na tsintsar wake
A hankali ta dago kan ta kali kofar shigowa ta na amsa sallamar ,
ta na ganin yarinyar ta saki dan karamin murmushi ta ce " Inaya har ki dawo , ina ki ka baro Nesrine "
Takowa yarinyar ta yi ta zo geffen ta ta zauna ta cire jakar ta ta ajiye gefe sannan ta kama tray din hannun ta ta na fadin " mun riga su fitowa shi ya sa na tafowa ta "
Murmushi matar ta yi kafin ta ce " shikenan tashi ki je ki cire kayan ki , ki watsa ruwa kin debo rana "
Jinjina mata kai ta yi kafin ta ce " toh mama , amma bara na ida tsintse waken sai na tafi "
Matse fuska mama ta yi ta kai hannu ta karbi tray din ta na fadin " Inaya tashi ki je na ce ko "
Dan murmushi ta yi kafin ta kai dan lips din ta saitin kumatun ta, ta sumbata kafin ta mike ta dauki jakar ta ta wuce dakin da ke fuskantar su
Ta na shiga dakin mama ta ji ana sallama
Murmushi ta saki ta na amsa sallamar kafin ta ce " Nesrine ina ki ka tsaya haka "
Wata kyakyawar budurwa ce ta shigo cikin gidan ta na sanye da uniform din school irin da Inaya, skin din ta chocolate ita ma kamanin ta sak irin na Inaya ba dan ta fi ta dan jiki ba da shekaru sai ayi musu daukar Twins , a killa a shekaru ta kai 17 zuwa 18
Geffen mama ta zo ta zauna ta kontar da kan ta saman kafadar ta sannan ta lumshe idanun ta ta ce " mama ni fa na gaji da zuwa makarantar nan, dubi duk jiki na ciwo "
" karbi nan ja'ira kawai, in baki je makarantar ba ki yi mi ko aure ki ke so na yi miki, shikenan zan ce ma Zayd ya ka kudin sadakin ki tun da na lura ya na son ki " mama ta fada ta na ajiye tray din geffen ta , sannan ta yi kokarin tashi
Da sauri Nesrine ta ce " a'a wlh mama, me zan yi da makaho kuma kurma, ai ba maza su ka kare duniya ba "
Dariya maman ta yi ta na shirin magana su ka jiyo muryar Inaya ta na fadin " Ai ko cikin mazan yaya Zayd na daban ne , ba dan Nakassar da Allah ya jarabe shi da ita, da wlh ko yar aikin shi baki kai matsayin zama ba " ta kai karchen ta murguna mata baki
Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta kali mama ta ce " mama kun gani ko, ita fa ta ke tsokana ta sai in na dake ta, ku ga laifi na "
" Ni ai gaskia na fada, kin san dama an ce gaskia daci gare ta " ta fada ta kama hanyar toilet
" mamaaaaa" Nesrine ta fada ta na jan sunnan
Kallon ta mama ta yi kafin ta ce " kin ga ko kar ki kuskura ki daura hannu saman ta kin san halin baban na ku da Abdoul ba su son abun da ya taba autar su dan haka kyale ta , ai kuma laifin ki ne kin fi kowa sanin yadda ta ke ji da Zayd shi ne za ki wani bata mishi sunna "
Kumbure fuska ta yi ta na fadin " amma mama haka zan zuba mata ido ta min magana yadda ta ga dama na fa girme ta sh........"
Mama ta katse ta de cewa " to sai ki kama girman ki ko ki kyale ta "
Ta na gama fadar haka ta juya ta shiga kitchen
Tsaki Nesrine ta yi kafin ta mike ta dauki jakar ta, ta wuce dakin da Inaya ta fito
Daki ne dan madaidaici sai yar katifar su da ke karchen dakin, da closet din kayan su ya na fuskantar katifar sai yar karamar dressing mirror
Ta na shiga ta Fada saman gadon ta yi rub da ciki ko hijabin jikin ta ba ta cire ba
A hankali ta fara sakin kuka kassa kassa ( ko kukan me ta ke oho 🤔🤷♀️)
Ta na cikin kukan nata Inaya ta shigo dakin ta na sanye da hijab zuwa guyiwa
Ta na jin shigowar ta ta yi saurin kauda kan ta gefe ta saka kanta tsakanin pillow ta na goge hawayen ta
A hankali Inaya ta ke takowa cikin dakin ta na dan wake waken ta , ta wuce wajen closet din su ta bude ta dauki wata gown mara nauyi launin blue ta saka sannan ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki daddumar ta, ta koma bakin gadon ta shinfida
Kallon Nesrine ta yi kafin ta ce " Nesrine tashi ki je ki yi Alwalla lokacin sallat ya yi "
Shiru Nesrine ba ta amsa mata ba, ko motsi ba ta yi ba
Dan tsaki Inaya ta ja ta na kunbure fuska ta ce " kar ki tashi in kin ga dama "
Ta na gama fadar haka ta fara gabatar da sallar ta
Nesrine ta na jin ta fara sallat ta yi sauri ta mike ta koma gaban closet ta tsaya ta bawa Inaya baya
Da sauri sauri ta cire hijabin jikin ta ta cire uniform din ta ta daura wata towel fara sannan ta saka hijabin ta , ta yi sauri ta fice dakin ta wuce toilet
After some minutes ta shigo cikin dakin
Lokacin har Inaya ta Kamala sallar ta , ta na zaune saman gadon su ta jingina a bayan gadon ta na rike da littafin ta ta na karantawa
Da sallama ta shigo dakin ta na sunkuyar da kai
Ba ta ce da Inaya komai ba ta wuce wajen closet din su , itama ta saka gown irin ta Inaya sai dai ta ta launin Red ce
Bayan ta saka rigar ta dauki hijab ita ma ta saka ta dauki daddumar ta
Inda Inaya ta shinfida ta ta , nan ta shinfida ita ma sannan ta gabatar da sallar ta
Ta na tsaka da sallar ta mama ta shigo dakin ta na sallama
Dago kan ta Inaya ta yi ta na amsa mata sallamar ta
" Yawwa Inaya, dan Allah tasso ki je kiyo min cepane yaran nan sun koma sangayar su " ta na gama fadar haka ta sa kai ta juya
Da sauri Inaya ta diro da ga saman gadon ta na murmushi dan dama na son fita amma ba hali
A hanzarce ta saka hijabin ta, ta saka dan takalmin ta ta fito
A harabar gidan ta isko mama cikin yar runfar da ke bakin kofar dakin ta , ta na zaune saman yar karamar kujera
Gaban ta ta karaso ta tsuguna ta na fadin " gani mama "
Dan murmushi mama ta yi kafin ta ce " to malama an ji za a fita shi ne ki ka tasso da sauri ko "
Sunkuyar da kai ta yi ta na murmushi dan mama ta gano ta
Dubu dayan da ke cikin hannun ta, ta mika mata ta ce " shikenan karbi ki sayo min albassa da timatir na dari biyar biyar ki yi sauri kin ga fa rana ta yi kar ki tsaya wannan shirmen na ki "
Yar dariya ta yi kafin ta ce " mama ni fa ba na tsaya wa shirme kin ga kullum sai na riga Nesrine isowa gida "
Ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi hanyar fita gidan
Da kallo mama ta bi ta har ta fita gidan sannan ta ce " kai ni wannan yarinyar Allah ka shirya min ita, a ce ki na girma ki na cin kassa "
Inaya kuma ta na fita gidan ta fara wake waken da ta saba yi
A hankali ta ke tafiyar har ta karaso wajen wata bishiya
Cen ta hango wani datijo zaune kassan inuwar bishiyar ga wasu kananan yara zagaye da shi su na rike da allo su na karatu
Tun da ta hango shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta fara takowa da sauri ta tinkaro bishiyar ta na sallama
A hankali ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta
Wani dan murmushi ya saki kadan kafin ya ce " Auta me kuma ki ke yi nan "
Riko hanayan ta baya ta yi ta na yar jujuyawa cikin shagwaba ta ce " mama ce ta aike ni cepane "
" shikenan yi sauri ki je, kin ga rana ta yi " ya fada ya na kokarin mike wa tsaye
Jinjina mishi kai kawai ta yi ta na murmushi ta wucewar ta
Ta na barin wajen ya kali yaran ya ce da su " ku ci gaba da karatu ina zuwa "
" Toh malam " su ka fada a tare
A hankali ya ke tafiyar shi ya na sanye da manyan kaya , ka na ganin ka san wannan datijon ya na cike da haiba da mutunci
Ya yi tafiya wajen minti biyar kafin ya iso gidan da Inaya ta fito
Bakin shi da sallama ya shigo cikin gidan
Mama ta na zaune inda Inaya ta baro ta ba ta motsa ba
Ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " sannu da zuwa Abban Abdoul "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " Amina ba na ce miki ki bar barin yarin yar nan ta na fita ba "
Sunkuyar da kai mama ta yi kafin ta ce " yi hakouri malam Nesrine ce ta na sallat shi ne na aike ta "
" Amina da sai ki bari ta Kamala, kin fi kowa sanin hatsarin da ke bibiyar Inaya cikin rayuwar ta tun shigowar ta duniya me a ba mu fuskanta ba , a dalilin ta mu ka baro Kaduna saboda barazanar da a ke mana , yanzu in su ka samu labarin mu na nan kin san fa baza mu tsira ba , ni ko makarantar da su ke zuwa dan kin matsa ne na hakura na bar ta, ta na tafiya , ba dan Zayd ya na bibiyar ta ba ban san abun da zai faru da ita ba , dan Allah ki bar barin ta na fita wlh bazan iya jure rashin ta ba " ya fada cikin rauni zuciya
( GA DUKAN ALLAMU AKWAI WANI BOYAYEN AL'AMARI A TATARE DA AHALIN GA 🤔🤔 )
Wasu hawaye ne su ka zubo mata ta cikin zafin zuciya ta ce " yanzu dan Allah malam haka za mu ida rayuwar mu kullum mu na gudu , mi mu ka yi musu da za su ringa bibiyar mu haka , kawai dan ka hana ma d'an su auren Inaya shi ne su ke neman su kashe mana ita, meye laifin ta a cikin wannan abun yarinya karama su na neman su lalata mana rayuwar ta " ta kai karchen kuka na kubce mata
Da sauri ta juya ta koma cikin dakin ta
Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya bi bayan ta shi ma ya shiga dakin ya na sallama
Bakin gadon ya isko ta zaune ta na kukan ta
Geffen ta ya je ya zauna ya kai hannu shi bayan ta ya na dan bubugawa ya ce " kiyi hakuri Amina, in sha Allah ba abun da zai faru da ita dan na mallaka ta a hannun wanda zai kulla min da ita fiye da mu "
Dago kai ta yi ta kale shi cikin kuka ta ce " ban gane ba malam, wa ka mallakawa ita kuma me ka ke nufi "
Hannun shi ya kai ya goge hawayen ta sannan ya mike tsaye ya ce " in sha Allah in lokaci ya yi za ki san komai "
Ya na gama fadar haka ya juya ya bar dakin
Ya na fitowa harabar gidan Inaya ta shigo ta na sallama hannun ta rike da leda baka sai murmushi ta ke gwanin ban sha'awa
Ya na ganin ta ya saki murmushi shi ya ce " Auta har kin dawo "
Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da takawa ta shiga kitchen
Ta na shiga shi ma ya fara takawa ya nufi hanyar fita gidan
Ya na fitowa waje ya isko Zayd ya na tsaye bakin kofar gidan ya jingina da bangon gidan ya na rike da sandar shi ya dan daga kan shi ya na kallon gaban shi
Abba na ganin shi ya saki murmushi ya ce " A Zayd ashe tare ku ke "
Jinjina mishi kai Zayd ya yi sannan ya juya ya fara takawa
Murmushi Abba ya yi ya girgiza kan shi ya bi bayan shi su