Showing 27001 words to 30000 words out of 122700 words

Chapter 10 - Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

573

ya mikawa Alhaji Jafar Yana fadin "Duba ka gani Yallabai ni tunda ba ganewa zanyi ba,naji Dadi da Allah yasa aka Gama wannan karatun ba domin na saka auduga na toshe kunnuwa naba da ba'ayi karatun Nan ba, tunda Wanda yaso auren nata yace in dai zatayi karatun Nan shi ya fasa, shi Kuma Dan uwanta na wajen kanena yace karatu Babu gashi tunda tana ganewa Kuma tana so, kaga yanzu duk gurin nan namu ita me yiwa mutane Allura".
Kallonta Alhaji Jafar ya karayi,sannan ya kalli Ardon Yana fadin.
"Yaushe ta Fara karatun ne na ganta karama amma har ta hada diploma?"
Gyara tsayuwa Ardon yayi Yana fadin "wallahi am tun tana aji hudu na furamare Dan uwanta ta kaita aji daya na sakandire tunda yayi wani zuwa suka zauna da kannen nasa yaga tana da kokari shine yace Mata idan ta Gama makarantar tana son taci gaba da karatu, shine tace Masa tana son ta Zama malamar asibiti, to tunda sukayi haka ya kudurci aniyar tsayawa akan karatunta shi yasa da akayi Mata chaaaa akan maganar aure yace Bai Hana ayi maganar aure ba. Amma ya Dora sharadin saidai idan mijin ze barta tayi karatu abinda ya gagara kenan aka fasa Amma duk yan uwanta anyi musu".
"Masha Allah. Allah ya Sanya Albarka, haka ake so a rinka barin Yara Mata suna karatu barin ma na bangaren lafiyar da malaman makaranta, yanzu ba cewa kayi ita ke yiwa mutane allura ba da sauran abubuwa? To da batayi karatun ba da basai an tafi wai gurin an nema ba? Ba komai in Sha Allah zatayi auren ta Kamar kowa".
Ardo ya amsa da "Allahumma Amin".
Ma'un Alhajin ya kalla "Asma'u kin amince na tafi da project din naki na duba a hankali in yasa said dawo Miki dashi".
Kai ta gyada alamar Eh.
Sunyi sallama da Ardo tawagarsu suka wuce zuwa Yola inda zasu bi jirgi zuwa Abuja.
Wannan shine silar haduwar Alhaji Jafar da Ammah, ya koma maida project da Kuma kafa gwanatinsa cikin ikon Allah suka yarjewa juna.
Lokacin da magana tayi karfi Rabi'a taso tada hankalinta saida Nanna ta taushe ta da kalamai masu kwantar da hankali.
Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu. Amarya ta tare cikin ikon Allah zaman Rabi'a da Asma'u ya kasance Zama Mai tsabta.
Wata uku da auren Asma'u ciki ya bullo duk masoyin Alhaji Jafar ya Taya shi murna sosai a lokacin ne Alhaji Jafar ya biyawa Rabi'a makka kusan abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta.
A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye amfanin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida.
Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji.
Murna gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu.
Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi wata biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem.
Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta haifi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma Ammah.

WACECE FATIMAH ZAHRA?
'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya har Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can.
Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a can yayi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda.
A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga iyayensa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah.
Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar.
Zahra nada wata biyar wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono.
Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja.
Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi Kuma ya koma Abuja.
Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta.
Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar da har abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba.
Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Zahra ta hakura ta barwa Ammah Zahrar.
Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin Kamar nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta.
Wannan kenan.


Ranar da za'ayi jarabawar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta.
Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Zahra ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna".
Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside locker ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana".
Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu"
"To naji maza Allah ya bada sa'a"
A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan".
Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan.
Masha Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako.
A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha.
Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sannan ya fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru Kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "yanzu Yallabai da kanka zaka rakata ai da Koda Hasana ko Hassan ka hadasu zasu kaita ko Kuma a fadawa cen kakanninta su turo a tafi da ita ai cacar kudin Kamar yayi yawa".
Daga Ammah har Alhaji Jafar din kallon Mamar suke ita dai Ammah shiru tayi yayin da Alhajin yace.
Saboda ban San darajar 'ya'ya ba zan hada Yara a tafiyar uwa duniya daga Nan har Jordan na kwanta a gida hanakli kwance ko?"
Kai ta gaigice tare da fadin "gani makudan kudi za'a kashe".
Wani kallo yayi Mata "kada ki kawo b'araka Rabi'a duk yaran dake gabana daya na daukesu yada zan yiwa abinda na Haifa haka zan yiwa marainiyar Allah. Da Kuma kike maganar cacar kudi idan zan jera shekara Ina Kai zahra Jordan kullum ba abinda ze girgaiza a cikin abinda na mallaka".
Ku tashi kuje.
Lokacin da zasu tafi anyi Mata tsara sosai Dan Nanna ma kilishi tasa aka yi Mai yawa na tsaraba.
Har kano su Ammah da yara sukayi musu rakiya.
Lokacin da sukaje Jordan din ba karamar murna kakanninta zukayi ba Dan Babu zato suka gansu, sun Kuma Kara yabawa da cika Alkawarin Alhaji Jafar Dan da kansa yayi musu Alkawarin ze kawo musu Zahra Dan ko a waya Bai fada musu zuwansu ba,sai address dai daya taba tambaya can wani lokaci.
A ranar Zahra taga zallar soyayya a gurin dangin Najwa Dan gidan cika yayi da 'yan uwa aka dasa sabon kukan rashin Najwar da kyar Abbie da Abbanta suka dinga Basu hakuri Dan ma Alhaji Jafar ba larabcin yakeji sosai ba saidai Wanda suke Jin turanci suka ringa magana dasu.
Lokacin da Alhaji Jafar din ze tafi masukin daya Kama a hotel Abbie hanawa yayi duk yanda yaso zillewa kin yarda yayi dole ya amince aka sauke shi a wani part dake kusa da nasa Ummee din, Dan ba karya dukiya dai Kam akwaita Dan shi kanshi Alhajin yayi mamakin yanda ya riskesu Bai taba kawo haka suke ba lallai yasan hadin Allah ne kawai da suka bawa Muhammad sani auren 'yarsu Dan tazarar Mai nisa ce a tsakanin su.
Kwanan Alhaji Jafar bakwai ya wuce Umara yayin da Ummee tayi Masa Alkawarin zasu hadu a Saudiyyar tunda zata kawo Zahrar Nan gurin iyayenta da 'yan uwa su ganta a cikin garin Madinatul Munawwara.
Satinsa daya da zuwa Suma su Zahrar sukazo Saudiyyar ita da Ummeen da Aunty Nawwara.
A Nan ma Saudiyyar Zahra taga gata iya gata Dan kowa Nan Nan yake da ita, Dan kanwar Ummee Hanifa sosai ta kafe sai dai a bar Mata Zahra ta tafi da ita Istanbul inda take aure Wai Bata yarda da zaman Nigeria ba.
Ankai ruwa Rana da ita kafin ta hakura Dan da gaske Alhaji Jafar ya bude Mata aiki Dan cewa yayi idan irin haka za'a ringa yi bazai Kara bawo musu ita ba saidai duk Mai son ganinta taje ya ganota Kamar yanda Ummee keyi, hakuri aka ringa bashi.
Saida aka Kai Zahra makka suyi kayi umara sannan suka fara Shirin baro kasar.l Sayyaya dai Zahra ta shata Dan wasu kayan sai a awon cargo akayo musu su.
Sarkar gwal da warwaro zobe kuwa kirar Saudiyya da Dubai zuwa kirar Bahrain sun Kai kala goma duk dai dai size din ta sai na Ammah biyu na Hasana ma biyu shi kanshi Alhajin anyone mass goma Sha Tara ta Arziki.
Ranar da zasu dawo Zahra Tasha kuka haka kakarta Ummee,har jidda sukayo musu rakiya Basu suka tafi ba sai da jirgin su Zahra ya tashi a sararin subahanahu wata'ala.
Saukar safe sukayi anan suka samu Bala direban Alhaji Dan Bai fadawa kowa sun taho ba sai Balan kawai, sau da yawa idan ya fada gashi Nan a hanya hankalin Nanna baya kwanciya har sai ya iso.
Lokacin da suka shigo harabar gidan suna tsayawa Zahra to garzaya cikin gida tana fadin "Ammah!!! mun dawo".
Da gudu Hameeda ta fito daga part dinsu, rungume juna sukayi suna ta tsallen murna Sai jikin zahra Hameedar ke shafawa gani take kamar canza Mata Zahrar akayi.
Da sauri Ammah ta fito tana "fadin wa nake gani ne haka Kamar bakin saudiyya zuwa ba notice?"
Alhajin ne ya Bata amsa.
"Surprised din ki mukayi ko Zahra na?.
Kai ta gyada masa.
Kayansu ne su Bala da Mai gadi suka Fara shigowa dasu kafin Alhajin ya nufi part dinsa na cikin gidan yayin da Ammah ta rufa Masa baya.

Har yayi wanka ya shirya Mama Bata shigo ba, har ya tambayar Ammah yayi Ina Rabi'a ? Tace Masa tana ciki watakila ko barci take.
Kusan kwana su Zahra sukayi tana baiwa Hameeda labarin abinda ta gani da inda sukaje a Jordan da saudiyya, wurin karfe biyu Ammah ta tashi zatayi nafila ta jiyo su suna Hira a dayan bed room dinta lokacin wuri biyu da rabi na dare, leko tace su kwanta basu san dare yayi sosai ba.

Washe gari an baje tsarabar Zahra an baiwa kowa dai dai gwargwado.
Amman tsarabar Hameeda daban take Dan har sarka Saida ta baiwa Hameedar.
Basifi sati biyu da dawowa ba jarabarsu ta fito ta Federal inda Zahra ta samu F.G.G.C KAZAURE yayin da Sulaiman ya samu F.G.C DAURA, Hameeda F.G.C AZARE. Salma ce kawai bata samu ba a cikinsu.
Sunyi murna Kuma sunyi bakin cikin rashin samun makaranta daya duk an watsa su Abban Kuma da ya Hassan sunce kowa ya tafi inda ya samu, ita Hameeda Bata da damuwa tana gida, su Kuma duka 'ya'yan Ammah duk sun fita waje danma hanyarsu daya sai an aje Zahra a karasa da Sulaiman.
Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka dauko hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu.
Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one.
A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Mata "sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa".
Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya.
Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "ni sunana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?".
Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C.
Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar gasu Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah.
Lokacin da akayi hutu Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman.
Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsokana.
Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha.
Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga FGC AZAREN itama a ss1.
A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida.
Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai.
Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin uba namiji ba itace komai nasa.
Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'a, cikin ikon Allah sai komai ya daidaita.

Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka dinki ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini.
Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito.
A kasa suka taka suna Hira har sulaje gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane.
Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta fito. Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa.
Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar.
Gaishe shi sukayi su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa".
Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da zafin Kasarmu".
Ta fada tana dariya.
Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?"
Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Allah."
Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi.
Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu.
Har kofar gida ya kawosu suna tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana".
Dan murmushi tayi tana fadar.
"Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi"
Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya takura Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra.
Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo ta wuce dakin su.

Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login