Showing 90001 words to 93000 words out of 122700 words
mamaki yake Bata "Wai menene hakan" tayi tambayar da ba Mai Bata amsa. abinda takeji wani Abu ne na daban Wanda Bata taba Jin irinsa ba akan kowane da namiji ba, cikin kankanin lokaci ya cika Mata zuciya ita abun har kunya yake Bata,ta gama bore harda su somewa dasu wunin Asibiti Kuma yanzu a wayi gari a ganta dumu dumu cikin soyayyarsa ai da kunya wlh.
Wani tunanin ta qarayi Bata San lokacin data rufe idonta ba tana ambaton "Ya Ilahiy wlh abun da matukar Allah ka agajeni gaskiya idan hakan ta kasance naji kunya".
Ta fada tana qara qanqame jikinta.
Saida ta Kusan Bata minti talatin tana abu daya sannan ta yunqura da kyar ta tashi,wanka tayi ta shirya cikin English wears yellow irin shaking material din Nan sai sukayi Mata wani irin kyau Karamin mayafi ta rufe gashinta dashi black Mai shara shara ana kallon bakin gashinta Mai santsi da laushi ta cikin gyalen, sama sama ta fesa turarenta ta fito parlourn ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta kawai sai Kuma sanyin A/C daya ratsa ko Ina,cikin takunta na nutsuwa ta doshi kitchen inda take jiyo motsin zilai a cikinsa.
Sansanyan kanshi ta ya Fara shiga hancinta zilan kafin ta karasa shigowa.
"Masha Allah! Uwar dakina dawisu sarkin ado, Allah ya barki gidan Yallabai muhmudu, ubangji ya kawo Mana kazantar daki Amma Bata shara ba".
Dan murmushi Zahra tayi tana Fadin kin jiki Aunty zilai ni kibar wannan maganar gaskiya, Ina kwana".
Ta fada tana komawa parlour biyota zilan tayi tana Fadin "yau fa abinda kikafi so nayi Miki" ta fada tana kokarin bude warmers din abincin,waina ce manya irin tasu ta Bauchi sai Kuma pepper soup na cow leg da kunun gyada Wanda yaji Madara.
"Wow! Amma aunty zilai kin gama min komai na gode" ta fada tana janyo plate din da zata Zuba, zilan ce ta karba da sauri tana fadin "haba dai gani a tsaye Zaki Zuba abinci da kanki to meye amfanina".
Rike plate din Zahra tayi tana fadin "Dan Allah kada muyi haka dake Ina laifin dafawar ma ai dadin sai yayi min yawa, Ina kwance Ina barci kina ta faman dawainya sannan Zuba abincin ma Sai anyi mini".
"To menene ai aikina ne".
"A'a wlh ba Aikinki bane a Nan cewa akayi ki tayani Zama kwarai".
Ta fada tana bude abinci akan dole zilan ta hakura ta koma kitchen inda take wanke waken alale zatayi musu cikin abincin Rana.
Bayan ta Gama yin break din parlour ta dawo ta kunna tasharta mbc max tana kallon wani film da sukeyi, tana Nan zaune taji karar door bell ta tashi ta nufi kofar ta bude yara ne kamar 'yan sheka sha uku haka suna rike da manyan ledoji kowa guys biyu a hannunsa.
Cikin girmamawa suka gaishe da Zahra tare da fadin "gashi inji Baba Malam yace a kawo Miki Kuma Yana gaishe ki".
Suka fada a tare, hanya ta Basu suka shigo da kayan ciki sai raba Ido suke suna kalle-kalle.
"Sannunku ku aje ku zauna, na gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi, a me kukazo ne?". Dayan da yafi magana yace "Yaya Habibu ne ya kawo mu Yana kofa gurin wancen mutumin" ya fada Mata.
"Masha Allah". Ta fada tana Kiran zilai, da sauri ta fito tana fadin. Gani uwar dakina".
"Kaya ne Baba Malam ya Aiko aka kawo min".
Gurin da kayan suke ta karasa tana fadin "Masha Allah 'yar gatan Baba malam, an gode madallah sai a Basu tukwaici". Zilan ta fada tana kokarin bude ledar dake kusa da it's.
"To Bari na dauko musu ki shiga da kayan ciki sai ki zuba musu abinci a robobin nan na take away Wanda aka kawo saboda zuba kayan gara Dan kada su zauna yau Ranar wanki da 'yan aikace aikacensu ne," ta fada tana yin gaba.
Bedroom dinta ta shiga ta duba Sam ba kudi a gurinta, Dan Jim tayi sai Kuma ta bude bedside locker ta dauko keys din dakin Mahmud daya Bata.
Kamar' Mai tsoron wani Abu kada ya kamata ta bude dakin, komai tsab hatta kamshinsa Yana dakin kamar yanzu ya fesa yabar dakin,limshe ido tayi tana shakar kamshi, komai na dangin electronic a kashe yake a dakin a hankali ta ratsa ta nufi inda ya nuna Mata yace idan bukatar wani Abu ya tashi ta dauka, locker din ta janyo 'yan dari biyar ne da dubu dubu ko wanne rapper uku uku 5k kawai ta Ciro daga cikin 'yan 1k din ta mayar ta rufe tana tunanin Kiran magaji yazo ya Ciro Mata kudin saboda irin haka Bata bukatar komai tunda ba abinda ba'a aje Mata ba wani abun ma Sai a shekara Bata nema ba.
Bayan ta kawo musu sukayi gdy suka fita, gurin Aunty zilan Zahra ta shige.
***********
Karfe biyar na yamma jirginsu Ammi ya sauka a sokoto, lokacin data fito Harabar da masu jiran saukar 'yan uwansu suke,Habu direban Hajiya Inna ne ya nufo Ammi da sauri Yana fadar "barka da sauka Hajiya, nine Hajiya Inna ta turo nazo na tare ki".
Ya fada Yana karbar karamar luggage din dake hannunta .
"To sannu da kokari nagode kwarai".
Direct gidan Hajiy innar ya nufa da ita da yake unguwar mabera, duk yanda Abban su Mahmud yaso ta zauna part dinta daya Gina Mata Amman ta nuna tafi son daga nesa dai.
Har kofar falon Hajiya Malam Habun ya kawo ta bisa umarnin Hajiya, lokacin da ze tafi dauko ta fada masa ya kawo Mata ita har kofar parlour.
Kafin ta fito Yara qananu guda biyu suka fito da gudu daga parlour wanda yayi dai dai da fitowar Ammi daga mota da gudu suka karaso, suna fadin ga Ammi! Ga Ammi" suka fada jikinta a tare suna fadin "Ina kikaje Ammi Baki tafi damu ba mukayi ta kuka".
Kansu ta shafa tana fadin "sorry My babies ba gashi na dawo ba, ai kuka Kuma ya Kare"
Hannunsu ta rike ta nufi kofar da suka fito, sun riketa ram kamar zata gara guduwa ta barsu.
A zaune Ammi ta samu Hajiya inna tana lazumi, gurinta ta nufa cikin takunta na nutsuwa tana fadin "Hajiya barkanmu da yamma".
.
Ajiye tasbahar dake hannunta tayi tana kallon Ammi wadda tayi wani tas da ita, bazaka taba cewa ta aje kamar' Mahmud ba, idan aka jera su mafi yawan mutane zasu ce yayarsa ce. Gefen Hajiyar ta zauna daga kasa wannan d'abi'ar ta ce Bata taba Zama a kujera matukar Hajiya na Kan kujera, cikin ladabi irin na D'a da uwa Ammi ta gaishe da Hajiyar Tana fadin "Masha Allah zainabu kin cika Alkawarin da Kikayi min Koda kuwa ba a lokacin bane nagode kwarai da gaske Allah ya Albarkaci zuciyar ki ya Baki rinjaye akan duk masu son su tagayyara Miki zuri'a, ki Kara hakuri akan Wanda kike yi lallai duk Wanda akace yayi hakuri an Bata masa ne, Allah yayi Albarka yanda kike min biyayya kema Allah ya Baki surukar da zatayi Miki fiye da yanda like min, Wai kin samu yin magana da mutumina kuwa bayan munyi wayar nan?".
"A'a har yanzu be nemi kowa ba ina ganin ko ba lafiya ba dai shirun tayi yawa ya Kamata ace zuwa yanzu yayi hakuri ya huce ya dawo gida".
Ammin ta fada cikin damuwa.
"Ba komai in Sha Allah lfy na fada Miki yanda mukayi da mustapha kema kince kina bibiyarsa ayi ta addu'a Allah ya sassauto da fushinsa ya waiwayo gida wallahi ko cikin dare yaron Nan ya Fadi min a Rai to barcina ya Kare Kullum ta Allah sai anyi mini saukar Alqur'ani akan Allah ya bashi kariya a duk inda yake wallahi nayi Dana sanin fada masa maganar da nayi danasan maganar tawa ze dauketa da zafi wlh da bazan fada masa ba yana cikin zafi".
Hawaye ne ya balle Mata kamar lalataccen famfo har da shashhshekar ta.
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh ba maganar ki bace tasa yabar gida nakin dai yazo Kan gab'a ne kawai".
"A'a keda Baki Nan mukayi yazo Nan Yana ta huci Dan motar dazo a ciki ma ko kashe ta baiyi ba ya fado min Kamar an jefo shi, Yana huci Yana Fadi wlh duk duniya ba Wanda ya Isa yasa ya auri safna Koda Matap sun kare shi Daman koya aureta biyayya ne zeyi Yana da wadda yake da muradin aure, ni kuma a lokacin bani da cikakken masaniyar abinda yake faruwa kinja layin kada a fada min gaskiyar maganar,Ina bude Baki sai ce Masa nayi idan ya ciki shi d'ane na halali ya shiga duniya ya Nemo min yarinyar da yake maganar a kanta Wanda take ganin darajarta tafi ta zuwairiyyar, wlh shiru yayi a inda yake tsaye kasa cemin komai yayi Kusan tsawon minti biyar, kafin ya kalli idona yace min wlh zakiga cikakken Dana halak, ki rubuta ki aje idan kin qara ganina a sokoto ba tare da ita ba to kuwa shege ne ni,idan Kuma ban sameta nida sokoto har abada ya juya ya wuce ko motar Bai kalla ba Kuma tun daga Ranar har Rana Mai kamar ta yau ban Kara saka mahmudu a idona ba, sai dai Babban yaronsa Yana zuwa ganina Yana kawo min duk abinda Mahmudun yake kawo min ciki kuwa harda magungunan da nake sha na hawan jini".
Ammi tayi mamakin Jin Sameer na zuwa gurin Hajiyar koda Wasa Bata taba Jin haka ba, Kenan wato kafa ya bawa mutane Yana cikin Nigeria din kenan bawai inda ake zaton zashi ba.
"Allah kyau Hajiya ki daina damun kanki, jikina Yana bani Yana cikin kasar Nan Kuma Yana da labarin komai tunda kikace min Sameer na zuwa, duk inda yake ya sani ya hana shi ya fada ne kinsan halin kayanki dai".
Mardiyya da Urat Hajiyar ta kalla Tana fadin "yan nema kunki iyayenku sai uwar wasu tun barinki garin Nan yaran Nan suka tare a Nan Wai saina kaisu Yamai gurinki tunda aka fada musu naje suka tada hankalin iyayen sai su dawo Nan idan Zan koma na tafi dasu, Kinga mardiyya jiya da Iyayen sukazo daki ta gudu ta rufe Dan ma kada su tafi da ita, ko makaranta sai dai direban ya biyo ya dauke su anan ya dawo min dasu Nan".
Kansu Ammi ta shafa tana fadin rigima ta kare tunda ga Ammin ku ta dawo ko?".
Kai suka gyada Mata a tare.
Masu aikin Hajiya ne suka shigo ta kofar baya daga kitchen suna fadin "lale marhabin da Ammi barka da zuwa".
Gaisawa sukayi a mutunce tana tambayar su iyalansu.
Abinci na musamman masu aikin suka gabatarwa da Ammi Wanda Hajiya ta hanasu sakat tun safe ake saukewa da dorawa da gaske Babu Mai shafewa Ammi Zane a gurin Hajiya tana sonta kamar me.
Sai bayan insha'i Ammi ta kwashi su Urat ta nufi gida cikin motar data Bari a gidan Hajiyar. So take ta bada mamaki yanda ta fice batare da sanin kowa ba a wayi gari a ganta batare da kowa yasan sanda ta dawo ba, duk gidan amintacciyar Mai aikinta kawai ta Kira ta fada Mata tana Nan Zuwa garin yay ko su Abeeda ba Wanda ta fadawa tasan zumudin su ze saka kowa ya sani.
************
Safa da marwa take tun bayan gama wayarta da Aunty Ladi ranta idan yayi dubi a bace yake Wai shi wannan yaron wane iri ne aiki akeyi a kansa Amma Kamar ana zubawa a teku wannan guri na uku ne da Aunty Ladi taje Mata a Jos Amma amsar daya ce wannan yaron yafi karfinta, Mata ne guda biyu a teaye a kansa da addu'a sannan yana da tsarin jiki na ban mamaki Nan kusa ba abinda zeyi tasiri a kansa sai ikon Allah.
Wayarta ta dauko Asabe ta Kira cikin k"an k'anin lokaci ta daga Kiran "kizo ina jiranki yanzu". Ta kashe wayar tayi wurgi da ita Kan gado.
Cikin abinda bai wuce minti Sha biyar ba Asabe ta shigo gidan ko part din Ammah Bata shiga ba kamar yanda ta Saba direct ta wuce gurin Mama.
Parlourn ba kowa ganin haka yasa ta wuce bedroom dinta a tsaye ta sameta tana kaiwa da kawowa Ido yayi Mata jawur kamar na tsohon mashayi.
Ko sallamar ta Mama Bata ba ta amsa ba ta, fara fadin "Ina ne garin da kikace min 'yar dago kawarki ta fada Miki da wani shahararren mutum Mai aiki kamar yankan wuka?".
Shigowa tayi ta zauna tana kallon mamar "Wai lafiya na ganki haka?"
"Ina fa lafiya! Aunty Ladi ce ta tasheni daga barci take fada min taje har guri uku ba sa'a, Wai yanda suka fada Mata yanzu ne ma Zahra ta gamu da Wanda ake ta fada Mana a baya bawai wadanda mukayi ta aiki a kansu ba, Kuma Shi wannan din duk ya fisu Shirin jiki Dan da alama yanda sihiri baya tasiri a jikin ita yarinyar shima baya yi a jikinsa, Wai wasu Mata ne guda uku a da maza biyu tsaye a kansa duk juyi sihirin baya kaiwa inda yake, yanzu Kiran da nayi miki ina son Jin tabbacin kin koma kin tabbatar da Mai gadin ya saka wannan abubuwan da Kika bashi?".
Dan murmushi tayi irin na kwararrun 'yan duniya din Nan kafin tace "Haba Hajiya shekara nawa muna tare ban taba ha'intarki ba sai yau an aiwatar da komai sai jiran sakamako kawai ai wannan yaron bama Azare ba Kasar Bauchin ma gaba daya shi da ita har abada, Kuma malamin da 'yar dagon ta fada min a wani gari yake cikin kasar katsina ana ce Masa Bakiyawa tace idan na shirya zata rakani garin iyayen mijinta ne daya rasu". Hake sukayi ta kullawa da kwancewa,Asabe nata Kara zugata akan ko nawa zata kashe kada ta Bari Ammah da 'yar zumunta su fisu komai, tunda ta Nan take samun nata rabon a jikinta idan Bata encouraging dinta itama zata rasa income nata.
**
Tun bayan ganawa da Bakinsa Mahmud ya shige bedroom ya Haye gado yaso ya Kira Zahra suci gaba da Hira Amma saiya fasa Dan yasan yanzu gari ya waye sosai a 9ja Bari ya kyaleta sai dare hirar zatafi tafiya yanda yake so. Bai tashi ba sai lokaci sallah, wanka yayo ya saka kananu Kaya yayi sallah yana cikin addu'a yaji ana knocking din kofa umarnin shigowa ya bayar Sameer ne ya shigo Bakinsa yaki rifuwa.
"Barka da Rana". Sameer ya fada Yana mikawa Mahmud wayar hannunsa.
Hannu yasa ya karba yaga menene yasa shi irin wannan murmushin.
Wani fine Baby ya gani nade cikin farin towel na jarirai fari sol.
Kallon shi Mahmud yayi Yana neman Karin bayani.
"Takwaranka ne madam ta haihu jiya cikin dare".
Cikin madaukaikin mamaki Mahmud ya kalli Sameer "are you serious?"
Kai ya gyada Masa Yana Fadin " yes sir".
Mahmud sai juya wayar yake Yana Kara kallon babyn.
"Masha Allah, my friend Allah ya Raya mana, amma me yasa ka taho ka baro yarinyar mutane a watan haihuwarta ai sai iyayenta suga rashin kyautatawar ka ga 'yarsu".
Shafa Kai yayi Yana Dan murmushi "ba wani Abu,idan na zauna me zanyi musu duk abinda ake bukata nabar musu".
Wani kallon baka da lfy Mahmud yayi Masa "an fada maka Bata bukatar kulawar ka ne a irin wannan lokacin?" wlh Dana San lokacin haihuwata yayi ba inda zakazo Kuma yanzu ka nemi visa ka koma gida daman Nan anyi clearing din komai U A.E din naji da komai kawai, naji kace takwara na nayi zaton sunan Abban koko za'a saka masa?".
"Ai umarninsa ne yace nayi masa huduba da sunan ka".
"To Masha Allah! Godiya ta har gida zanje na yiwa Abban tafi karfin ta waya Allah ya Raya Mana Mahmud yayi Masa Albarka, kaje ka Fara shiri tun yanzu ka shiga kasuwa kayi musu abinda ya Dace".
"In Sha Allah".
Godiya Sameer yayi ya nufi kofa Yana fita alarm na shigo Masa Wanda Saida ya girgiza shi baya yayo yana Murda kofar ze dawo ya jira yayi locking dinta, dariya yayi Yana Fadin "manya gatan Wasa, Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi".
A Ranar cikin dare suka bar Kasar su duka Sameer yayi Nigeria shi Kuma Mahmud ya nufi U.A.E .
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 34
AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu.
'yan uwa muna barar addu'oin ku bisa rashin abokiyar aiki da mukayi ECCD co-ordinator ta KIRIKASAMMA LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE muna rokon Allah s.w.a ya jikaanta yayi Mata Rahama yasa Aljanna makomarta tare da Iyayen mu da sauran Al'ummar musulmi Baki daya ya Raya abinda ta Bari ya Albarkaci bayanta.
______ Misalin karfe uku da rabi jirgin sun Mahmud ya sauka a DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT (DXB) cikin amincin Allah, yana cikin kusan rukunin mutanen karshe a fitowa, yana sanye da suit ash colour na kamfanin Armani hannunsa sanye da ogogo Rolex, baya tare da komai sai jakar laptop dinsa a hankali yake gangarowa cikin takunsa na cikakken namiji me ji da lafiya da karfi, direct gurin da taxin airport suke ya nufa, baya bukatar asan yazo garin so yake ya tantance wata jimurda da aka hada, taxin ya shiga saida sukayi balance a titi sannan ya fadawa direban ya kaishi JW moritte marquis hotel cikin harshen larabci,sunyi tafiya mai tsayi kafin su karaso hotel din, bashi da matsalar kama daki dan tun yana china yayi booking din dakin ta online, katin dakin kawai ya karba ya koma waje yin 'yan uzurirrika daga baya ya nufi ciki, wanka ya fara kafin yayi order abinci, sai da ya gama komai sannan ya kwanta dan yayi matukar gajiya, yaso kwarai ya kira 'yar gidansa amma yana son su tattauna sosai, sai yanzu yake jin haushin wani ra'ayin nasa badan haka da suna tare da ita suna hutawarsu, yanzu kadaicin rashinta da be dameshi ba, wlh da beyi alkawari ba da visa zesa ayi mata ta sameshi a nan saboda hotel din yayi masa, yana daga cikin lattest hotels na duniya be taba sauka a wani hotel ba a dubai sai BURJ AL ARAB JUMAEIRAH dakinsa parmanent ne duk mai hulda dashi a dubai nan suka sani, duk da yana da gidaje a kasar shi be fiye son yakai abokanin bussiness dinsa gida ba. Wannan shigar ta sirri ce shi yasa ya canza sheka baya son asan ya shigo kasar mamaya sake son yakai wasu gurare, yanda har ya gama abinda yake yabar kasar wani be sani ba duk da abune