Showing 102001 words to 105000 words out of 122700 words

Chapter 35 - Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

589

yayi min text Wai an wuce dake Asibiti, kinsan kuwa yanda hankalina ya tashi? Daman kina yin irin hakan ne ko yanzu ya Fara Miki?".
Dan walainiya tayi da idanunta tana fadin " Naji fa sauki Daman inayi kawai wannan ne yayi min tsanani sosai, amman tunda akayi min allurai da drip na warke, kaga ai ba sai munje Asibtin Malam din ba ko?". Wani kallon Baki da lissafi yayi Mata, shi Yana can ya kasa tsugun da ransa ita Kuma tana fada masa wani shirme.
"Zuwa can ba fashi, kuma da izininwa Kika taho gida jinya kin tambayeni Zaki zo gida?" Narai narai tayi da Ido abinda ke tsuma shi kenan yaji Yana neman sakin layi.
"Kai Yaya wallahi na fada maka Zanzo gurin Ammah Kuma ka amince kace nazo koka manta Ranar da zaka tafi?" Ta fada a shagwabe tana zubawa Masa sexy eyes dinta da suka Kara wani hasken wahala data Sha.
"Kawai dai kin min wayo tunda kin fini sanin takan duniya kin fini ilimin boko me zurfi shine zakiyi min education, haka ake cewa ko?".
Shiru tayi Masa.
"Kiyi magana Mana nifa bana son Shiru sai Naga kamar jikin ne"
"Nifa na fada maka na warke sai wani jikon Kuma".
Zaro Ido yayi Yana Mata kallon mamaki.
"Sai wani jikon kamar Yaya? Kenan har kina tunanin Zaki qara fuskantar wani ciwon bayan wannan?".
Kai ta gyada Masa alamar Eh.
"Pls talk ki bude Baki kiyi min bayani as how kike expecting Zaki Kara irin wannan ciwon?".
Sai da ta kauda kanta ta daina kallonsa sannan tace Masa.
"Nifa each and every month sai nayi wannan ciwon".
Ta fada tana Kara juyar da kai.
Cikin damuwa yace. "Pls juyo muyi magana Ina son sanin yanda ciwon yake ne Zan fadawa wani doctor Kinga ai saina San komai kafin na fada Masa yanayin ciwon"
Cikin Jin kunya da nauyinsa tace. "Nifa idan zanyi period ne nake yin ciwon cikin Baya sauki sai anyi min doclofenic injection yake denawa".
"Ok, to idan period din yazo Kuma shike nan baya Kara ciwon?".
Kai ta gyada masa. "Ki cire hijabin Naga yanda Kika rame tunda Nima daba ciwon nayi ba na rame lokaci daya dubi yanda nayi Rama? a lokaci aiki ma zanyi amma na kasa tabuka komai".
Rufe bakinta tayi cikin mamaki tace.
"Dan Allah ka daina haka ka manta a dakin Ammah fa nake idan ta shigo fa ta ganni a yanda nake me kake son na fada Mata?".
"To ya za'ayi Kenan Ranar data ganki da ciki Kuma a jikinki tunda kina kunyar taga muna video call ba hijabi kamar Wanda ta aikata alfasha Allah idan na dawo dole asan abinyi na Fara gajiya gaskiya sai ragaita nake kamar marayan da bashi da uwa, alhalin Allah ya Gama min sutura, koba haka ba?".
Shiru tayi Kamar ruwa ya cinyeta idan ta biye masa kunya ze Bata tunda taga alama Yana neman fitsare idanunsa.
Jin tayi Shiru yasa Shima ya bar zancen ya koma Kan batun tafiyar su Asibiti.
"Goben idan Allah ya kaimu magaji ya kaiki ki dauko wayarki tunda tana gida ki dauko Yan abun bukata tunda sai kun Gama komai kafin ku dawo wata Kila zaku dauki lokaci ba'a Gama gwaje-gwajen da zasuyi Miki ba, itama wannan Matar ta dauki abinda ya Kanata nata saiki fada Mata".
Sun Dade suna wayar har Ammah ta wuce part din Abba Basu Gama ba, sai kusan Sha daya ya hakura sukayi sallama.
Da safe tunda wuri Ammah ta saka magaji yakai Zilai gidan ta karkashe kayan electronics, ta cire duk abinda ake ganin ze iya lalacewa ta Mika gidan maman junior bisa Umarnin Ammah.
Karfe bakwai da rabi Mai kyau su zilan sun koma gidan Ammah da kayan Zahra a jaka set biyar da sauran tarkace na bukatar yau da Kullum.
Sam Mama Bata da labarin kwanan zahrar a gidan Sai da zilai ta shigo da Kaya a hannu magaji Kuma karamar luggage a hannunsa da sauri ta aje bowl din dake hannunta ta nufo Zilai tana fadin "lafiya kuwa daga Ina haka zilai?"
Gaishe ta zilan tayi tana fadin "munje mun daukowa Zahra kayan sawarta tunda Bata koma gidan ba Nan muka kwana daga asibitin gida mukayo". Ikon Allah wallahi ban sani ba, Babu Wanda ya fada min tun daren, Bari na shiga Naga jikin nata".
Suka nufi part din Ammah.



✨✨✨

AUREN HUCE HAUSHI

✨✨✨

MAMAN FATEEMAH.

Page 37.


_______Cikin wani irin takun Jin Dadi da karsashi Mama ta shiga parlourn Ammah tana fadin "Ina patient din take? Ashe nan Kuka kwana jikin ne yaqi Dadi bayan mun taho? wlh ban sani ba sai yanzu da naga zilai ta shigo da kaya ta fada min". Ammah ce ta fito faga kitchen din part din ta tana fafin "ko daya sangarta ce kawai Wai kada ciwon ya tashi cikin dare, kamar an fada Mata a Nan din ciwon baze tashi ba".
Dan murmushi Mama tayi "ai kinsan yanda take da son gida ai inaga idan sun dawo ma saita zauna a nan din tunda ba'a San ranar da mijin nata ze dawo ba gara tana kusa tunda Naga alama ba wani iya riqeta zeyi ba da farawa da iyawa, Allah ma yasa Bata da juna biyu ai da abun yayi yawa ga zawarci ga goyo".Dan Jim Ammah tayi Dan da gaske maganar ta doketa wane irin mugun fata ne haka bako kawaici gurin fadin maganar.
"Allah ya rufa asiri, duk abinda Allah ya tsarawa zahra Zan karba da hannu biyu ba komai, idan Allah ya hukunta Mata rabuwa dashi bani da tsimi bani da dabara,kinsan shi dare ga Mai rabo hantsi ne, fatan da muke dai Allah ya rabata da wannan ciwon me bibiko".
Zahrar ce ta fito Shar da ita cikin doguwar Rigar material Baki da pink din flowers manya ta saka gyale medium a kafadarta tana baza kanshi kamar anyi barin turare a jikinta a hankali ta shigo cikin takunta na rausaya tana amsa wayar sajida wadda ta kirata tana dubata da jiki.
"Ke kuma waya fada miki bani da lafiya?" Zahra ta fada tana Zama kusa Auta da yake breakfast ze tafi school.
Tunda zahrar ta shigo idanun mama ke bin zahrar da kallo.
Wayar taci gaba da amsawa tana fadin "jikin fa da sauki kawai shine yake ta bankama abun kema fa kinsan ciwon tun Mana kazaure shi ne fa yaketa faman tsallen tsinka tsimma akansa".
Ta fada tana dariya kasa kasa.
"Amma Baki da kirki mijin naki ne me tsallen tsinka tsimman? Saura kadan nayi Miki tawaye bestie irin wannan cin fuska haka?".
"Sai anjima Zan kira".
Ta fada a hankali duk da Daman idan ba Kuna kusa sisai ba bazakaji abinda take fada ba.
Sai da ta kashe wayar sannan da dubi inda Mama take zaune ta Dan rankwafa kada daga zaune tace
"Mama Ina kwana?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa tana fadin "ya jikin duk da dai ba alamar ciwo a tare dake, Banda son yawo Ni banga abin tafiya har Kano ba akan ciwon mara na Mata".
Badan Ammah ta jawa Zahra layi ba da Babu abinda ze Hana ta bawa Mama amsar maganarta ba to ba Hali sai zilai ce ta magantu "To Mama tunda yace taje a duba lafiyar ta ai dole taje tunda da gaske Yana cikin damuwa".
Dan tabe Baki tayi tana fadin. "Ai kam sai kuje nasan dai rabe-rabe zakuyi a gidan uban gidan nasa".
Duk abinda ake Ammah najin su amma ko kallon su batayi ba, haka zilan ma Bata Kara fadin komai ba ta fice daga parlourn.
Hamza ne ya leko parlourn ya gaishe da Ammah tunda sun gaisa da Mama, Zahra ta gaishe shi Ya amsa yana fadin "ya jikin naki? Ku fito inji Abba zaku wuce kanon".
Ta amsa da "to Yaya, jikin da sauki nafa ware wlh, kawai dai".

"To Allah ya Kara lafiya".
Ya juya ya koma.
Zilai ce ta shigo da sauri tana "Ammah zamu tafi ayi Mana addu'a".
Dan murmushi tayi "Allah ya tsare ya bada lafiya".
"Allahumma Amin".
Gurin Ammah Zahra ta karaso a hankali ta rungumeta kamar zatayi kuka, zamu tafi Ammah saina Kira idan munje kada ki Kira Aunty Hasana tunda Bata Dade da tafiya ba, Allah yasa ma gobe zamu juyo gida wallahi bana son zuwa nifa".
Bayan ta Ammah ta Dan shafa tana fadin "kuje ba komai In Sha Allah za'a dace a gano menene matsalar tunda suna da Qualified Gynecologist doctors, Allah ya tsare hanya".
Kai ta gyadawa Ammar ta saketa ta koma ta dauki hand bag dinta sai lokacin tayiwa Mama kallon Ido cikin Ido.
Zamu tafi Mama sai Allah ya dawo damu". Tayi gaba tana rike da hannun Musaddiq sukayi waje, Bata bi takan abinda mamar ke fada ba, da sauri mamar ta rufa musu baya ko sallama batayiwa Ammah ba, wani lokacin Ammah tana mamakin yanda Mama ke nuna tsana da hassada akan Zahra idan abin ya taso Mata Bata iya hiding dinsa dole saita nuna an gane.
"Allah ya raba na gari da mugu li'ilafi quash".
Ammar ta fada tana komawa kitchen inda take kokarin hadawa Abba break fast.
Zahra na rike da hannun Musaddiq suka fito compound din.
Mama na fitowa sukayi kicibus da sahura da sauri ta kyara Mata tabi Zahra a baya, ta nufi part dinta ita Kuma sahurar tabi Zahra da sauri.

Ganin Abba a harabar gidan ya hana sahura garasowa gurin zahrar dole taci burki a gefen second gate din. Zahra gurin Abban ta nufa Yana ganota ya Fara fadar "Masha Allah! Uwata jikin yayi kyau, ya kika kwana?".
"Da sauki Abba, Ina kwana?"
Ta fada tana tsugunnawa kusa dashi.
"Lafiya kalau Aina leka dana dawo daga masallaci akace Baki tashi ba".
"Eh Ammah ta fada min, nifa Abba dama hakuri akayi da zuwan Nan nafa warke ba inda yake min ciwo yanzu".
Sameer ne ya shigo da alama daga wurin Baba Malam yake Dan harda Habib suka shigo, gurin Abba suka nufo Habib ya gaishe da Abban sannan Zahra ta gaishe su shida Sameer din suka dubata, mikewa tayi suka nufi inda Malam Bala direba yake jiran Auta su tafi makaranta, sai ya shiga ya zauna sannan Zahra ta bashi 1k, tace ga kudin chocolate Nan idan ka dawo Ammah zata baka wasu na saka Aunty zulai ta debo maka".
"Nagode Aunty Allah ya sauwaqe Miki Zan Miki addu'a idan nayi sallah, malam Bala ne ya karaso suka gaisa da Zahra ya tada motar suka fice Musaddiq Yana daga Mata hannu.

Ta juyo kenan ta hango zilai da sahura sun nufi gurin su Abba suna gaishe su sannan Habib ya karbi key din motar suka zuba kayan dake hannun su.
Sallama su Sameer sukayiwa Abban suka nufi gurin motar, zahrar ce ta dawo gurin Abban tana fadin "zamu tafi Abbana ayi Mana addu'a"
"Allah ya tsare hanya uwata ya Baki lafiya yasa daga wannan zuwa Asibitin a samu warakar wannan ciwon".
"Amin Abba nagode mun tafi sai nu dawo" ta juya ta nufi motar.

Har gurin motar Abban ya karaso Yana musu Addu'a da fatan sauka lafiya.
A hankali Sameer yayi kwana ya nufi gate din fita Abban Yana daga musu hannu, haka ma Ya Hamza shima Saida yaga ficewarsu sannan ya koma side dinsu, sunzo fita Sameer ya dunkulo kudi yaba Mai gadi cikin murna ya Fara jero Masa Addu'oi da fatan Alkhairi har yayi Dan nisa suna jiyo muryarsa.
A wurin gidan sarki Habib ya sauka, sukayi sallama da Sameer yayiwa zahra sallama da fatan samun lafiya Mai dorewa, yayi gaba zuwa ina zaya.
Sun mika a tafiyar sosai Sameer ya Dan juyo kadan Yana fadin.
"Madam tun jiya nake Kiran wayar ki ba'a dauka".
Dan kwantar da Kai tayi jikin seat din tana fadin. "Wallahi rabona da wayar tun jiya da safe a gida na barta lokacin Ina Zan iya tunawa da wata waya Ina tunanin ko ranar karshen ce tazo, sai dazu da Aunty zilai ta dauko min nabi wasu missed calls din kafin na Kira taka number din ya Hamza ya shigo yace kazo mu fito, na gode kwarai da kulawar ka Allah ya Raya Mana babyn mu". Ta fada tana Dan murmushi.
Shima murmushin yayi tana fadar "wato baby kadai Zaki tambaya Banda mamansa wato saboda sunan mijinki ne son Kai ko?.
Hannunta ta saka ta rufe fuskarta.
Dariya zilai tayi tana fadin tuba muke Yallabai ai baza'a Fara haka ba, gani tayi baby shine bako".
"Kin Kare ta dai kawai Aunty".
Tafiyar awa biyu da minti Arba'in da biyar suka shigo Kano.
Suna area mariri Sameer ya lalubo Rukayya.
"Da fatan komai yayi yanda akeso ya zama ready ko?"
Sauraren amsar da take fada Masa yake, kafin yace "ok mun shigo ki Kira mommy tasa salmanu ya kawo iya Rahane yanzu".
Bai jira abinda zata fada ba ya kashe Kiran.
Wani Kiran ne ya shigo masa, shima dai yana da alaqa da zuwan nasu duk dai zahrar naji tayi mamakin Yanda Sameer yake magana cikin ladabi irin haka to shida waye yake wayar Wanda ya jibinci lamarinta haka? Wata qila inda sukeyiwa aiki ne suka dauki nauyin zawa Asibitin nata, haka ta ringa sakawa da kwancewa, shi Kuma Sameer shiga can kurda can har suka shigo Nasarawa G.R.A sultan road.
Tunda suka shigo Kano zilai ke baza idanu, Tana bawa idonta abinci, ita fa zilai duka zuwanta Kano baifi sau uku ba,
Shima Ammah take yiwa rakiya idan wani uzurin ze kawota.
Gidaje ne na garari take gani da ban mamaki yinsu ake kamar baza'a mutu a barsu ba, tana ganin gidajen da take mu'amala dasu sun Kai sun kawo Amma yanzu sai take ganin tamkar akurki ne kan wadan da take gani Bata gara sarewa ba Saida taga gidan da Sameer ya dosa, take hantar cikinta ta kada, innalilllahi takeyi a zuciyar ta, Nan da nan jibi ya Fara karyo Mata Daman tana mamakin gidan da zahrar ke ciki na can Azaren to kuma saiga wani, duk da Bata San mamallakinsa ba, wata Kila karar kwanace tasa ta biyo zahrar irin wannan gidan da sai ayi dambun Naman ka na waje baiji ba.
Kofar wani mahaukacin gate ya tsaya yayi horn sau biyu aka bude suka shige.
Ba zilan ba ita kanta Zahra ta sare da lamarin gidan Dan tasan yes Sameer masu kudi ne ko kungiyoyin su suna sakin kudaden aiki kamar ba gobe amma Bata taba tunanin ya mallaki irin wannan mahaukacin gidan ba. Dan da gani ba tambaya mamallakinsa yaci ya tada Kai. A kofar parlourn ginin da yafi ko wane tsaruwa da kyawun gani ya tsaya yana hamdala ga Allah s.w.a.
Wata matashiyar buduruwa ce ta fito daga parlourn cikin rigar atamfa fitted tana takun yanga da gayu ta nufo motar tana fadin "sannunku da zuwa, Amma wallahi I am very surprised Dana ganka yanzu".
"Rukayya Kenan kin dauka Ina Miki Wasa ne idan Kinga banyi driving ba nine bansa kaina ba".
Dariya tayi "ai na yarda Kuma nasan wannan assignment ne me mahimmanci a gurinka".
Fitowa yayi Yana fadin "yauwa sannunki da kokari, kuma haka ake tarar Baki a garin ku? kinzo kinata surutu kin tare Mata kofar fita".
"Oh! Sorry" ta fada tana budewa Zahra kofa duk da Bata ganinta sosai saboda tintac glass ne a motar.
Dan matsawa tayi ta bude Mata kofar, kanshin da yayi Mata sallama ne yaja hankalin Rukayya ta kalli kofar lokacin Zahra ta sako kafarta daya Kan fuskar zahrar idanun Rukayya suka sauka.
"Kam bala'i"
Rukayyar ta fada a zuciyar ta "wacece wannan din Kuma? Tun jiya lokacin da ya Sameer ya aiketa shopping na abubuwan amfanin gida da kayan Mata ready made take Masa kwawar ya fada Mata na waye? sai dai yace Mata wata ce Zaki ganta yarinya ce ko sa'ar ki Bata kai ba yayanta ne ya hada su ya kawota Asibiti, sai oga yace a sauketa a gidansa har su gama da asibitin.
Rasa wane yare Rukayya zatayi Mata tayi saboda tasan wannan ko zo da hausa Bata sani ba duk da shigarta ta hausawa ce. Aunty zulai ce tayi magana lokacin data fito "haba yallabai Ina laifinta gashi ta fito ta tarbe mu".
Dan murmushi zahra tayi lokacin data fito daga motar gaba daya ta kalli Rukayyar tana wani smile Mai daukar hankali tana fadin "sannu Aunty mun gode" ta fada tana mika Mata hannu, ba Karamin mamaki Rukayya tayi ba Jin zahrar na zazzaga tsantsar hausa bako gargada. Bangaren Sameer zahrar ta kalla tana fadin "Haba oga Ina laifin Aunty na ko wannan fitowar da tayi ai shima Yana cikin entertaining ne mun gode".
Ta fada lokacin data rike hannun Rukayyar.
Sai lokacin zilai ta Dan samu Peace of mind ganin Rukayya tasan dai da alama gidan bana macuta bane duk da ba tana zargin Sameer bane,yau din ce wata iri baka saurin amincewa da mutane.
"Sannunku da hanya".
Rukayyar ta fada tana kallon Zahra, yayin da Sameer ya shiga motar ya nufi parking lot ya ajeta.
"Yau Aunty mun gode"
Zulai kuwa sai kalle kalle take tana jinjina girman gidan Dan wasu gine - gine take hangowa na Alfarma ga shuke-shuke Nan sai wani sanyin kamshi ke tashi a gidan ko Ina Kuma tas ba alamar datti a cikin, dukiya dai Mai sunan dukiya an kasheta a gidan Nan.
Ita tunda uwarta ta kawo ta duniya Bata taba shiga irinsa ba, sai yau da dalilin uwar dakinta Zahra ya kawo ta.
Maganar Rukayya ce ta dawo da ita cikin hankalin ta.
"Bismillah mu shiga daga ciki".
Rukayyar ta fada tana nufar kofar parlourn numbers ta daddanna ta bude musu kofa ita dai zilai yau jinta take kamar ba cikin kasar take ba.
Lokacin da suka shiga parlourn ba zilai ba kifin rijiya ita kanta zahrar sai da wani shock ya shigeta na wucin gadi, badan Zahra tana fita waje ba Kuma kakanninta masu dashi ne kuma tayi zaman syprus taga guraren hutawa da yawa da gidajen Alfarma da Babu abinda ze Hana ta zabga kauyanci, dan Babu karya naira tayi kuka a cikin parlourn Nan tamkar fadar sarauniyar ingila komai na ciki off-white ne da sirkin ash colour ba tarkace da yawa sai dai an kawata shi da wasu irin cutains masu azabar kyau dan shi kadai abin kallo ne, sai fremes masu kyau da tsari da wasu irin flowers, sai wani special kamshi daya hadu da sanyin A/C ya bada yanayi Mai dadi, sai plasma kusan bango guda.
Zilai dai 'yar kauye sak ta koma ko Zama kasayi tayi sai da Rukayya ta juyo tace Mata Bismillah ki zauna Mana ku Sha ruwa".
Ta fada tana yin gaba ta nufi wani steps gurin dining table ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login