Showing 93001 words to 96000 words out of 122700 words

Chapter 32 - Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

599

mawuyaci hakan ta faru.
Barcinsa yasha sosai dan har akayi sallar magariba be sani ba, lokacin daya tashi ana gab da kiran sallar insha'i, a gurguje yayi wanka ya zura sabuwar jallabiyar daya saya cikin kayansa a kasar, a cikin dakin yayi sallar magariba ya fito yabi lifter zuwa masallaci,koda suka idar da sallah be dawo daki ba a nan harabar hotel din ya Zauna da gaske yanayin gurin ya burge shi sosai, coffee yayi order ba'a jima ba wata matashiyar balarabiyar yarinya ta kawo masa coffeen sai yaga kamar 'yar gidansa, nan da nan yaji duk rintsi ita yake muradin gani number dinta ya lalubo ya kira duk ba baya son kira direct yafi son ta Whatsapp.
Suna zaune a parlour ita da zilai tana Shan mutuniyar tata farm fresh, Kira ya shigo a wayarta dake kusa da ita, tayi mamakin ganin code din Dubai har sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, batayi magana ba Shima baice komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa zilan Fadin "naji kinyi shiru koba Kira bane".
Karamin tsaki Zahra tayi "wlh na daga amma naji shiru inaga ko wrong number ne dan code din na Dubai ne ni kuwa waye ze kirani daga Dubai da dai Aunty Nawwara Bata saudiyya da saina dauka ko sunje ne da mijinta tunda business man ne, Bari na kashe wata kilama ba'asan an Kira ba"..
Kafin ta dauke wayar daga kunnen ta taji yayi magana cikin husky voice kada ki kashe min waya, ki bude data zamuyi magana". kit ya kashe Kiran wayar tabi da kallo a zuciyar ta tana Fadin "ikon Allah shine Kuma a Dubai ya illahiy, to Wai wannan Dan talikin waye shi lamarin fa Yana neman Zama abin tsoro fa, yace Yana yiwa kungiyoyin waje aiki ita Kuma a gefe guda wani Abu yake yi irin na Mai bada umarni Kuma bataga yanayi gaban kowa ba sai ita, kamar Ranar da taji yana Kiran zayyan da umarnin daya Bashi akan lallai ya sameshi da safe Kuma Bai karya Umarnin ba"
Wayar ta kalla tana mikiwa zuwa bedroom dinta Saida ta shiga ta duba data idan Babu ta saka tunda Sam Bata taba saka data ba tunda ta Fara amfani da wayar datar data gani tayi bala'in Bata mamaki 4.5 BT ta gani sub din shekara daya ne.
Cikin sofa ta zauna Tana juya wayar Bata bude datar ba, wani Kiran ne ya sake shigowa still dai nashi ne, dagawa tayi tana fadin Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, meya hanaki bude datar danace a bude?"
Shiru tayi ta kasa magana,.
"Wai ko sai nayi ramuwar sayen bakin da banyi bane ake min jan aji irin haka. Dan Allah kimin magana kona samu nutsuwa wlh ji nakeyi Kamar na gudo tun ba'a gama ba duk kin mamaye ko Ina na kasa komai sai tunanin ki, Ni danasanin zuwan ma nakeyi gashi sun rarraba mu wasu suna London mu kuma suka kawo mu hadaddiyar daular larabawa, shine nace Bari na kira na fada Miki Koda abinda kike bukata na taho Miki dashi tunda da kudinki a gurina"
"Kudina kuma? Name nene kuma yaushe na baka".
"Bake Kika bani ba ke aka bawa na manta na Baki Sai a Nan na tuna danaga Kaya irin naku na 'yan Mata".
Ya fada Yana dariya.
"Wai 'yan Mata".
Ta fada tana Dan turo Baki irin bataji dadin Nan ba.
"Au ashefa an wuce wannan stage din ko?"
Ya fada da alamun zolaya.
"Wato kinki bude data sai kin cinye min 'yan canjin da aka saka Mana kinsan dai ni ba iya saka Kati zanyi a kasar Nan ba, pls Dan Allah ki bude datar na ganki kona samu nutsuwa nayi aikin daya kawoni, naso ace kina gefena a wannan gurin Kinga dakina kuwa? da Hali gareni anan zamuyi honey moon irin Wanda naji su Habib suna fada idan ana hira ko Zaki biya ki taho ki sameni?"
Ido ta ware kamar Yana kallonta.
"Na biyoka nayi maka menene?"
"Kiyi min abinda mace take yiwa mijinta ai kin gane?".
"Ya Salam haba Ya Mahmud menene haka kaifa yayana ne".
Wata dariya ce ta kubce Masa "A yaushe na zama Yayanki? Ki gyara zancen niba Yayanki bane, haka kawai ki haramta min abinda Allah ya halasta min idan Zaki Ware ki Dan ina dawowa labarin ze canza salo gara mu fuskanci juna ki tausaya min Kinga Sameer fa ya Zama Daddy madam dinsa ta haihu sunyi min takwara,ai gara muma mu zage dantse ko?"
Dokin haihuwar da aka fada Mata ita ta Hana ta gane inda nasa zancen ya dosa, cikin nuna farin ciki tace "Dan Allah da gaske yaushe Fateehar ta haihu? Masha Allah! Allah ya Raya kace mu sai Kano ko Yaya?".
"Allah bakinki ya kiyayi fada min yayan Nan tsabar kinibibi kawai yau Kika tashi dashi Wai wani Yaya kamar a kauye, kibar 'yan garinmu su Fadi Amma Banda ke wato Ni da yake ba Dan bokon kirki bane ba baza'ace min sweetie ba ko irin su my love ko Dear, saboda almajirin soro ne ni ko?"
"A'a wlh ni ban fada ba, kawai dai Naga abokin Ya Abdul Hakeem ne kai ai kaima yayan ne".
"To anki wayon, Kuma da kike cewa Zaki Kano ganin yaro keda wa zakuje kuma waye ze kaiki Kuma kice Mata wacece ke".

"Address zata turo min Mana, Kuma maganar kaiwa sai Malam Bala direba kaimu nida mujiba wuni daya dai, Kuma nace Mata matar yaron mijinta ce ko ba haka ba?
"Yayi Kam Amma saina dawo ki rakani muje tare anfi saurin ganeki ga kafarki ga tawa, kice na sawo Miki kayan baby na zuwa barka kenan? ko kema a hado Miki kayan naki babyn? tunda da karfina Zan dawo wata kilan ni double shoot ma zanyi tunda Nima Dan biyu ne Ina da twins sister Aishat".
"Twins sister da gaske?"
"Kin taba ganin nayi Miki karya? wlh mu biyu Ammin mu ta haifa first born dinta, mun B'ata ne da ita shiyasa bakisanta ba. Amma nan gaba zaki santa ne Amma fa Zaki Sha surutu Dan sister Aishat parrot ce".
"Amman laifin me tayi maka da zafi haka? Mu namu twins din basa doguwar batawa gaskiya gashi kaima Ammin irin na Ammah tayi mace da namiji".
"Ki Bari kawai labarin da tsawo sai na dawo ai nace Zaki San duk labarina kaf ba abinda Zan boye Miki tunda kin sarkafo min zuciya tun kina free matured dinki Kika Hana duniyata zaman lfy,da farko na dauki irin mutum ya burge ka ne Ashe diban Karan mahaukaciya Kikayi da gudan tsokar kirjina".
Dariya maganarsa ta bata.
"Au dariya ma kike min ko? bayani zakiyi da yarenki, yanda nayi ta fama da garari saina fanshe kayana tas idan Zaki shirya ki shirya".
Cuno Baki tayi kamar tana gabansa ta Fara turza kafa tana fadin "Ni yaushe kaga Ina maka dariya kawai dai... ni banyi maka dariya ba kaifa yayana ne koka manta my big bro....." Ta wani ja cikin salon da ita kanta Bata San tayi ba.
"Ya salam" ya fada a hankali Dan yanda tayi magana har cikin bargonsa.
"Kinaso ki karya min budget ko?"
Ya jefa Mata tambayar.
"Wane irin budget Zan karya maka kana Nan Ina Nan".
"Idan kina min irin haka ai sai kisa na saki layin Dana hau na tattaro ya nawa ya nawa ko komo gida ko ba'a gama ba".

"To me nayi daga magana tom shike Nan sai anjima".
"Wlh Kika kashe min Kira sai kinzo Dubai ko a kafa ne kuma saina yi Miki abinda bazaki manta ba Dan tarihi me kyau Zan kafa Miki ki kashe ki gani, muna hira kina bani nutsuwa Zaki gudu nida ake yashewa Yan canjina Baki tausaya min ba shine Zaki tsere ki barni da Mata masu farauta ta ko? Yanzu haka guda uku tun dazu suke shawagi a gabana suna tunanin irin nasu ne Dan hannu".
Gyara Zama Zahra tayi kirjinta ba dukan tara tara bama uku uku ba.
"Mata kace ko me?"
"Eh Mata Mana bake kina min rowar ganin halalina ba to gashi Nan free sai Wanda yayi maka ka zabi son ranka, ba nace ki bude data na kalli kayana ba Amma kika Kiya Kinga kuwa yanzu saina duba na darje na zaba ta rage min dare, koya kikace my previous?"
Ya Dana Mata kiss ta cikin wayar ya kashe abarsa.
Yana fadin gobe ma idan bace ki bude datar ki qiya, saina kowa Miki kishina ba gaske kafin na kaiki Ina zakiyi da hujja Amma ki shiga yanzu ai Africa ce da sauran gyara.

AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATEEMAH

PAGE 35.


________Yana katse Kiran ya tashi tsam ya nufi masaukinsa laptop dinsa ya janyo ya shiga aiki sai kusan karfe daya ya kwanta lokaci bayan lokaci sai yayi murmushi idan ya tuno yanda suka rabu da 'yar gidansa yayi zance mata tana neman tikitawa kanta lissafi Wai ita me miji, kamar ta wani san dadin mijin,Saida yayi wanka yayi nafila sannan ya kwanta.
*
Zahra kasake tayi da waya a hannu kamar itace Mahmud din "me yake nufi da zasu rage Masa dare kenan neman Mata yajeyi?"
Take wata zuciyar tace Masa A'a Yana zolayarki ne da manemin matan ne koda karfin tuwo saiya nemi wani Abu a jikinki, kauda wannan tunanin tayi daga zuciyar ta tasan zato zunubi ne, parlour ta koma gurin zilai sukaci gaba da hirarsu sai kusan Sha daya suka shiga ciki.
Washe gari Zahra Bata tashi da wuri ba sai kusan Sha daya, tun cikin dare bata Jin Dadi wata irin murdawa mararta ke Mata, tana samun irin wannan pain din duk karshen wata idan zatayi period Amma wannan yanda yake mata yayi tsanani sosai tun wurin karfe ukun dare ciwon ya tashe ta farka a gigice, inda Allah ya taimaketa Bata sakaci ta rasa maganinta duk rintsi Yana tare da ita, a lokacin ta sha cikin ikon Allah lokaci kalilan ciwon ya lafa ta koma barci da Asuba ma data tashi sallah da sauki sosai sai Kuma yanzu data farka taji Yana neman dawo Mata, da kyar tayi wanka ta sake inner wears ta zura rigar matarial marar nauyi ta koma ta kwanta idan tana wannan yanayin ko turare Bata so sai guda daya kawai body mist ne na strawberry shi ta fesa ta koma ta kwanta Dan abinci dai baya ciyuwa a irin wannan yanayin.
Ganin Sha biyu tayi Zahra Bata fito ba yasa zilai nufar bedroom din nata ta gani anya lafiya kuwa?
Knocking tayi taji Shiru ta qara you taji Shiru Bata kara ba uku ba ta tura kofar a can tsakiyar gadon ta ganota a kudundune, da sauri ta karasa gaban gadon tana ambatar sunan ta "Zahra kafiyarki kuwa har Sha biyu ta gota Baki tashi ba abin Karin ki har ya Fara sanyi?"
Da kyar ta dago ta kalli zilan cikin miryar marar lafiya tace Mata "bana Jin dadi tun cikin dare marata take ciwo".
"Subahaballahi Kuma Kikayi Shiru Baki fada ba idan haka ne bani da amfani Kenan ace tun cikin dare kina fama da ciwo ki kasa fada mini, ina maganin da kike Sha yake na dauko Miki Ni wlh cewa nake tunda ance idan Kikayi aure ze dena, to na dauka kin rabu dashi yanzu, ai haka wannan likitar ta fada Miki zuwan mu na karshen ko?".
Kai Zahra ta gyada Mata kawai alamar Eh Dan ita kadai tasan azabar da takeji.
"Fada min Ina maganin yake na dauko Miki"
A hankali tace mata "Na sha".
"Kin sha Kuma marar Bata Dena ciwon ba?"
"Eh" ta fada tana runtse ido saboda azabar ciwo.
Fita zilai tayi da sauri ta koma dakin da aka sauketa ta lakubo keyboard dinta ta lalubo number Ammah, lokacin tana tare da Abba suna maganar komawa makarantar Imam Kiran zilan ya shigo.
"Abba Bari na daga Kiran Nan Zilai ce naji ko lafiya".
"In Sha Allahu ma lfy".
Abban ya fada.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu"
Ammah ta fada bayan ta daga wayar daga can zilan ta gaishe da Ammah sannan ta Dora da fadin "wlh Ammah jikin Zahra ne ba Dadi tun cikin dare ciwon mararta ya tashi Tasha maganin Kuma a banza shine nace Bari na Kira na fada Miki Koda abinda zakiyi mata tunda kema Aikinki ne ko Kuma a turo Mana malam Bala ya kaimu Asibiti taga likitar ta" .
"Ikon Allah! Yanzu ina zahrar?".
"Tana daki tana faman mukususu kamar me nakuda wlh abin gwanin ban tausayinsa".
"To shike Nan ki dubata za'a San yanda za'a yi ki jira".
Ta kashe wayar ta dubi Abba Wanda Shima itan yake kallo, kafin tayi magana ya rigata.
"Meya samu Uwata naji Kuna magana Bata da lfy ne?"
Ajiyar zuciya Ammah ta sauke "wlh ciwon mararta ne Wai ta tashi tun cikin dare Tasha maganin da take Sha Amma ba wani cigaba shine zilan tace ko Asibiti zasu koma suga likitar da take gani Dan munyi expecting idan tayi aure zasu rabu to Kuma a yanda zilai ta fada min kamarma yafi na baya zafi".
"Ikon Allah! Allah ya saukake Bari a tura musu magaji ya kaisu Asibitin tunda duk sauran basa Nan sai mu bisu daga baya mu kuma, ai hakan yayi ko?".
Kai ta gyada Masa tana kokarin tashi da nufin tafiya, riko hannunta yayi ya mayar da ita inda ta tashi dayan Kuma Yana Kiran wayar magaji.
"Ka dauki mota kaje can hayin banki zaka Kai uwata Asibiti".
Ya kashe Kiran yana kallon Ammar.
"Ina zaki Kuma Kika tashi? Ki kwantar da hankalinki in Sha Allah ba wata damuwa Kika sani ko jika zamuyi kwanan nan"
Ya fada Yana dariya irin tasu ta manya.
Itama Dan murmushi tayi tana fadin Allah yasa".
"Amin yauwa kokefa dauko gyakenki mu bisu wata Kila muje tare tunda gani a gida araha sai nayi aikin bariki tilas ne".
Zilan Ammah ta Kira ta fada mata su shirya ga magaji Nan ze kaisu Asibitin, Suma zasu samesu a can..
Dakin Zahra zilan ta koma yanda ta barta haka ta sameta, kusa da ita zilan ta matsa tana fadin na hado Miki ko ruwan shayi ne kisha Asibiti zamu".
Kai ta girgaiza Mata alamar bazata Sha ba.
"Ki daure ko kadan ne Dan Allah Kinga wata Kila ayi Miki allura gara kici ko kadan ne".
"Cornflakes".
Abinda ta iya fada Kenan ta koma ta kwanta.
Ba laifi tasha cornflakes din da Dan dama, rolling kawai tayi suka nufi parlour zilai na rike da ita. Basu jima ba sukaji dirin mota alamar magajin ya karaso Kenan, zilaice ta bude kofar tun Bai karaso ba direct inda zahrar ke kwance ya nufa akan two seater.
"Sannu Adda ya jikin naki?"
Da kyar ta cira Kai ta dubeshi tana fadin "da sauki".

"Allah ya Kara sauki, kamota muje kada Rana ta karayi yanzu twenty five minutes to one fa".
Zalai ta riketa tana tafiya da kyar suka fito compound din Zayyan yana zaune Yana game a waya tunda bashi da aikinyi a Nan sai zama,ba zato yaga an fito da Zahra haka, da sauri yayi wurgi da wayar Allah ya taimake kan jacket dinsa ta fada da sai dai wata ba ita ba, ya nufo gurinsu Yana tambayar "Lafiya meya faru? Oga kuwa ya sani? sannu" duk a lokaci daya yake jero wadannan tambayoyin da gani a rude yake.
Magaji ne ya nufi inda yake suka Kara gaisawa Yana farin.
"Ba wani abun damuwa bane Bata Jin Dadi ne zamuje Asibiti kada ka damu".

Zilai magajin ya duba "kun fadawa mujinta kada mu tafi babu sanin sa".
"A'a bamu fada Masa ba ai ko daga bayane an fada Masa yanzu dai muje Asibitin wannan ma wani Bata lokacin ne".
Da sauri Zayyan ya bude musu gate suka fita yayin da Zayyan din ya dauko wayarsa Yana Kiran Mahmud.
Ya kirawo shi Amma Sam taqi shiga sai text kawai Zayyan ya tura Masa ya koma ya zauna yana mamakin ogan nasa na neman gurin Zama a wannan Dan gurin shi ko takura ma yaga alama bayayi wata sabuwar rayuwa yake shimfidawa cikin kwanciyar hankali.

Direct A&E magaji ya nufa zilai ce ta taimawa Zahra ta fito daga mota suka shiga ciki shi Kuma magaji ya nufi inda ze karbo file.
Ba jimawa yazo ya kawo file din, bayan duguwar tambayar da wata likita da take on call tayi Mata ta rubuta Mata magunguna da allurai da drip ana cikin saka Mata ruwa su Ammah suka shigo dakin, ma'aikatan da masu jiyyar suna ta gaishe da Abba, gaban gadon Abban yaje ya tsaya sunan ta Abban ya Kira ta bude Ido ta kalli Abba tana kokarin tashi zaune "A'a uwata koma ki kwanta ya jikin naki?"
"Da sauri Abbana, Ina kwana?"
"Lafiya kalau".
Ammah ce ta matso tana fadin "sannu Ashe ciwon cikin ne ya tashi?"
"Eh Ammah wlh har yafi Wanda nakeyi kamar Zan mutu".
Ta fada tana goge hawayen daya zubo Mata.
"A'a uwata Banda kuka ai kin girma".
Abba ya fada Yana dariya. Itama Zahra dan murmushi tayi ta juya Kai kunya ta kamata ta.

Abba Bai bar Asibitin ba Saida aka Maida Zahra Aminity ward.
Tun bayan tafiyar su Zahra Zayyan ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya nemi number Mahmud tafi cikin carbi amsa daya balarabiyar da akayi linking da computer ke bashi wadda ba fashimta yake ba, sai dai hasashe kawai number Bata tafiya take fada Masa.
A gida Abba yayi sallar Azzahar bayan an fito ne ya fadawa Baba malam Zahra tana Asibiti Bata Jin Dadi.
Cikin nuna jimami Malam yace "tun yaushe take Asibitin ba'a fada min ba, kuma menene yake damun diyar tawa?".
"Wlh ciwon cikin ne take fama dashi tun cikin dare shine dazu Mai Taya ta Zama ta kita Asma'u ta fada mata, sai nasa magaji ya Kai su Asibitin sai suka Bata gado Wai zasuyi Mata hoton cikin da sauran gwaje-gwaje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login