Showing 105001 words to 108000 words out of 122700 words
shige wata kwana.
Zahra zilai ta kalla "Wai Ina ne Nan din Kuma gidan na wanene nifa duk a rude nake na kasa samun nutsuwa ko kadan, irin wannan gidan ai sai sarki ko wani gagarimin Mai kudi".
Da watsa hannu Zahra tayi.
"Toni Ina nasan amsar tambayar taki, Nima duk daya muke dake bansan komai ba, nasan dai yace zamu zauna a Nasarawa GRA kawai ba wani Karin bayani da yayi min". Rukayyar ce ta shigo dauke da babban tray da robobin farmfresh dasu ruwa da Shani na gwangwani, sai fruit fresh ones.
"Bismillah kusha ruwan sai muje ku huta sai kuci abinci".
Sannu Zahra tayi Mata, itama zilan tayi mata, Sameer ne ya shigo da wani matashin saurayi da luggage din Zahra da 'yar madaidaiciyar jakar zilai a hannunsa ya gaishe su ya aje ya koma.
Rukayya ce nufo inda Sameer din yake tana fadin "Ya Sameer Dan Allah ka jirani Zan bada sako gurin mommy ka taho min dashi"
"Kefa Ruky kina da damuwa kiyi Abu Mai mahimmanci sai ki tsaya kina Wasa".
"Allah Yaya da gaske nakeyi ka taimaka min".
"Ok"
Gurin su Zahra ya duba Yana fadin "sannunku madam kun sha hanya ki huta zuwa dare zamu fita Asibitin doctor tace mu hadu da ita a Nan Asibitin Nasarawa zataga patient yau a can da dare saita dubaki idan yaso sai mu hadu da safe a malam din".
"To ba damuwa in Sha Allah Zan shirya da wuri nagode".
Ya juya ya fice daga parlourn.
Zahra tayi mamakin ganin favourite drinks dinta da aka kawo, more especially farm fresh Amma Bata kawo komai ba ta dauki abin arashi ne kawai.
Bayan Sameer Rukayyar tabi suka fice daga parlourn.
Saida suka sauka daga steps din gurin sannan Rukayyar ta dubi Sameer tana fadin "big bro Dan Allah wacece wannan din? Meye matsayinta a gurin Ya Mahmud nasan wlh ba banza ba yace a bude Mata wannan apartment din nasa".
Tsaki Sameer yayi "na dauka want important Abu Zaki fada min Ashe tsabar gulma ce a cikinki, ba abinda yayi Miki zafi a lamarin yarinyar Nan yanda Kika ganta haka Nima na ganta bansan ko wacece dinsa ba tunda baiso in sani ba, Dan haka kada rawar kanki tasa ki fadawa Dr Haseena wani Abu Koda zata tambayeki kice Baki San komai ba".
Tunda ya Fara magana Rukayya tayi zuru tana kallonsa yanda ya kiciccife yasa tayi masa alamar (?) Tasan there's something behind.
Amma fadan dayafi karfinka sai ka mayar dashi Wasa.
Dan jinjina Kai tayi tana fadin shake Nan Bari na koma kada suga an barsu su kadai".
Ta juya ta koma Zuciyar ta fall da tambayoyin da Babu Mai Bata amsarsu.
Lokacin da ta shigo sun gama suna Dan hira.
Cikin bada uzuri Rukayyar tace "kuyi hakuri na barku ku kadai Bari na Fara rakaki naki masaukin kafin na dawo na rakaki Aunty ta fada tana kallon zulai".
"Babu komai muje na shigar Mata da jakar kayanta.
Rukayyar ce a gaba su Zahra suna bayanta, saida suka wuce parlour uku kowanne Yana wane na Bata zulai da abin harya daina Bata tsoro tunda taga abin bana karewa bane, wani corridor ta nufa suna biye da ita wasu steps suka gangara suka shiga, wani parlourn suka shiga Mai azabar kyau fiye Dana baya, kofofi biyu ne a cikin wani arc suna kallo juna, kofar hannun dama Rukayyar ta nufa saka Kati ta bude kofar tana tana fadin Bismillah". Tana murmushi.
"Mu shiga Mana". Zahra ta fada.
"A'a iyakata Nan, dakin na manya ne bani fa hurumin shiga ciki".
Jin haka yasa zilai Jan burki, itama jagabar da tasan ciki da Bai na gidan tana fadin haka inaga ita 'yar karere.
Aje luggage din tayi tana fadin. "A fito lafiya uwar dakina".
Suka juya Rukayyar na fadin Bari muje sai kin fito.
"Ok, nagode.
Zahrar ta fada tana janye da luggage din ta murda handle din da siririyar sallama a bakinta. Bata iya karawa ba taja ta tsaya tana waro idanu waje na mamakin abinda idonta yayi arba dashi...
AUREN HUCE HAUSHi.
MAMAN FATEEMAH.
Page 38.
A hankali ta ringa tafiya kamar wadda ke tsoron kada a kamata, abinda ta gani ne ya Bata matukar mamaki wannan bed room din tamkar an dauko na can Azare na Mahmud an aje a Nan, hatta da curtains din windows din iri daya ne ba banbanci, Abu daya wannan yafi wancen shine girma wannan yafi balance akan wancan, Amma tamkar an dauko shi an aje, ita abin da farko tsoro ya bata hatta kamshin turarensa taji a dakin jiki ba kwari ta dosana ta zauna a gefen bed din tana Kara karewa dakin kallo tabbas a gizo idanunta ke Mata ba abinda ta gani haka yake, bata Kara tabbar da kamshin Mahmud takeji ba Saida ta zauna kamar lokacin ya saka ya fita daga dakin.
Dan dam tayi Jin ta Fadi sunan Mahmud fatsal sai taji wani bambarakwai a bakinta duk sai wani irin Abu ya darsu a zuciyar ta.
A shagwabe kamar tana magana da wani ta Fara fadin "to me ma zance masa ne? Kuma Wai Nan din dakin waye da suke kamanceceniya da nasa har kanshin ba banbanci?.
Ba Mai Bata amsar tambayar Dan haka ta Dan zamo kadan tana janyo luggage dinta tana fito da abinda ke ciki,wanka take sonyi duk jinta take a takure indai tana period sai a hankali sam Bata da sakewa ko misqalazarratin, Banda dole Babu abinda ze sakata barin gida a irin wannan condition din.
Luggage dinta ta janyo a hankali ta Fara fito da abinda ke ciki, na Kan mirror ta Fara diba ta nufi inda yake lokacin data karasa ba karamin mamaki tayi ba ganin irin kayan shafar da take amfani dasu har da wasu daga cikin irin turarukanta ta gani Banda su freshner na fesawa.
Bata fasa aje na hannunta ba, gurin kayan ta dawo ta bude cloth set din data gani tana budewa tayi arba da kayan Mata Babu abinda Babu, harsu shoes da bags, dasu inner wears.
Mayarwa tayi ta rufe ta dawo da kayan a hannu ta mayar inda ta dauko su.
Wanka ta shiga Nan ma wata duniya ce aka hada, ta jima tana gasa jikinta Dan idan Tana irin wannan condition din Bata kaunar abinda ze hadata da ruwan sanyi ko kadan.
Bata wani Bata lokaci ba gurin shiryawar ta saka doguwar Rigar atamfa glitter purple, Rigar tayi Mata das a jiki mayafi light brown ta saka touching din jikin atamfar sai takalma suma light brown din plat, haka nan taji tana son saka turarensa Mai sanyin kamshin Nan dauka tayi ta fesa ta nufi hanyar ficewa daga dakin.
Saida ta fito yanzu ta karewa wannan parlourn kallo yafi duk Wanda ta gani a baya tsaruwa kunjerun dake ciki ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba Bata taba ganin irinsu ba duk kuwa da gidajen Alfarma data shiga ta bangaren Ummee.
A hankali ta ratsa ta wuce tabi hanyar da suka biyo suka shigo.
Ba kowa a parlourn lokacin data shiga sai dai tana jiyo Dan Karan plates haka kamar ana wanke-wanke.
Zama tayi taga ta inda wani ze gitta tunda ita dai ba sanin Kan gidan tayi ba. Wata Mata taga ta fito daga wajen dining ta wata kofa da manya food warmers a hannunta,ta aje a kan table din har zata juya ko jijinta ne ya Bata da mutum a gurin yasa ta juyo tana duban cikin parlourn, Ido suka hada da Zahra da sauri matar da gangaro daga steps din dining din tana fadin "Masha Allah, ko surukar tamu ce ta fito?".
Ta fada tana nufo Zahra dake zauna tana murmushi, itama iya Rahanen murmushi take har ta karaso gurin zahrar.
"Sannu Mama Ina yini"
Zahrar ta fada.
"Yauwa sannu yarinya ya kukazo?"
"Lafiya kalau Alhamdulillahi".
"To Masha Allah, sunana iya Rahane nice mommy ta turo na zauna dake kafin ki gama abinda ya kawoki".
Ta fada tana Dan tsugunnawa a gefen zahrar.
"To Mama na gode, Amma Dan Allah ki daina tsuguna mini kinyi jika Dani idan Ni ban Baki irin wannan girman ba to kema bai kamata ki bani ba, Dan Allah ki tashi"..
"A'a 'yata Allah ne ya Baki Dan na tsuguna Miki Babu laifi".
Kafin zahrar ta samu zarafin Mai da Mata amsa Rukayya ta fito daga inda iya Rahane ta fito ganinta da Zahra yasa Rukayyar ta karaso gurin su tana fadin "har kinyi me?"
"Harna fito Ina Zan iya Zama a wancan lungun Ni kadai kamar mayya ai Naga kokarin matar gidan nan data iya zama a cikinsa, Daman jiranki nake dakin da Kika rakani na matar gidan ne gara ki hadani da zilai mu zauna tunda duka kwana nawa zamuyi mu tafi kada a samu matsala kinsan halinmu Mata da zargi naje na manta wani Abu daya danganci namu na Mata a samu rashin yarda a tsakanin masu gidan Dan na bude cloth set Zan zaka kayana saina tarar da kayanta a ciki Kinga ai Bai kamata na shigar Mata dakin ba ya Zama Bata da sirri kenan".
"Wannan gaskiya ne ranki shi Dade kinyi tunani me kyau a kam".
Iya Rahane ta fada.
Zama Rukayyar tayi gefen zahrar tana fadin ai gidan Mai shi ko auren fari baiyi ba, kayan da kika gani duk nakine bana kowa bane Dan ya Sameer ya bani kudi nayo siyayyar jiya Dan a Nan na yini nida su suhaila Dan furnitures din dakin ma jiya aka sakasu Ina ga ba wata macen data taba zama a cikinsa Banda Mai gidan to kece ta biyu da Kika zauna, bama a dakin yace a sauke kiba dayan yace sai Yaya Sameer yace na Baki wannan ya wadatar kawai.
"Iya aje a fito da sauran abincin sai muje kiyi lunch din tun, shigarki ciki ya Sameer ke kirana Wai kinci abincin Baki da lafiya na tabbar kin Sha magani ni har mamakinsa nakeyi Bai dauki lamarinki da Wasa ba gaskiya".
Iya Rahane ce tace "Haba Rukayya yaushe Alhaji karami Zeyi wasa da lamarin iyalin Mahmud, Nima da Mommy ta kirani Saida ta Kira shi ta fada Masa nice zanzo ya amince kafin Nazo, ya jaddad min na kular Masa da ita yanda ya kamata, Kinga kuwa ai baiyi laifi ba ko?".
Kai kawai Rukayyar ta iya gyadawa mamakin duniyar Nan ya gama kasheta a zaune "matar Mahmud? Haba biri yayi Kama da mutum, tasan ba banza ba ya Sameer keta rawar kafa ya kasa tsaye ya kasa zaune akan lamarin, Kuma da alama itama yarinyar ninketa sukayi ta bai-bai Dan da alama batasan waye hakikanin mijin nata ba, gaskiya ta tayata murna dan ta zama Mai sa'a duk da shima Saida ya dauko diamond a cikin zinarai, Dan Daman wannan irin matansu ne.
Gurin dining din Rukayya tayi Mata jagora suka nufa tana fadin "kice min matar big bro ce Amma nayi mamaki gaskiya sun lullubeni Amma ki Bari kawai bazance naji ba Naga iya gudun ruwan ya Sameer sai wani cewa yake kanwar abokinsa ce".
Ita da zahra Dan murmushi take tunda ba gane Kan zancen tayi ba.
Abinci ne yakai kala biyar Rukayya ce ta bubbude wa zahra tana fadin "Auntyn mu ki zabi Wanda kike so a zuba miki".
"Kaji Aunty ni basai kin zuba min ba haba dadin sai yayi min yawa hakan ma na gode, ina Aunty zilai tazo muyi lunch din".
"A'a nan naki ne ke kadai na Kai Mata nata dakin ta tun dazu".
********
Knocking din kofar akeyi a tana zaune ta Sha uban gayu kamar wadda zata wuri dinner ta biki sai kanshi ke fita a jikinta Mai Dadi tana rike da wayar ta tana addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba.
Umarnin shigowa ta bayar tana kallon kofar, Basira ce yarinyar dake aikin shara da goge-goge a bangaren ta, tsugunnawa tayi tana fadin "barka da Asuba Ammi".
"Barka kadai Basira har kin fito da wuri haka, lafiya dai ko?"
"Lafiya kalau Ammi Daman Hajiya Inna ce tazo ita da Abie".
Littafin ta aje akan bed side tana fadin "Hajiya Inna kuma"?"
Kai Basira ta gyada alamar eh.
"Kije gani Nan fitowa in Sha Allah".
Ta nufi clothset dinta ta dauko gyale mahadin shaddar ta fito daga bedroom din.
A hankali take saukowa daga stairs din shar da ita tun kafin ta karasa saukowa kamshinta yayi musu sallama, cikin takunta na nutsatstsiyar mace Mai aji da yarda da kanta ta da tarin ilimi Hadi da wayewa, sallama tayi musu tana nufar gurin Hajiya Inna ko inda general yake Bata kalla ba.
Kusa da Hajiyar ta zauna lokacin da take amsa sallamar tata.
"Ina kwana Hajiya".
Cikin nuna kauna da kulawa Hajiyar ta amsa tana tambayar ta Ina su uratu Ammin tace Basu tashi ba tunda yau ba zuwa school.
Ammin ta Dan juya bata yarda sun hada Ido dashi ba tace Masa. "Barka da Asuba".
Shiru yayi Mata kamar beji abinda ta fada ba, itama Bata kara bi takansa ba, Hajiyar na ankare dasu.
Ammin ce tace "Hajiya me yasa Kika fito yanzu da sassafe idan kina son ganina basai ki turo nazo ba basai kin taso da kanki ba Dan Allah kiyi min wannan alfarmar kada wani Abu ya taso nason ganina ki taso ki taho saboda ni".
"To in Sha Allah hakan baze Kara fatuwa ba nima ba zuwan kaina bane jiya Muhammadu ya sameni da dare yake fada min wata maganar da banji dadin ta ba, shin da gaske ne bakije inda yake ba tunda Kika dawo? Idan ya Kira wayarki bakya dauka, yazo da kansa yafi sau biyar kin rufe kofa?".
Shiru Ammi tayi shi Kuma general kamar ya rungumeta a gaban Hajiyar haka yakeji Dan gani yayi ta wani Kara yin fresh da ita bazaka taba cewa ita ta haifi wadannan yaran ba, ta koma masa danya sharab da ita ga uwa uba ko runhu ka rike Kan sakko bazaka taba ganinta a hargitse ba ta San kanta sosai yanda ya kamata, da kyar ya iya saita kansa a gaban Hajiyar.
"Kinyi Shiru zainab kenan abinda ya fada gaskiya ne?"
Sadda Kai ta Karayi kasa sai Jin shashshekar ta sukayi.
"Subahaballahi haba zainab ko lokacin da lamuran suka jagule Baki zubar da hawaye ba sai yanzu, kiyi hakuri na fada Miki duk Wanda za'ace yayi hakuri to an zalunce shi ki yafewa mijinki wallahi rashin samun kulawar ki tasa ya runtse ido ya iya fada min abinda Bai kamata na sani ba, na roqi arziki ki dubi girman Allah da manzonsa ki rungumi mijinki da 'ya'yan ki kiyi boyayyiyar aure yanda Kika saba".
Sai da tayi kukanta Mai isarta sannan ta share hawayen ta sai lokacin taji wani gululo ya fice daga kirjinta.
"In Sha Allah ya wuce Hajiya har abada ki tayani bashi hakuri hakan baze qara faruwa ba".
Dan karamin tsaki Hajiyar tayi "Babu hakurin da za'a bashi, shida ya shuka rashin kirki, kece dai da hakurin ai cewa nayi bana zuwa shi daya Bata yaje ya gyara kayansa tunda Allah yasa kikazo gidan Nan Baki taba kawo min qararsa ba sai shine gemai gemai dashi ze dauko jiki ya kawo korafi ashe Babu dadi king...
Dan gyaran murya yayi "Hajiya kiyi Shiru komai ai ya wuce basai kince komai ba, tunda dai nayi abinda takeso ai shike Nan kowa ya ganni a Nan da ranar Allah na taso tsohuwa ta gaba ta min biko".
Ammi dai Shiru tayi Bata tanka ba sai Hajiya Inna ce tayi dan murmushin su na manya Wanda suka San jiya suke ganin yau. Ammi duk sai taji wata kunya ta lullubeta, wani lokacin maza kunyarsu kadan ce wallahi duk girmansu idan sukayi wani abun sai kaji kamar kananun yara, kome ya fadawa Hajiya ya taso ta da wannan safiyar?.
"To shike nan sai ka bamu guri ko tunda Allah yasa taga girmana ta yafe".
"To shike nan yaushe Zaki koma gida?".
Kafin Hajiyar tayi magana Ammi ta rigata.
"A Nan zata wuni da magari ba za'a maidata gida".
",To kaji sai ka tafi naka uzurin tunda 'yata ta yanke hukunci".
Baice komai ba ya nufi part dinsa da yake bangaren ta, harya danyi nisa ya juyo Yana kallonta ido cikin Ido da wani yanayi a tattare dashi.
"Kuyi breakfast Dani a kawo min ciki".
Kai ta gyada masa ya wuce ciki.
Yi Hajiya Ina tayi kamar bataji me yake fada ba ta cewa Ammi.
"Muje ki bude min dakin ko lazimi ban Gama ba yaje ya daukoni Dana ce yaje za'a kawoni ma cewa yayi A'a".
Ita dai Ammi ba baka sai kunne tare suka shiga dakin da Hajiyar.
*******
A qalla sun dauki minti kusan Sha biyar kafin Zahra ta Gama. Parlour na biyu Rukayyar taja Zahra suka shiga Bai Kai na farkon girma ba Amma ba karya Shima ya hadu kamar jira ake su zauna wayar zahrar ta dauki sansanyan kidan ringtone din ta.
"Amma"
Ta fada tana picking din Kiran sallamar Ammar ta amsa tana fadin "kiyi hakuri Ammah wallahi yanzu na fito daga wanka naci abinci, yanzu nake son kiranki na fada Miki mun sauka lafiya".
Daga can Ammar ta amsa Mata da "babu komai da fatan dai komai lafiya ba wata damuwa? zilai ce taso daga min hankali Wai wani gida aka kawo ku gari guda bata taba shiga ko kwatankwacin irinsa ba kamar Kuna wata kasar ita tsoro takeji".
Dariya sosai zahra tayi Jin yanda zilai ta nadi zance ta fesawa Ammah.
"Kai haba Ammah kyale Aunty zilai rudunta ne kawai, gidan Dan babba Kam babba ne Amma komai normal Ina Jin gidan wani friend din oga Sameer ne aka kawo mu, Kuma momin su oga Sameer ma Saida ta turo Mai aikinta daya da kanwarsa daya Aunty Rukayya gata ma nuna tare ku gaisa".
Wayar zahrar ta mikawa Rukayya suka gaisa da Amma, godiya Ammar ta dinga yiwa Rukayyar har kunya ta kamata tace Kuma ta bawa Zahra number din mommy ta kirata tayi Mata godiya.
Sallama sukayi da Ammar suna kashewa Kiran ya shigo international tana gani tasan shine.
Dagawa tayi tana masa sallama Jin muryarta ba kamar jiya ba ya sauke ajiyar zuciya a hankali da Bai yarda ba da Sameer ya fada masa kamar batayi ciwo ba sai yanzu da yaji muryarta tana fita ba kamar jiya ba.
Sallamar ya amsa Yana fadin "my previous...".
Wani deeply saida tsikar jikinta ta bada wani yarrr. "Wash" ta fada.
Kara Kiran sunan yayi a hankali ciki wata murya Mai tada zaune tsaye "me ya faru ne to jikin ne"?".
"A'a ba komai" ta fada a shagwabe.
Rukayya na ganin haka ta Miki tana nuna Mata tana zuwa Dan ta barta ta sake yanda ya kamata.
"Alhamdulillahi