Showing 6001 words to 9000 words out of 122700 words
Qungiyar yake in dai kana musu aiki idan wani Abu ya sameka Mai Dadi ko marar dadi su zasu tsaya maka".
"Alhaji yace min kun shiga dazu bayan sallar magariba har da bakin kunyi Masa godiya, kun kyauta haka ake so".
Lokacin Mahmud ya koma dakinsu Habib baya Nan gurin da yake aje makullin lifan dinsa ya duba ya kuwa you sa'a yana nan, lodojin ya zube a kan gado ya dauki makullin ya rufe dakin ya hau mashin din yayi gaba.
Bai dawo ba sai kusan Sha biyu da rabi har lokacin kuma Habib baya dakin yasan suna can suna kujuba kujuba.
Yauma Zahra taso kwana a dakin Aunty Hasana saboda tana bukatar kadaicewa Amma Sajida ta matsa Mata da mita Saida suka tafi Amma fa zuciyarta Bata da nutsuwa gashi tana ankare da Aunty Hasana tun jiya da dare a taje can gida cikin gari Bata da nutsuwa ko alama Amma tana ta kokarin ta basar sai dai ko Yaya mutum ya shiga damuwa indai kayi Masa farin Sani zaka fahimta, ita Abu mafi Bata mamaki yanda aketa kwaramniyar bikin ba wani canji sai dai abunda baza'a rasa ba duk da Daman ba wata muguwar bidi'a ba ta had'a, walima ce kawai Bata Sami ba saboda tace ita malam Tijjani Ahmad zeyi Mata Kuma bayanan yana Umara.
Tunda tayi sallah ta kasa tashi daga gurin tana kallon su Sajida sunata sabgarsu, Amma ita da wata irin faduwar gaba ta tashi ta rasa nutsuwarta kwata kwata da kyar ta tsahi sauko kasa gurin Aunty Hasana a fall ta sameta tana hadawa Abbansu Haidar break fast.
Gurin dining din ta karasa tana gaishe shi sannan gaida Auntyn.
Dakin Auntyn ta shiga kwanciya tayi tana ta faman sakawa da kwancewa zuwa yanzu dai tasan tabbas da matsala sai dai yanda ba Wanda ya fad'a Mata shi yasa itama ta zubawa sarautar Allah Ido taga iya karshen film din tasan ko menene yau dai za'a yita ta Kare tunda yau ne deadline duk wata kunbiya kunbiya za'a zazzageta.
Tun karfe goma Mai yiwa Amarya make up tazo Amma kememe Zahra tace ita bataso a kyaleta aka dunga yiwa kawayenta, ganin guri ze kure ne Sajida take ta fadawa Aunty Hasana Saida tazo sannan akayi Mata light makeup Amma fa duk da hakan tayi karshen kyau, farin material ne ta sakata Mai touching din sky blue sai aka daura Mata head shima sky blue din takalman da pos din duk sky blue din ne.
Wani san sanyan kyau tayi na ban mamaki, komai na Zahra Mai kyau lallai zaharar ce Dan duk cikin kawayen Bata da mahad'i.
A babban masallacin juma'a za'a daura auren Masha Allah, ango ya fito Shar abokansa sai mamakinsa suke Basu taba sanin kyawunsa da cikar haibarsa ya Kai haka ba sai daya fito sun Sha mamakin kwarai har wasu suka Fara kokonto a kansa, Yana kallon yanda idanun sukayi Masa caa.
Dan dakakkiyar getzener ta saka ga takalman da agogo ga hula, Sam bazaka taba cewa Wai alamajirin malam bane ba, ga wani irin kamshin tunda ta tumkaro taron abokanensa kamshin ya hade gurin.
Daga gefe sameer ne da abokinsa Naraddeen suna tsaye lokacin da Mahmud ya fito Sameer ya kalli Naraddeen din yace "wallahi wannan guy kwallon Dan duniya ne na rasa Gane kan alkiblar daya kalla Wai aure zai daura shi kadai kamar marara gata, ni so nake Naga karshen wannan wasan kwaikwayon nasa.
Daga inda yake tsaye ya kafe Sameer da Ido ko Bai fad'a ba yasan me yake nufi tun jiya yake tuhumarsa aka zuwa da abokinsa da yayi duk da ya nuna Masa wannan ba wata matsala bace Amma har yanzu Yana hukunta shida idanunsa.
Masha Allah dubban mutane ne suka shaida daurin Auren FATIMAH ZAHRA AHMAD SANI da Angonta MAHMUD MUHAMMAD DANGE akan sadaki dubu dari uku lakadan ba ajalan ba.
Daurin aure daya bawa dubun mutane mamaki bare wadanda sukazo daga bangaren Mushahu sunyi mamaki kwarai sunan Amarya dai shine Amma ba mijin daya gayyato su bane yayin da yan unguwa ya Zama abin kasawa a faifai ana yawo dashi, da yawa na ganin beken Alhaji Jafar na aurawa bakon da ba'asan asalinsa ba yarinya kamar Zahra yayin da wasu ke fadar ai Dan ba 'yarsa bace shi yasa yayin wannan danyan aikin.
.......
💋❤️AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️
Page four🔷
___________''📖🖋️
Wata marokiya ce irin dattawan Nan da suke bin manyan marok'a ta biyo tawagar masu dawowa zuwa gida kasancewar gidan ba nisa daga masallacin juma'ar, itace ta rangad'a guda har sau uku ta Kara da fadin "Alkawarin Allah ya tabbata an daura auren Fatima Zahara'u da zukeken Angonta Mahmud Ubangiji Allah ya bada zaman lafiya da kazantar daki Bata shara ba, munzo much arziki mubar arziki a gurinsa.
Kamar saukar aradu haka maganar ta shiga kunnen Hajiya mama, batasan lokacin data tsallake mutanen falonta ta fito ba dankwalinta a hannu, tana fadin "me naji ana fad'a wa aka daurawa aure da Mahmud naji kowa".
"Eh haka ne Kam Alkawarin Allah ya ciki Zahara'u ta Zama matar Mahamuda"
Ta debo wata gudar ta Kara rabsawa.
Dai dai lokacin Hajiya kaltume aminiyar Ammah ta fito ta dukulawa wannan marokiyar kudi sannan ta Mika Mata babbar leda Mai abincin biki har da ruwa da lemo.
Cikin rashin nutsuwa Hajiya mama ta nufi dakin Amma ko sallama Babu ta Fara fadar "Hajiya kinji abinda naji ko kunnena ne ya jiyo min ba dai dai ba?".
Kallonta duk 'yan dakin suke kafin Ammar tace Mata "nima haka naji kamar yanda kikaji sai dai ko shirme takeyi ita Mai rokon tunda ba sanin su tayi ba".
"Eh gaskiya Kam sai dai hakan".
Ta juya ta koma daki. Bata zauna a falon ba uwar daki ta wuce, Asabe ce ta rufa Mata baya, a tsaye ta sameta ta Goya hannu a baya tana Dan Kai kawo a tsakanin gado da madubi.
Waiwayowa tayi tana kallon Asaben kafin ta zauna a bakin gado, kusa da ita Asaben itama ta zauna.
Tana fadar "Haba Hajiya Dan Allah ki nutsu bana son ki bada wata baraka a sabgar Nan keda na fad'a Miki Daman malam na BANDE yace wannan karon aure sai anyi Amma ba da Mushahun ba, Amma abinda yake daure min Kai malam na banden yace Wanda zata aura a nesa yake Kuma yaga haske so sai akan lamarin duk yanda yaso ya Bata lamarin abin Bai yuwu ba shine nace kawai a kyale tunda dai Wanda muke son a fasa da shin din aikin ya yuwu, nasan dai da wuya ta Sami irin Wanda ta rasa a bay".
"Haka ne Amma abin dubawar waye wannan din sanan me yasa aka kudundune zance? Wai fa Dan munafurci Hajiya Asma'u cewa tayi Bata Sani ba ke kin yarda Alhaji ze aurar da Zahra Bata da masaniya, ko meye ma dai kyawaun ya kare a auren Hadi tunda nasan ba wani sai Mushahun shi Kuma ya Kara gaba kamar sauran".
Ta fad'a tana kwafa, mikewa tayi tana gafar "Bari na fita sai Naga kul uwar daka".
"Allah ya taimaki uwar dakina, aikinki Yana kyau".
Asabe ta fad'a tana mikewa itama.
**********
Daga gurin daurin aure Kai tsaye gidan gonar Alhaji Jafar suka wuce har tawagar angon bisa umarnin Alhajin tun safe ya turo Mai sunasa (magaji) yaje ya fadawa Baba malam.
Anci an Sha kamar ba gobe mutane sunyi mamakin irin wannan karamar arzikin dan duk zarin mutum sai dai yaci ya Bari ruwa da lemo kuwa kamar banza.
Abokan Mahmud kuwa sai Dan biki suke Masa.
A gidan malam ma Masha Allah anci an Sha Yara sun san ana biki a gidansu, Iya Abu ma tayi nata taron komai baja baja makotanta ma sunsan ana hidimar arzki a gidan Kuma Suma sunzo Mata harda masu riko abin arzikinsu su kawo Mata.
******** A guje Faruq ya Fado falon Aunty Hasana,danta ne na uku Yana rungume da babbar rigarsa ta daurin aure daya saka Yana Fadi "Aunty Zahra wallahi Naga mijinki ba wannan Uncle din bane na kano wallahi wanna yafi shi kyau Baki gani ba yanda yake rabawa marok'a kudi ba, Kuma Dan gayu ne sosai Naga Uncle Abdul Hakeem ma ya rugume shi Yana ta dariya, Dana tambayi Auncle Imam yace min sunansa uncle Mahmud".
Tunda ya shigo Yana karadin Nan ta zuba masa Ido tana sauraren abinda yake fad'a, kana ganinsa kasan har zuciyarsa abinda yake fad'a din gaskiya ne, wani irin gingirin taji kanta yayi mata, nan ta sulale ta kwanta kan kujerar ta saka hannunta ta rufe fuskarta wasu hawaye na zubo Mata masu zafi.
Sajida da Amatu suka nufi gurin Faruq din suna neman Karin bayani.
Yayin da wasu da yawa suke ta sabgar ciye ciyensu Dan Suma Kam an kawo koma enough.
Kamar yanda ya fad'a haka Suma ya mayar musu Dan su harda Karin bayanin yayi musu kasancewarsa Mai surutun tsiya.
A hankali Sajida ta kamo hannun Zahra Dan Bata fatan wani daga cikin bakinsu su fuskanci an samu matsala gaskiya, kamar masu you shawara suka shiga dakin Auntyn saboda Nan ne baza'a shigo ba.
Bakin gadon ta zaunar da Zahra ita Kuma ta janyo stool ta zauna har lokacin Bata saki hannunta ba,tana Jin yanda ilahirin jikinta yake rawa.
Hannun ta Kara jimkewa cikin nata tana fadar.
"Cool down Mana bestie haba take it easy, kada ki tada hankalinki Taya Zaki kama maganar faruq kinsan dai ba wani hankali ya Gama Masa jiki ba".
Kai ta shiga girgizawa cikin muryar Kuka tace.
"Wallahi Saji akwai matsala kema Kuma kin sani sai dai kik'i fad'a idan ba matsala Ina su Maryam da mukayi dasu zasu zo tun kwana ukunda suka wuce Ina shi kanshi uban gayyar ina su Deeni dasu Aliyu, kowa ka Kira sai dai kaji switch off baka haka ba".
Ta fad'a tana fashewa da wani irin Kika.mai taba zuciya.
"Kiyi shiru Dan Allah kada ki janyo hankalin mutane Mana kinga ga Amatu can zataji dasu ki nutsu har muji meye gaskiyar maganar Mana".
"Ki barni nayi kuka wallahi na gaji nikenan kullum matsala daga wannan sai waccan na rasa a Ina matsalar take ni wallahi bana son kowa ma a kyakeni haka Nan bana son auren, bana so wallahi ni nagaji Allah Jordan zan tafi bazan zauna ba, bazan Kara Zama a kasar nan ba".
Ta fusge hannunta daga na Sajida ta yunkura ta tashi ita dai Sajida Bata San ta Yaya akayi ba sai ganin Zahra tayi ta kifa kan gadon tana wata irin fuzga da gudu ta karasa kusa da ita tana jijjigata tana fashewa da kuka tana fadin "ki tashi Dan Allah wayyo Allah na".
Baba Tabawa ce ta bude kofar ta shigo, Dan tunda tana kusa dasu Faruq ya shigo da wannan maganar duk da tasani Dan Aunty Hasana Bata rufe Mata komai ba ta fad'a Mata tun jiya, shi yasa data ga sun nufo dakin hankalinta ya kasa kwanciya ta biyo su tasan koya Sajida zatayi Mata kalamai ba kamar ita ba tunda abinda babba ya hango yaro koya hau iccen rimi bazai gano ba.
Turus tayi tana kallon Sajida dake Kuka bil hakki tan jijjiga Zahrar.
Da sauri ta karaso tana fadar "ke 'yan Nan menene haka?".
Hawaye jage-jage Sajida ta dago tana fadar "wlh Baba Tabawa kawai tana kuka tana maganganu tana tashi kawai sai Naga ta yanke jiki ta Fadi?.
Wani ruwa Baba Tabawar ta dauko a kan bedside fregde din Nan ta zubawa Zahrar a fuska Amma shiru ta Kara watsa Mata Nan ma shiru cikin tashin hankali ta lalubo Yar wayarta rakani toilet ta mikawa Sajida "ungo maza Kira min Aunty zakiga an saka Maman Ali yi sauri".
Bugu biyu Auntyn ta dauka tare da sallama, gani Sajida ta rasa me zatace ne yasa ta mikawa Baba Tabawa wayar.
Can Kuma tana ta faman" hello Baba"
Abinda taji kenan lokacin data Kara wayar a kunne cikin sauri Baba tace "yi sauri ki turo a Kai Zahara'u asibiti wallahi gata Nan a suma min yayyafa ruwa a banza".
Bata jira taji me za'a fad'a ba ta kashe wayar.
Abdul Hakeem Aunty Hasana ta lalubo a waya lokacin suna tsaye shi da Mahmud suna magana wayar Abdul Hakeem dince ta Fara ringing Sunan Aunty Hasana ya gani ya daga har zai Fara Mata abunda ya saba ta tsayar dashi tana fadin "Dan Allah maza kaje gidana ka dauko Zahra ku wuce asibiti mu hadu a can wai Suma tayi"
Kit ta kashe wayar.
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yake ta Nanatawa da sauri Mahmud ya tambaye shi "lafiya meya faru".
"Bari kawai ba komai Ina zuwa yayi gaba da sauri jikinsa har rawa yake Yana tafe Yana laluben key din motarsa. Da sauri Mahmud ya biyo bayansa' Sam baiji key din ba sai daga baya ya tuna tana hannun mustapha yaje gari ya dawo.
Tsaki yayi daidai lokaci da Mahmud din ya karaso Yana fadar"Dan Allah Wai menene Naga duk a rude".
"Bari kawai Wai Zahra ce ba lfy zan kaita ASIBITI".
Kallon yayiwa Abdul Hakeem din kafin yace "shine Kuma zakaqi fad'a min".
Hannu yasa ya yafito Sameer, cikin bada umarni yace
"Dauko motar can kuje da Abdul zaku Kai madam asibiti". Ya juya ya koma gurin su Habib.
Har sukaje gidan Auntyn Abdul Hakeem Bai daina mamakin Mahmud ba, yanayin yanda yayi maganar kawai kasan da abinda ya taka umarni fa ya bada, su dai a zahiri ai Sameer ne uban gidan Mahmud tunda kowa yasan aikin NGO's ya kawo shi garin har suka hadu da Mahmud din suka dauke shi yake musu aiki a sauran makarantun tsangayun na cikin gari Dana kauye.
Da sauri Abdul Hakeem din shiga gidan Auntyn ta kofar baya gurin kitchen ya shiga koridon dakunan barcinta.
A tsaye cirko cirko ya samu su Baba Tabawar har lokacin numfashinta Bai dawo ba.
Da sauri ya karasa gaban gadon yasa hannu ya dauketa kamar wata Baby yayi waje da ita. Sajida da Baba Suka rufa Masa baya.
Da sauri Sameer ya bude Masa seat din baya ya sakata Sajida ta shiga ita da Baba shima Abdul Hakeem ya shiga gaba da gudu Sameer ya fizgi motar. Saida ya daidaita a titin sannan ya kalli Abdul Hakeem din "ina muka nufa?".
"F.M.C zamuje tunda yafi kusa".
Nan da Nan aba karbeta likitoci suka rufu a kanta, suna Nan tsaye Aunty Hasana tazo ita da Inna maimuna sai Hajiya kaltume.
Suma tsayawa sukayi a gurin Baba Tabawa tana maida musu yanda akayi ita dai Sajida ba baka sai sharar hawaye take.
Su Abdul Hakeem suna suna gefe daga zuwansu Mahmud ya Kira akai sau biyar idan ya Kira Sameer sai ya Kira Abdul Hakeem, daga Jon yanayinsa kasan Yana cikin damuwa abinda ya Kara daure Abdul Hakeem Kai yandq Sameer yake amsa wayar Mahmud cikin kulawa da bada girma.
Sun dauki a kalla minti arba'in kafin babban likitan ya fito sannan sauran Suma suka fito.
Su Abdul Hakeem sun bin bayan likitan kamar yanda ya bukata Amma ganin an gungoro Zahrar a gadon daukar marasa lafiya yasa suka nufe ta da sauri suda su Aunty Hasana.
Wanda ya turo gadon ne yace "ai ta farfado ba wata matsala ana so ne dai ta samu hutu sosai jininta ne yaso Hawa Amma cikin ikon Allah anyi controlling dinsa".
"Oh no 'yasu Allah ka dubi lamarin wannan 'yar maraiya duk da Bata tashi da rashin gata ba sai yanzu ka kawo Mata Tata jarabawar Allah ka shiga cikin lamarinta".
Aunty Hasana ta fad'a itama tana goge hawaye.
Baba Tabawa dasu Sajida suka amsa da "ameen ya Rabbi"
Dakin 'yan da'i da'a aka kaita tunda tana bukatar isolation.
Saida komai ya Zama dai dai an saka Mata drip sannansu Sameer sukaje gurin likitan. Fad'a yayi so sai akan yanda akayi har karamar yarinya kamar wannan damuwa tayi Mata yawa har har take barazana ga lafiyar ta.
A can gidan biki Kuma Amma ta rasa inda su Hasana da Inna suka tafi Dan hankalinta Bai kawo Mata Hajiya kaltume ma Bata Nan ba sai da abokiyar zamanta tazo sannna ta fuskanci itama Bata Nan din wayarta ta dauko ta Kira Hasana, lokacin tana zaune gaban gadon da aka kwantar da Zahrar.
Sunan Ammah ta gani sai lokacin ta tuna Ashe Bata fad'a Mata ba.
" Assalamu Alaikum Ammah".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, wai Ina Kika tafi ne babu ke Inna maimuna ma Bata Nan Hajiya kaltume ma banganta ba".
Dan Jim tayi har Saida Ammah tace "kina jina?"
"Eh inaji Ammah duk muna tare dasu, muna Nan gurin Zahra Bata Jin dadi ne Amman da sauki yan haka barci take".
"Wane irin zance ne wannan kamar Bata Jin dadi Kinga Hasana fadi min gaskiya yanzu kina Ina?".
" Muna F.M.C wlh jikin da sauki sosai kawai sunce ana dai San ta huta ne, kada ki tada hankalin Dan Allah".
"To Allah ya kyau Amma Ina hankali ze kwanta".
Waje Aunty Hasanar ta fito gurin su Baba tabawa da sajida tace
"Baba tabawa Dan Allah kuje gida da sajida tasan inda aka aje abubuwan da zasu bawa kawayensu tunda yau zasu wuce sai ki fad'a musu tana gida gurin Abba, ta kalli Sajida ke Kuma duk tmbayar da saying Miki kice Baki Sani ba mu barsu a haka".
Kudi ta mikawa Baba tabawan sannan ta karasa gurinsu Inna maimuna da Hajiya kaltume, Suma bayi tayi musu na Kiran Ammah tace suje gidan Dan hankalinta ya kwanta.
*********
Da kyar Amma ta Bari akayi sallar magariba ta shiga bangaren Alhaji Jafar ta same shi da Hassan da Abdul Hakeem suna magana akan Zahra Hassan Yana ta mitar meyasa Abban yayi haka ai da hakuri kawai akayi har lokacin da Allah ze kawo Mata wani.
Dan murmushinsu na manya yayi Yana "fadin wannan ma in Sha Allah Babu Dana Sani a cikinsa ni nasan nagartar Dana gani tare da yaron yasa na bashi, Kuma ko bayan Raina zakuce na fad'a muku".
Jiki ba kwari Amma ta gaishe da Alhajin tana Masa ban gajiya tare da godiya.
Sannan ta Dora da fadin "Dan Allah ko zaka Bari naje Naga jikin nata?"
Tsai yayi Yana kallon ta "da kinyi hakurin zuwa Suma da anjima zasu taho gida yanzu ma daga cen muke ko zuwan mu Bai isar ba?"
Cikin Jin nauyinsa tace "A'a ya badatar"
Ta tashi ta nufi kofa da kallo Abban ya bita ita kanta tausayi take sashi da gani zuciyar ta ba Dadi.
Da sallama suka shiga dakin lokacin Aunty Hasana tana sallar insha'i ita Kuma zahra farkawarta kenan tana kokarin tantance Wai inane ma Nan din inda ta gani idan dai ba gizo idanunta ke Mata ba