Showing 111001 words to 114000 words out of 122700 words
matsalarki kada ki watsa Masa qasa a Ido ki sage Masa gwiwa akan kokarinsa, kije idan Allah yasa Babu komai shike Nan idan Kuma anga abinda ke kawo ciwon a magance shi".
"Wannan gaskiya ne".
Zilai ta fada tana sauke girkin.
"To in Sha Allah na daina iya".
"Yauwa kokefa fa ai idan Kika Fara da haka ko lalular da tafi haka baze Maida hankalinsa ba duk da ba fata ake ba".
"Dan Allah Aunty zilai bani wayarki na Kira Ammah tawa tun jiya ta kashe kanta taki kunnuwa".
Ta fada tana istigifari a zuciyar ta Dan tasan karya ta shara.
" To Bari na dauko Miki tana can a daki"
Ta wanke hannunta ta nufi kafar fita Zahrar tana biye da ita, sai da suka fito zilan ta kalli Zahra "uwar dakina Dan Allah Wai Kinga kuwa dakin da aka ajeni a ciki Dan Allah muje kiga wannan duniyar da aka sakani kamar dakin gidanki,to acan dai bana Hawa gadon Amma wannan akai na kwana har naso in makara Allah yasa ita Iya Rahane Bata makara ba".
Dariya Zahra tayi tana fadin "daina fada Aunty zilai sai a Raina mu wallahi, muje Naga dakin naki Daman ban San inda kike ba Koda tsoro ze kamani sai nayo gudun hijira".
A parlour na biyu suka shiga wani corridor bazaka taba cewa da dakuna a gurin ba steps ne kamar goma suka haura sama Nan ma wani parlourn ne da two three bedrooms biyu suna kallon juna sai Daya daga gefe.
"Masha Allah" Zahra ke fada a zuciyar ta tana mamakin gidan Wai wane irin gida ne wannan gari guda compartment guda kawai ya hada irin wadannan mahaukatan falukan da bedrooms din Nan to yaya sauran parts din suke?.
Dakin dake hannun hagu ta nufa ta bude, daga inda Zahra take ta hango wani Royal bed milk Mai azabar kyau, Bata Kara gaskata maganar zilan ba Saida ta shiga ciki, a gefen bed din Zahra ta zauna tana fadin "Bari na Dana gadon Aunty zilai".
Dariya sukayi su suka "kin gani ko wallahi nifa a jiya da kyar nayi barci duk zulumi ya isheni ji nayi Ina tsoron gidan yayi girma da yawa, na jinjinawa matar gidan".
"Wai Mai gidan Bai taba aure ba a gaba dai ze kawo matar".
Baki zilai ta Kama tana fadin "to shi wane irin kudi ke gareshi da ze Gina irin wannan gidan Yana saurayinsa".
"Bani wayar Aunty zilai wannan hirar ba karewa zatayi ba kada lokaci ya kure yau daga Asibitin cikin gari zamu gidan su oga Sameer na gaishe da mommy". Wayar ta Bata suka fito tare ta Kira Ammah suka gaisa sun jima tana fada Mata abubuwan da akayi mata jiya da Kuma komawar da zasuyi yau, karfafa Mata gwiwa itama Ammar tayi tana fada mata ta kwantar da hankalinta In Sha Allah ba komai.
Lokacin da suka fito har Iya Rahane ta shirya table din Rukayya ma ta fito.
Kallon su Rukayyar takeyi ganin daga bangaren da suka fito.
"Aunty Rukayya Ina kwana?"
Zahra ta fada.
",Lafiya kalau matar big bro, ya Naga kin fito daga bangaren mu".
"Au kema a can Kika zauna kika ki zama a dayan dakin kusa Dani".
Baki ta bade tana kallon Zahra. "Na shiga dakin Mai gidan na zauna tab ai wannan part din sai ku".
"Mu suwa daga zuwa bakunta sai mu zaqe Ina laifin can din wallahi transfer zanyi, Ina dalili Ni kadai kamar mayya kufa Nan ku uku ko ihun neman taimako kayi an taimaka maka amman Ni kuwa ko kasheni za'ayi sai dai a dauki gawar da safe".
"Tab wallahi ba inda Zaki zauna a Nan ba haka big bro yace ba,a can yace ki zauna Dan haka Babu Mai canza wannan Umarnin".
Dan turo Baki tayi "Ni na taba ganin haka mutum ya ringa saka doka a gidan mutane inaga baisan girman gidan ba shi yasa yake bada wannan Umarnin, gaskiya da sake".
Time Rukayya ta duba a waya kizo muyi break yanzu zakiga ya Sameer yazo tunda da wuri za'ayi Miki sauran gwajin".
Suna cikin break din Sameer yazo Saida ya jira a mota suka Gama sannan suka tafi, a ANC department suka samu doctor Haseenar sun awon ciki.
Ba yabo ba fallasa ta tarbesu ba kamar jiya ba ko yanda suka ringa Yi jiya da Rukayya yau ba haka bane daga gaisawa Bata Kara cewa komai ba, itama Zahra saita Kama kanta Rukayyar ma haka. Gwajin jini ta Kara tura Zahrar ta hadasu da wata ma'aikaciyar su ta rakasu main lab aka dauki jinin.
Lokacin da suka dawo sun Gama ante-natal din gwajin jira ta dauko da scanning din ta Kira Sameer tana fadin mu hadu a office dina".
Ta kashe tana fadin Bismillah Ruky muje office dina tunda mun Gama da Ante-natal sai zuwa anjima zamu Fara gyne".
A kofar office din suka samu Sameer din ya rigasu zuwa.
Sai da suka zauna sannan suka gaisa da Sameer din, bayani ta farayi Masa na gwaje-gwajen jinin jiya "a cikin jininta ba wata cuta ko kadan kawai scanning ne ya nuna Mana akwai matsala a mahaifarta ta fibroid amman be wani girma sosai ba za'ayi aiki a cire mata tun kafin ya girma Amma zamuyi admitting dinta zuwa one week tana karbar magani kafin ayi surgery din, Dan haka sai ta Kira mijinta ta fada masa yazo da mutane muna son jini leda biyu, zamu jira results din Nan ya fito total blood count za'ayi Mata".
Rukayya ce tayi farat ta tambayi doctor Haseenar "yanzu dole sai tiyata baza'a iya Shan magani ba a warke?"
Kallon tsab Dr Haseenar tayi Mata kafin tace "hanya mafi saukin rabuwa dashi ta sai dai aikin gaskiya".
Tunda doctor Haseena ta Fara bayani gaban Zahra ya yanke ya Fadi idan da abinda taki jini a rayuwar duniyar Nan to tiyata ce.
Nisawa Sameer yayi kafin ya samu karfin halin fadin.
"Thank you so much doctor kome kenan zakiji idan munyi communicating da mijinta saina kiraki later"
"Ok.ba damuwa Allah ya sauwaqe".
"Amin".
Rukayya ta fada Dan zahra ba bakin magana har suka shiga mota tana cikin tashin hankali, kuka takeyi irin na zuci din Nan sai dai hawaye kamar an bude famfo.
Saida suka fita daga Asibitin har sun shiga court road sannan Sameer ya Dan juyo, Madam kiyi hakuri in Sha Allah ba wata matsala idan Allah yasa yin surgery din ne yafi Alkhairi ayi kawai Kinga kema saiki huta da zulumin ciwo duk wata".
Rukayya ce juyo tana fadin "gaskiya kada ki yarda a yanka ki haka kawai Ni banma yarda da maganar Haseena ba, kawai ta jawo Miki wahala Ni Daman da anyi shawara Dani da Babu abinda zesa Haseena ta duba matar big bro haka kawai taje ta jawo Mata matsala da gangan bakaga yau sai wani share mutane takeyi ba, wani ya Hana big bro din ya aure ta".
Wata uwar harara Sameer ya zubawa Rukayya "Billahillazi Zan saukeki a Nan ke wace irin mutumce da bakinki bashi da controlto me kikayi ke Nan? wannan ai shashanci ne keda Zaki kwantar Mata da hankalinta shine Kika sokawa zancen wuqa".
Ita dai Zahra maganganun Rukayya sun daga Mata hankalin kenan da wata jikakkiya a tsakanin wannan likitar da Mahmud.
Wallahi ko likitoci sun Kare wannan ba zata Kara dubata ba shi yasa Kennan jiya ta damu da sanin waye mijinta da dangartakar ta da Mahmud.
Tunda Sameer ya yiwa Rukayya buyagi Bata kara magana ba har sukazo junction din gidan shatima. "Wai yaushe mommy taje gidan Hajyr makwararin?".
"Dazu da safe na kaita Wai zasu karbi lefen mujahida".
"Ok Allah ya Sanya Alkhairi. Dan Allah ya Sameer Zan sayi alawar Madara idan ka tsallaka Zan kaiwa Hajiyar makwarari".
"Kice dai Zaki saya bawai Zaki sayawa Hajiyar makwararin ba".
"Allah tana son shi sosai"
A kofar gidan Hajiyar yayi parking Babar mommy ce.
Da karadi Rukayya ta shigo gida yayin da Zahra da Sameerke biye da ita a baya, suna runfa ana hira da kunnen Rukayya da 'ya'yan dangi da mommy masu karbar lefen basu Fara zuwa ba gaishe dasu yaran sukayi suka fice, sukabar mommy kawai. Cikin nuna kulawar mommy ta kalli Rukayya dake gaba. "Ba dai har kun gama da asibitin ba?"
" Mun Gama kin ganta Nan Wai doctor Haseena tace zata yankata tayi Mata tiyata Dan nace ban yarda da ita ba shine ya Sameer yake ganin bekena".
Sallama Zahra tayi tana Dan tsugunnawa tana gaishe da mommy cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa da Kuma alamun tasha kuka.
Mommy kallonta tayi tana fadin "Masha Allah tabarakalla sannu ya jikin naki?"
Da sauki sosai".
To Allah ya Kara lafiya naji Rukayyar na fadin tiyata za'ayi Miki".
"Eh haka suka fada"
Hajiyar makwararin ce ta fito tana fadin "wa nakeji kamar Rakiya a gidan nan waye ba lafiya naji ana magana tiyata".
" Kin ganta Hajiya, matar Mahmud mutumin ki ce".
Mommy ta nuna zahra.
" Wai Amaryar ce? Sannu kinji menene ya sameki?"
Rukayya ce ta fada Mata.
Mommy ta kalla "Ni Zan hada Mata maganin wannan lalurar ba sai anyi Mata aiki ba, ki huta Rukayya ki shiga Nan kurmi ki sawo min abin hada maganin a Nan na hada Mata insha Allah sai dai ya narke yabi jinin al'ada.
"Amma gaskiya ba wanda ze yanka ta Kamar kabewa ku 'ya'yan zamani komai a yanka ta haka ne daji yake shiga ai ta fama da rai idan yazo da karar kwana kiga an mutu, daina kuka, samiru kiwawo min mijin nata na fada Masa da bakina Babu me yi Mata danyan aiki ko haihuwar fari Bata yi ba a jawo mata tsuguniya mazan yanzu marasa hakuri".
Ta fada tana nufar uwar dakanta.
Ita dai mommy Shiru tayi Saida Hajiyar ta shige sannan ta dubi Rukayya "Wai Ke Sai yaushe hankali ze Gama Miki jiki? Kinzo kin kwatsa zance gashi Nan kin tubzura Hajiya Mai hanata hada maganin Nan sai Allah, itama Kuma Mai lalurar maimakon ki kwantar mata da hankalinta A'a tashin farko kin sokawa zancen wuka, ai kin kyauta".
"Wallahi ba haka bane mommy Kinga dai muna good term da Haseena amma wallahi yau kamar ma Bata taba gani na ba sai cin magani take yiwa mutane da dacin rai want ya Hana Ya Mahmud din ya aureta taga yarinya ta gigice zatayi mata illa haka kawai".
Maficin dake kusa da ita Mommy ta jefawa Rukayya tana fadin fita ki bani guri tunda kin Zama babbar kwabo kin tasa yarinya gaba kina fadar abinda be Dace ba".
Wata uwar harara Sameer ya saukewa Ruky ji yake kamar yayi Mata duka duk ta cakude lamarin tana kokarin ta saka jinin yarinyar mutane ya hau, tun sassafe Mahmud ya Kira shi Yana fada Masa ya kira Rukayya yace ta fadawa Zahra ta bude wayarta ya manta shaf sai fa yanzu ya tuna.
Wayarsa ce ta Fara ringing "shine ya kira" ya fadawa mommy.
"Ka dauka kayi Masa bayanin halin da ake ciki".
"Nasan Haseena ce ta fada Masa shine ya Kira yaji".
Wayar ya saka a speaker yanda zahrar ma zataji.
Bai jira komai ba ya Fara fadin "Sameer wace magana naji Haseena tana fada min? kada ka Bari su taba min yarinyar nan Zan kaita inda ya Dace, naji tana fada min wasu nonsense wallahi idan na shigo saina Bata Mata rai, ita harta isa ta fada min son ranta who is she? Yanzu ina ita zahran take? Tun jiya jikina ya bani an samu problem wayar ta fa ta rufe ta Hana nayi magana da ita fa".
Tashi Sameer yayi tsam ya fita ya cire wayar daga speaker saboda kada yayi katobara.
"Gamu Nan a makwarari gidan Hajiya Zahrar sai kuka takeyi,ita Kuma Ruky sai tinzira ta take kada ta Bari a yankata har Hajiyar makwarari taji tayi tsallen Albarka tace bata san wannan magana ba, ita zata hada Mata maganin hausa Wanda ze narke ciwon, wallahi sun caza min kai har na rasa yanda zanyi da rigimar Hajiyar, yanzu haka kasuwar kurmi zata aiki Rukayya ta sawo Mata mahadin maganin da zata hadawa zahrar".
"Yanzu dai bazan Gane kome kake fada ba hadani da Zahrar muyi magana"
"Ok Bari na kira ta dakin mujahida Naga ba kowa a ciki ka kwantar Mata da hankali duk ta shiga damuwa sosai sai kuka takeyi"
Rukayya dake zaune a tsakar gida ya yiwa nuni data Kira Zahra, lokacin da suka fito Yana tsaye suna ciga da maganar.
Wayar ya Miko Mata ya nuna Mata dakin mujahida yayi nufi waje.
Tana shiga cikin dakin tana Jinsa Yana faman hello, hello tayi shiru karshe ma ta sakata wayar a flight mood tayi kwanciyarta a katifar mujahadar tana goge hawaye.
"Me kake son fada min Kuma? naji komai me Za'ayi bazan zauna a garin Nan ba wallahi, gida Zan tafi kuma idan ma ciwon ne ai Ina da inda za'ayi min maganin ba sai Nan ba, da gata na da komai na zauna sai watangaririya nake yi Dani".AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 41.
📖🖋️
________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala.
Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi".
Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" .
Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala.
Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" .
Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya.
Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa".
Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna".
Ta taso tana karbar tabarmin.
"Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki".
Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi".
"Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita".
Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar.
A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki.
Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?.
Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah".
Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita.
"Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi".
Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron.
"Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa"
'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi".
"Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba".
Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba.
Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata".
"Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida".
Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata".
Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata.
"Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi".
"Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba"
Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne".
Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.
Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa.
Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask