Showing 30001 words to 33000 words out of 122700 words

Chapter 11 - Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

578

ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu.
Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka bijiro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira.
Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izininsa duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma nemi Jin wacece daga cikin yaran suka gada Masa zahra ce, nan ya amince musu da addu'ar Allah ya hada kawunan su.
Tun daga lokacin Sahal ya Fara zuwa gurin Zahra cikin ikon Allah tayi na'am dashi Basu Dade sosai ba sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a unguwar yasan irin soyayyar da sahal yakewa zahra kusan Kullum da yamma Yana nan makale da ita, a haka har manya suka shiga maganar aka tsaida lokaci wata shida inda zasu tafi Colombia inda yake hada masters dinsa ita kuma zata Fara nata degree din.
Anyi lefe na garari Wanda ya dauki Baki fiye da tunanin Mai tunani, an kashe kudi Kamar ba'a San zafinsu ba.
Lokacin da bikin ya rage baifi saura wata biyu ba sai lamarin ya Fara canzawa kwata -kwata Sahal ya rage zuwa gurin Zahra haka ma sai a kwana a wuni Bai kirata ba, duk wani zazzari da yake na bikin su events din da yake ta faman damun zahra da maganar duk ya daina Kai tafi-tafi sai ayi kwana uku hudu har sati Bai kirata ba, da farkon abin tana kiransa taji ko lafiya a yanayin yanda yake amsa Mata wayar saita hakura da Kiran nasa, tun Ammah na zuba ido har ta samu Zahra a wani dare ta tsareta da tambayar ko wani Abu ya hadata da Sahal ne? Ta Bata tabbacin ba abinda ya hadasu sai dai ta fada Mata yanda suka ringa yi dashi a kwanaki idan ta Kira shi.
Addu'a Ammah ta Bata tace ta ringa yi itama zataci gaba da yi, Mata sannan ta umarceta da kada ta Kara kiransa a wayar ta zuba ido kawai.
Duk abinda Ammah take na shirye-shiryen Baki Bata fasa ba, tayi waya mutanan Jordan ma sunce suna Nan tafe Amma a daure a turo Zahra Kamar saura wata data bikin.
Ba'afi sati daya da waya da kakanninta na uwa ba sakon kayan dakinta ya sauka Nigeria daga Istanbul kayan da suka gigita Mama Dan ba kayan Wasa bane set din gado har hudu kujeru set uku bayan electronics kuwa wasu har ba'a San amfaninsu ba sai dai idan an duba manual din.
Alhaji Jafar yayi fada Kamar ya Ari Baki lokacin daya Kira Abbie akan danme zasuyi Masa haka toshi meye amfaninsa da bazasu Bari yayi Mata kayan dakin ba.
Hakuri Abbien ya shiga bashi akan su basuyi Dan su Bata Masa raiba, sunga abinda ya kamata suyiwa diyar Najwa kenan.
Ammah da Mama Alhaji Jafar ya Kira ya fada musu tunda an Riga an yiwa zahra kayan dakin da duk abinda ya kamata to ga fifty million Nan ya baiwa Zahra idan komai ya nutsa saita Fara business na abinda take son sayarwa sannan ya Bata shanu biyar.
Kuka Ammah ta saka saboda Dadi ta rasa bakin da zatayi Masa godiya, yanda take dawainya da wannan marainiyar Allah Bai taba gajiyawa ba.
Mama ce ta Ari bakinta tana ta yiwa Abban godiya da saka Albarka sai faman dariya tace bakinta yaki rufuwa, tun Ammah na ganin dariyar farin ciki ce har ta Fara wani tunani na daban, Nan da Nan ta Kori shaidan akan abinda zuciya ke sawwala Mata.

Lokaci na Kara tafiya daukewar ma'amala na Kara yawaita a tsakanin Sahal da zahra, yanzu ta Kai kwata-kwata sun daina waya dashi, ana saura kwana talatin da hudu a Fara biki Wanda yayi daidai da saura kwana uku zahra da Hameeda da Abdul Hakeem su tafi Istanbul. Dan direct gurin kanwar Ummeen Hanifa zasu tafi daga baya su Ummeen sun samesu a can, idan an Gama komai su rankato Nigeria Dan da gaske Ummee ta shiryawa bikin sosai.

Washe gari, tunda gari ya waje Mama ke Kai kawo tsakar gida duk da ba aikinta bane ba Kuma halayyarta bane hakan. Yayin da a bangaren Ammah ta rasa me yake Mata Dadi duk kasala ta baibayeta jinta take Kamar ma zazzabi na neman rufata...
💋❤
💋❤️



✨AUREN HUCE HAUSHIN ✨️

💋❤️
💋❤️

STORY
&
WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH.

🔷✨PAGE ELEVEN✨🔷 (11)
________Misalin Sha biyu da rabi na Rana kawar Mama kuma Aminiyar Asabe tazo gidan macece wayayya Mai kisisina Bata fiye zuwa gidan sosai ba sai lokaci lokaci, ta Dan jima a dakin Ammah suna hira har tana tsokanar zahra da Amaryar gobe ana dariya.
Part din Mama ta shiga suka kule a master bedroom dinta.
Batafi awa daya da zuwa ba, wasu Mata suka shigo gidan lokacin Ammah tana bangaren Abba.
Zilai Mai aik cei ta leko tana fadin "uwar dakina anyi baki kuwa ko Ammah zaki yiwa magana Naga bakin nata be"
Mayafi karami ta Dora a saman gashinta da tayi parking dinsa har wajen kugunta Yana reto Baki sidik dashi jikin Nan nata Kamar ka taba jini fito.
Lekowa tayi tana musu sannu da zuwa tare da gaishe su tana fadar "ku shigo daga ciki Bari na Kira Ammar".
Ta fada tana zura silifar a kafarta.
Daya daga cikin su ukun ne ta tabe Baki ta kauda Kai tana fadar "kirawo ta tazo ba sai mun shiga ba tunda ba Zama mukazo ba"
Ita dai Zahra gaba tayi yayin da su Zilai masu aiki suka zuba musu idanu suna kallon kallo ya junansu Dan daga Jin lafazinsu sun San ba abin Arziki ne ya kawosu ba.
Kafin Ammah ta fito daga bangaren Abba sahura Daya Mai aikinta ta leka ta fadawa Mama anyi baki. Da ita da Asaben suka fito Asaben na fadin "lale barhabin kushigo Mana kun tsaya daga wajen"
Wata ce daga cikinsu Bata farkon da tayi maganar ba tace "A"a Hajiya ba Zama mukazo ba munzo ne mu karbi kayan lefen da muka kawo na Sahal yace baya yi akai kasuwa".
Lafazin da Ya yiwa Ammah sallama kenan lokacin data fito Zahra na biye da ita.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Abinda Ammah ta fada kenan a zuciyar ta Nan da Nan wani jibi ya taso Mata.
Salatin Mama da Asabe ne ya fito da Alhajin daga part dinsa yayin da su Zilai sukayi cirko-cirko duk wuta ta dauke musu Dan maganar tasu ba karamin razani tasa a zukatansu ba.
A hankali ya karaso kusa da Ammah Yana tambayar meke faruwa ne kafin tayi magana Mama tayi tsagal tana fadin "wane irin cin mutunci ne Alhaji ba laifi tsaye bana zaune zasuzo suce a Basu lefensu Wai auren amfasa".
Ta karasa fada tana fashewa da kuka tana maganganu, ita kuwa Ammah ba abinda take sai ambaton Allah yayin da Zahra ta nemi gefen inda aka shuka filawoyi ya zauna Dan ji tayi Nan da Nan jiri Yana nema kayar da ita, itama bakinta ba abinda yake sai ambaton Allah.
Kallo Daya Alhaji Jafar yayiwa Baki ya kawar da kansa Dan da alama da rashin mutunci suka shigo gidan. Gyaran murya yayi kafin yace "Masha Allah munji sakonku Amma Dan Allah ku koma kuce musu zuwa anjima inshallah Allahu za'a dawo da duk wani Abu daya kasance nasu ne har sadakin da suka kawo Allah yasa hakan yafi Alkhairi".
Yana Gama fadar haka ya juya dakinsa ya barsu a Nan a teaye, Dan dukkansu ba karamin kwarjini yayi musu ba.
Ammah part dinta ta nufa duk kwakwar mutum baze taba Gane Yanayin da take ciki ba.Dan Allah yayi Mata wata irin zuciya Mai iya danne bacin Rai da wuya ka Gane fushinta tana da hadiye fushi sosai, dakin suka bita suna Bata magana Mama sai sharbe take tana Dan Allah wannan wane irin cin zarafi ne da tazarce ace saida komai ya kankama sannan za'a bullo da wannan cin zatafin dan a wulakanta yarinya har a ringa yi Mata wani gani -gani aga Kamar wani Abu tayi yasa aka fasa".
Sai lokacin Ammah tayi magana tana fadin "ba komai Mama Daman can haka Allah ya nufa ba mijinta bane Kuma maganar mutane su ringa ganin Kamar wani Abu marar kyau ne yasa aka fasa na barsu da Allah yayi Mani maganin komai, ba komai haka Allah ya nufa rubutaccen Al'amarine baya goguwa".
Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta sun jima a falon suna tattaunawa kafin su koma dakin mamar su Zilai kuma suka nufi in da Zahra tace zaune suka dinga Bata magana duk da Bata want rude ba a nitsenta take.
Duk wannan kwamacalar da akayi su Hameeda da Salma basa Nan sunje Aiken Mama.
Tunda Alhaji Jafar ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye Bai taba zaton karamar magana daga gida irin Honorable ba Amma ya hanasu kayan ne Dan ya tabbatar da daga Ina maganar take shin da sanin uban yaron da waliyayansa ko Babu Dan yanda sukayi komai cikin girma da mutunci ya kamata ko baza'ayi auren ba to a rabu cikin mutunta juna.
Su malam Bukar da Yayan Alhajin Wanda suke 'yan maza Alhajin ya Samu da maganar basuyi kasa a Gwiwa ba zuka nufi gurin waliyyan Sahal sai dai maganar haka take Dan sun tsame ma hannunsu daga lamarin tunda iyayensa Basu da lissafi, Wai yaron ne yace musu shi baze iya auren Zahrar ba yanzu ba wadda ya tsana kamarta duk duniya".
Lokacin da suka dawowa da Alhajin wannan labarin ransa yayi matukar baci, a ranar aka maida duk wani Abu da yake mallakinsu ne.
Sai dare Abban ya Samu kebewa da Ammah in da ya ringa tausarta da kalamai masu Dadi har ta Samu ta Samu nutsuwa Amma fa kasa kwana tayi a dakin nasa.
Lokacin data dawo daki Zahra Bata tafi nasu bangaren ba tana dakin Amma a kan gadon tayi rigingine idanuta a rife hawaye na zurarowa daga gefen idon wani Abu yake Mata yukuki a zuciyar ta.
Har Ammah ta bude kofa zahra Bata sani ba saida ta zauna a kiss da ita taji shashhshekar kukanta kasa -kasa.
"Tashi zaune magana zamuyi".
Daga sama taji maganar Sam bata San Ammar ta shigo ba.
Ba musu ta tashi zaunen tana koge fuskarta da tayi wajir.
"Meye dalilin da Sahal ya fasa Aurenki ko ya sanki 'ya mace ne".
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Zahra ta dago ta kalli Ammah kafin ta fasa kukan da take dannewa tana na zuci. Kai ta shiga girgizawa tana wani irin numfashi nKamar wadda zata shide.
Kafin Allah ya batan ikon bude bakinta ta magantu. "Wallahi Ammah ban taba abinda kike tuhumata ba Koda wasa wallahi zan rantse Miki da Alur'an a bani zanyi Alwala in ratse, idan na taba Zina Ammah Allah ya haramtamin shiga Aljannarsa ranar Alkiyama"
Ta fada tana wani irin kuka Mai taba zuciyar Mai sauraro.
"Shitttt.....kada na Kara Jin wata magana makaranciyar wannan daga bakin ki. Ba zarginki nakeyi ba na kasa samun nutusawa ne tun lokacin da sabbin halayensa suka Fara fitowa, nake cikin zulumi da taraddadi saboda sanin yanda rayuwa ta Zama abinda ta zama, ba komai kansa yayiwa ke kuma Allah yayi Miki Albarka ya bakin Wanda yafi Sahal".
Bata iya amsawa a fill ba sai a zuciyar ta.
Tun bayan faruwar lamarin Zahra ke cikin damuwa Dan ma Haneeda tana tausarta da kalamai na kwantar da hankali. Ammah ta Kira su Ummee ta fada musu komai sun so kwarai zahrar taje Amma Alhaji Jafar yayi uwa yayi makarb'iya akan suzuzo idan hankali ya kwanta, da haka suka bar zancen.
A Dan tsakanain ne Aunty Hasana tazo, sun Sha jajantawa sosai da Ammah itama sai da ta tsare zahra da tambayoyi kala kala, daga karshe ta Kare da nasiha Mai tsoratarwa sosai.
Lokacin da zata koma Jos ta nemi zata tafi da Zahra Abban bai Hana ba Yana ganin idan tayi nisa da garin zatafi Samun kwanciyar hankali.
Zamanta a Jos Mai Dadi ne Dan daga baya ma fafutukar nemar Mata admission mijin Aunty Hasanar ya Fara ba'a samu wadda ake so ba, sai diploma ya nemar Mata a wata private school ta Fara computer science.
Hankalinta ya kwanta sosai ta cire soyayya daga zuciyar ta Sam taqi ba kowa fuska akan soyayya duk da yanda ake kawo Mata Rida.
Ranar wata litinin sun Gama lectures dinsu na safe suna zaune da wata course mate dinta 'yar kabilar Tiv suna wani Assignment jininsu ya hadu da jannifer sosai Dan har gidan Aunty Hasana tana zuwa idan zasuyi wani aikin.
Bayan sun Gama ne suka nufe caf'e na cikin makarantar a cire musu hard copy din aikin suka tarar da cinkoson mutane dole tasa suka fito waje ayi musu.
Har sun Gama sun fito suna niyyar tsallaka titi ne wata mota Mai azabar kyau ta tsaya dai dai inda suke tsaye. A hankali na ciki ya sauke tinted glass din motar, wani guy ne da gani hutu ya ratsa shi sosai, murmushi yayi musu idonsa na kan zahra
Yana fadin "sannunki"
Jannifer ce to amsa masa Dan tana Jin hausa Kamar jakar kano.
"Yauwa sannunka" ta fada.
Kofar ya bude ya fito Yana sanye da kananun Kaya,fari tas dashi kamar irin ruwa biyu din Nan half cast Dan sumarsa a nannade take kamar irin ta buzaye din Nan.
Cikin kwarewa da yadda da Kai kalli jannifer Yana fadar "Naga kawarki ne inso da fatan zakiyi min campaign".
Dariya tayi tana kallon Zahra wadda tayi kicin kicin da fuska Kamar zatace wayyo Allah.
"Gaskiya na tafi tunda Baki da aikin Yi ke saiki zauna".
Zahra ta fada tana nufar titi ganin an Sami space din tsallawa.
Jannifer da Dan jima dashi kafin ta shigo cikin makarantar, Koda ta shigo Bata yi Mata maganar komai ba har suka Gama lacture dinsu suka tashi. Direban su Aunty Hasana ya dauke su ya ajiye jannifer a hanya kasancewar su zahra sun gaba dasu Amma hanyarsu daya sau da Daman sukan tafi tare ranar da jannifer Bata zuwa shagonsu.
Ranar Saturday misalin hudu da rabi haka su zahra da yaran Aunty suna compound din gidan tana Dora Yara kan lilo marry go round suna Wasa kusan duk weekend a Nan suke hutawa da yamma tunda islamiyyar safe suke zuwa a weekend.
Mai gadi ne ya nufo gurin da suke Yana fadin Zahara'u ki fadawa yallabai Yana da bako a waje".
Auntyn ta fadawa Abban su Faruq Yana da bako inji Mai gadi.
Lokacin daya fito yayi mamakin da baiga bakon ba ya nufi gate Yana tambayar Mai gadi, shine yace "ni ne na hana ya shigo tunda yace bakasan da zuwansa ba bilhasal ma yace baka sanshi ba"
Kofar Mai gadin ya bude masa ya nufi gurin da motar take yayin da shi kuma na cikin ya fito. Da gaske baisan yaron ba, hannu ya bashi sukayi musahiha sai Kuma sukayi shiru Ya Aliyun ne mijin Aunty Hasanar yace Masa "ko kaine maisallama Dani?".
"Eh nine"sai Kuma ya danyi shiru.
Ya Aliyun ne yace "my friend pls talk feel free with me".
Nan yayi Masa bayanin yaga Zahra ne Yana sonta shine ya biyota gida, ya fada masa sunansa MUNEEB mahaifansa Kuma Alhaji Salman Mai fata. Kallonsa ya Aliyu ya karayi yayi mamakin yanda d'a Kamar na Alhaji Salman Mai fata yake da irin wannan tarbiyya ganin yanda mahaifansa yake da mahaukanta kudi Kuma yasan 'ya'yansa sosai Amma da yawansu gata yasa sun lalace basa ganin kan mutane da gashi.
Ya Aliyun yaji dadi sosai ya Kuma bashi damar zuwa gurin Zahrar sannan ya Dan fada Masa wacece Zahrar a gurinsa.
Lokacin da ya Aliyun ya koma bayani ya yiwa Aunty Hasana na abinda ya faru itama ta bada goyon baya tasan ko yanzu Zahra tayi gaba Allah ya Bata Wanda yafi Sahal Dan ba karya ba hadi a tafiyar.
Da dare Aunty ta Samu zahra da maganar da farko tuburewa tayi akan ita Bata so saida Aunty ta fito Mata ta bayan gida sannan ta fashimci abinda Auntyn take son ta Gane.
Washe gari Aunty har da ita aka hadawa MUNEEB abin tarba, Zahra ta Dade tana mamakin yanda akayi yasan gidan su Amma data Zama very curious sai ta gano duk yanda akayi jannifer ce ta bashi address dinta. Yau ma da yamma yazo, falon Ya Aliyu aka bude Masa yayin da Mai aikin Aunty shema'u ta Kai Masa abin tarba.
Wata straight gown ta saka ta atamfa glitter Mai ruwan peach colour sai madaidaici gyale kalar lemon green irin touching din jikin atamfar sai takalmi shima lemon green din plat Mai kyau. Bata daura dankwalin kayan ba. Ta fesa turenta Amber oud gold, tun kafin ta karaso kamshin ta ya fada Masa zuwanta, kofar ya zubawa idanu ai lokacin data shigo da sallama Saida ya Dan samu shock na wucin gadi Ashe ranar ba inishin Zahrar ya gani ba yanzu ne yaga zahirinta, a kasa ta zauna kan carpet tana gaishe shi kanta Yana kallon kasa. Nan ya gabatar Mata da kansa da abinda ya kawo na son aurenta, bai matsa Mata na lallai sai yaji ra'ayinta a sannan ba shima bai jima ba ya tafi, bayan ta shigo ne Mai gadi yayi knocking a kofar falon shema'u ta bude manyan ledoji ne ya Mika Mata guda biyu yace a bawa Zahara'u inji bakonta.
Tun daga lokacin Koda yaushe Muneeb yana hanyar gurin Zahra,r tun tana dari dari dashi har ta sake, shi mutum ne Mai saurin shiga Rai Yana da wasu Qualities da zasusa asoshi.
Kafin su rufe wata biyu sunyi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a family din Mubeen yasan da zaman Zahra haka itama nata sun San Muneeb Dan har Azare yaje ya gaishe su da ashirin bama sha tarabta Arziki ba,har Saida Abban su yayi Masa fada sosai akan kada ya Kara musu haka in dai Yana son su Shirya.
Sun daf da Gama diploma dinsu Iyayen Muneeb sukayi maganar aure, ba Bata lokaci aka saka Rana ba'a wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login