Showing 3001 words to 6000 words out of 122700 words
daya Kuma Yana Miko Masa kudi, kallon na mine yayi masa.
"Kudin sunyi yawa ne a sayan man Saida naje na duba maga yawansu". Ya fad'a Cike da ladabi, hannunsa ya zura a aljihun wandon jikinsa ya dauko wasu ya Kara Masa, sannan ya Kuma dauko wasu ya bashi alamar ya baiwa abokan aikinsa.
Godiya suka dunga jero Masa Dan inda sabo sun saba da Alkhairinsa.
Kai tsaye gurin Ashiru Mai shayin ya nufa duk da dare ya Fara Amma yasan yanzu 'yan term din nasa Basu Isa tafiya gida ba Dan sukan Kai har daya na dare suna hira.
Makullin lifan din ya mikawa Bashir Yana fad'a "Jazakumullahu khairan".
Habib ne yace "Wai Dan Allah Ina kaje a rufe wayarka tun dazu nake nemanka fa daga inje in dawo kawai na nemeka na rasa sai su Salisu ne sukace kazo nemana ka wuce unguwa".
Kusa da Habib din ya zauna na fadin "wash Allah wlh duk na gaji".
"Da kayi aikin me".
Cewar Habib.
"Bari kawai ba aikin da nayi Amma Wanda yake fuskantoni ba sauki kazo muje gida akwai sakonka da Malam ya bani na baka".
Ya fad'a Yana kikewa tare da mikawa su Bashir hannu yayi gaba gurin lifan din Habib.
Dakinsu Mahmud ya bude daki ne madaidaici da gado guda biyu da wardrobe ta jikin bango sai mirror irin na croom din Nan da AC, kasan dakin shimfide da tayil, lokacin da akazo aikin NGOs din ne aka yiwa Malam nashi falon da Kuma irin wadannan dakunan guda uku sai Kuma dakunan Yara almajirai sama da kasa.
Dakin sai kamshi yakeyi, sau da yawa Habib kanshi Yana mamakin wasu abubuwan na Mahmud sai dai ba fuskar da ze tambaye shi duk kuwa da amincin dake tsakaninsu.
Saida Mahmud yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya
Zauna a gefen gadon Yana fuskantar Habib kafin yace.
"Kai inaga fa nan da kwana uku zan ankwance".
Ya fad'a yana wani killer smile.
Zabura Habib yayi ya tashi zaune sosai Yana fadar
"Kamar Yaya?"
"Kamar yanda na fad'a maka, tsayar Dani da Malam yayi kenan yace Alh Jafar ya bani auren yarinyar Nan da ake bikinta wadda Abdul Hakeem ya kawo Mana IV last week".
"Ban Gane ba bafa ta Yaya hakan zata faru?"
Kafada ya dage alamun shima Bai Sani ba.
"Dan Allah kayi min bayani yanda zan fahimta a sakani a duhu wallahi".
"Iya abinda na Sani kenan kawai ance an bani idan inaso inyi shawara".
Cikin madaukakin mamaki Habib yace "to Kai ya kace masa?'
"Me zance kuwa na karba na gode, kasan har abada ba jayayya tsanina dasu iyayene sak, sun min abinda kowane uba yakewa dansa sun min gata sun Kula Dani lokacin da bana Gane gabas bane Gane yamma bana Gane fari bana Gane Baki,
Sun zamar min garkuwar data Hana kowane harbi ya sokeni, Toni kuwa wanen irin butulu ne da zan watsa musu kasa a Ido sufa sun san waye ni Amma suka runtse idonsu suka bani basu nuna min kyama ba, sannan ka dubi yarinyar da aka bani diamond ce fa a cikin gold kasan bani da abinda zan tunkari irin wannan yarinyar da sunan soyayya bare har aje ga maganar aure".
Tunda ya fara magana Habib yake Masa kallom mamaki Yana jinjina karfin ikon Allah, lallai wani lamarin sai Allah.
Da kyar ya Sami zarafin fadin "Masha Allah! Allah ya Sanya Alkhairi Abu yayi Dadi amma fa ka daina fadar Wai baka da abinda zaka tunkare ta wlh kafin wanna lagwanin Wanda zata aura say millions shi har wani namiji ne kawai Abu daya Sani yana da kudi mu Kuma bamu dasu Amma muna da abinda bashi dashi".
"Kamar Yaya me muke da shi Wanda shi bashi dashi? ka duba fa kaga irin yanda yake shiga babban yaro ne ga manyan motoci mu Ina muka gansu"
Dan karamin tsaki Habib yayi Yana fadain "ana gabas kana yamma ana maganar nagarta da mutunci da cikar Kamala da siffar mazantaka kana wata maganar, mu an fad'a maka haka zamu dawwama bazamyu arzikin ba".
Dariya Mahmud yayi "maida wukar abin Bai Kai haka ba ko Daman haushinsa kakeji ne ban sani ba?"
Habib tsayawa yayi galala Yana kallon Mahmud kafin ya karayin wani tsakin "Allah ya sauwake zanji haushinsa Ina ruwana dashi kawai da Daman can no banga dacewar su ba Kai Nifa idan Malam yasa Yara suyi Mata addu'a har cewa nake suyi Mata addu'a Allah ya Bata gwarzon miji na nunawa sa'a".
"Amma wallahi Habib baka da mutunci shi wannan ba gwarzo bane?"
"Ina fa namiji Yana rausaya kamar mace".
"Kaga Yi closing din wanna chapter din yayi zamuyi da wannan lamarin kaga dai komai fa Sai a hankali Dan abinda nake Sami daga wannan organization din ba Isa wannan shidimar zasuyi ba ga yarinyar Mai zafi ni kamar ma tsoronta nakeji fa".
Ya fad'a Yana dariya.
Sun jima suna tattaunawa yanda zasu bullowa lamarin.
_______
Tunda garin Allah ya waye Amma take ta kaiwa da kawowa tsakanin kitchen da dakinta zuwa dakin Baki, Saida aka kammala abincin breakfast aka babba mutane sannan ta samu ta koma daki inda ta samu kanwar Babarta Inna Maimuna a uwar daki.
Kallonta tayi "Asma'u ya kamata ki karya kinsan Ina tunanin zuwa anjima gidan ze Fara cika bazaki Sami damar Zama kici wanti abun karki ba, waini ina Hajiya Mama ne Naga yau Bata leko ba?"
"Tana bangaren Alhaji Nima nayi wannan tunanin Amma ai lafiya ita keyin shiru".
"Hakan ne Kam".
Cewar Inna maimuna.
******
Katagum road
A dakin Aunty Hasana Zahra ta kwana ita da Autart Haneefa, sai kusan goma ta tashi daga barci wayarta ta Fara dubawa ta tarar da missed calls rababa Amma Sam babu nasa ko na wani daya dangance shi, duk na kawayen da abokanin arziki Bata bi rakansu ba ta shiga toilet wanka tayi, lokacin data fito Sajida ta Samu a dakin ta shigo Mata da breakfast dinta nan, tunda ta fito Sajida ke kallon ta har ta karaso gurin mirror inda sajidar ke zauna murmushi Zahra tayi Mata tana fadin "wannan kallon fa ko na canza Miki ne?".
Kai ta gyada Mata "gaskiya Kam ba haka na Saba ganinki ba, meye yake faruwa ne? nifa tun jiya nake nema Deeni da wannan cussing din na Mushahu Aliyu, ta Aliyun tana shiga ba'a dagawa Amma su sauran wayoyinsu switch off".
Da rausayar da kanta tayi tana Dan watsa hannuwa "wallahi bani da masaniyar me yake faruwa nima hakan take kamar ke Amma nasan dai kome aje ciki yau dole su shigo garin. Ni wallahi da Aunty Hasana zata yadda da an hakura da wannan mother's day din nifa duk abin ya fice min daga Rai gani nake shima wannan aure ba yuwuwa zaiyi ba nasan dole da wata a kasa ai ba haka muka tsara abubuwan ba Amma kin ko daya fa basuyi attending ba".
Ta karasa maganar idanunta na cikowa da hawaye.
Hannunta Sajida ta kamo ta rike tana fadar. "Hqba Bestie kada kiyi Kika in Sha Allah ba wani matsala sai Alkhairi kada ki Bata lokacin farin cikinki mana".
Aunty Hasana ce ta shigo da sauri alamar wani Abu zata dauka turus tayi tana fadar "ke me zan gani Zahra kukan dai? haba you have to be very strong Mana kada ki yadda aga rauninki a kowane janibi ki Zama jaruma Mai iya fuskantar ko wane kalubale, kada ki kara saka damuwa a zuciyarki zan fita Amma in Sha Allah bazan Dade ba ki shirya kuje sama naji suna cigiyarki".
A bangaren Mahmud kuwa bayan anyi sallar Asuba a masallaci ya zauna yayi azkar dinsa Saida gari ya Fara haske sannan ya fito lokacin su Malam sun Gama karatun da sukeyi da maza magidanta.
Da sallama ya shiga falon nasa lokacin Abubakar Yana mayar da littatafan mazauninsu, sai da ya zauna sannan ya Dan rankwafa Yana gaishe da malam, Amma sai ya moko Masa hannu sukayi musabiha Yana fadin. "hakan shine sunnar Annabin Rahama Muhammad s.aw.w."
Shiru falon ya dauka bayan fitar Abubakar Malam Bai tofa ba haka Mahmud shima, Malam ne ya kauda shirun "Ya ake cikin Mahamuda wace shawara ka yanke?".
"Ba damu Baba Malam na karba na gode ayi min godiya Allah yasa hakan yafi Alkhairi".
"Allahumma Amin. Allah ya Sanya Alkhairi ya Baku zuri'a Mai Albarka Allah yasa ace gara da akayi hakan"
A zuciyarsa yake ta amsawa da Amin.
Harya yunkura zai tashi Malam yace "koma ka zauna, Ina zaka bamuyi maganar inda zaka ajeta ba da sauran shirye-shirye".
Sadda Kai yayi haka Nan yaji wani irin nauyin malam din ya taso Masa.
Kansa Yana kallon kasa yace "so nake muyi shawara dasu Habib yanda muka yanke saiya fad'a maka".
"A'a ba haka za'ayi ba nizan bada sadaki da kayan goro da alewa sai Kuma shaddoji da za'a kawo an jima Suma dinkakkune tunda abun yazo a kurace, sai Kuma gidan Nan na Hayin Banki mukullin na gurin Binya tun jiya na bashi nace yau zakuje a duba abinda za'ayi Masa".
Mahmud kasa magana yayi shi wannan gatan har yayi Masa yawa komai anyi Masa.
Rarrafawa yayi kamar yaro har gaban Baba Malam ya rinka godiya har Saida yayi Masa fad'a.
********
Amma ce da Inna a uwar dakin Ammar bayan dawowar Ammar daga bangaren Alhaji cikin tashin hankali Innar ta kalli Ammar tana fadin ke Asama'u wace irin magana ce wannan yaushe hakan ta faru duk bamu da masaniya?"
Dan nisawa Ammar tayi.
"Wallahi Nima ban sani ba Amma yace kada yaji kada ya gani naja bakina nayi shiru yana zargin kowaye yake lalata lamarin auren yarinyar Nan na kusa yake tunda yace min Malam Bukar ne yayi binciken Dan haka bazai cewa kowa komai ba har sai bayan daura auren tukunna".
"Ya fad'a Miki waye mijin?"
Kai ta girgaiza Mata alamar A'a.
Nifa Ina gudun garin AUREN HUCE HAUSHI a kwaso bara gurbi Wanda za'azo ana Mana dariya".
"Gaskiya bana tunanin haka Inna mu bita da addu'a kawai Allah ya Zama gatanta yasa albarka a ciki.
💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️
Story & written
By
✨MAMAN FATIMAH.✨
INA MIQA SAKON TA'AZIYYATA GA 'YAN UWANA
HAJIYA MARIYA ALIYU ( JIMMAN ADO)
HAJIYA BILKISU ALIYU (UMMA IKKI)
HABIBA ALIYU (UMMA HABIBA)
Na rasuwar mahaifinsu ALHAJI ALI DAN HAYA MAGAMA KAZAURE.
Allah ya jikansa ya jaddadda Rahama a gareshi tare da sauran musulmi.
Page three 🔷
📖🖋️
.............. Tunda Mahmud ya fito daga gurin Baba Malam yake nazarin yanda zai bullowa lamarin, baya son ko kadan a Sami kurkure, guri ya Sami nesa da makarantar kasancewar Alhamis ce Yara basa karatun safe sai ya zamana yawancin su suna dakunan su.
Waya ya Ciro daga aljihun wandonsa yayi dialing din number Bata jima tana ringing ba kada daga magana ya Fara "kana jina Sameer sakon Dana turo maka kada a samu kuskure kayi kokarin ganin komai yayi yanda ya kamata fa".
Dan Jim yayi alamun ana fad'a Masa wani abu
"Ok to shi kenan take care".
Ya kashe wayar.
__
Nama ne da kayan miya ake ta shigo dasu cikin gidan da manyan kuloli sabbi Hajiya mama ce a kofar kitchen din na tsakar gida tana bada umarnin abinda za'ayi, yaran dake shigo da kayan ta kalla "wannan fa daga Ina?".
Magaji ne ya Bata amsa kafin yaron data tambaya ya fad'a Mata "tare muke Mama na abincin bakin Abba ne".
"Ikon Allah Naga ai an kawo wasu da sassafe dazu gasu nan har an kusa Gama aikinsu".
"Eh to shi dai yace a kawo wadannan ma".
Magajin ya fad'a Yana shiga dakin Amma.
"Kai dawa Kuma kake tafiya kana magana"
Cewar Inna maimuna.
Kusa da ita ya zauna Yana fadin "nida Hajiya mama ne kayan miya ne da Naman rago Dana kaji Abba ya Kara badawa aka kawo shine take magana ko yayi yawa kame?"
Dan murmushi Amma tayi "Abban Nan naku baya son a zauna lafiya wallahi magaji kamar zai aurar da Yara uku sai irin wannan shidima yake haka".
Kai magajin ya jinjina "Amma kenan kin manta yanda Abba keson Zahra ai kawai kowa ya zuba Ido ana auren uwar masu gida tab ai kowa sai yasan anayi Yasin, ki Bari kawai Ammah Nan zan kawo nama a ajiye min".
Ya fad'a Yana dariya ya nufi kofar fita saboda sallamar wasu Mata da yaji a kofar dakin.
___
Daki Mahmud ya koma ya samu Habib a tsaye a tsakar dakin da alama daga wanka ya fito, saida ya Gama wayar sannan ya kalli Mahmud.
"Wai ina kaje ne? Naga fitowarka daga gurin Baba Malam kafin na saka caji na nemeka na rasa, Bilya ne ya kirani Wai mu sameshi a hayin Banki shi Yana can yaje da masu aiki su duba yanda za'ayi gyaran"
Dan Dafe Kai Mahmud yayi ya Dan fesar da numfashi.
"Ikon Allah Wai Daman kamar jira kuke ace za'ayi min auren Nan kowa sai rawar jiki yake yi, daga fad'a shine har ya want kwashi jiki da masu aiki ya tafi tun garin Bai Gama watstsakewa ba".
"Naka wasa ne Alaji, aini yanzu haka mun Gama magana dasu Bashir sunce mun gasu Nan zuwa har suna cewa shegen zurfin ciki ne da Kai baka fad'a musu ba jiya ko kunya kakeji irin ta Mata".
Ya karasa maganar Yana dariya.
Har ya nufi gurin mirror ya tsaya "kaji na manta ba Salis yace na tura Masa cikakken sunan da ze saka a IV da zeyi a waya ya turawa friends na kusa".
"Ok ba matsala ka tura Masa kawai da sunan aika Sani ba saina maimaita make ba".
Misalin karfe Sha daya na safe wata bakar Hilux sabuwa kar ta dira a kofar gidan Malam Bukar.
Lokacin yaran sun firfito suna sugogin su masu wanki nayi masu wasa nayi Amma idan ba fada maka akayi bazaka taba cewa yaran Almajirai bane kowa cikin tsabta Kuma a lokacin anyi hutun makarantar book shi yasa basayi tunda suma tsarin makarantar gwamnati suke bi.
Mutane biyu be suka fito daga motar da sauri 'yan samarin dake kusa taso da sauri suna fadin barkan ki da zuwa kasancewar sun saba dasu sosai sune wadanda suke kawo musu tallafi daga organization din.
Da sauri suka bude musu falon saukar bakin Malam kafin wani ya shiga ya fadawa Malam din.
Ba jimawa Malam din ya fito suka gaisa a mutunce, sannan suka gabarwa da kayan abincin da suka kawo sannan suka gabatar Masa da bukatar daukar Mahmud zuwa wani taron karawa juna Sani na makarantun tsangaya Wanda za'ayi a kano, tunda shine Wanda suka dauka aiki a Nan tsangayar yake wakiltar su kuma gobe juma'a za'ayi taron na Rana daya ne kawai.
Dan Jim malam din yayi kafin yace " Ikon Allah malam Sameeru ga koshi ga kwanan yunwa WALLAHI shi Mahmudan dai baze Sami damar halartar taron nan naku ba, domin a goben in Sha Allah za'a daura Masa Aure".
Cikin wani irin madaukakin mamaki Sameer dake kusa da Malam din Kuma jagaban tafiyar ya kalli Malam Yana cewa.
"Aure! Kuma Malam?".
Kai ya jinjina Masa alamar tabbatarwa, "yanzu haka suna can gidan da ze zauna ana dudduba gyaran da za'a Masa duk da gidan Bai jima da kammaluwa ba kasan kullum abin duniya sabuntashi akeyi".
Kai ya jinjina ya hadiye wani yawu da kyar shifa duk ya shiga rudu meye hakan Wai Kuma.
Fara'ar dole Sameer ya kirkiro Yana kallon Malam yana fadar "Masha Allah Abu yayi Dadi to ai mu wannan lamarin namu ne munzo a dai dai kenan tunda Abu ne na ma'aikacin mu koma kunya zatayi Masa malam kada kuyi komai yanzu zanyi waya za'ayi duk abinda ya kamata tun daga abinda ango ze saka har abinda za'aci duk Yana karkashin kularmu tunda mu yakewa aiki, Kuma zamu zauna sai an daura auren damu in Sha Allah. Maganar taron Kuma sai dai a daga zuwa wani lokacin Dan bamaso wani yayi missing gaskiya".
Tunda Sameer ya Fara Kora bayani malam ke jinjina Kai saida yake Aya sannan ya Sami zarafin magana.
"To malam sameeru anyi haka abin fa da yawa kids bakuzo da Shirin wannan abun ba kunzo Kuma kuyi ya kuyi makarbiya ai da wahala abun".
Dariya Sameer din yayi Yana fadar "malam ba abunda ze gagara kungiyoyin masu karfi ne, yanzu ma ga wannan saboda biyan sadaki".
Ya aje Masa cheque na Banki suka Mike Yana fadar "Bari na Nemo shi a waya sai muje muji meye shirye-shiryen nasu, a huta lfy".
Suka kad'a suka fita.
_____
Kyakykyawan guri ne Aunty Hasana ta kama inda za'ayi mother's day din gurin ya kayatu ba karya kudi dai an kashe su gurin Kama event center din, anyi taron Mata 'yan gayu kamar ba gobe amarya tasha kyau kamar a dauke ba boye.
Ga wani slow music da mc din ya saka na wakar Amarya da ango kowa ka gani cikin nishadi yake sabanin Amarya da Yayarta Banda ta Riga ta gayyato mutane harda wadanda sukayo Mata tafiyayya sukazo da ba abinda ze saka tayi wannan taron to Amma mutum Bai Tara Sani ga Allah ba.
An raba kayayyaki na alfarma na bikin, sai magariba taron ya tashi, zuwa yanzu 'yan Qananan maganganu sun Fara fita a tsakanin kawayen Zahra tunda har zuwa lokacin ba wani duriyar Ango ko wani nasa, sai Dan kus-kus ake abinda yafi bada mamaki bai wuce ganin anata faman programs ba normal.
Su Mahmud Basu samu kansu ban sai bayan sallar insha'i lokacin suka zauna Dan wuni guda suna ta faman sunturi daga can zuwa can abin dai ba sauki dan su sameer suna zuwa gidan suka babbago aikin da sai anyi sati ba'a Gama ba Dan sunce tsarin gidan gaba daya za'a sake, basunda ta cewa tunda oganninsu ne sai godiya suka dunga zubawa harda su Bashir.
Gurin karfe goma malam ya Kira Mahmud a waya yace yazo cikin gida ya same shi.
Saida ya leka falon iya Abu suka gaisa tana faman jansa tana ita ce ta karfen Dan haka ita zata koma sabon gidan a kawo Amarya nan.
Da haka ya karasa turakar malam Yana zaune a falo Yana sauraren wa'azi a TV, yayi sallama Malam din ya bashi izinin shiga, Nan kasa ya zauna Yana gaishe da malam din.Wasu manyan ledoji malam din ya nunawa Mahmd Yana fadin.
"Dauko wadan can kayan ka duba daya Wanda nasa a kawo maka ne biyun Kuma wadannan masu kungiyar ne ta taimakon tsangayu suka kawo ga lemuka can da ruwan roba sun kawo yafi catoon dari sunce kada ayi abinci ma duk za'a kawo, har na rasa da wane bakin zan gode musu, sai dai Ina rokon Ubangiji s.w.w yafi mu yabawa, naji su Habibu ma sun ce sun dauko aiki Mai yawa a wancan gidan ko?"
"Eh wallahi munyi-munyi su Bari suka Kiya Wai haka aikin