Showing 117001 words to 120000 words out of 122700 words

Chapter 40 - Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

595

gidan su saliha sani Musa ne tare mukayi Excel da ita".
Cikin ikon Allah suna tsayawa a kofar gate din motar ya Abba ta shigo shida Abie dinsu sun dawo daga kwangwalam bodar NIGER inda sukaje gaisuwar mahaifar amininsa data rasu jiya, sun biya ta kazaure gurin wani abokin aikinsa daya kwanta a Asibiti Shima a Nan sukayi dare.
Ganin mota a kofar gidan yasa Abie yace Abba ya tsaya yaje yaji ko lafiya Yana fita Mai gadi ma ya fito Yana ganin Abba ya karasa gurin da sauri, fitowa Sameer yayi ya tarbesu Yana Mika musu hannu sukayi musabaha Yana fadin "Ayi hakuri munzo cikin dare ba sanarwa,Daman munzo mu tafi da zahra ne tun Rana tazo Bata Fadi zata kwana ba sai Yanzu mijinta ya dawo gashi ba waya a hannunta, ganin da sauran daren yasa muka biyo samunta".
,"Ok. Ba damuwa muma Yanzu shigowar kenan munje unguwa tare muke da Abie".
"To mu karasa Mana na gaishe shi ya juya yabi bayansu suka nufi gurin Abie din, Rukayya gani tayi kamar akwai rashin kyautawa ace tana kallo aje a gaishe da babban mutum tana zaune sai kawai ta fito ta rufa musu baya.
Cikin girmamawa Sameer ya gaishe da Abie din sai Jin muryar Rukayya sukayi daga baya tana gaishe da Abie din, hankalin Ya Abba biyu ya kasu ga wata murya data fizgeshi lokaci Daya ga Kuma bayanin da yake yiwa Abie.
""Ba wani Abu Bari a Kirawo Umman tasu saita fada Mata ta fito wannan ai shashanci ne ya za'a bar yarinya ta nemi gurin kwana da mijinta da komai".
Sameer ne ya Dan shafa Kai.
"Ayi hakuri Abie mijin ne baya Nan sai yanzu ba dadewa ya shigo kasar".
Mazaunin direba Abban ya koma suka nufi ciki tunda Daman Mai gadi ya bude gate Yana jiran su shigo.
A waya Abie ya Kira Umma har lokacin idanunta biyu da wuya tayi barci matukar tasan mijinta baya Nan da sauri ta dauki wayar tana Masa sannu da zuwa.
"Yauwa ya amsa a takaice Yana fadin. "ki taso bakuwar da kikayi a gidan mijinta ya dawo gasu Nan a gate". Ya kashe Yana nufar part dinsa.
Shiru tayi waye ya fada masa da bakuwar a gidan jiki ba kwari ta nufi dakin sajida, barci ta Samu tanayi sadidan kamar Nan duniya Bata da damuwa Kota sisi dakin ta shigo tazo bakin gadon ta tsaya tana Kiran sunan ta a hankali, tana fadin "tashi ki kimtsa ki fito ga Mai gidanki can zaku tafi gida". Idanun tadan zaro tana fadin "wallahi bazani ba Umma kice musu bana nan
sai hawaye"..


AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH.



Page 43.
_______ kuka zahra keyi ba kakkautawa a hankali Umman ta zauna kusa da ita, ki daina kukan Nan kiyi hakuri ki tashi ku tafi, kiyi ta addu'a Allah ya kawo Miki saukin ko menene damuwar, kada ki Kara tunanin yin irin haka idan Abu ya dameki ki tafi kibar gida ba shine maslaha ba kinji, tashi ki cire Rigar barcin ki canza suna jiranki Kinga dare ya farayi inaga tun Rana suke bulayin nemanki sai Yanzu suka samu inda kike".
Kai ta gyada tana goge hawayenta, Bata taba tunanin yau zata koma gidan Nan ba Dan ita a budget dinta daga Nan gaba zatayi Dan kasar tayi niyyar tsallakewa tayi gaba abunta tunda passport dinta yana jaka, to Wai ta Yaya suka gano tana gidan Nan Wama yasan gidan a cikinsu, to shi yaushe ya dawo?
Haka zuciyarta ta dunga sake-sake.
Fita Umma tayi ta Bata guri ta canza Kayan, jiki a mace ta fito ta iske Umma da Ya Abba a parlourn, gaishe da Ya Abban tayi ya amsa Yana fadin "wallahi kin wahalar da mutane da wannan Daren Kika sakasu fitowa har da mace Ina jinma mijinta ne"
.ita dai zahra Shiru tayi Masa ta nufi Hanyar fita daga parlourn tana fadin "ummah na tafi Saida safe".
Ta fada tana yin gaba "to Allah ya tashemu lafiya kiyi hakuri da safe idan Allah ya kaimu ki bude wayar zamuyi magana".
"To Ummah in Sha Allah Zan bude". Suka fice daga Fallon. Ya Abban Yana biye da ita tun kafin ta karaso Rukayya ta taho cikin sassarfa ta ringume Zahra tana fadin "wallahi kin dauki alhakina da Hajiyar makwarari Kinga kukan da muka Sha yau? Tambayi Ya Sameer kiji duk kin tashi hankalin mu".
Wani sanyi ya ratsa Ya Abban Jin Rukayya ta ambaci Sameer da yayanta, daman Kuma yaga Kama ta zahiri duk da dare ne Bai Hana shi ganin kamannin nasu ba.
Shiru zahrar tayi Mata ita sai Yanzu taji wata kunya duk ta rufeta, me kenan tayi? Shike Nan zasu dauka fa tayi yaji ne dole ta magantu.
"Wai Dan Allah Aunty Rukayya ku kasa barina nayi kwana ko Daya ne a gurin Ummata nifa bada wata manufa ba na taho kawai dai nasan idan nace zanzo ba Bari Oga sameer zeyi ba zece saina nemi izinin....."
Sai tayi Shiru.
"Izinin wa za'ace ki nema?".
Gaba tayi kawai ta nufi gurin da Sameer yake tsaye jikin kofar driver, da wannan damar Ya Abba yayi amfani ya matso kusa da Rukayya yana fadin "Ashe Aunty tasha kuka zanso Naga kina matse hawaye".
Kallonsa tayi haka nan taji yayi Mata kwarjini.
'yar dariya tayi tana fadin "Ina yini?"
"Lafiya kalau beauty, ki saka min number ki Zan kira naji ya kukaje gida tunda sister Zahra har wayar tayiwa tawaye".
Ya karasa Yana murmushi itama murmusawar tayi tana karbar wayar, number ta saka Masa ta Mika Masa wayar tana fadin "bari na wuce ya Sameer Yana jirana"
Tayi gaba.
"Ok saina kira shima gurin Sameer din ya nufa sukayi sallama, ya leka ta window Yana yiwa Zahra magana.
Tunda suka dauki hanya ba Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciyar Zahra ke sauka kadan- kadan.
A hankali zahra ta bude Baki tace "Dan Allah oga sameer kayi hakuri na Bata maka Rai bada niyya nayi ba kawai dai Ina son Naga Ummah ne Naga kuma kamar bazaka yarda naje na kwana ba".
"Ba komai kawai, Daman Yanda su mommy suka tada hankalin su ne ya daga min hankali nasan ba Bata zakiyi ba tunda da kafarki Kika fice".
Shiru tayi tasan magana ce ya fada Mata a kaikaice, tasan a kule yake da ita kawai dai Batasan dalilin Daya hana yayi Mata buyaji ba, Dan taga alama ya iya tijara Yanda ya karewa Rukayya dazu ko shi yasa taja bakinta tayi shiru Yanzu.
Sha biyu da minti goma yayiwa Mai gadin gidan horn Saida ya leko shima Sameer din ya fito Yana ko waye sannan ya bude.
Yana shiga da motar Maimakon yaje kofar main parlourn sai taga yabi ta baya ya nufi wani gani Mai azabar kyau ko Ina tar kamar dauko ginin akayi aka aje ga wata 'yar baranda data hade ginin biyu an saka glass anyi kamar katanga da wasu irin flowers masu kyau a jere ana ganinsu gurin yayi matukar kyau da burgewa a kusa da steps din da ze sadaka da
Main parlour, Zahra ba tayi kokarin bude side din da take zaune ba, dan juyowa Sameer yayi "Dan Allah kada maganar nan ta fita kawai da safe ki fada musu mun Dade a Asibitin ne yasa Kika bamu dawo da wuri ba sun kulle, kiyi using da Nan kawai ki barsu su a can, Rukayya zata kawo Miki kayanki da safe kiyi idan Allah ya kaimu".
"To nagode".
Abinda ta iya fada kenan, ta bude ta fita Rukayya man ta fito tana fadin " Bismillah kizo muje na rakaki".
Tare suka jera suka hau zuwa kofar, ita Kanta kofar abin kallo ce ita Yanzu zahra abin har ya daina Bata mamaki so take taga iya gudun ruwan bayin Allah nan Kullum lamarin su ba baya yake ba gaba yakeyi daga Nan sai can suna shiga ta Kara jinjina girman lamarin Wai shi wannan abokin nasu wane irin kusancin ne a tsakanin su da za'a dunga sauke ta a duk inda akayi ra'ayi. Wannan part din yafi wancan komai parlour sun Kai hudu, a cikin parlour na uku ne suka taka steps ya Kai shida sannan suka shige want korido ko Ina tadal sai wani special kamshi ke tashi bedrooms ne guda biyu a jere, Rukayyar ce ta Dan juyo tana murmushi "to madam gasu Nan saiki shiga Wanda kike so ki kwanta, tunda kin samu muna yawon dare kamar marasa gaskiya, Zan Baki shawara sai kin Zama jaruma fa a gidanki Dan Ya Mahmud wallahi Mata rubibinsa suke, idan kikace Abu kadan Zaki fece kece ki tafi kece a kwana Dan idan yayi wata tafiyar sai ki kwana hamsin Baki saka shi a idonki ba, pls you have to be very strong gaskiya kada ki yarda a gano Ina kike da lapse akwai damuwa kwarai ki rike mijinki da kyau ki mutunta shi ki girmama iyayensa zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah, zabi na rakaki dakin na wuce barci Kuma nakeji tunda Allah yayi Mana gyadar dogo ya rabamu da kwanan zaune to matar big bro ta Bata Ina Ni Ina barci ai sai kwana sallah".
Ta fada tana 'yar dariya.
"Ki sakani kowanne Wanda za'a sanwa ya taba cewa way gutsiri nan? Duka zaman na yau zuwa gobe ne Dan gida zamu koma bana son wani surgery a Nan idan ma yimin din za'ayi ba wannan Mai fuska kamar Jan karas din zatayi min ba muma muna da qualified a can Dan dai kada nayi musu dashi ne kawai".
"Kinga mu Shiga na koma dare Karayi yakeyi gara naje na kishingida".
Dakin da yake facing dinsu ta bude MashaAllah" ta fada Tana karewa dakin kallo sannan ta juyo tana fadin mu kwana lafiya"

Kallonta Zahra keyi tana son tayi Mata tambaya Amma ta rasa ta Ina zata Fara, Dan Yanda tasan gudan Nan da Yanda take fadar wasu abubuwan akan Mahmud ga Kuma abinda Hajiya kakarsu ta fada Mata dazu maganganun suna kamanceceniya da juna amma Bari ta Adana tambayoyinta da sauran lokaci.
"Nagode Aunty sai da safe, Amma fa Ina Jin tsoron gurin nan fiye da can din wallahi, Kinga Nan ba kowa. Allah mu kwana tare ko kin tafi bazan iya barci ba".
Dan Jim tayi tana tunani ita Kanta Bata San dalilin Ya sameer na kawota Nan ba, amma tasan dole da dalilinsa nayin hakan.
"Ok ba damuwa Bari naje na dauko sleeping dress Dina da naki saina dawo"
"Ok, yauwa Aunty ki taho min da phone Dina tana cikin bedside".
Ta nufi Hanyar fita, wayarta ce ta dauki ringing number ce tasan Wanda ya Karba ne dazu a ta daga da sallama suka Kara gaisawa ya tambaye ta ya suka zo gida ta fada masa lafiya kalau sukayi sallama ta fice.
Kofar ta rufe ta farko tayi gaba tana fadin "kamar wata Rukayyar mahaukata na shigo wannan part din na kwanta a can ma naki kwana ballentana a Nan yarinya Allah ya kawo mijinki ki tarairayi kayanki kuna gefe Naga alama sai nayi Mata budedden karatu sannan zata gane mace har Mace ta fita kunya Amma ki tsaya kina Wasa da damarki".
Ta wannan barandar Mai glass ta Shiga Daya part din da yake tasan wanancin lambobin kofofin tunda duk sati suke zuwa da sauran yaran gidansu suna gyara bedrooms din kawai sauran Kuma da masu aikin da sukeyi dakunan kwanan ne dai Batasan dalili ba masu aiki basa shiga.
Ko Ina tsit a gidan baka Jin komai sai kukan kananun kwari da dai daikun tsuntsaye ta gefen inda zahrar ta kwana ta wuce da gaske ko ita data Saba da Shiga gidan wani lokacin tsoron Yana kamata bare a irin Nan da sauri ta shige parlourn na uku ta wuce corridor da za sadata da dakunan.
Tana bude dakin zilai ta bude ta fito tana fadin "sannunku da dawowa, Dan Allah lafiya kuwa tun rana sai Yanzu sha biyu ta wuce?'.
"Lah ba wani damuwa munje unguwa ne motar ta samu matsala sai dazu muka shigo garin muka biya gidan mommy a can muka Shantake Sai Yanzu ya Sameer ya kawo mu".
Wani sanyi zilai taji a ranta, "to ai shikenan Allah huta gajiya da ko barci na kasayi ina ta tunani barkatai".
"Kai haba ba komai Allah ya tashe mu lafiya ta bude kofar ta shige itama Zilan ta Koma ciki.

Tun bayan fitar Rukayya zahra ta dosana gefen ta zauna ta zabga uban tagumi, da sauri tashi ta fito ta dauko handbag dinta ta biyo Hanyar da suka shigo kofar fitar ta murda tajita bam ko motsi batayi, tayi tayi taji kamar tana taba dutse, hakuri tayi ta juya sai lokacin tsoron ya rufeta da gudu ta shige dakin tana turo kofar, dube-duben makulli kofar ta Farayi ita dai bataga gurin wani key ba har zata hakura taga wasu numbers a jikin wani Abu kamar switch din kunna wuta numbers din ta Danna Yanda suke a jere taba taba ta karshe taji want Dan sound daga jikin kofar handle din ta Kama zata bude taji ta rufe gam, sai lokacin ta Dan samu peace of mind, ta nufi gadon ta aje jakar a gefe ta nufi toilet dole saita sake gyara jikinta. Tana Shiga ta cire rogar material din sajida data sako ta taho da ita ruwan zafi ta hada tayi wanka ta fito da towel a jikinta sanin ba wasu kayan sakawa a Nan yasa ta Haye gadon daga ita sai towel ta rage hasken dakin ta janyo lallausan bargo ta rufe jikinta sai fuskar kawai ta Bari a hankali ta Fara Addu'oin kwanciya barci, kafin ta Gama barcin yayi awon gaba da ita.


Karfe Daya da rabi daidai jirgin Max air ya sauka da duban jama'a daga kasahe daban daban na duniya, cikinsu harda Muhmud Muhammad Dange, a hankali yake tako stairs din jirgin sanye yake da kananun Kaya Ash T- shirt da black jeans a jikinsa sai jakar laptop dinsa a kafadarsa.
Yana karasa saukowa wani matashi fari marar jiki ya nufe shi Yana fadin "barka da sauka yallabai, ga key din motar Nan a hannunta oga yace na kaika gida, sai Balarabe ya bimu da wata motar sai mu dawo tare dashi".
Hannu ya mikawa Mai bayanin Yana fadin "bani key din kawai kace masa na gode kwarai da kulawasa, zanyi driving da kaina".
Mika masa Yana fadin "Allah ya tashemu lafiya kayi min godiya sosai ya Ciro kudin America ya mika Masa sannan ya bar gurin.
Lokacin Daya fito daga airport din Daya da minti ashirin da bakwai, tuki yake cikin nutsuwa sau biyu kawai ma'aikata suka tsayar dashi, har yazo gate din gidan ba Wanda ya Kara tsayar dashi, sau Daya yayi Horn Mai gadin ya falfalo da gudu yana leken waye a Nan baisan motar ba Dan haka ya koma ya dauko abinda ze Bashi kariya.
Kafin ya bude ya fito, Mahmud ya fito ya harde hannusa a kirjinsa ai Mai gadin Yana ganinsa yayi sauri ya koma da gudu Yana Fadin "barka da sauka fari Mai farar Aniya Allah ya Kare gabanka da bayanka baya Mai goya marayu"
Dan murmusawar Mahmud yayi Yana fadin "wani Abu sai Malam Musa shi Babu ruwansa da dare". Ya fada Yana kunna Kai harabar gidan wadda take kamar rana, mutane hudu ne suka bullo daga mabambantan gurare. Parking lot suka nufa sun San Mai gidan ne tunda suka jiyo hargagin Malam Musa. Shima da gudu ya karaso gurinsa Yana cigaba da Yi Masa kirari.
Sun gaisa sosai dasu har kusan minti biyar sannan yayi musu sallama Saida safe ya nufi babban part din, Murtala ne yayi sauri ya sameshi "yallabai Ina ganin madam din kamar tana can sabon gurin can Dan Nan Naga Sameer ya ajesu dazu ita da Rukayya kanwarsa, can ya nufa Yana mamakin me yasa Sameer ya kaita can alhalin yace a barta a tsohon part din.



AUREN HUCE HAUSHI.





MAMAN FATEEMAH.





Page 44

_________ kamshinta ya Faraji Yana shigowa parlourn, wani limshe idanu yayi Yana ayyana abubuwa da yawa a ransa, direct ya wuce bangaren bedrooms din Yana jinsa cikin nishadi, wato Sameer Yana expecting dinsa ne a kasar shi yasa ya bude Mata nan kenan, a hankali ya taba handle din kofar farko ya jita a bude Shiga yayi komai tsab, iska ya huro daga Bakinsa ya aje jakar laptop dinsa a Kan sofa da take dakin, ya zauna a gefe Yana cire takalman kafarsa, wanka yake son ya Fara kafin ya Shiga gurin waccen danger girl din "yar yarinya ta Hana shi sakat duk ta birkita Masa Lissafi" ya fada a fili Yana rage kayan jikinsa.
Wanka ya shiga bai wani dauki dogon lokaci ba ya fito saboda dare ya Fara nisa ga gajiyar zaman guri daya, pyjamas ya saka masu kalar sky-blue ya fesa turarensa ya dauki wayoyinsa ya fice daga dakin ya nufi dakin da zahrar take, wani Abu ya taba mai Kama da socket din electric na kunna wuta sai kofar ta bude,a hankali ya shige Yana Jin kamshinta yanda ya cika dakin, shi dai yawanci duk matan da suka zamar Masa dolensa suna bala'in son kamshi, yana ida shigowa kofar ta rufe Kanta Wai Abu ya taba ba Wanda zahra ta taba ba, yayi gaba Yana nufar gadon inda ya hangeta ta kudundune cikin bargo, da gani a tsorace tayi barcin, wayoyinsa ya aje a Kan bed side ya zauna a gefen gadon Yana Kare Mata kallo, shifa duk hankalinsa ba a kwance yake ba tunda aka fada masa matsalar dake damunta yaji ba shida sauran nutsuwa idan ba zuwa yayi ya ganta ba, Kuma Dole ma yasan abinyi akan ciwon Nan ko ana Wasa da wasu lamuran Banda lafiya baik'i tasan kowaye shiha a wannan lokacin dole ya dauketa ya kaita inda za'a dubata Masa ita duba na gaske.
Remote din AC ya dauka ya rage gudunta dakin yayi sanyi da yawa duk da Yana son sanyi amma wannan yayi yawa, a hankali ya saka hannu ya janye bargon daga fuskar ta barcinta takeyi shower cap din dake Kanta ta cire sai gashi Baki sidik Yana ta walqiya a cikin Dan hasken data Bari a dakin, Kara zame rufar yayi har zuwa kirjinta jikin sai wani glowing yakeyi Jin sanyi Yana shigarta yasa ya juyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login