Showing 30001 words to 33000 words out of 81675 words
Dariya yayi da cewa. "Ke wani zubin kamar baki da wayo Sam.
In banda abinki ai babbar cutarwa dazaki mata d'ayane shine kisa mijinta ya dena kusantarta. Ina akan abinda kukema kishi kenan mata. Idan kika mata haka kin kasheta da ranta. Dan zata zama photo ne agidan kece matar gida. Dan azahiri ADAMS zai dinga nuna miki kulawa dan kin d'auke madarajarta agaresa.
Amman idan kikace zaki haukatar da ita ko kisaka fad'a atsakaninsu ko kizama kece kyentattatciya agidan ko yarabu da ita ko ya dinga wulaqantata da sauransu nagaya miki hakan dawowa kanki zaiyi..
Shuru TAUDHAT tayi tana nazarin maganar tashi..
Can taja numfashi da kallansa tace nayarda da abinda kace. Kuma na gamsu.. Yanxu bani maganin na qara gaba..
Miqa mata wani kulli yayi da cewa.. Ki kwab'a da jinin al'adarki ko ruwan ni'imarki.
Karb'a tayi da cewa "nagode bara naje..
"Ai bakiji qarashen zancen nawa ba.
"Toh kuma menene yanxu.
"Kishiyar sirikarki Hajjiya Rukayyat tayi miki illa fah.
Waro ido waje TAUDHAT tayi cikin tsoro tace.. "Metayi min😳
"Tabaki wani abinci kinci wanda yake d'auke da magani..
Gyara zama TAUDHAT tayi da cewa.. "Eh haka ne. Dan sunzo kawo kayan aure na tabani nama me d'auke da magani akan maganin mata ne. Wai tabama kishiyata mah? Shiyasa take juya Adams yanda take so. Dan haka gashi nima naci danta d'aukemu duk d'aya ne..
Murmushi yayi da gyara zama shima yace.. "Toh ba gaskiya bane.
Kinsan maganin me tasaka miki aciki..
Girgiza mishi kai TAUDHAT tayi.. Yaci gaba da cewa. Maganin hana d'aukar ciki ne..
Maganin dabazaki tab'a haihuwa da ADAMCY ba tabaki. Ammafa shi kad'ai. Zaki iya haihuwa da wani amman banda Adams. Wannan shine gaskiyar zance...
D'ora hannu aka TAUDHAT tayi ta zambad'a ihu dana cewa.. "Kutumar bura'uba.. Meyasa tamin haka.
Tab'e baki malamin nata yayi da cewa.. "Nima ban sani ba. Dan nayi duba nagane meyasata yi miki hakan banga komai..
Da b'acin rai TAUDHAT ta katseshi da cewa. "Hmm lalle ta ibo ruwan dafa kanta.. Dubamin kagani itama banda ikwan yi mata komai kamar na NUFAISAT ne..
Gayara zama yayi dayin zane zanansa can yayi murmushi dace mata.. "Kina da ikwan yimata komai dan tana wasa da sallah.. Sannan itama ai biye biye takeyi sosai.. Qilama tafiki yi. Dan daga dukkan alamu tayi mugayan abubuwa sosai akan jama'a..
Sheqewa da dariya TAUDHAT tayi da cewa.. "Kasan me zaka mata.. Girgiza mata kai yayi.. Taci gaba da cewa. So nake kajefeta yanxu ka kwantar min da ita yanda zata kasa komai arayuwarta..
"Kai TAUDHAT. Ayi haka
"Mezai hana kuwa. Kashe min rayuwa tayi fah.
"Kuma fa haka ne.
"Ashe kagane. Maza jefe gangan jikinta naji sanyi araina.
Ba b'ata lokaci yahau yin wasu surkulle nan take ya jefa wani dutse sannan ya kalleta da cewa.. "Tashi kije gida zakiji tana asibiti. Kuma ba abinda zasu iyayi mata..
Dariya TAUDHAT tayi da cewa.. Tukwicin wannan abun daka min shine zan had'a kai dakai kamin ciki mijina ya raini d'an malam..
Washare baki yayi cikin matuqar jin dad'i yace.. "Kai amma TAUDHAT kin biyani dan naji dad'i sosai..
Tashi tayi da yafa gyalanta ta sab'a jakarta tace.. "zaka jini bayan kwana biyu.
"Ina nan ina jiranki sarauniyar mata.. Takawarki lafiya. Ba wata mace daza tasha gabanki Hajjiya TAUDHAT..
"Kwad'awar taka ta isa haka. Kaidai kaga tafiyata..
Cije baki yayi cikin matuqar jin dad'i. Shi kad'ai yasan abinda yake ma murnah
Sam bata wucce gidansu ba gidanta ta wucce. Amman takira Adams ta gaya mai ta wucce gida basai yaje gidan nasu d'aukarta ba.. Dan tayi baqi ne. "Ok. Yace mata.. Sannan takira mamanta tagaya mata ta wucce gida..
Da misalin qarfe tara na dare NUFAISAT ce kwance kan d'aya daga cikin kujerun falanta. Tunani take meya hana ADAMS dawowa gida da wuri Yau
A hankali tad'auki wayarta dan takirasa sai kuma taji dawowarsa damasu tsaransa...
Da sauri taje ta bud'e mai kofar falanta dan tasan nan zai fara murd'awa..
Aiko haka ne. Dan part d'inta ya fara nufa kamar yanda ya saba.
Ganinta a bakin kofar ya bashi mamaki. Kan yayi mata magana ta rungumesa tana cewa.. "Haka kawai naji gabana na fad'iwa na rashin ganinka da banyi ba lokacin daka saba dawowa. Duk dako. Bayau bane karo na farko daka tab'ayin hakan.
Murmushi yayi da d'ago da fuskarta da yayi ya manna mata kiss da cewa.. "Wallahi momy Rukayyat ce bata da lafiya.. Wai tana shiga kitchen sai qarar fad'uwarta akaji..
Salim ne ya kawota asibiti. Saidai duk binciken da doctors sukayi basuga abinda ya haifar mata da hakan ba..
Cikin damuwa NUFAISAT tace.. "Ikwan Allah. Toh yanxu me yake damunta.
"Komai fa najikinta yanxu ya dena aiki.. Kawai bakinta ne yake aiki wajen magana da idanunta da suke ganin mutane
NUFAISAT taja numfashi tace.. "Toh dama mutane sunayin irin wannan ciwan ne..
"Gaskiya ban tab'a gani ba. Ki kwantar da hankalinka zata samu lafiya..
Cikin damuwa taraba jikinta da nashi tace.. "Toh Allah ya yarda..
"Amiin yace daci gaba da cewa. Bara naje nayi wanka naga qawar tamu dan kwata kwata a gajiye nake..
Murmushi tayi da cewa. "Kadai fara cin abinci danna hango yunwa cikin kwayar idanka..
Shafa gefen fuskarta yayi da bata amsa.. "Dama anan nake danafi jin dad'i danfa gaskiya kinfi TAUDHAT kula dani.
Murmushi taqarayi da fad'in. "Zan koya mata komai wanda zaisa kaji tafini kula dakai.
"Bana tunanin hakan. Nadaifi yarda dazaki koya mata daidai da yanda kike min
"Toh idan nayi mata hakan aizata qara da tata basirar. Kaga kenan dole tafini kula dakai
"Kawai dai naji saida safe.
"Dan Allah katashi da wuri dan musamu zuwa duba momyn akan lokaci..
"Murmushi yayi da cewa.. "Kema kinsan bana wucce lokaci..
"Nafa fad'ane kawai dan naji dad'in bakina
"Idanko haka ne nayi miki alqawarin bazaki ganni ba.. sai qarfe goma na safan..
"Wayyo Allah mijina dan Allah karkamin wannan horan.. Duk da cewar a d'akin y'ar uwata kake zanji ba dad'i sosai idan nakai wannan lokacin banga kyakkyawar fuskarka ba..
"Alk'awarifa nayi. Dan haka ki kwantar da hankalinki dan saina cika.. Yana fad'in mata hakan ya ficce daga falan yana murmushi..
Dafe kanta tayi da kulle kofar tata tana cewa. "Najama kaina. Kai baka san kuncin danakeji araina bane idan naga ka fito daga part d'in TAUDHAT....
....
Da gaske Adams yaji canji agun TAUDHAT canjin dabai tab'a ji arayuwarsa ba.. Dan sanda ta aikata abinda da malamin nata yace tayi.. Dan zama tayi tajanyo sha'awa tayi amfani da ni'imar tata wajan kwab'a maganin.. Sannan tasaka bayan sallar Isha'i
Daqer da sid'in goshi Adams ya iya barinta acikin wannan dare
Shi kansa yayi mamakin kansa..
Dan kwata kwata wannan dare bai samu wani ishash shan bacci ba
Hakan yasa ana idar da sallar asuba bai wani tsaya zakirorin daya saba ba. Ya dawo gida ya kwanta. bashi ya tashi ba sai kusan tara saura
Kuma ahakan ma yana had'a ido da TAUDHAT saiya tuno da daran nasu na jiya nan take sha'awa ta kamasa. Har saida yasamu biyan buqatarsa agaggauce sannan hankalinsa ya kwanta..
Lokacin daya gama shirinsa na fitta office goma saura minti uku..
A hankali ya kalli TAUDHAT yace.. "bazan tab'a yarda da cewar ba abinda kikamin fittarki jiya da kikayi.
Kallansa tayi da murmushi tace.. "Ni TAUDHAT me zan yima mijina kuwa.
Murmushi yayi da cewa "Nafa jiki jiya fiye da yanda nasaba jinki..
"Inaga dai addu'atace ta karb'u wacce nakeyi babu dare babu rana akan Allah yasa kadinga jina fiye da kowace ranah arayuwarka..
Murmushi ya qarayi da fad'in.. "Hmm.. Najiki kuwa. Dan atahirin rayuwata bana tunanin natab'a kaiwa wannan lokacin ba ranar asabar da lahadi ba? ban fitta ba. Ina tunanin tun angwanci na da NUFAISAT..
Dariya tayi da cewa. "Wata qila nima dai kanasan kayimin kara ne wajen hakan...
"Ai kin rigada kinci amarcinki babu kara. Kawai dai naji can jin yayimin ne. Dan ALLAH gayamin miye sirrin..
Tashi tayi cikin shauqi tayafa gyalanta da cewa. "Babu wani sirri. Kaga jeka kaga qawata ina mota ina jiranku kar Ammi tace meyasa bamuzo da wurri ba..
Waro ido ADAMS yayi cikin wani hali yace.. "Ya Allah. Kinsan na manta momy na asibiti. Allah yasa su doctor Aryan sunyi mata wani qoqari..
"Lalle kace kanka ya kulle da yawa..
Bai kulata ba ya ficce daga falan ya nufi na NUFAISAT
Kallan harara NUFAISAT d'in tayi masa.. Yayi murmushi da rungumarta yana cewa.. "Amin afuwa nayi lefi yau ko
Kwace kanta tayi da cewa.. Sam ban d'auka da gaske zaka kai qarfe goman dakace ba..
Shi sai yanxu ma ya tuna wasan nasu na jiya. Dan haka ya fake dace mata ai alk'awari yayi mata...
Da hakan yasamu kanta.
A mota suka tadda TAUDHAT
Sanda sukama kansu kallan kallo ita da TAUDHAT kana ita TAUDHAT d'in tayi mata murmushin qarfin hali dace mata.. "Barka da safiya k'awa da fatan kin tashi lafiya..
Da nuna farin ciki sosai NUFAISAT tace da ita.. "Barka dai.. Fatan kema kin tashi lafiya..
Daqer tace mata lafiya lau. Shima dan taga Idan Adams na kansu ne...
Haka NUFAISAT ta shiga motar ADAMS shima ya shiga direban ya jasu masu tsaran lafiyarsa suka sasu a tsakiya cikin motocinsu suma..
Da suka iso asibitin NUFAISAT kamar tayi kuka ganin halin da mommy Rukayyat take ciki..
Ganin da gaske kukan take sanyi sai kawai taficce daga d'akin taje gun Ammi da kwantar da kanta kan cinyarta ta fashe da kuka tana ce mata. "Dama Ammi irin wannan ciwan yana kama mutum lokaci d'aya haka..
Ammi tace "bar kuka NUFAISAT addu'a take nema. Nima wannan shine karo na farko dana tab'a ganin ganin hakan..
ADAMS ganin NUFAISAT ta fitta sai yabi bayanta..
Ganin hakan yasa salim fitta shima danya d'auko wayarsa amota.. Saiya kasance daga TAUDHAT sai Hajjiya Rukayyat..
Dama Dady yana gida..
Dan haka sai TAUDHAT ta kalli Hajjiya Rukayyat da yatsina fuska tace da ita... "Hmm.. Bake tantiriya ba. Haka siddan dan baqin hali kika bani nama naci dan kawai karna haihu da ADAMS.
shine dana gane kece kikamin hakan nima nayi miki hakan. Dan haka kisa aranki bake ba tashi saidai abaki abinci a baki awanke miki kashi da fitsari har qarshen rayuwarki..
Zaba mata ido Hajjiya Rukayyat tayi da mamaki tace.. "Wai kina nufin kece kikamin wannan abun..
TAUDHAT ta gyad'a mata kai cikin taunar cingam tace. "Nice mana.. Yasan ranki. Wallahi nice nan nayi miki..😃
Aiko nan take Hajjiya Rukayyat tafara gurnani nasan tashi amman abin ya faskara. TAUDHAT tayi dariya daci gaba da cewa.. kaji banza. Wai tunaninki zaki tashi ne.
Da b'acin rai Hajjiya Rukayyat tace.. "Zako kici ubanki idan natashi. Dan saina miki abinda harki mutu bazaki tab'a mantawa dani ba...
Dalla mata harara TAUDHAT tayi da cewa.. "Muci uban juna dai. Dan inke kin kwana kina shiri ni a hanya na kwana.
Kajimin muguwar mata haka siddan ki hanani haihuwa da mijina. Shegiya azzalima...
Shigowar Adams da NUFAISAT ne yasa TAUDHAT saurin yin shuru..
Dan fittan Adams rarrashin NUFAISAT d'in yayi dace mata.. Yanxu ba kuka momy take so ba. Addu'a takeso. Dan haka tatashi taje tayi mata addu'a zaifi da kukan da takeyi...
Muje zuwa y'an hannuna👐🏼...
https://www.instagram.com/p/BkZOMcllfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15ya4yksqqc7d&r=wa1
[7/4, 3:13 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 16☆
Gefanta NUFAISAT taje tazauna tana cewa.. "Sannu momy. Bara nayi miki addu'a..
Shuru momy tayi mata dan ranta ba qaramin b'aci yayi ba. Jin TAUDHAT ce tayi mata wannan abu.
A hankali taji tana jin dad'i ajikinta kasancewar addu'ar da NUFAISAT take mata. Jitake kamar ana fusgar wani abu ajikinta. Idan kuma NUFAISAT tayi shuru sai taji abin ya dawo mata..
Anan taqara yarda da abinda TAUDHAT ta gaya mata..
Ammi ta koma gida tayi wasu y'an aikace aikace sanda tadawo sannan su NUFAISAT suka bar asibitin..
Saidai suna tafiya Hajjiya Rukayyat ta d'agama su Ammi da salim da Dady hankali akan amaida ita gida Wannan ciwan nata bana asibiti bane.
Abin ya basu mamaki sosai.. Nan suka shiga lallashinta kan tayi hakuri ad'an gwada sa'a anan d'in aga abinda Allah zaiyi..
Saidai fur taqi yarda.
Lokacin data tayar musu da borin bakwai na dare ne... Dan haka a lokacin ko suka maida ita gida..
Abinda dako yasa Hajjiya Rukayyat rikice musu shine.. Wata aminiyarta Hajjiya Hadiza ce tazo dubata bayan tafiyarsu NUFAISAT. Shine Hajjiya Rukayyan take bata labarin TAUDHAT ce tayi mata hakan.
Shine ita Hajjiya Hadizan take ce mata tota koma gida. Dan wannan ba aikin asibiti bane. Dan saidai su b'ata mata lokaci. Dan haka takoma gida zata dinga zuwa tana kawo mata magani harta samu sauqi
Hajjiya Rukayyat tace yanxu bazata iya samun sauqi lokaci d'aya ba
Kallan mamaki Hajjiya Hadiza tabita dashi tana bata amsa. Kema kinsan cuta lokaci d'aya take kama mutum. Sauqi ko sai'a hankali.
Kedai ki kwantar da hankalinki. Tunda yanxu munsan meyajawo miki ciwan. Baki da matsala wajen samun magani. Kawai bakin aljihu zaki bud'e dan idan tana taqama ita gwanace toh wallahi mune gwanaye. Zataci ubanta ne. Badai tatab'omu ba.
Murmushi Hajjiya Rukayyat tayi danta yarda da qawar tata Hajjiya Hadiza...
Toh wannan shine abinda yasa ta hura masu Ammi wuta kan sai ammaida ita gida..
Kuma ita Hajjiya Hadiza tace mata Hakan ne dan tasamu nata raban ajikin Hajjiya Rukayyat d'in
Dan tasan tunda taganta cikin wannan hali ba qaramin sakar mata bakin aljihu zatayi ba wajen san tabi bokayen da suke bi tasamo mata makarin aikin da TAUDHAT d'in tayi mata
Ataqaice dai Hajjiya Hadiza tasa aranta zata nema mata magani ammanfa saita d'auki biyar ko bakwai tana samun nata kafin ta nemo mata maganin
Suna isa gida ko Ammi takira NUFAISAT da TAUDHAT awaya ta gaya musu komai dan haka duk ran da suka tashi dawowa suxo gida kawai dan sunbar asibitin.. Toh sukace mata.
Salim ya kalleta da murmushi yace.. "Ammi dakin bari nasan ya Adams zai gaya musu..
Itama murmushin tayi da cewa. Gwara dai dana gaya musu dan ka sanshi da mantuwa..
Hajjiya Rukayyat na jinsu tayi shuru tana saqa hukuncin da zata d'auka akan TAUDHAT idan tatashi...
Dake shi Adams yana da matsala. Sam baya iya kwana baiji mace ba. Idan ko kikaga ya kwana bejiki ba. To qila kunyi fad'a ne ko yaga kina bacci me nauyi ko rashin lafiya. Toh shine zai barki amman bazai raba kansa dake ba wajen jin d'uminki.
Hakan yasa yaji NUFAISAT a wannan dare. Kasancewar ranar girkinta..
Abin yazo mishi awani saban salo..
Yadai sani yafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali agun NUFAISAT. Dan nesa ba kusa ba tafi TAUDHAT gamsar dashi.
Amma sai gashi jiya yaji dad'in TAUDHAT dad'in dabai tab'a tunanin samu daga gareta ba.
Ga kuma NUFAISAT Sam sai yajita babu dad'in komai ko kad'an. Wai me yake faruwa ne..
Kamar zaima NUFAISAT magana washe gari lokacin da yake breakfast.. Sai kuma ya fasa..
Abinfa bai canja zani ba. Dan yauma hakan ne ya qara kasancewa dashi agun NUFAISAT d'in
Har Allah Allah yake washe gari tayi wato girkin TAUDHAT yajita ko zai dad'a jin abinda yaji daga gareta..
Haka ko akayi.. Yana shiga girkin TAUDHAT yaji komai zamzam..
Washe gari yana breakfast ne kawai amman hankalinsa na kan NUFAISAT.. Tunani yake wane irin canji ya samu agunta ne haka me d'aga hankali..
Shuru yayi da barin abin aransa har izuwa lokacin daya koma girkin NUFAISAT d'in..
Still abinda yaji awancan girkin nata shiya qara ji..
Dan haka da safe suna breakfast ya kalleta cikin so da qauna yace.. "Kiyi hakuri matata zan gaya miki wani abu Sam bana San kiyimin wani kallo na daban. dan zan gaya miki ne saboda bana San rashin fahimta ya shiga tsakanina dake. Dan sirri na naki ne. Kuma aganina idan nabar wannan batun da zan gaya miki araina ban miki adalci ba. Saboda zan nuna miki wasu hali wanda bamu saba dasu ba ni dake. Hakan yasa na yanke shawarar gaya miki dan karkiga canji ki zargeni..
Shuru NUFAISAT tayi gabanta na fad'uwa dan tunkan taji miye abun taji hankalinta ya tashi...
Ahankali ta kallesa da cewa.. "Babu hakan tsakanina dakai. Magana indai ta fahimtace kaima kasan ina fahimtarka.
Dan haka fad'i kawai babu wani abu..
Zan gaya miki Amman ki tabbatar bazaki canja min ba. Dan nasan zakima maganar wata fassara ta daban.
"Nace maka Karka damu. Nime sauraranka ce da fahimtarka aduk lokacin dakaso na saurareka kona fahimcekan..
Jan numfashi yayi da cewa.. "Wancan girkin na TAUDHAT daya wucce ba Wannan na shekaran jiya ba. Naji dad'in TAUDHAT fiye da kowace ranah arayuwata.. Nasan da cewa kece macen da kike iya sarrafani yanda nake jin dad'i kuma nake samun gamsuwa gamsuwar da take zama a Zuciyata nake kasa mantawa dake. Sosai na shiga mamakin meyasa naji canji kuma yanxu daga gareki.
Wato matata tunda naji TAUDHAT a wancan girkin nata na rantse miki girkin da kika shiga kafin Wannan jinki nayi wani iri. Sam na nemi Wannan jin dad'in da nake samu daga gareki na rasa. Jinki nayi babu dad'in komai ko kad'an..
Cikin tashin hankali ta qara kafeshi da ido tace... "Banfa gane me kake nufi ba. Ban fahimta ba. Wallahi kwakwalwata ta d'auke. Dan Allah me kike nufi. Wallahi ban gane ba'
"Yafa dace ki gane ki kuma fahimta. Wannan abu ne bana wasa ba. Yanda kikaji na gaya miki haka shine gaskiyar zancen. Ina San jinki kamar yanda nasaba jinki matata. Dan ALLAH ki temaken kisan yanda zakiyi ki dawo kamar da. Dan bana San abin yayi nisa. Saboda na saba dake. Ke kanki kinsani. Wannan bakwan abu ne ya shigo rayuwarmu.
Sam bana San na fuskanci wata matsala daga gareki..
Nasan kuma kin dad'e da fahimtar hakan...
Adams na kawowa nan azancensa ya tashi da d'aukar jakarsa har yakai kofar fitta daga