Showing 39001 words to 42000 words out of 81675 words
sallama duk da baqin hali irin na Hajjiya Rukayyat sanda itama taji aranta kamar karya tafi..
Salim mah jiyayi kamar yayan nasa yayi tafiyar shi..
Haka lokacin da yakema matsaransa sallama akan su kwantar da hankalinsu ba abinda zai samesa yaudai ranah d'aya ai ba wani abu bane. Fatansa dai suba matansa kulawa dan baya san yaji wani abu ya faru dasu... Da sanyin jiki suka bashi mukullin motar da zaiyi tafiyar da ita.
Haka yaba Sunusi ya shige bayan motar Sunusin ya zauna wajen mazaunin direba yajasu sukabar harabar gidan zuciyar Adams cike da qaunar iyayen nasa....
Biyan Sunusi akayi wato d'aya daga cikin direbobin Adams d'in..
Kasancewar direbobin nasa uku ne..
Kuma shima kansa Sunusin sanda yayarda zaiyi abinda suke so sai daga baya kuma yazo yana na damar yanda yake qoqarin cin amanar ogan nasa wanda yayi masa dukkanin gata..
Wannan dai maqiyin nasa ne har yau yake san neman rayuwarsa.. Dan dad'ewar da yayi wajen lamfo kamar ya rabu da Adams d'in shekara da shekaru. Ashe dad'ewar shirye shiryen yanda za'ayi ya cimma burin nasa akansa ne..
Toh yau yana neman cin sa'a da nasara akansa...
Dake ADAMS bai san yanyar garin Gwamben ba shiyasa sam baisan inda Sunusi yake jefa k'afar motar tasu ba...
Hasalima shi karatun jaridarsa yake yi idan yaji Sunusin ya tsaya awani
waje yakan kalli wajen idan yaga da mabarata ko gajiyayyu sai yaba Sunusin kud'i ya basu....
Sunsha uwar tafiya wanda sai yanxu nadamar qin shiga jirki tazoma Adams.. Danshi arayuwarsa bai tab'a tafiya irin wannan ba..
Cak ADAMS yaji Sunusi ya tsaya da tuqin mota. Duk da bacci ya fara fuzgarsa. Jin tsayuwar motar shiyasa shi bud'e idansa..
D'ago kansa da zaiyi kawai saiya gansu kan titi gashi gabas da yamma cikin daji suke.. Dajin dabazai iya cewa ga inda suke ba.. Gashi abin mamaki wasu mutane ya gani su goma.. Murd'add'u da alama ma kad'an daga cikinsu sune way'anda suke kawo mai hari shekarun baya dan yaga hakan atattare dasu..
Uku bindiga ne ahannunsu sauran kuma qarfuna ne da sandina a nasu hannayen..
Fitowa Adams yayi kamar yanda Sunusi ya fitto..
Cikin Dariyar mugunta suka d'aga bindigarsu sama suka setata akan Adams..
Cikin sauri Sunusi ya fashe da kuka yace dasu. "Dan Allah karku cutarmin da oga na. Karku kashesa.
Nayi muku abinda nayi muku amman ina cikin nadama. Saboda naci amanar wanda ya yarda dani. Na munafurcesa bayan yayi min dukkan gata.. Wallahi me gida nayi maka abinda bai dace ba. Dan Allah ka yafemin.. Sunusi ya qarashe maganar da kallan Adams ya kama qafarsa alama ban hak'uri..
Cikin mamaki Adams ya kalli Sunusi yace.. "Wai me yake faruwa ne..
"Oga way'annan mutanan ne suka bani kud'i me yawan gaske sukace duk yanda za'ayi nayi dan kayo tafiyar nan dani. Dan sun samu labarin zuwanka gwamben kuma a mota. Shine sukace nakawo musu kai cikin dajin nan da zaran tafiya tayi nisa. Oga ban san manufarsu ba. Kawai na duba yawan kud'in da suka ban ne.. Sunusi ya fad'i hakan daci gaba da kuka..
Nan ADAMS ya rintse idansa yana tuna yanda yabar matansa iyayensa. Ya tabbatar tunda ya had'u da way'an nan mutanan wannan karan ba barinsa zasuyi ba.
Dan haka da wani hali ya kalli Sunusin da cemai. "Karka damu Sunusi nayafe maka.
Aiko kan Sunusin yace wani abu wani daga cikin masu d'auke da bindigar ya harbe kan Sunusin da bindigar hannunsa...😨
Jikake fasss..
Ai arikice Adams ya tashe yaje ya rungumesa yana me kiran sunansa.. "Sunusi Sunusi Sunusi katashi katashi dan Allah.. Amma ina ko alamar motsawa Sunusi baiyi ba.. Saboda rai yayi halinsa...
Gabaki d'aya Adams ya rikice fad'in musu yake.. Kun kashesa fah. Ya mutu. Wallahi kun kashesa.. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un... Haka Adams yaketa fad'a hankalinsa tashe..
"ADAMCY kenan.. Mun gayama kabar garin Kaduna idan kana san ganinka da lafiya kuma a raye..
Sai kaqi. Ka zauna abinka baka tare da wani tashin hankali. Saboda kayima kanka gata kana da masu tsaro..
Sai gashi yau tunaninka ya toshe ka fito inda baka tab'a zuwa ba batare dasu ba..
Oganmu ya gaya mana bokan Wanda yasa shi wannan aikin akanka ya gaya masa idan har kana garin Kaduna sunansa da azziqinsa bazasu tab'a suna ba. Bazai tab'a zama wani ba. Shi kuma yana san ya fika tako ta'ina....
Wannan dalilin yasa yace mu kashe masa kai.
Saidai mu bamu san muyi maka hakan saboda katab'a temakwan oganmu. Shine yasa muke maka dukkan tsiya dan mu hanaka tashi bare kaci gaba da aiwatar da harkokinka.
Saiya kasance katashi. Muka dad'a maka wani dukan dace maka kabar garin Kaduna idan kana san zama da rayuwaka. Amman kaqi.
Yanxu ma ba kasheka zamuyi ba. Saboda mu ba butulu bane munsan wanda yayi mana. Zamu qara maka wani dukkan ne wanda bazaka moru ba bare kaci gaba da aiwatar da ayyukanka ka hana wancan maqiyin naka cika burinsa...
Kan ADAMS yace wani abu sun fara kai masa duka a inda suke da tabbacin idan suka dakai bazai iya muruwa ba.. Da qarfuna da sandinansu suka fara kai mishi wannan duka
Duk da cewar bawai kallansu yake ba. aa yana qoqarin kare kansa. Dan sosai suma yayi musu b'arna. Wajen rama abin da suke masa. Toh kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin qarfi.. Hakan ne yasa yaqi cin galaba akansu.. Dan d'aya daga cikin su yana d'aga sandarsa saiko ya sauke ta a qeyarsa wanda nan take ADAMS ya jirkice ya zube awajen tamkar wanda ya mutu. Dan babu alamar rai atare dashi
Ba qaramin tsoro bane ya kamasu.. Dan ogansu yace musu kada su kuskura su kasheshi.
Sudai mai dukan daba zai moru ba. Shiyasan abinda zai cema wanda yasa shi aikin...
Aiko Ahankali suka fara tab'ashi suna cewa.. "Mun kashe shi fah. Yanxu me zamucema oga..
D'aya daga cikinsu yace.. "Ga shawara.. Me zai hana mukaisa *Rugar malam jauro..* Kasan rugace wacce ba kowa bane yake da sani akanta. Saboda tayi cikin daji da yawa.
Me zama a wannan ruga sai Wanda ya taki abubuwa da dama. Dan bakowane mutum bane yake iya rayuwa awajen. Kasancewarta muguwar riga....
Cikin sauri wani cikinsu shima ya amshe da cewa.. "Kaga shike nan asirinmu ya rufu agun oga.. Dan idan mukace mai munyi yanda yace muyi zamu zauna lafiya dashi.
Idan ko mukace mun kasheshi saiya d'auki ran d'aya daga cikinmu..
Kaga rugar Malam Jauro bame zuwa bare asan da zaman gawarsa awajen.
Idan ko muka yar dashi anan kaga dole atsince shi kuma labari yajema oga..
Shuru sukayi suna nazari
Can wanda ya harbi Sunusi yace. "Wannan shawarar tayi. Kunga sai musa Sunusi shi kad'ai a buhun barkonan kamar yanda ogan yace. Sai muce mai gabaki d'ayansu ne mukasasu a buhun bamu san ya akayi aka rasa ADAMS d'in ba.
Kowa cikinsu yayarda da wannan shawarar.... Dan haka suka kinkimi ADAMS suka sashi cikin motarshi. Sannan suka saka Sunusi abuhu irin babban nan wanda yake d'auke da barkono aciki. suka kullesa. uku daga cikinsu suka shiga motar ADAMS d'in d'aya yajata.. Sannan sauran suka shiga cikin dajin inda suka ajiye motarsu dan kar'a ankare dasu.
Sannan suka kusa cikin wani daji me nisan tsiya. Dan sai tafiya suke kamar basa tafiya.. Akalla sunkai kusan biyu na dare kana suka iso rugar.. Saidai basu bari sun qarasa cikinta ba dan sunsan illar dake cikinta..
Ad'an nesa da rugar cikin dajin suka yada Adams...
Suka juya abinsu da barin wajen...
Washe gari da misalin qarfe takwas suka samu fitowa daga rugar...
Nan suka d'auki hanyar garin Kaduna. Sanda sukayi awa uku kana suka samu kansa a garin Kadunan. Sannan sukaje unguwar su Dadyn ADAMS suka bar Sunusi cikin motar da key na motar Adams d'in sannan suka bar unguwar.
Amman sanda suka zaro wata kwarab'abbiyar waya suka kira num na Dadyn Adams kamar yanda Ogansu ya basu suka gayamai ga Adams nan da direbansa cikin unguwarsu da alama yana cikin wani hali... (Kuji fa masu karatu)
Suna gaya mai hakan suka kashe wayar da cillar da ita awajen sukayi tafiyarsu..
Lokacin da Dady ya d'auki wayar tasu yana zaune ne shida Hajjiya Rukayyat da Ammi. Suna magana akan rashin jin Adams d'in daba suyi ba awaya. Gashi basu da number na Yusuf kona Ibrahim d'in.. Aiko da sauri Dady ya tashi jin abinda suka ce mai yana me cewa "Subhanallah.. Nan su Ammi suka buqaci suji meya faru. Da sauri ya gaya musu ya fito waje yana cilla ido yaga ta'inda zaiga motar Adams d'in
Aiko ya d'anyi nisa da tafiya cikin layin nasu saiya hango motar..
Da sauri ya qarasa gareta yana duba amman baiga kowa aciki ba sai wayoyin ADAMS dana Sunusi..
Yana bud'e Boot na motar sai yaga qatan buhu fari kallo d'aya zaka mai kasan na barkono ne.
Yayi duba iya duba wajen wai kozaiga Adams alayin amma baiga kome kamarsa ba.
Hankalin Dady ya tashi matuqa dan haka nan ya shiga kiran wayar da suka kirasa da ita nan yaji akashe.. Saiya kira wani amininsa babban d'an sanda yana gayamai yaxo yanxu unguwarsu ankawo mai motar d'ansa Adams kuma baya ciki da alama wani abu nasan faruwa.
Ai dajin hakan yacema Dadyn gashi nan zuwa..
Haka yazo da yaran aikinsa suka hau caje motar basuga komai ba. Sai kwarab'abbiyar wayar da suka yar nesa da motar.
Ogan nasu yace abud'e mai buhun barko nan nan.
Aiko dan yaransa suka bud'e mai saiko ganin sunusi sukayi cikin barkono..
Nan suka fitto dashi anan suka gane yazama gawa dan ga shedar harbi nan akansa bai b'uya ba..
Hankalin Dady yayi matuqar tashi nan ya yanke jiki ya fad'i sumamme..
NUFAISAT da Ammi da sukaji labari nan suma haka suka zube sumammu.
Masu qarfin halin Hajjiya Rukayyat ce da TAUDHAT..
Nanfa zance ya baza gari an nemi ADAMS ba'a agansa ba..
Hankalin y'an uwa da abokan arziqi ya tashi matuqa..
Dan b'atan mutum yafi mutuwarsa Shiga tashin hankali. Saboda idan mutuwa yayi ba shakka damuwar ta dabance.
Idanko b'ata yayi kullum tunani mutane zasu shiga yi koyana wane hali koya mutu koyana raye oho
Wannan yasa hankalin kowa yayi mayuqar tashi.
Nan aka fara sanarwa a gidajen radio da gidan talabijin yanar gizo wajen nemansa.
Anan Yusuf yasan Adams ya b'ata...
Dan haka ba shiri ya baro garin gwambe dan shima ya rasa nutsuwarsa ganin baiji Adams d'in ba.
Dama Ibrahim bawai agarin gwanben yake ba. aa Aure ne kawai mamansa takeyi agarin dan tarabu da mahaifinsa. Hakan yasa shi yake gun Mahaifinsa anan cikin garin Kadunan.
Dan haka tare da Yusuf suka dawo Kaduna suna masu san jin ba'asin yanda akayi Adams ya b'ace.
Babufa ADAMS babu labarinsa sam cikin garin Kaduna.
Dan har y'an sanda da masu farin kaya kaf sunyi iya binkikensu basuji labarin Adams ba..
Dare da rana safe da yamma malamai addu'a suke akan Allah ya bayyana Adams..
Dan a binciken istaharan duk malamin da yayi ya nuna ADAMS yana *RAYE* saidai yana cikin wani mawiyacin hali
Jin hakan da Dady yayi shiyasa jininsa qara hawa a asibiti..
NUFAISAT ko ba ita tasamu kanta ba sanda tayi sati a asibitin tadawo hayyacinta..
Saidai tasaka salloli agaba dare da rana akan Allah ya fitto mata da mijinta ya karesa aduk inda yake.
Haka TAUDHAT duk ta karad'e malamanta da bokayenta sun bata tabbacin Adams yana raye saidai baza suce ga inda yake ba.
Gaskiya itama hankalinta ya tashi sosai.
Ganin hakan yasa masu tsaran lafiyar Adams d'in suka fito sukace su suna zargin Ibrahim shine ya b'atar da ADAMS kuma ba mamaki shine ya kashe Sunusi.
Jami'an tsoro sunsasu agaba kan sufad'i dalilinsu na fad'in hakan..
Nan suka gaya musu shine yasa wasu suka kaima ADAMS d'in hari a shekarun baya.
Kuma yaxo ya buqaci dasu kulle dashi dan shi rayuwar ADAMS d'in yake buqata..
Ai dajin wannan batu nan take ogan y'an sanda yasa yaransa suje su nemamman Ibrahim aduk inda yake..
Sunci sa'a tare da Yusuf suka dawo daga gwamben dan haka basusha wahalar ram dashi ba..
Dafarko yayi musu gaddama akan baisan komai akan labarin ba.
Kuma qarya masu tsaran lafiyar Adams suka masa na wai shine yasa wasu suka kai mai hari..
Sam jami'an tsoran basu wani yarda da Ibrahim d'in ba
Dan haka nan suka hau gana masa azaba cikiko harda guntule mishi y'an yatsu guda biyu..
Ai yana jin azaba ya gaya musu shine yasa aka kai mai hari shekarun bayan. Kuma da gaske shine yasa yanxu a kashesa akuma kashe Sunusi dan karya tona musu asiri..
Jami'an basuji mamakinsa ba dan sun saba ganin abin mamakin irin hakan
Dan haka sai suka buqaci suji dalilinsa nayima Adams d'in hakan...
Ba wata kwakkwaran magana dan cemusu yayi.... Tun suna skull ADAMS yake samun nasarori arayuwa amman shi baya samu.
Haka shi LEEKITAN ZUCHIYA ne hakama Adams d'in shima LEEKITAN ZUCHIYA ne.. Saidai sunan Adams yafi fitowa duniya tasanshi fiye dashi..
Haka tafanni kasuwancin da yakeyi nan ma ya qara fito da sunansa ko'ina aka sanshi...
Wannan dalilin shiyasa yaji hassadar Adams d'in takamasa. Saiya bara bin bokaye kansu dak'ushe tauraran Adams su d'aukaka nashi.. Saidai abin bai yuhu ba. Sakancewar shi me ibada ne. Shine kawai ya yanke shawarar yasa akasheshi. Nanma way'anda yasa sumai hakan baisan dalilinsu na kasa kasheshin ba har akaro na biyu..
Shine yanxu yayi amfani da wannan damar dayaji Adams d'in yace bazaibi jirgiba ba motarsa zaibi. To shine yacema yaran aikin nasa duk iya wiya kadda subar ADAMS darai awannan karan....
Sosai jami'an tsaran suka jinjina hassada da baqin hali irin na Ibrahim.
Sun buqaci daya gaya musu inda yaran suke. Way'anda yasa su kashe Adams d'in
Ya gaya musu inda suke. Amman anyi duban duniya suma ba'a gansu ba
Wannan yasa hankalin jami'an tsaran ya tashi dan Ibrahim ya tabbatar musu da cewar wallahi bayan inda ya gaya musu baisan inda kuma suke ba...
Ayanxu dai Ibrahim yana hannun jami'an tsaro dayi musu aiki me tsanani.. Dan sunce bazasu sakesa ba har sai ranar da akaga ADAMS. dan ba zama zasuyi ba zasu dinga nemansa ne har Allah yasa adace..
Ammin Adams tana cikin wani hali. Kullum tunaninta ADAMS ne
Ba dare babu rana rokwan Allah take kan ya fito mata da d'anta cike da lafiya..
Haka NUFAISAT itama tunaninta ADAMS d'in ne kuka take cikin dare tana rokwan Allah ya bayyana mata mijinta..
TAUDHAT mah tana cikin damuwa dan har tafara tunanin yanxu idan ba'aga ADAMS ba. Ya zatayi wajen rayuwa da wani namijin..
Yusuf ma ba'a barshi abaya ba. Dan kullum addu'a yakema Adams babu dare babu ranah. Haka indai zai fita saiyaje gurare da dama wai kozaiga Adams d'in..
Dady kam jiki babu sauqi dan likita yace saiya cire damuwar Adams aransa sannan zai samu lafiya..
Lokaci na tafiya amman har yanxu shuru kakeji babu labarin Adams.
Yau kusan watanni tara kenan babu amo babu labari...
TAUDHAT da NUFAISAT sunsa aransu bazasu tab'a barin Auran Adams ba suna nan suna jiran dawowarsa dan sunji aransu da gaske bai mutu ba....
Wannan kenan me karatu🙅🏻♀
Kuci gaba da bibiyata ni Rahma Nalele ina tare daku y'an hannuna👐🏼👐🏼👐🏼.. Jiya naso turo muku Allah bai yarda ba
[7/11, 2:55 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 19☆
Sannan way'anda sukama ADAMS dukan nan suna nan cikin garin Kaduna suna jinyar kansu cikin b'oyayyan guri...
Dan nagaya muku shima Adams bawai kallansu kawai ya tsaya yi ba. Yayi musu b'ar me yawa. Dan dai kawai suna jin tsoran karsu kasheshi ne ogansu yad'au hukunci akansu banda haka da tun fara artabun nasu zasu sakar mai bindiga.
Dan duk da suna tare makamai ahannunsu sanda ya nuna masu iyakarsu.
Ya fasama d'aya daga cikinsu gefan ido d'aya Wanda nake kyautata zatun yama rasa idan..
Haka ya karya wani ma acinya.
Yama wani duka a gabansa. Inda kunsan da wiya mutum yake tsallake duka awannan waje batare daya shiga ukunsa ba.
Sannan ya kaima Wanda ya kashe Sunusi mugun bugu a hanci Wanda nan take kamanninsa suka canja. Dan hancin ya samu mugun rauni. Ga baki hak'ura sun zube..
Wannan tunda yayi masa haka yar iyanxu kansa yaqi dawowa daidai..
Ogansu yayi mamakin hakan sosai. Dan bai tab'a kawowa masu jin dad'in rayuwa suna tare da qarfi haka
Wannan kenan me karatu
************
Rugar malam jauro wata hatsabibiyar ruga ce da take nan cikin d'aya daga qauyukan garin gwambe. Saidai tayi daji da yawa kasancewar malam jauro yana da arziqin shanu masu yawan gaske..
Wannan dalilin yasa mutane suke zagawa suke mai sata san ransu. Lokacin daya ankare da hakan shine yayi wani abu Wanda duk Wanda ya shigo rugarsa da niyar sata to ba makawa mutuwa zaiyi..
Abin da yayi yana amfani da haline da abinda kazoyi.
Wannan yasa jama'a da dama suke ganin rugar ba wajen zuwa bace saboda yanda suke ganin kawarwaken mutane da sun shiga wajen.. Duk Wanda ko sukaga yaje rugar lafiya ya fitto lafiya cewa suke akwai abinda ya taka..
Babbar Ruga ce sosai danta tara ainiyin fulani masu wayan gaske.
Way'anda basu san hayaniya. Dan kallo d'aya zaka musu ka kirasu da fulanin daji.
Basu san komai na rayuwa ba sai kiwo...
Saidai sun bambanta da jahilan mutane saboda malam jauro shahararran malami ne.
Yana da sani akan ilimi na addinin musulinci.
Wannan yasa duk inda suka fito idan zasu aiwatar da al'amuransu gabanka bazaka kirasu da jahilal ba.
Dan sunsan ilimi na addinin musulinci
Malam jauro ya koyar dasu Qur'ani me girma su fiqhu ahalari qawaqidi da sauran littattafai na addina..
Bayan wannan basu da sani akan komai sai kiwo..
Gwaggwa Yawo wacce suke kira da Yawo tana d'aya daga cikin mutanan da suke zama cikin wannan Ruga..
Saidai