Showing 9001 words to 12000 words out of 81675 words

Chapter 4 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

na shirya kula da cikinka kamar yanda duk mata tagari takeyima mijinta...

Tana gama furucin. tatashi ta kwashe kayan da kaiwa kitchen tawankesu tsaf...
Daga falan nata taji muryar Aseeya da Larai suna gaisheta..
Da Murmushi tafitoh tana amsawa.. Tana me tambayarsu kowa dai yana lafiya ko..
D'aga mata kai sukayi alamar tabbatarwa
Zama sukayi KAMAR yanda suka saba wajen tayata hira..


Can da misalin ƙarfe goma Sha d'aya saiga TAUDHAT taxo gareta..
Ganin zuwan TAUDHAT d'in yasa su Aseeya barin falan..
Da wani hali yau NUFAISAT d'in ta tarbi TAUDHAT d'in..
Ganin hakan yasa TAUDHAT d'in tambayarta ko tana lafiya
Jan numfashi NUFAISAT tayi cikin kuka tace... "Yazanyi Y'ar uwa.. ADAMCY Aure zai ƙara......
"Aure😳... TAUDHAT ta nanata had'e da dafe ƙirji da waro ido.
"Eh Aure zai qara TAUDHAT.. Saboda yana San ganin farin cikin iyayensa..
Wai so suke suga yaransa..
Yazanyi TAUDHAT..
Ji nake kamar nayi hauka.
Kinsan baqaramin San ADAMCY nake ba
Ina jin tsoran karya kasance wacce zai Auran shed'aniyace. Taxo ta rabani dashi..

Shuru TAUDHAT tayi.. Dan tafi NUFAISAT d'in shiga tashin hankali..
Dan numfashi har wani sama sama yakeyi...
Cikin tashin hankali tace.. Towa zai Aura..
"Ban sani ba TAUDHAT.. Bansan wacece ba
Saidai ya gayamin in saka ran zuwanta akowane lokaci..
Sannan bazai qara cin girkinki ba.. Nawa yake San ci..
Shuru dai TAUDHAT taqarayi... Zuwa can tunaninta ya bata mezai hana tayi amfani da wannan damar wajen Jan NUFAISAT d'in zuwa ga saban bokan nata..
Tabbas Idan ya ganta ba makawa Auran yarinyar dazaiyi kanta zai koma..
Yin wannan tunanin nata yasata Jan numfashi ta kalli NUFAISAT d'in cikin tausayawa tace... "Dama akwai wani malami me bada magani... Wanda wata mata tayimin kwatancen inda yake d'azu.. Ta tabbatar min Idan har yaba Wanda bai tab'a haihuwa magani. To Sha Allahu asatin mutum yake samun ciki...
Shine fa hankalina ya tashi naketa sauri Nazo na gaya miki...
Ashe da raban zanji wannan mummunan labari...
Shuru NUFAISAT tayi.. Can tace.. "Mezai hana yanxu muje wajensa ko Allah zaisa mu dace..
Aiko da mafificin farin ciki TAUDHAT ta wangale mata baki wajen cewa.. "Maza kirasa awaya muje yanxu pls.
Ba musu NUFAISAT ta d'aga wayarta takira ADAMCY Wanda yake wani companynsa na had'a kafet..
Cikin muryar lallashi take cemai dan Allah zata wanigu yanxu zata dawo..
Dafarko yaqi yarda. Sai Daga baya ya yarda..
Aiko da murna tashirya suka ficce...

TAUDHAT ce me tuk'i. Yayinda NUFAISAT taketa addu'ar Allah yasa ta dace agun wannan malami...


Sunyi tafiya me d'an nisa inda suka dire tafiyar a wani daji.. NUFAISAT ta kalli TAUDHAT ad'an tsorace tace.. "Me zaisa wannan malami yaxo cikin daji haka ya zauna...
Murmushi TAUDHAT tayi da cewa.. "Ai kinsan manyan malamai bayin Allah basu cika zama cikin gari ba. Sunfi zama cikin daji saboda hakan yafi basu damar bautar Allah cikin nutsuwa..
Gyad'a kai NUFAISAT tayi dan tagamsu da abinda TAUDHAT d'in tace...
Fitowa sukayi tare da nufar matan da suke zauna jikin bukkar wajan..
Kallo d'aya zaka musu kasan jiran fitowar wata suke jira daga cikin bukkar..
Da Murmushi TAUDHAT tagaishe tare da shigewa cikin bukkan kai tsaye..
Azahiri wasu daga cikin matan wajen sun nuna mamakinsu ganin hakan da tayi..
Hatta NUFAISAT tayi mamakin hakan... Hmm kodai menene gwara suyi sutafi dan haka kawai taji gabanta na fad'uwa da wajen... Sam sai taji hankalinta bai kwanta da wajen ba..

Itako TAUDHAT tana shiga cikin bukkan ƙarema Matar dake shirin cire kayan jikinta kallo take.. Da alama zata tsinannan zai aikata masha'a da itane kamar yanda yasaba yima duk wacce tazo neman temako garesa..
"Wai me yake damunki ne TAUDHAT.. Mezayasa baki tashi shigowa gareni sai kinga ina niyar San biyan buqatata...
D'an gajeran bokan Wanda kallo d'aya zakamai kasan tsinannene banda fad'uwar gaban da zakaji agaresa shike fad'in hakan...
Murmushi TAUDHAT tayi da fad'in.. "Na d'auka kasan da zuwana yau..
"Aikin San zan sani.. Ko bada NUFAISAT kikazo ba.
"Eh da Ita nazo..
Kecewa yayi da wata shegiyar dariya yana me cewa... "Tunda nake arayuwata ban tab'a ganin macen data had'e kamarki ba... Saidai NUFAISAT tayi miki zarra.. Koda zakiyi zaman kishi da Ita. Dolene kiyi hakuri da ita..
Watoh TAUDHAT.. Yau burinki zai cika tunda naga NUFAISAT kamar yanda na gaya miki..
Dama ƙamshin jikinta kawai nake San d'an ugwalli yaji.. Dazaran tashigo bukkan nan yaji aikinki yaci...
Saidai kuma tun daga nan zatayi miki tsana me me muni.....
"Idan buqata zata biya.. Ban damu da tsanar da zatamin ba... TAUDHAT takatseshi da fad'in hakan tana meci gaba da cewa.. Bara na turota yanxu.. Saika sallami wannan matar Idan mungama tadawo Ku d'ora daga inda kuka tsaya.. Takai ƙarshen zancen nata da nuna matar nan data shigo tagansa da ita gami da ficcewa daga bukkan...

Atareko suka fito ita da Matar dan tana ida zancenta yama matar nuni da ido akan taficce..

"Wai zaki iya shiga..
"OK.. NUFAISAT tace da TAUDHAT tana me shigewa cikin bukkan...
Saidai cak tatsaya tana me ƙarema cikin bukkan kallo tun daga sama har qasa
Gabanta ne yayi mugun fad'uwa... Nan take ranta yayi mugun b'aci.. Danta gane inda TAUDHAT takawota..
Miye had'inta da boka
Meyasa TAUDHAT tayi mata haka..
Meyasa. Meyasa ta yaudareta..
Kallo d'aya zakama cikin bukkan kansan durk'ushe kake gaban boka....
Aiko azuciye ta fitto daga cikin bukkan ta nufi TAUDHAT d'in idanta ya kad'a yayi jah.. Cikin jin zafinta tace da ita... "Ina kika kawoni TAUDHAT..
"Wajen malami mana NUFAISAT. Koba haka na gaya miki ba.
"Ƙarya kike TAUDHAT.. Ba wajen malami kika kawoni ba wajen boka kika kawoni..
Me nayi miki TAUDHAT..
Meyasa kika yaudareni
Kinfi sanin na yarda dake fiye da kowa arayuwata..
Tunda nake ban tab'a kawowa araina zanzo wajen boka danya temaka min da wani abu nashi ba..
Kashi yau kin kawoni wajensa TAUDHAT.. Kin kawoni wajen La'ananne. Kin kawoni wajen tsinanne. Kin kayoni wajen matsiyaci.. Me zai bani imba tsiya ba..
Toda Allah na dogara bada kowa ba..
Kin nunamin kema baki sanshi ba... Saidai alamu sunnuna kinmai farin sani...

"Haba bawar Allah.. Meyayi zafi haka. Kema imbanda kanki akulle yake. Aiyaci kigane tun farko wajen boka takawoki..
TAUDHAT bayau tasaba zuwa nan wajen ba..
Ni nan nizan gaya miki wacece TAUDHAT..
Kin gani dai akan idanki yanda tana zuwa tashige garesa kai tsaye...
Kiyi hakuri Idan kuka koma gida kyayi mata fad'an yanda ranki kesu...
Amma bawai kitsaya nan kina mata fad'a ba..
Gaskiya kiyi gaba karki jawo mana fishin boka. Dan kaf bokayan garinnan ba Wanda baisan TAUDHAT ba. Gata kyakkyawa. Gata karuwa. Gata me San kud'i. Gata mesan maza. Gata mebin bokaye... D'aya daga cikin matan wajen ce ta katse NUFAISAT da fad'in hakan..

Jin hakan yasa ran NUFAISAT qara b'aci. A zafafe ta tafigge makullin motarta tashige cikinta da sauri tatadata saiji kake jinnnnn nananana...😰 ta figi motar kamar zata tashi sama.. Kowa awajen sanda ya tsorata da yanda tatashi motar...
Tab'e baki TAUDHAT tayi ganin tafiyar NUFAISAT d'in...
Cikin nuna rashin damuwa haka ta fad'a cikin bukkan tana me kallan bokan nata zatayi magana ya d'aga mata hannu da nuna mata wani turare yana cewa.. "Kawai kwanta najiki da kyau.. Ba musu TAUDHAT ta cire kayanta da kwantawa gefansa.. Nan suka aikata masha'arsu Wanda tad'aukesu awanni..
Sanda yayi yanda yakesu da Ita San ransa. Kana ya barta da bata turaran yana me gaya mata tasan yanda zatayi tasa ADAMCY ya shaqi ƙamshin.. Yana tabbatar mata da lalle Idan ADAMCY ya shiqi ƙamshin ko alokacin Idan tayarda saiya aureta ba makawa...
Dariya TAUDHAT tayi damai godiya zata ajiyemai kud'i yace tabarshi yayi mata abin kud'inta...

Haka TAUDHAT tasaka kayanta da barin dajin zuciyarta tam cike da farin ciki....

Muje zuwa masu karatu.. Auntyn luv takuce


[6/11, 11:56 AM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 08☆


Da mutuƙar ɓacin rai NUFAISAT ta jefar da gyalanta akan kujer falan nata..
Nan tahau zaga ɗakin tana me cije leɓe da tunano abinda ya faru tsakaninta da TAUDHAT..
TAUDHAT ta yaudareta.. Yaushe TAUDHAT ta lalace haka.. Yaushe tunaninta ya juye haka. Yaushe al'amuranta suka canja haka..
"Hmm mutum kenan..
Ta furta hakan abayyane tana ƙoƙarin zama.. Saidai kanta idda zaman nata. Zainab yayarta tashigo falan da sallama...
Aiko da sauri taje ta rungumeta tana me fashewa da kuka. Faɗi take... "Ashe haka mutum yake Aunty Zainab.. Ace kaf mutanan duniya arasa wacce zata yaudareni sai TAUDHAT...
"Ke waime yake faruwa ne.. Zainab ta tambayeta hankali tashe lokacin da tasamu nasarar zaunawa kan ɗaya daga cikin kujerun falan tare da ita...
Babu ɓata lokaci nan NUFAISAT ta kwashe duk abinda ya faru tsakaninta da ADAMCY daran jiya da yau da safe.. Sannan taƙare da bata labarin abinda ya wakana tsakaninta da TAUDHAT..
Shuru Zainab tayi cike da mamakin komai..
Ta tausayama ƴar uwar tata Dan tasan kishiya da zafi take.. Sannan tasha mamakin TAUDHAT matuƙa
Cikin wani hali ta dubi ƴar uwar tata tace.. "Kwantar da hankalinki sister.. Kishiya ba abar tada hankali bace.. Musamman idan kika yarda da kanki.. Nasan tunanin dazai fara ziyartar kwakwalwarki duk lokacin da kika tuna za'ayi miki ita.. Shine baki haihu ba. Kina tsoran kar mijinki ya wulaƙantaki.. Kina tsoran kar sanadin hakan kishiyar ta rainaki..
NUFAISAT karkisa tunanin ko ɗaya daga cikin waƴannan aranki. ADAMS ba irin waƴannan mutanan bane.. ADAMS bazai taɓa wulaƙantaki ba.. B'cos yana miki wani so. Wanda yafi ƙarfin akirasa da MASEEFAR SOOH..
Zaiyi Auran ne dan mahaifansa badan ya gaji da ƙaddarar da Allah yasaukar miki ba...
Kiyi nazari. Kiyi tunani. Ki nutsu kiyi amfani da iliminki wajen kishin da yake shirin tumfaroki.
Kiyi hakuri kamar yanda mummy ɗinmu tayi lokacin da Dadynmu ya qara Aure..
Amatsayina na ƴar uwarki.. Zan nemi wata alfarma daga gareki.. Karki ƙara kaima wani kukanki imba Allah ba..
B'cos ba abinda wani zai iya yimiki akan abinda Allah ne ya lamince musu da suyi..
Nasanki da ibada. Toki dage wajen gayama Allah buqatarki kamar haka.... _ALLAH KAINE ALLAH. ALLAH BA WANI SARKI A BAYAN KA ALLAH. ALLAH NA ROK'EKA IDAN WANNAN AURAN ALKAIRI NE AGARENI DA MIJINA ALLAH KA TABBATAR DA ALKAIRIN.. ALLAH IDAN BA ALKAIRI BANE AGAREMU ALLAH KA HANA YUHUWARSA. ALLAH IDAN YA KASANCE SAI ANYI. ALLAH KADUBENI DA FUSKAR RAHMA. KAYAYEMIN KUNCI DA BAQIN CIKI DA TASHIN HANKALI DA DAMUWA. BAMA NI NASAN KA YAYAEMIN BA. KOWA DA NAKE TARE DASHI YA SHEDA HAKAN. ALLAH KA DORANI AKAN MIJINA DA ABOKIYAR ZAMANA. KA HANA MUNAFUKAI DA MAHASSADA SHIGOWA CIKIN AL'AMURANA DA MIJINA DA ABOKIYAR ZAMAN TAWA.. ALLAH KA MALLAKAMIN MIJINA. KA HANESA KUNTATAMIN KAHANESA WULAƘANTANI KA HANESA AIKATAMIN ABINDA ZAISA MAQIYANA SUYIMIN DARIYA. ALLAH NABAKA AMANAR KAINA. DA DUK WANI ABU DAYA SHAFI RAYUWATA. KA KYENTANI FIYE DA WANNAN BAIWAR TAKA DA ZAKA HAD'ANI ZAMA DA ITA..._
Sister ki dage da wannan addu'ar karki qara yarda da wata qawa arayuwarki..
Batun TAUDHAT idan tazo gareki. Karki nuna mata kin canja mata matsayi afuskarki. Nuna mata tabi Allah. Tadena aikata duk wani abu da wannan matar tagaya miki akanta... Daga nan saikice mata daga yau ba'ita bake..
Karki kuskura ki qara qawance da TAUDHAT.. Nagaya miki..

Share hawayenta NUFAISAT tayi da kama hannun yar uwar tata tace. "Insha Allah Aunty Zainab zanyi duk abinda kikace min..
Nagode ma Allah daya bani ƴar uwa kamarki. Kin bani shawarar dazata kaini ga hanyar dacewa..

"Yauwa ƴar uwata.. Ki sama zuciyarki hakuri da dangana. Komai yayi farko zaiyi qarshe kinji
Gyaɗa mata kai NUFAISAT tayi alamum amsawa...
Haka dai Zainab tadinga kwantarma da NUFAISAT hankali har NUFAISAT ɗin tafara tunanin toh kishiyar tazo mana mezata tare mata..😀
Nan Zainab tatayata abincin ranah wanda za'a kaima ADAMS d'in. Ta koya mata wasu qananun abubu na girkin saboda yamma tayi tana San tafiya gida...

Ba qaramin farin ciki sosai NUFAISAT taji ba. Lokacin da mijin nata ya kirata awaya yana nuna mata farin cikinsa na yanda yaji dad'in abincin da ta aikomai


Da misalin qarfe shidda ne TAUDHAT tafesa wankanta me matuƙar kyau. Ita kanta bata buqatar ace mata tayi kyau dan da gasken gaske tayi kyau d'in.. Cikin jar atamfa me ratsin blue. ɗinkin doguwar riga me bajajjen hannu irin na yara ƴan zamani.. Sosai ɗinkin ya karɓi jikinta abinka da farar mace..
Nan tafeshe jikinta da turaran da boka yabata. Kana tad'auki jakarta da gyalanta ko kallan mahaifiyarta batayi ba tasaka takalminta taficce daga gidan sai gidan NUFAISAT...


Dake lokacin NUFAISAT take sakaran dawowar ADAMSY kasancewar lokacin lokacinne lokacin dawowawarsa. Hakan yasa take fes da ita kamar yanda tasaba kimtsa kanta kan lokacin dawowarsa..
Tana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun falan nata TAUDHAT tashigo da sallama murya a sanyaye...
D'auke kanta NUFAISAT tayi bayan ta amsa mata sallamar..

Amunafunce TAUDHAT tazauna tana me fuskantar NUFAISAT d'in cikin sanyin murya tace.. "Nasan da cewa ban kyauta miki ba. Ina neman gafararki. Dan Allah kiyafe min. Hakan baza taqara faruwa ba. Wallahi nayi miki alƙawari..
Ahankali NUFAISAT ta kalleta da cewa... "Karki nemi gafarata TAUDHAT. Kije kinemi gafarar Allah. Dan nasan kinfi sab'a mishi fiye dani.. Nasani kin sani.. Dan haka kiji tsoran Allah ki koma garesa kidena aikata duk abinda wannan matar tafad'a min akanki. Ki tuba ki koma ALLAH. Allahn yasa mu dace gabaki d'aya amiin...

"Nagode NUFAISAT. Kuma insha bazan qara aikata ko d'aya daga cikin abinda kikaji ba.... TAUDHAT tace da ita hakan...

Kan NUFAISAT tayi magana saiga ADAMCY ya shigo falan da sallama...
Da wani yanayi NUFAISAT taje ta rungumesa tana me nunamai farin cikinta naganinsa da tayi
Gaskiya ADAMS yaji dad'in hakan. Kasancewar bata saba yimishi hakan agaban TAUDHAT ba..
Yana San tadinga bashi kulawa agaban kuma waye ba wai TAUDHAT bama..

"Wow uwar gidana. Kinga yanda kika tafi da zuciyata kuwa..
"Hmm.. aikai LEEKITAN ZUCHIYA ne. Tunda natafi da ita. Sai kasan yanda zakayi kadawo da ita..
Lakuce mata hannu yayi cikin matuƙar farin ciki yace.. "Abubuwa biyu sun sauya daga safe zuwa yanxu..
"Toya zanyi da raina💋. Tunda na ɗaura ɗammarar bama megina dukkanin abinda zai sashi farin ciki...
Qara rungumarta yayi cikin so da k'auna... Kana yaɗan zareta kaɗan daga jikinsa ya kalli TAUDHAT tare da sakar mata murmushi yace. "Yau qawarki ta shareki takulani ko.
Murmushin itama ta mayar masa da cewa.. "aidama abinda yadace dani kenan Idan dai kana cikin gidan nan...
Tafadi hakan da tashi tana me sab'a jakarta ta ƙaraso kusa dasu yanda ADAMS zai shaƙi ƙamshin tana. Tana meci gaba da cewa.. Nizan tafi..
"Tofah🤔 yau bazaki bari ya rage miki hanya ba.. Cewar NUFAISAT
Kan tayi magana sai ADAMSY Wanda kansa yayi masa wani dum kasancewar ya shaqi qamshin turaran na TAUDHAT. ya sakarma NUFAISAT kiss awiya. Wanda yasata qanqamesa a lokaci d'aya kuma ta kallesa. Yace.. "Barta tatafi sweetheart. Yau bazan rage mata hanya ba. Kasancewar tasaka wani turare mara dad'i. Saidai duk da hakan yana tab'a ZUCHIYA.. Yana aika mata da wani saƙo. Sakwan da yake barazanar tarwatsata...
Azahirin gaskiya idan nace zan d'auki lokaci ina shaqar qamshin. Ba makawa komai zai iya faruwa da ZUCHIYATA...
Afurgice NUFAISAT tazare jikinta daga nasa. Taqara tsaida idanta akansa sosai tace.. "Ba wani saƙo dazaiyi barazanar tarwatsa ZUCHIYARKA idan har banice nabaka wannan sakwan ba.. Mezaisa kaji hakan daga TAUDHAT..
Taɓe baki yayi tare da kallan TAUDHAT ɗin ya maida kallan nasa kanta yace.. "Bansan me zance miki ba. Kasancewar yau nafara jin hakan. Kuma..

"Kuma me.... Sannan meyasa kaji hakan... NUFAISAT ta katseshi da faɗin hakan cikin sauri..
Da wani hali Yakama hannunta da cewa.. "Nima ban sani.. Ya kamata kiyi wani abu akai. Dan yanayin yana qara shigata sosai fah..
Saurin kallan TAUDHAT tayi wacce kawai tayi saƙale tana kallansu kamar bata gane me suke cewa ba tace da ita.. "TAUDHAT kificce daga falan nan kije gida kawai sai nazo. Dannafi buqatar daidaituwar ZUCHIYAR MIJINA fiye da tsayuwarki anan...

"Laaa😦. Karki damu!.. Wata ranah nidake zamu daidaita zuciyar inda muna raye.. TAUDHAT na faɗin hakan taficce daga falan zuciyarta tam farin ciki. Dan tasan tunda ya shaqi qamshin. Kuma ya magantu akan qamshin tasan yarigada ya shigo hannu...
Saidai tatsorata sosai ganin bai rikice ba
Dan tatab'ama wani alhajinta shigen irin hakan. Alhajin na shaqar qamshin. Nan take ya rikice mata.. Tobataga hakan agun ADAMCY ba. "Hmm. indai kere na yawo zabo na yawo wata ranah zasu had'u..
Tafad'i hakan abayyane lokacin da masu gadin gidan suka bude mata get d'in gidan danta fitta....



NUFAISAT ta kalli ADAMS tace.. "wai me TAUDHAT take nufi da wannan kalmar na zumu dai-daita ZUCHIYAR nida ita.
Janta ADAMS yayi izuwaga shashinsa yana cewa.. "Ki kula dani awannan lokacin yafi ki tsaya kina min wannan wawiyar tambayar...
Shuru NUFAISAT tayi kawai bayan sun kasance a bedroom nasa tana me tayasa cire kayan jikinsa dan yashiga wanka...


Muje zuwa. Rahma nalele ce🧕🏻 taku ƴan hannuna...👐🏼
[6/11, 11:57 AM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 9☆


Bayan ya fitto ya tarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login