Showing 12001 words to 15000 words out of 81675 words

Chapter 5 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

da kayan data fito mai dashi na bacci
Doguwar rigace dai me santsi. Sanda ya feshe jikinsa da turare da mayika kana yasaka da gabatar da sallar magrif saboda lokacin da ake kira har akayi sallar yana wankan.
Sanda ya sallame sannan ya fitowa falan yana me wurga ido alamun nemanta. Aiko can ya ganta kan dining tayi dagumi kawai alamar tana cikin wani hali.
Rungumarta yayi ta baya batare dayace komai ba.
Can data samu nutsuwa daga d'uminsa saita kama hannunsa ta zaunar dashi kan d'aya daga kujerun wajen wacce yafi zama akanta. Ta had'a mishi komai na abin data girka masa tare da zuba nata ta zauna idanta cikin nasa tace. "Ina fatan wannan yafi na d'azu dad'i. Murmushi yayi tare da cewa. "Ai daga ganinsa zaifishi dad'n. Musamman idan nayi duba da yanda yaketa zuba qamshin nan.
Murmushin jin dad'i tayi da fad'in. "Saidai kamin afuwa abisa Kalmar daka fad'i d'azu. Na wai karna qara bari wani yasamin hannu akan abinda zakaci.
Wallahi duk aunty Zainab ce tasamun hannu daga na d'azu harna yanxu da zakaci
"Karki damu matata. Saida nayi furucin nagane dole sai ansaka miki hannu kafin nasamu yanda nakeso.
Murmushi tayi dad'an duqawa ta sakar mai kiss agoshi tace. "Nayi maka alqawari mijina. Daga aunty Zainab ba wacce zata dinga samun hannu akan abinda zakaci. Ita d'imma nawani d'an lokaci ne. Dantace 2 month kawai zata d'auka tana koyamin
Murmushi yayi shidai yana San matarsa. A hankali yace mata. "Allahma yasa ki iya a 1 month kawai.. "Insha Allah zanyi qoqarin iya duk wani abu Wanda nasan zai dace dakai Wanda zaka soshi. Ka qaunaceshi. Kaji dad'in shi koda a 1 month d'inne
Yaji dad'in furucinta sosai. Hakan yasa yace mata idan tagama taje ta canja kaya. Tace ina zasu. Yace yau rakiya zatamai zuwa gidansu dady amman saiya dawo daga sallar isha kannan ma itama tayi sallar.. Toh tace mai tare dajin wani mafificin dad'i saboda yanda yake kod'a abincin yana nuna mata santinsa azahiri danya qara qarfafa mata gwiwa

Haka daya dawo ya d'auketa basu zame ako ina ba sai'a gidansu.
Nan masu gadin gidan suka hau zubewa kamar yanda suka saba wajen girmama shi
Yayi musu kyauta me tsoka inda suka dinga saka mai albarka.
Anan babban falan gidan suka tarar da Dadyn nasa da Amminsa harda Hajjiya Rukayyat da Salim Nan suka sube suka shiga gaishesu.
Da farin ciki Dady da Amminsa suke amsa musu. Banda Hajjiya Rukayyat. Dan dama haka abin yake awajenta. Idan har Ammin ADAMS ce da girki bata sake fuska a wannan ranah. Dukko da cewar rabin lokacin nata ne..
Salim ya gaida Adams da NUFAISAT. Suka amsa da kulawa. Sannan Dady ya qara tsaida idansa akan Adams yana cewa. "Sannu ADAMS kunzo lafiya? "Eh Dady dafatan muma mun sameku lafiya. "aa lafiya lau lau. Yanxu nake maganarka kuwa da d'an uwanka Salim. Ashe kana kan hanya.
"Eh Dady. Allah yasa ba lefi nayi ba. ADAMS ya fad'i da murmushi cikin wasa.
Murmushin shima Dady yayi da cewa.. "Bakayi komai ba. Kawai hirar taka tazo ne. Nayi farin cikin yanda kazo min da NUFAISAT. Dan dama ina San mata magana akan Auran dana saka kayi.
Murmushi ADAMCY kawai yayi
Dady ya numfasa da kallan NUFAISAT yana me cigba da cewa. Kiyi hakuri NUFAISAT. Bawai zai qara Auran bane danke. aa zai qarane sabodani. Nasan kina da nutsuwa da hankali koda abin ya faru bazaki kawo wata matsala ba. Tuna hakan danayi shiya bani qarfin gwiwar ce mishi yayi. Allah yayi miki albarka ki dage da addu'a idan kina da rabo Allah yabaki me albarka..
Qara sunkuyar dakai NUFAISAT tayi cikin ladabi tace.. " Dady ba komai insha Allah baza'a samu matsala daga gareni ba..
Murmushi Dadyn yayi cikin jin dad'in furucinta yace. "Allah yay miki albarka
"Ameen tace. Ammi tadafa kanta cikin jin dad'i tace. "Nagodema Allah daya bani sirika me hankali. Me kaifin tunani. Allah ya dubeki yabaki masu albarka.
Kwantar da kanta NUFAISAT tayi kan cinyar Ammin tana cewa amiin Ammina...
Tsaki Hajjiya Rukayyat taja tare da tashi tana kallan NUFAISAT tace da ita. "Kizo falo ki sameni Inasan magana dake. Tana fad'in hakan tabar falan afusace. Jiki asanyaye NUFAISAT takalli mijinta Adams Ya gyad'a mata kai alamar taje. Nanko tatashi tabi bayanta inda tataddata afalan nata tana zagaye.
"Momy gani. (Dake haka suke kiranta dashi )
Da sauri Hajjiya Rukayyat takalleta da cewa. "Ke wata irin shashashace. Waya gaya miki kishiya dad'ine da ita. Kishiya ba'abokiyar zama bace abokiyar gabace. Karki kuskura ayi miki ita. Banda sakarci irin naki wata macece me hankali zatayi abinda kikayi. Ko'an gaya miki so haukane.
Wallahi kika yarda Adams yayi Aure kashinki ya bushe agunsa. Bar ganin yanxu yana wani nuna miki so yana samun d'a daga wajen wata zaifara wulaqantaki yaga toke amfanin me kike masa daga qarshe ya turaki gidanku da farar takarda na saki....
Da sauri NUFAISAT takalli Hajjiya Rukayyat cikin matuqar tsoro. Itako ta gyad'a mata kai alamar tabbatarwa.
Gaban NUFAISAT yashiga fad'uwa ganin halin data shiga yasa Hajjiya Rukayyat cigaba da cewa.. Wallahi kima kanki qiyamal lalli kisan duk hanyar daza kibi kibi dan hana wannan Auran tabbatuwa. Idan kin kasa kizo zankaiki inda za'a share miki hawaye.
Gumi NUFAISAT tagoge da mayafinta tace da ita. "Toh momy zanyi tunani nagode.. Tana fad'in hakan taficce daga falan da sauri ta fad'a falan Ammi tazube kan ɗaya daga cikin kujerun falan tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun falfalangi.
Itako Hajjiya Rukayyat murmushin mugunta tayi tare da cije leb'e tana rayawa aranta wata qila ta'iya cin galaba akan NUFAISAT. Danta hango tsoro muraran akwayar idanta...
Murmushin jin dad'i tayi tare da gyad'a kai tashige bedroom d'inta

Suko su Dady da Ammi da Adams da Salim hira suka b'arke da ita sosai duk akan halin NUFAISAT ne Wanda suke ganin da wiya yasamu mace me hankalinta.
Sanda goma tayi Adams yama Dadynsa sallama sukafito daga falan shida Amminsa
Sunyi mamakin ganin yanda lokaci d'aya sukaga canjawar NUFAISAT. Danga damuwa muraran akan fuskarta har wani gumi take.
Ahankali Ammi tazauba dab da ita tare da dafata tace. "Y'ata meya sameki kike cikin damuwa haka. Shuru NUFAISAT tayi mata. Ganin hakan yasa Ammi murmushi tacigaba da cewa. Wato Rukayyat ce tajefaki cikin wannan halin ko. Ahankali NUFAISAT ta gyad'a mata kai tare da rushewa da kuka..
Ammi bata tambayeta miye ba. Amman tayi kokarin rarrashinta har tasamu tayi shuru. Sannan tayi mata nasiha akan taguje sakama zuciyarta zancikan da zasu dameta gudun kar wata ranah tasamu babbar matsala da ita. Kuma duk abinda zataji akan sharhin da za'a mata kan matsalarta taji tsoran Allah wajen yanke hukuncin daya dace da ita.
Godiya sosai NUFAISAT tama Ammiin sannan Ammin tabada turare suka mata sallama da barin gidan

Shuru haka suke tafiya amotar bame magana acikinsu har suka iso gida.
Wajen baccinsu ne anan Adams ya kasa jurewa ya rungumeta yana tambayarta me momy Rukayyat tagaya mata Wanda yasata shiga cikin wani hali haka.
To dama bawai tagama kukan nata bane agidansu dan haka saita qara b'arkewa da kuka wiwi
Cikin rikicewa yahau lallashita yana cewa tunda batasan cewa komai to tabar kukan haka ya ishesa.
Bata dena ba. Sanda ya had'e bakinsa da nata yahau aika mata da wani shu'umin kiss da wasu sakwanni kana tadena kukan tahau manne masa dajin dad'in yanda yake aika mata da sakwannin
Can da suka samu nutsuwa saita fara cewa. "Dan Allah mijina kamin aikin gafara kai kad'ai nake so. Nake ji. Nake qauna. Nake fatan kasancewa dakai har agidan Aljanna. karka wulaqantani kamar yanda momy Rukayyat tace zakamin. Tace min zaka wulaqantani dazaran kasamu d'a daga wata mace badaga gareni ba. Sannan zaka korani gidamu da farar takadda na saki saboda lokacin zakaga bani da amfani agareka. Idan hakan ta kasance agareni mijina hauka zanyi. Wallahi mijina harkacewa zanyi. Dan Allah kamin aikin gafara karka bari zuciyarka taraya maka hakan ko'a mafarki ne bare a zahiri. Wallahi sanka nake irin dayawa d'in nan.
Murmushi yayi da qara maqaleta jikinsa yana me shafa kanta cikin soo da qaunarta. Yasani Hajjiya Rukayyat ta tsoratata da yawa. Gashi ita bata iya shiga damuwa da tsoro ba. Gaskiya Allah ya sakama matarsa dan tacutarmai da ita cikin lokaci qanqani.
Da sanyin murya yake cemata... "Ki kwantar da hankalinki matata. Bana d'aya daga cikin waƴannan mazajen da suke aikata hakan ga Uwargijayensu. Wallahi NUFAISAT idan aka cire mahaifana bani da wani sauran abin so arayuwata kamarki. Hatta haihuwan bata shigeni ba kamar yanda qaunarki tashigeni.
Dan Allah kibar ZUCIYATA tasamu nutsuwa wallahi bazan tab'a wulaqantaki cikin hankalina ba. Dan bana tunanin zan qaunaci wata mace kamar yanda na qaunaceki. Saidai kinsan d'an Adam agizine koda hakan tafaru dani agaba karki zargeni kimin uziri dan Allah...
Zatayi magana ya hanata maganar saboda aika mata da yayi da wani sakwan na soyayya...

NUFAISAT tana qaunar qaunar mijinta irin sosai d'innan
Shiyasa tsoro yake kama zuciyarta idan aka kawo mata batun rabuwa dashi.
Haka Adams ya raya mata wannan daran da bata farin cikin da ita kanta sanda tayi mamaki
Danji tayi kamar aranar yafara Love da ita❤



Itako TAUDHAT tana zuwa gida tacire kayan jikinta dan itama kanta turaran na bokan nata ya isheta. Dan bashi da dad'i da gaske kamar yanda Adams yace
Wanka taqarayi dayin sallah kana tamiqe agadanta tare da fad'awa tunanin gata a qirjin ADAMCY..... Nanko take ta lumshe ido tare da rungume filo cikin San kasancewa a yanayin.
Bata d'auki lokaci tana tunanin ba wani Alhajinta ya kirata akan yana San kwana da ita. Aiko tana jin hakan tadiro daga gadan nata da zarar jakarta da key na motarta tacema mahaifiyar tata bazata dawoba sai gobe. Bata jira cewar mahaifiyar tata ba taficce abinta.
Haka uwar tabita da kallo tana me addu'ar Allah ya shiryar mata y'ar tata ya kuma cire mata tsoranta dan tasamu damar yanke mata akan abinda takeyi kamar yanda kowace uwa tagari takema y'arta.


Rahma Nalele ce Y'an hannuna 🤝🏻🧕🏻
[6/21, 12:22 AM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 10☆


Washe gari da cikakken farin ciki Adams ya yabar gidan nasa. Kasancewar yabar matar tashi da farin ciki.
Da misalin qarfe biyu ne na ranah Adams da abokinsa Yusuf suke tare cikin ofishin Adams d'in. Abincin da NUFAISAT ta'aikuma da Adams d'in suke ci
Sai Adams yake ma Yusuf bayani akan Auran da yake San qarawa. Yusuf ya qara tsaida kallansa akansa da murmushi Yace.. "Toh yanxu ta ina zaka fara. Bayan nasan NUFAISAT ita kad'aice madubin dubawarka. Bayan ita ba wata wacce kake da ita afannin so. Yanxu ta ina zaka fara kenan
Shafa kansa Adams yayi da murmushi Yace. "Da wai na yanke shawaran Auran TAUDHAT. Kasan cewar itace tasan NUFAISAT fiye da kowa. Ba wani abu dazata mata wanda zai zama na Allah wadai. Sannan ita kanta NUFAISAT nasan hankalinta zaifi kwanciya da TAUDHAT d'in. B'cos tana Santa sosai na tabbatar zan iya samun zaman lafiya agidana tunda sunsan kansu.
Shuru Yusuf yayi cikin nazari yana tuna yanda TAUDHAT da NUFAISAT suke. Tabbas Auran TAUDHAT shine abinda ya dace da Adams. Kasancewar TAUDHAT tafi kowa sanin NUFAISAT. Kuma zasu iya samun zaman lafiya me d'orewa. Saboda suna San junansu. Kuma sun taso ne tun yarinta.
Kallan Adams Yusuf yayi da cewa. "Gaskiya kam ka Auri TAUDHAT. Saboda na tabbatar bazata cutar da NUFAISAT ba. Saboda kaga yanda suke qaunar junansu. Sun taso tun yarinta. Kuma kowa yasan halin kowa. Sunsan abinda in sukama junansu zai b'ata musu rai. Haka sunsan abinda idan sukama junasu zai faranta ransu.
Ka aureta kawai.
Murmushi Adams yayi da cewa. "Nima abinda na duba nagani kenan..
"Gaskiya kayi tunani me kyau Amman wani hanzari ba gudu ba. Shin ita TAUDHAT d'in tana sanka kuma zata amince da hakan kuwa.
Jan numfashi Adams yayi da cewa. "Hmm ai nadad'e ina hango qaunata cikin kwayar idanta.
cikin dariyar Yusuf yace. "Lalle kace zata fad'o hannu. "Sosai ma kuwa. Adams ya bashi amsa cikin sauri. Girgiza kai kawai Yusuf yayi dacigaba dacin abincinsa dan yafi kowa sanin irin farin jinin da Adams yake dashi agun jama'a. Maza nasu San daban haka mata nasu San daban
Yusuf abokin Adams ne tunna k'uruciya. Yawancin halaiyar Adams Yusuf yana dasu. Hakan yasa Adams yafi yarda da Yusuf fiye da kowa a cikin abokanayansa. Haka shima Yusuf d'in ya yarda da Adams fiye da kowa
Yusuf yana kyau hankali da nutsuwa san soyayya. su biyu ne iyayansu suka haifa shi da qanwarsa Nazifa. Iyayansu sun rasu sun suna qanana. Hakan yasa suka tashi a qarqashin kulawar kakarsu Hajjiya Delu.
Saidai iyayan nasu sun tafi sun bar musu dukiya me tarin yawa.. Dake Yusuf d'in kasuwanci ya karanta sai kawai ya karb'i dukiyar tasu gun qanin babansu yahau juya musu ita. Sosai Adams yake qara bashi haske akan kasuwancin. Duk da shi karanta yayi Amman Adams ya fishi wayewa akai.
A yanxu dai Nazifa qanwar Yusuf d'in tana secondary skull. A islamiya kuma takusa yin sauka. Yusuf yana ji da ita sosai. Yana Santa sosai. Hakan yasa yaqi yin aure da wuri saboda yana San yasami mace tagari wacce zata kulan mishi da qanwar tasa tasota ta qaunaceta dan Allah
Wannan dalilin yasa yaketa gwada mata da nuna musu yana matuqar ji da qanwarsa dazaran yaga kin fara nuna masa wani hali akanta na yanda yake nuna miki kulawarsa akanta. Toh nan take zai rabu dake. Har yanxu a haka yake. Wannan shine labarin Yusuf a takaice.


TAUDHAT ko sun tsula tsiyarsu sosai ita da Alhajin nata. Dan bai barta ba sai kusan sha biyu na safiyar yau. Bata koma gida ba sanda tabiya supermarket tayi sayayyanta dan ba qaramin kud'i ta cajesa ba
A haka takoma gida da kaya niqi niqi. Naci dana sawa dadai sauransu
Ita dai mamah mahaifiyarta ido ne kawai nata akanta.


NUFAISAT ko Auntynta Zainab na tare da ita tana qara ganar da ita tafannin girki. Dan yanzuma da daddare wani kayataccen girki take had'ama megidan nata.

Bayan TAUDHAT ta huta wanka tayi tanufi gun bokan nata tazayyane masa abinda ya faru tsakaninta da Adams wajen jin qamshin turaran da yaji. Wai tajishi shuru bai nemeta ba. Anya turaran ya bigesa dakyau kuwa.
Dariya bokan ya sheqe mata dashi yana me cewa. "Ai ina tabbatar miki tunda ya sheqa saiya aureki. Kuma ga ranar Auran naku dashi nan. Ya shafi gefansa dawani abin shed'anancinsa. Aiko muraran saiga TAUDHAT da ADAMS cikin d'aki d'aya. Tana zaune kan gado shima yana gefanta. Da lillib'i akanta irinna amare.
Aiko ganin hakan yasa TAUDHAT fashewa da dariya tace. "Ina sanka boka. Dan aikinka nakyau. Yanxu yaushe zaizo gareni.
"Ai kisha kuruminki kawai cikin daran nan zaki gansa. Godiya tamai sosai bayan ya d'anata ta karkad'e jikinta ta koma gida da matuqar farin ciki yau Adams zaizo gareta.



Sai farin ciki NUFAISAT take ganin yanda yake nuna santinsa akan girkin nata. Tace. "Yau fa nakai awanni ina had'a komai. Ba mamaki shiyasa yau santinka yafi na jiya.
Murmushi ya mata cikin so da qauna yace. "Allah ya dad'a miki albarka matar aljannah. "Amiin mijina
Bayan yagama ne tana kan ciyarsa yake ce mata. "My luv kinsan wacce na yanke shawarar Aura. Girgizamai kai tayi kuma da sauri tace. "aa. Sannan bana San nasan kowacece tunda dai auranta zakayi ai dole nasanta.
"Nasan zakiyi farin ciki da ganinta. Saboda kina qaunarta kuma.. "Haba mijina. Dan Allah kabar batun haka. Dan zuciyata tafara rawa. Karka b'atamin farin cikina.
Murmushi yayi da kama fuskarta yace. "Har abada bazan tab'a b'ata miki farin cikinki ba matata. Kiyarda dani
Kwantar da kanta tayi akan kafad'arsa tace "naji ana kiran sallah in tashi maka daga kan cinya ko.
"Eh. Amman daga masallaci zan wucce wajen qanwar taki kina da sak'o gareta Wanda zan bata ne. "Aa Saidai kagaya mata ina gaisheta. Sannan ta kulammin dakai sosai. Idan tabari kadawo min gida rai ab'ace saina hukuntata.
"Insha Allah ko zan gaya mata.
Haka NUFAISAT tatashi daga jikinsa ya sakar mata kiss da rungumarta kana ya ficce daga falan. Tana jin fitarsa wajen get hawaye ya zubo mata. Ahankali tace "baka iya yimin qarya ba mijina. Sannan wannan gaskiyar da ciwo take. Zan iya jure komai arayuwata amman bazan iya jure ganinka da wata ba. Tana kaiwa qarshen zancen nata tarushe da kuka wiwi. Harda d'aga hannuwanta ta d'ora aka tana me cigaba da cewa.. Wayyo Allah mijina aure zaiyi. Mijina kishiya zaiyimin. Mijina yau ya tafi zance gun wata. Dan Allah zuciyata kimin adalci kidena jin wannan zafin da rad'ad'in nan ki sake kibarni na huta dan wata rana bama zance ba wallahi raba shinfid'a zanyi dashi......
Haka NUFAISAT ta dinga sambatu ita d'aya. Daga qarshe dai tayi toilet tayo alwala ta gabatar da sallar i'sha tare da kaima Allah kukanta akan ya cire mata damuwa da kishi akan Auran mijin nata


Da gaske Adams daga masallaci gidansu TAUDHAT ya nufa.
kunsan dama a kintse TAUDHAT d'in take. Tunda bokanta ya tabbatar mata da zuwan Adams gareta cikin daran
Dan haka tana ganin wayarsa tamiqe jikinta na rawa ta d'auka da cewa. "Ina maka fatan ALKAIRI mijin k'awa.
Da murmushi Yace "Tare dake. Ina ƙofar gidanku Allah yasa ina da raban ganin kyakkyawar fuskarki. "Mezai hanaka gani. Bayan nida qawata duk mallakinka ne. "Insha Allah kuwa. Zanso dai naganki yanxu kafin kicinye min lokaci na awaya.
"To kakashe mana. Daka juyo da fuskarka izuwa ƙofar gidamu daka ganni katabbbatar bazan cinye maka lokaci ba.
Murmushi yayi bayan ya juya ganinsa ga kofar gidan nasu nanko ya gantan a kofar gidan. Hakan yasa ya kashe wayan. Dayi mata nuni data shigo cikin motar. Ba musu tashiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login