Showing 42001 words to 45000 words out of 81675 words
ba'a wajen ainihi tayi rayuwa ba aa zama ne dai ya kawo ta cikin dajin ita da d'anta Musa..
Dan ita asalinsu y'an qauyen Jos ne BASA.
Yawo yaranta biyu ne aduniya. Rahma da Musa qaninta..
Mahaifinsu ya mutu ne bayan sati uku da Aurar da Rahma da yayi ga wani d'an garin Kano. Wanda bai sanshi ba haka kawai dan ya ganta yace yana Santa Sai kawai ya bashi ita wai ya yaba da hankalinsa..
Dan kawai ya d'auki wata d'aya yana zuwa tad'i wajenta.. Dake kunsan Bafulatan mutum dasan kud'i nan take shiko saurayin ya dinga masa kyauta kala kala. Hakan yasa yace wai yayarda da hankalinsa. Amman ya masa alqawari idan ya aura masa y'arsa Rahma zai dinga zuwa duk wata biyu yana kawo musu ita suna ganinta..
Shiko saurayi yayarda da hakan.
Ita dai yawo hankalinta bai wani kwanta ba. Gani take saurayin d'an yankan kaine. Yana aure mata y'a zai yanke mata kai.
Dan haka tanuna ita bata amince da auran ba. Shi kuma mijin nata yace ya amince. Haka tanaji tana gani ya d'aura ma Rahma aure da wannan saurayi ya kuma saka Rahman gaban motar saurayin yace tama mijinta biyayya dan yayarda dashi😨😨😨
Yowa tafi kwana uku tana kukan rabuwa da Rahma
Lamarin d'aurin Auran ya faru da kwana uku tayi mafarkin saurayin ya yanka mata y'a..
Aiko wayewar wannan safiya data tashi ba abinda take Sai kuka..
Shiko mijin nata ce mata yayi Dan tasa hakan aranta ne shiyasa tayi mafarkin hakan..
Jinsa kawai tayi Amman tasa aranta da gaske sirikin nasu ya kashe mata Y'a...
Tana cikin jimamamin hakan ne kuma da sati biyu mijin nata ya rasu..
Wannan yasa tsoro ya kama zuciyarta..
Ana yin Arba'in d'in rasuwan mijin nata sai tace da Musa ya saida shanunsu kaf zasu tashi daga basa nan qauyen Jos su koma qauyen yola ko gwambe..
Haka musa ya yarda da zancenta ya sayar dasu kamar yanda ta buqata shine fa basu zame ako ina ba sai'a garin gwambe
Ahankali suka fara gane kan garin. Kasancewar Yawo tafi san zaman daji saita dinga neman sani akan dajikan da suke qauyen gwambe. Anan taji ta gamsu tayarda da zama a Rugar malam jauro..
Sai Musa yasai musu shanu agun Malam Jauro ya fara ciwansu. Aiko cikin iko na Allah nan shanun nan suka dinga haihaifafa ya tarasu da yawan gaske.
Anan yaga wata wacce yake so ya Aura sunanta Hasiya.. Hasiya macece me hankali da nutsuwa tunda Musu ya furta mata yana santa da aure taji tana sanshi da qaunarsa..
Hasiya y'a d'ayace agun iyayenta. Wanda makwaftan junane su dasu Musan
Suma iyayenta basu da wasu danji dan suma zuwa rugar sukayi kamar yanda su Yawo d'in sukazo..
Sun yarda da auran Musa da Hasiya iyayenta nan aka d'aura musu aure.
Saidai watansu takwas da auran Musa ya rasu ya bar Hasiya da ciki..
Anan hankalin Yawo ya tashi matuqa dan dama su biyu gareta. Gashi bata san inda Rahma take ba. Da gaske saurayin nan ya kasheta kobai kasheta ba oho..🙂 Shid'in kuma da take kallansa taji dad'i Gashi ya tafi..
Wannan dalilin yasa tad'auki san duniya ta d'ora akan cikin da Hasiya take dashi...
Hasiya na tashi haihuwa tahaifi mace santaleliya me kama da ita sak.
Saidai ita baqa ce. Irin baqin nan da bature ke cewa black beauty..
Kallo d'aya zaka mata kasan kayi gamo da baqar bafulatana..
Gashi Mahaifiyarta fara mahaifinta fari danginta farare amman ita tazo baqa..
Ranar suna yarinya taci suna FaÉ—ima.
Dake malam jauro ne ya rad'a mata sunan haka kawai yaji yana qaunar yarinyar. Dan yarinya ce me shiga rai tun zuwanta duniya haka mutanan wajen suke tururuwa wajen san ganinta.
Dan da wiya kamata kallan farko bakaji tashiga ranka ba..
Hakan yasa Malam Jauro yake kiranta da Musulma.. Shine Yawo take kiranta da MUSLEEMA.
San duniyar nan haka Yawo da mahaifan Hasiya suka d'auka suke nunama MUSLEEMA
Kaf cikin Rugar nan babu black beauty Sai MUSLEEMA
Hakan yasa kowa yasan da zaman MUSLEEMA awannan Ruga..
Ayanxu shekarunta goma sha biyu.
Kuma a qa'idar Rugar malam jauro yara y'an mata suna kaiwa shekaru goma sha uku ake Aurar dasu..
Wani d'an malam jauro ne yake san MUSLEEMA. Ayanxu haka har an saka musu ranah..
MUSLEEMA yarinyace me sanyi haka. Tana da d'an surutu tsiwa idan tasanka kuka saba..
Tana da manyan ido shanyayyu irin na me jin bacci d'innan. Ga dinful d'inta me sata kyau idan tayi murmushi ko dariya. Ga jiki na d'aukar hankali..
Zara zaran yatsunta abin kallo ne. Sannan tana da Gashi me tsawo me santsi da sheqi irin na ainiyin fulani.
Alamu sun nuna MUSLEEMA bazatayi irin wannan tsawan nan me yawa ba. sannan bazatayi qajarta irin me munin nan ba
Sannan baza'a kirata siririya ba. Haka baza'ace mata lukuta ba.
Idan me karatu yana san ya hango yanda jikin MUSLEEMA yake. Toh yayi amfani da jikin wannan jurumar Y'ar film d'in wasan hausan nan wato MARYAM BOOTH...
Abu uku kawai MUSLEEMA zata nunama Maryam booth shine tafita mazaunu HP. Zata fita breast idan taqara girma. Haka kaza lika zata fita diri na jiki na d'aukar hankali idan taqara girma still..
Sannan ita bata da hanci can. Hacinta gajere ne🙂
Sam idan Mazaje masu san mata kyawawa sukaci garo da MUSLEEMA baza su d'auketa ba. Dan ko kusa baza su sata a sawun mata masu kyau ba..
Cewa zasuyi gata baqa gata da gajeran hanci sam bazasu kirata da kyakkyawar mace ba
Amman ga mutumin dayasan ailihin kyau ga y'a mace yana ganin MUSLEEMA zaiyi gudu dan saceta ya b'oyeta inda babu Wanda zaina kallanta bare ya gane masa sirrin dake tare da ita..
Mahaifiyarta tayi wani aure saidai itama bata wani dad'e ba tarasu dan haihuwanta d'aya cikin rashin sani tana jan ruwa a rijiya tana magana santsi ya kwasheta tafad'i Sai jinta akayi acikin rijiyar tafad'a tsumdum. Tayi mutuwar shahada Dan ba'a kaiga I cirota ba tace ga garinku nan...
Iya tashin hankali iyayanta da Yawo sun shiga. Dan Hasiya mutum ce..
Haka iyayenta suka roqi alfarma kan iyayen mijinta subar musu d'an data bari Suleiman..
Dake mijin yayarda haka suma suka yarda...
Shine fa ya kasance Yawo take riqe da MUSLEEMA su Kuma iyayan Hasiya suka riqe da Suleiman..
Wannan shine labarin MUSLEEMA da yanda tazo duniya...
******
Abinda ya faru awashe garin ranar da Y'an iskan nan sukama ADAMS wannan duka suka yadashi Rugar malam Jauro shine..
Ita dai MUSLEEMA bayan tayi sallar asuba makarantar malam jauro ta nufa kamar yanda tasaba. Yana karantar dasu karatun bayan sallar asuba zuwa qarfe takwas na safe..
Qawarta Aisha ce me biyo mata to jiya a gidan kusa dana malam jauro ta kwana gidan yayarta data haihu..
Hakan yasa take tafe ita kad'ai yau..
Taga Adams akwance Sai tsoro ya hanata kulawa dashi..
Dake makarantar tana da d'an nisa da gidansu haka ta dinga tafiya tana waige dan ganin Adams ya tsaya mata arai..
Duk da ba ganin fuskarsa tayi ba.. Amman ya tsaya mata arai matuqa
Har aka tashi daga makarantar hankalin MUSLEEMA nakan ADAMS..
Dama malam jauro na lura da ita Dan haka da'aka tashi saiya kirata yana tambayarta me yake damunta ne yau. Yaga kamar hankalinta baya kan karatu..
Cikin nutsuwa ta gayamai taga wani mutum ne a can kusa da gidansu. Kuma da alama mutuwa yayi..
Murmushi malam jauro yayi Dan tunaninsa ko masu zuwayi masa sata ne sukazo rai yayi halinsa..
Dan haka saiya kira liman da yaransa biyu ciki harda Wanda zai Auri MUSLEEMAN yace suzo akwai wani Wanda ya mace can kusa da gidansu MUSLEEMA..
Aiko cikin sauri suka rangad'o zuwa ganin wanene kuma wannan..
MUSLEEMA tana gaba suna binta a baya har takaisu inda taga ADAMS.
Aiko yana nan kamar yanda ta gansa...
Hankalin me gari da liman yayi matuqar tashi ganin Adams haka. Sun gane mugun duka aka masa Wanda duk Wany'anda suka masa wannan duka sun ilmantu da dukan mutane a inda suke da tabbacin zai zamame mutum illa arayuwa..
Duk wani gu Wanda ido yake tsoran a tab'a mai ajiki Sanda suka tab'amai
Malam jauro yaga sab'anin abinda yake tunani..
Nan take tausayin ADAMS ya kamashi yace maza su kinkimesa su kaishi gida.
Wajen d'aukar nasa ne liman yake tabbatarma da malam jauro karaya bakwai ce a jikin ADAMS.
Malam jauro yaqara jinjina wannan rashin tausayi irin na mutane..
MUSLEEMA ko tunda taga fuskar ADAMS hankalinta ya tashi. Tausayinsa ya cika zuciyarta.. Nan take tafara kuka tana me qarajin tausayinsa aranta.
Daqar malam jauro da liman suka iya shawo kan kukan nata tatafi gida.
Sun tabbatar da lalle yarinyar me tausayi ce..
Da kuka tashiga gidan nasu lokacin Yawo na dama kokon safe..
Aiko da sauri tatashi ta tareta tana tambayarta... "Meya faru dake yanxu kuma da sassafe.
"Wani mutum nagani kusa da gidanmu d'azu zani makaranta. Shine da aka tashi malam dasu Iro da liman suka biyoni na nuna musu shi. Yawo bakiga yanda akamai duka ba. Wasu ne suka jimai ciwo sosai ajikinsa. koma ya mutu ne oho
Shuru Yawo tayi dan tayi tunanin ko masu zuwa yima malam jauro d'in sata ne. Amman dataji batun duka Sai tunaninta ya canja..
"Kinga ba komai zauna kiyi kalacen ki.
"Ni bazan iya cin komai ba. "Toh yanxu me kika san ayi. "Nidai kizo muje gidan malam kiga mutumin kinga saimu dinga zuwa dubasa ko☹
"Ohni Yawo.🤔 zamuje amman Sai munyi kalace..
Jin hakan yasa MUSLEEMA d'auko tabarma ta shinfid'a a tsakar gidan nasu wanda yasa sumunti ta d'auko kokon nasu da kosai suka zauna ita da Yawon suka cika cikinsu..
A al'adar MUSLEEMA idan tawowa daga makaranta bayan taci abinci shara takeyi da wanke wanke saitayi wanka saita zaga wajen ciwansu ta duba lafiyar dabbobin da taga zata iya dubawa. Idan da matsala tazo ta gayama Yawo idan babu matsala haka zata zauna cikinsu tana me kula dasu na lokaci me tsawo. Sallah ce take tadata. Idan tayi takan fitta su had'u da qawarta Aisha suta wasansu da hirace hiracensu..
Toh yau ko sharan da wanke wanken batayi ba tatashi ta azalzalama Yawo wai saidai tatashi suje gidan malam taga wannan mutumin...
Yawo tace bazata ba saitayi mata wanke wanke da shara tukunna
Haka MUSLEEMA tayi tana turo baki. Wai adole ranta ya b'aci...
Tana gamako suka kullo gidan da nufar gidan malam jauro.
Kallo d'aya Yawo tama Adams gabanta yayanke ya fad'i.. Hankalinta kuma ya tashi.. Saboda ganin da tayi yayi mata kama da y'arta Rahma.
Ga irin idansa nan irin na Rahma ne. Irin na MUSLEEMA.
Ga hancinsa mah irin na Rahma Y'arta ne..
A dibibice ta kalli malam jauro tace... "Malam a ina Kaga wannan bawan Allahn..
" aa MUSLEEMA bata gaya miki bane. Ai itace taban labarin yanda tagansa.
"Eh nima taban labarin na dai d'auka ko a kid'ime take ne.
"aa gaskiyar kenan tagaya miki... "Ammako ko suwaye ne suka mishi haka suncika azzalimai.
"Wallahi yanxu ni da liman zancen da muke kenan. Ko daga ina yake. Wayaxo ya yayada shi Allahu ya'alamu.
Amman nasa su Iro suje kewayenmu su bincika ko wani nasu ya b'ace. Dan ga wani cikin rugata yana jin jiki..
"Eh hakan yayi. Allah yasa anan kusa yake..
"Amiin..
Jan numfashi liman yayi da kallan malam jauro yace. "Na gyara mai karayoyin dake jikinsa. Gashi nasaka mishi magani a raunukan nashi. Allah yasa a samu kansa nan da kwana biyu..
Da sauri MUSLEEMA ta katse liman da cewa. "Babba yana da rai koya mutu.
Murmushi duk sukayi yace mata shi yace da ita. "bai mutu ba MUSLEEMA..
Malam jauro yace. "Nasa Suleiman yaje can cikin garin na gwambe ya kira É—ana Usman. Dan naga kamar saiya saka hannu cikin lamarin ciwan nasa..
Gyad'a kai liman yayi da cewa.. "Ya kamata kam. Kan malam jauro yayi wata magana saiga Usman ya shigo da sallah shi da Suleiman d'in..
"Kaga yanxu muke maganarka nake gaya musu na tura Suleiman ya kiraka kaduba mana Wannan bawan Allahn..
"Eh had'uwa mukayi dashi ahanya dan nima nan na nufo dubaku. Sai yake gayamin wai dama guna zaizo dan kana san nazo na duba wani Mara lafiya..
"Ni na manta ma yau qarshen wata Yayi ranar zuwanka. Ka ganshi nan Mara lafiyan matso ka ganshi dakyau..
Duba na tsanaki Dr Usman yakema ADAMS yana jin mamaki cuwukan dake jikinsa..
Can ya kalli malam jauro mahaifin nasa yace. "Wannan fa Sai an kaishi asibiti dan maganin gida bazai gamsheshi cikin sauri ba.
Dan haka ya zama lalle yau na kuma saimu tafi tare daku dan kuji binciken da za'ayi akansa.
Liman yace.. "Wannan ai ba damuwa. Jeka duba umman taka ka fito muje.
Tashi Dr Usman yayi yashiga can cikin gidan malam inda mahaifiyarsa take. Anan take bashi labarin yanda aka damu Adams. Usman ya tausayama Adams sosai. Hakan yasa zuciyarsa takasa nutsuwa.. Dan haka sai kawai yay ma Mahaifiyar tashi sallama ya fito. Daidai lokacin da liman ya fito daga gidansa dan gayama iyalinsa. Haka suka saka Adams a motar Usman d'in. Liman da malam jauro suma suka shiga motar MUSLEEMA tace zata bisu. Daqer suka lallasheta kana Usman ya jasu basu zame ako ina sai'a ba sai'a cikin garin gwambe cikin asibitin DOCTOR AHMAD...
Anan aka shiga duba lafiyar Adams lungu da sak'o.
Bancike ya nuna TUNANIN ADAMS YA D'AUKE.. Bashi ba tuna wani abu daya faru dashi arayuwa. Sai in yaqa wani nasa ko an ambaci wani abun daya sani wannan ne kawai zai iya sawa asan shi asan daga inda ya fito..
Kasancewar daga cikin garin gwambe zuwa rugar malam jauro akai tafiya me d'an nisa. Sai kawai liman da malam jauro suka tare a gidan Usman danshi ya buqaci dasu zauna kasancewar ana saka ran marfad'owar ADAMS d'in nan da kwana biyu..
Dan yana jiye musu wahalar da zasu sha wajen dawowa idan suka koma gida
Hakan yasa suka yarda.
Anan ko Ruga MUSLEEMA tana cikin wani hali. Dan tunanin Adams ya damu Zuciyarta. Haka kawai taji tana sanshi tana qaunarsa tana tausayinsa.
Yawo na lura da ita. kallanta kawai takeyi dan itama Adams d'in ya bala'in shiga ranta..
Gani take kamar shi d'in jininta ne..
Kwanan Adams hud'u a asibitin ya farfad'o. Saidai kamar yanda binken ya nuna ya manta komai na rayuwa akansa. Hakance ta kasance..
Malam jauro ko sai tambayarsa sunansa yake. Ido kawai Adams yake binsa dashi.
Usman yayi murmushi yace.. "Angayama Baffa tuninsa ya d'auke yanxu ba abinda zai qara tunawa arayuwarsa sai in yaga wani nasa kutunna.
Kwana d'aya su malam jauro suka qara sukace ma Usman zasu koma Ruga dan Allah ya kula da ADAMS kamar jininsa zasu dinga zuwa duk qarshen sati suna dubasa.
Nan yabasu tabbacin zai kula dashi kamar yanda zai kula da kansa..
Dasu malam jauro suka dawo gida Yawo da MUSLEEMA sunzo sun tambayesu ya jikinsa..
Nan liman yake gayama Yawo ga matsalar da shi Adams ya fuskanta na d'aukewar tunani..
Da tausayawa Yaro tace Allah ya dawo mai da tunanin nasa nan kusa.
Saiya kasance kullum Idan MUSLEEMA tazo karatun asuba gun Malam jauro saita tambayesa jikin ADAMS
Tun yanace mata jiki da sauqi harya gaji da amsa mata..
Dayaga tafara zuwa da ranah da yamma tana tambayarsa
Saiya fara d'aukarta duk sanda zasu duba Adams d'in shida Liman.
Hakan ne yasa hankalin Musleema kwanciya. Dan tana ganin Adams d'in yana samun sauqi sosai.
Yau malam jauro ya shirya shida liman suka nufi cikin garin na gwambe lokacin watannin ADAMS bakwai Usman na lura da lafiyarsa su kuma suna masu zuwa dubasa.. Adams ya samu sauqi sosai..
Ba abinda yafima Malam jauro dad'i da kulawar da Usman yabama Adams d'in sai ganin yanda ADAMS din yake amfani da ilimin addinin da Usman d'in ya bashi.
Sallarsa anitse. Komai nasa dakeyi a nitse yakeyi.
ADAMS yafi gane yaran Hausa dan shi Usman yafi masa ba fullanci ba.
Dake dama rugar malam jauro had'akata ce. Ana jin Hausa ana jin fillanci. Hakan yasa su malam jauro jin dad'in yanda ADAMS din yaji hausa.
Usman yace da mahaifinsa malam jauro yasama ADAMS suna Ahmad kasancewar basu san sunansa ba. Sunji dad'in sunan dan haka suma sukace da sunan zasu dinga kiransa.
Haka suka dawo da ADAMS cikin Rugar malam jauro suna masu yimai addu'a akan Allah ya dawo mai da tunaninsa Susan daga inda ya fito..
Saidai da suka dawo MUSLEEMA taje tasama malam jauro daru kan saiya bata Yayanta Ahmad ya koma gidansu..
Murmushi yayi da kallanta yace idan naba Yawo shi a'ina zata sashi.
Tace ai akwai d'akuna agidansu tashare ko'ina duk inda ya zab'a anan zai zauna..
Da farko malam jauro yaso qin yarda Amma dataje tasa Yawo agaba da kuka dole Yawo tazo ta ruqi malam jauro yayarda Adams ya koma gidansu MUSLEEMAT
Abin yama MUSLEEMA dad'i.. Dama shima Adams baya san nesa da MUSLEEMA.
Saboda tun lokacin dasu malam jauro suke zuwa da ita dubasa ya lura da qaunar da take masa.
Hakan ne yasa yafi sakewa da ita fiye dasu su malam jauro d'in..
Saboda yanda take da dad'in hira Gashi Yana tsintar kansa cikin nisha'i idan Yana tare da itan..
Sosai itama Yawo taji dad'in yanda ADAMS ya dawo gidan nasu..
Yana zuwa gun malam jauro d'aukar karatu da safe da yamma idan ya dawo kuma ya shiga daji cikin awaki yana dubasu.
Tunda ya fara kula da dabbobin nasu Sai Yawo taga kamar yafi kowa iya kiwo
Dama ya hutashar da MUSLEEMA dan yanxu bata zuwa ciwan..
Dan Idan kaganta a wajen ciwan to taje hira da yayan nata Adams ne wato Ahmad kamar yanda suke kiransa dashi....
Sha kuk'uwa me tsanani tashiga tsakanin MUSLEEMA da ADAMS
********
Malam jauro ne da liman amininsa da Yawo da d'ansa Iro da MUSLEEMA suke zaune kan tabarma a kofar gidan malam jauron..
Malam jauro yace.. "Dama abinda yasa na taraku magana nake san nayi daku akan alqawarin Auran dake kan MUSLEEMA da d'ana Iro ganin da