Showing 18001 words to 21000 words out of 81675 words
Lokacin tana kan sallaya dan takasa bacci kwata kwata. Hakan ne yasa ta yanke shawarar d'auro alwala tafara bada lafula tana rok'ar Allah. Sanda taji idanta na rufewa kana tabi gado ta kwanta.
Ko baccin awa biyu batayi ba taji ana kiran sallar asuba. Nanko ta duro da qara d'auro alwala tagabatar da sallar raka'atailinfijir kana tayi sallar asuba tana cikin lazimi bacci me qarfi yayi awan gaba da ita☹
Ba ita ta farka ba sai kusan goma da rabi... Aiko da sauri tatashi hankalinta ad'an tashe tana tuna abinda momynta ta gaya mata akan ta daure zuciyarta ta had'a musu breakfast qarfe takwas. Aiko cikin sauri sauri gudu gudu tahau had'a musu me sauqi. tia da soyayyan dankali da kwai had'i da fafesun kazar da auntynta Zainab tayi mata jiya tasa cikin furish dama dan tabasu tayi mata...
Sanda tayi wanka tasaka wasu fitunannun kaya riga da siket ne na atamfa d'inkin ya karb'e irin sosai d'innan. da feshe jikinta da turaranta sannan taje taleqa ta window taga Sam ADAMS bai fitta ba. Amman kamar ana kwankwasa mata kofa d'azu. Tayi ma tunanin ko shine ya fitta. Tab'e baki tayi da sake labulanta tana rayawa aranta qilama su Asiya ne
Haka ta nufi baban falo falan dazai sadata da shashin TAUDHAT haka dana Adams d'in to anan tajera komai na abinda tayi musu kan dining.. Sannan tayi shashin Adams d'in.. Bata ganshi ba. Sai taji gabanta ya fad'i tatsaya tana tunanin taje d'akin amaryar ne kota koma shashinta...
Abinda da yafaru ko da Adams da TAUDHAT shine.. Bayan yata sheta sallar asuba sai shi yayi masallaci. Bai dawo ba sai kusan qarfe bakwai da rabi kamar yanda ya saba dawowa.
Anan ya dinga buga kofar NUFAISAT da kiran wayarta amman shuru
Yana cikin hakan ne kiran wayar Yusuf ya shigo mai waya akan dan Allah yazo asibitinsa yanzu zaikai Hajjiyansu can ciwan zuciyarta ne da alama ya tashi dan gashi tana dafe da zuciyar wai tana mata zafi kuma tana numfashi sama sama.
Da sauri Adams yace toh ya kaita gashi nan zuwa.
Aiko da sauri ya koma shashinsa ya shirya ya ficce shida masu tsaransa basu dire ako ina ba sai'a asibitin nasu. Anan yaga harsu Yusuf d'in sunzo
Da sauri ya shiga nubata. Aiko ya samu nasarar gane me yasa hakan tafaru da ita. Wai damuwace..
Yusuf Yace "narasa me yake damun Hajjiya wallahi
Murmushi ADAMS yayi da cemai. "Yaci ace Yanxu ka gane miye matsalarta. Zata samu kanta nan da awa biyar. pls ka temakemu kagano damuwarta dan Allah.
Toh Yusuf yace mai.
Anan suka bar qanin babansu Yusuf da matarsa dan Yusuf d'in yace yunwa yakeji Adams yace toh yazo su koma gida susamu abinda zasuci.
Lokacin da suka dawo gidan ne NUFAISAT ta shiga wanga Lokacin sha d'aya saura. Shine sukayi shashin TAUDHAT inda tayi farin ciki da hakan amman bata nuna musu ba tace musu bara ta shiga ciki ta had'a musu abinda ya dace.
Anan Yusuf yake mata tsiya wai amarya da aiki anya basu takurata ba
Murmushi kawai tayi mai da nufar kitchen d'in nata
Adams yace wallahi na zak'u naga NUFAISAT. Kagafa har Yanxu banji motsinta ba kusan 11. Yusuf Yace "mu bata minti goma idan bamu jita ba sai'a b'alla kofar muga ko lafiya. "Aiko haka za'ayi. Adams ya bashi amsa da fad'in hakan cikin damuwa.. Wannan shine abinda ya faru
Har NUFAISAT ta nufi yin shashinta sai kuma ta kalli agogwan falan Adams d'in taga sha d'aya daidai. Dan haka sai kawai tayi qarfin halin murd'a kofar dazata sadata da falan amaryar tana meyin sallama
Aiko karab ta had'a ido da Adams da Yusuf
Murmushi ta sakar musu da qarasa shigowa falan tana me cewa.. "Amin afuwa tunda nake arayuwata ban tab'a makara irin nayau ba.
Tsaki Adams yaja da kallan Yusuf Yace.. "Kasan Allah na manta da wannan kofar da zata sadani da ita.
Yusuf yayi murmushi da cewa. "Nima nayi mamaki sosai danaga ta b'ullo tanan
NUFAISAT tazauna kusa da Adams tace kaddai kanata bulayin buga min waccar kofar.
"Yanxu ma muka yanke shawarar zuwa mu b'alle ƙofar taki muga ko kina cikin k'oshin lafiya..
"Ina lafiya lau. Yanxu dai bara na gaisa da amarya sai muje babban falo danna had'a muku komai na breakfast
Murmushi yayi da shafa gefan fuskarta yace. "Nayi missing d'inki matata. Dana jiki shuru wallahi duk bana cikin nutsuwata. "Yanxu dai ina kadawo normal
Kiss ya sakar mata a kumatu da fad'in. "Sosai mah.. Bara na kira miki amaryar dan tashiga kitchen ne had'a mana abinda zamuci.
"Toh na hutashat da ita dannayi komai.
Murmushi ya sakar mata da kwala ma TAUDHAT kira da AMARYA...
Da sauri TAUDHAT tafito daga kitchen tana niyar amsawa. Amman ganin NUFAISAT kusa da Adams saita tsaya cak tana me yarfe hannu da alamata wanke hannun tayi..
Da sauri NUFAISAT tatashi ta nufi TAUDHAT da mamaki take ce mata. "Har sab'anin da muka samu yakai kishigo cikin gidan nan kikasa fara shigowa shashina saina abokiyar zamana har kina tayata aiki.
Sosa qeya TAUDHAT tayi cikin wani hali dan taji wani iri tace da ita. "Aina d'auka ya gaya miki jiya cewar nice Amaryar taki.....
Cikin furgita NUFAISAT tace.. "What😳. Da zaro ido... Ta juya da kallanta ga Adams sannan tadawo da kallanta gareta tacigaba da cewa... Me kike cewa. Kina nufin kicemin kece wacce ADAMS ya Aura matsayin matarsa ta biyu✌🏼..
D'aga mata kai TAUDHAT tayi da cewa.. "Eh ni ce ya Aura. Saboda yasan zakiyi farin ciki sosai da hakan....
"Farin ciki. Wane irin farin ciki. Kefa TAUDHAT ce. Aminiyata wacce na d'aukeki amatsayin y'ar uwata. Yau kece agabana kina gayamin wai mijina keya Aura saboda yasan zanyi farin ciki da hakan.
Haba TAUDHAT wannan wata irin amsa kike bani. Daga tambayarki saiki jefeni da muguwar kalma irin wannan. Tayaya kike tunanin ADAMS zai iya rainon zuciyarmu nida ke..
Dafa Y'ar uwa kike kirana. Aminiya qawa. Amma jiya ki rasa wanda zaki Aura sai mijina..
Shuru TAUDHAT tama NUFAISAT tana me kallan qasa. Ganin hakan yasa NUFAISAT tafe kanta dayake barazanar tarwatsewa ta kalli Yusuf arikice tana me cemai!!! Kana ganin abinda yake faruwa tsakanina da TAUDHAT Yusuf.. Waifa fad'amin take wai mijina ADAMS ta aura..
Ka tuna natashi da ita tun yarinta. Na rayu da ita har gidan aurena. Wai yau itace take amatsayin kishiyata YUSUF
Shuru Yusuf yayi cikin matuqar tashin hankali danshi wallahi sai yanzu ya gane kuskuran da suka tabka..
Sam alkairin Auran ya hango wallahi ko kad'an bai kawo cewa hakan zata faru ba. Sam ya manta kishi irin na mata..
Adams ya tashi cikin tashin hankali idansa akan NUFAISAT yace.. "Wai me yake shirin faruwa ne. Nayi hakan dan naga farin cikinki amman yanaga sab'anin hakan.
Cikin zubda hawaye NUFAISAT ta kallesa da wani b'acin ran da tunda yake da ita bai tab'a ganinta cikinsa ba tace dashi... "Dalla rufema mutane baki munafuki azzalimi wanda ya manta abinda ya dace ya duba wanda bai dace ba karasa wacce... Ai bata qarasa futucinta ba!!! ya wani d'auketa da marin daya daqarqare iya qarfinsa da shi. Dan kalmar munafuki azzalimin data ambatasa dasu ta shigesa sosai..
Da gaske sanda NUFAISAT taga wasu taurari suna mata yawo afuskar. Dan bata tab'a cin karo da wannan azafaffen marin ba.
Hakan yasata dafe wajen da sauri ta tsaya dan dawowa hayyacinta na sakwanni. Kana kuma tafara ja da baya da baya tana kallansu d'aya bayan d'aya cikin matuqar razana da sanyin murya tace. "Na shiga uku ni NUFAISAT.. Qarshen rayuwata tazo.... Tana fad'in hakan ta fad'i sumammiya..
Da sauri dukkansu su ukun sukayo kanta. TAUDHAT fad'i take.. "Na shiga ni TAUDHAT. Dan Allah NUFAISAT ki tashi kiraya zuciyar dake qaunarki. Idan ba ADAMS bazan iya rayuwa ba. Zuciyarsa na tare dake. Idan kika mutu binki zaiyi. Wallahi a daran jiya yaqara jefamin qaunarsa a zuciyata kuma ina da tabbacin idan nayi k'ok'arin bar miki shi saina fara haukacewa kafin nabar duniya..
Ba qaramin tashin hankali ADAMS ya shiga ba. Haka ma Yusuf dan ko kad'an ba motsi ajikin NUFAISAT..
By Rahma Nalele Aunty luv... Ina yinku y'an hannuna🙌🏻
[6/23, 3:14 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 12☆
Da sauri ya d'auki wani ruwa dake cikin gora a gefansa ya fara yayyafa mata... Fad'i yake. "Ki tashi NUFAISAT dan Allah ki tashi. Nayi kuskure na kuma yarda da duk abinda zaki cemin.
Sam NUFAISAT bata da alamar motsawa. Ganin hakan yasa ya kinkimeta bai direta ako ina ba sai cikin motarsa. Haka Yusuf da TAUDHAT suka shiga motar ko sauraran masu tsaran baiyi ba ya fige motar ahargitse yabar gidan. Aiko masu taransa da sauri sukabi bayansa.
Kaf y'an asibitin basu tab'a ganin rikicewar ADAMSY ba sai yau. Dr Aryan ne yashiga duba NUFAISAT dan ko kad'an Adams baiyi tunanin dubata da kansa ba.
Dan duk hankalinsa a tashe yake. gani yake kamar ta mutu. Dan hakan bai tab'a faruwa da ita ba...
To idan tamutu yayi yaya da rayuwarsa. "Kai ina NUFAISAT ba zata mutu ba. Ya fad'i hakan a bayyane cikin tashin hankali
Da sanyin jiki Yusuf ya kama hannunsa da zaunar dashi yana me masa magana cikin sanyi da lallashi.. "Kanutsu ADAMS. Insha Allah NUFAISAT zata tashi kamar komai bai faru ba. Kuskure ne dai munyi shi arashin sani. Gyarashi kuma kaine da alhaqin hakan..
Shuru Adams yama Yusuf kawai
"ADAMSY ka kwantar da hankalinka. Gata can nasamu kanta ta farfad'o... Ai dajin hakan dukkansu sukayi d'akin da take batare da sun tsaya sunji qarashan abinda Dr Aryan zaice musu ba.
Tana kwance akan qaramin gadan na d'akin. Hawaye ne yake zuba mata dan tuno da abinda ya faru da tayi.
Tana ganin shigowarsu tawani rumtse idanta.
Ganin hakan yasa ADAMS zuwa ya durqusa a gabanta da kama hannunta yace.. "Nayi kuskure matata. Nayi miki lefi my luv. Saidai bazan qara aikata miki hakan ba.
Bud'e idanta tayi da saukewa akansa tace.. "Ka rigada kayimin komai ADAMS. Ka b'ata tunani na tuntuni da qaunarka. Ba yanda zanyi in cire hakan daga zuciyata. Yanzu kazo ka Auri qawata aminiyata wacce tasanni ciki da bai. Hakan bai isheka ba kabini da abinda ban tab'a tunani ba. Marina fa kayi ADAMS. Marin daban tab'a jin irinsa ba arayuwata. Wallahi saika sakeki dan bazan iya zaman kishi da TAUDHAT ba. Saboda ina MASIFAR SANKA DA KISHINKA. Inda ace wata ce ba TAUDHAT ba na tabbatar bazanji ciwo azuciyata kamar haka ba...
Dafe kansa Adams yayi da hannu d'aya. Yayinda d'ayan yake riqe da hannayenta. Idansa ne ya kad'a yayi jajar saboda b'acin rai. Bai tab'a tunanin akwai ranar da NUFAISAT zatace mai wallahi saiya saketa ba.
A hankali ya maida kallansa gareta yana mece mata. "Wallahi NUFAISAT saidai ki mutu da Aurena akanki. Dan kalmar saki bata cikin agenda ta!
Har abada nidake zamu rayu rayuwar da bata qarewa. Dan har agidan aljanna ina rokwan Allah dayasa ki zama matata..
Na aikata miki hakan da zuciyar d'aya ne NUFAISAT..
Wallahi ban iya yi miki qarya. Na rantse miki da Allah na Auri TAUDHAT ne dan kawai na faranta ranki. Ganin danayi kinfi kowa saninta. Kinfi kowa amincewa da ita. Kinfi kowa jin dad'in zama da ita. Shiyasa na aureta dan aganina zakifi kowa farin ciki da hakan..
"Kadena danganta wannan had'in naka da matsayin zan samu farin ciki acikinsa. ADAMS akwai abubuwa da dama da ban sani ba agame da TAUDHAT. Wallahi Zuciyata zafi take min tana tafasa da k'una idan natuna TAUDHAT itace kishiyata.
Bazan iya da TAUDHAT ba Adams. TAUDHAT tafi qarfina. Ina da tabbacin alkairin da kake hangowa agareta kuma agareni bazaka tab'a samunsa ba.
Danta b'ata tunanina lokacin dana san wasu abubuwa akanta..
Dan Allah mijina ka sawwaqe min dan ayanxu nafi buqatar qaunarka ta kasheni agidanmu dana zauna zaman kishi da TAUDHAT....
Miqewa ADAMS yayi da sakin hannunta. Yace "bazan sakeki ba NUFAISAT.
kuma idan har ayanzu ma ina amsa sunana na mijinki' ina umartarki daki tashi namai dake gidana yanzu yanzu. Wannan shine qarshen maganata dake anan. Ya qarashe furucin da miqa mata d'ankwalinta..
Kuka NUFAISAT tafashe dashi wiwi tana cewa. "Wayyo Allah kakawomin d'auki cikin wannan matsalar data kusantoni. Allah Kaine kace nayima mijina biyayya akan komai banda sab'anka. Narok'eka Allah daka sanyayamin Zuciyata na iya bin duk abinda yacemin acikin wannan halin da nake ciki dan bana San na sab'a maka.
Tana gama fad'in hakan tatashi da karb'ar d'ankalin nata tayafa akanta gami da tashi tana me tafiya cikin yali yali. Ganin hakan yasa TAUDHAT nufanta amunafunce danta riqeta alamar temako.... Aiko azafafe NUFAISAT ta wurga mata wani mugun kallo daja da baya tace. "Karki kuskura ki tab'ani...
Jan numfashi Yusuf yayi da bugan kafad'an Adams da yake kallansu. Aiko cikin sauri Adams ya gane me Yusuf yake nufi
Dan haka saurin matsawa ga NUFAISAT yayi cikin kulawa ya tarota jikinsa. Zata mishi masifa saidai suna had'a ido tafasa. A haka ya kaita har motar tashi gidan gaba. TAUDHAT tashiga baya. Shi kuma ya zauna wajen mazaunin direba. yana niyar tada motar ne d'aya daga cikin masu tsaransa yace.. "Oga daka bari nakaisu gidan. D'aga mishi hannu Adams yayi alamar aa. Sannan yaja motar yana gayama Yusuf ya jirasa yanxu.
Girgiza kai Yusuf yayi cikin damuwa dan har ga Allah baiji dad'in abin daya faru ba. Ji yake kamar basu kyautama NUFAISAT ba. Haka yana ji kamar abin da sukayi shine ya dace. Tunanin dayafi tsaya mai arai dai shine basu kyauta ma NUFAISAT ba kawai.. Haka yayi shashin da suka Kwantar da Hajjiya kakarsu. Anan yaga Nazifa qanwarsa taxo da abinci. Dan haka yaci kad'an bawai dan har alokacin yana tare da yunwar tasa ba. Kawai dai yaci ne dan karta mishi illah...
Su Adams ko babu me magana acikinsu. Ahaka suka iso gida yace duk susamesa a babban falan nasu...
Qarfin hali kawai NUFAISAT tayi taje falan bayan tawanke fuskarta a part d'inta
Adams sasu yayi a tsakiya ya kalli NUFAISAT data d'aure yace da ita... "Ki tausasa zuciyarki matata. Dan bazan iya rayuwa babuke ba. Ina San kiyi hakuri na d'auki lefina na Auran TAUDHAT da nayi. Na kuma yarda nayi miki lefi. Dan Allah ki yafemin ki zauna da lafiya a d'akinki dan samun farin cikina. Sannan kiriqe girmanki ki saki ranki ki rungumi y'ar uwarki Ku zauna lafiya dan kinfi kowa sanin bana san fitina da tashin hankali
Shuru NUFAISAT tamai bata da alamar cewa komai. Ganin hakan yasa ya maida hankalinsa gun TAUDHAT yaci gaba da cewa.. TAUDHAT na aureki ne dan samun d'orewar farin cikin matata. Saidai kinga yanda al'amuran suka sauya. Ina San matata ina San rayuwa da ita. Dan Allah ki zauna da ita lafiya ki riketa kamar yanda kuke da. Dan nasan zata dawo tayi miki kallan dada take miki danna samu sukuni acikin gidana... Kima NUFAISAT biyayya TAUDHAT ki bita idan kina San samun farin cikina agidan nan
Jan numfashi TAUDHAT tayi ranta yayi masifar b'aci. fad'i take aranta Wallahi saita gyarama NUFAISAT zama acikin gidan. Dan bazata d'auki rainin hankali agabanta mijinta ya dinga nuna mata yafi San uwargidansa akanta ba... Tsaida tunanin nata tayi da kallansa ta sakar mai murmushi da cewa. "Ba komai mijinmu insha Allah zanyi abinda kace min.
Da sauri NUFAISAT takalleta ranta cike da tsanarta taja mugun tsaki da cewa. "Nidai bazan shiga harkarta ba. Amma katabbatar idan tashigo harkata zan yaga mata rashin mutuncin da bata tab'a ji da ganinsa ba Wallahi.
Kallanta Adams yayi da mamaki dan shi ko'a mafarki idan akacemai NUFAISAT zata nuna tsana ga TAUDHAT haka wallahi bazai yarda ba. Bare a zahiri. Girgiza kai yayi dace mata. "Watoh bakiji abinda na gaya miki ba kenan. Zaman gaba zakiyi da ita kenan...
Sanda ta gallamai harara kana tace "Allah ya bamu zaman lafiya... Tana fad'in hakan tatashi da saurin shigewa part d'inta
Da kallo ya bita kawai. Ganin hakan yasa TAUDHAT tashi itama tabar mishi falan tana kisa abubu aranta.
"Mata mata saidai abarku. Ya fad'i hakan abayyane tare da tashi ya koma dining ya fara cin breakfast d'in da NUFAISAT d'in tayi musu d'azu dan suci. Sanda ya gama yaje ya ibi jinin TAUDHAT kamar yanda sukayi shida ita a daran nasu na jiya sannan ya ficce daga gidan zuwa offishinsa.
Yusuf bai tafi ba. dan nan ya tarar dashi yako bashi labarin yanda yayi dasu. Yusuf ya kallesa yace. "Gaskiya Adams sai yanzu naga rashin dacewar Auranka da TAUDHAT.
Murmushi ADAMS yayi da gyara zamansa kan kujerar offishin nasa yace da Yusuf d'in.. "Koma dai miye yanxu ya wucce Yusuf kawai fuskantar gaba zamuyi. Nidai bazan iya rayuwa babu NUFAISAT ba. Haka kuma bazan iya sakin TAUDHAT ba saboda wani dalili nawa.
Dan haka Dan Allah ka tayani da addu'a kan Allah ya shiga tsakaninsu ya daidai tamin kansu.
Jan numfashi Yusuf yayi dace mai toh kawai...
Kakar Yusuf tasamu sauqi tashin datayi. Danji tayi kamar tafi kowa lafiya aduniya. Dama hakan Adams yake fata. Nan Yusuf yasata agaba kan tagayamai me yake sata shiga damuwa haka. Murmushi tamai da cewa Aurenka nake San gani Yusuf.
Jin hakan yasa Yusuf dariya dace mata zanyi kwanan nan. Adams shima dariyar yayi da basu sallama
Kana yabi takan bincikensa akan jinin TAUDHAT... Aiko baida matsalar komai. Ma'ana baya tare da cuta...
NUFAISAT ko shigewarta part d'inta fad'awa tayi kan gado cikin kuka takira momynta tazayyane mata komai akan ba wata bace kishiyarta Ashe TAUDHAT aminiyarta ce😭
Mommy tayi mamaki sosai dajin hakan.
Dan haka tace mata taxo gobe gida zata bata shawara akan yanda zata zauna da TAUDHAT d'in
Sosaifa mamakin Mommyn d'in NUFAISAT ya qaru bayan sun ajiye waya ita da NUFAISAT d'in
Dan ita sai yanzu tatuna