Showing 72001 words to 75000 words out of 81675 words

Chapter 25 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

hakan gasu Khalit..
Murmushi ya sakarma YAWO yace.. "Unguwa zasu rakamu.
Itama YAWON murmushin ta mayarmai da cewa... "Toh kudawo lafiya...


Har sun shiga mota saiga Haneepha tafito da sauri daga part d'insu tana cewa.. "Dady ina zaku nima zan biku..
Murmushi yayi mata dayima masu tsaransa nuni dasu bud'e mata motar itama ta shiga.
Aiko tana shiga Adams yaja motar dan yacema masu tsaran nasa subari basai sunyimai rakiya ba yanxu zai dawo..

Tun ahanya ko yakira abokinsa doctor Aryan yabashi tak'aitaccen labarin dacigaba da cemai pls su had'u yanxu a asibiti ya gwada mai jininsa dana yaran....
Jan numfashi doctor Aryan yayi da cemai ai yanama asibitin tun d'azu sakamakwan matarsa tatashi da naquda tun da safe. Dan haka ya qaraso kawai zai samesa..

Bayan sunkai Nan Doctor Aryan ya ibi jininsu Khalit da Khalil da Rahma dana ADAMS yahau binkice.
Masha Allah bincike ya nuna Khalit Khalil Rahma ƴaƴan ADAMS ne..😀
Nan ADAMS yaja numfashi da rungumarsu kamar zai cinyesu haka yadinga sakar masu kiss..
Cikin tausayawa NUFAISAT ta goge hawaye. Doctor Aryan ko murmushi yayi da bama ADAMS hannu yace.. "Na tayaka murna d'an uwa. Dan samun uku a lokaci d'aya ba qaramin abu bane....
Kan ADAMS ya bashi amsa saijin kukan Haneepha kawai sukayi. Tana cewa itama ayi mata abunda akayima su Khalit dan Dadynta yayi mata kiss ya rungumeta itama..😟
Dariya sukayi dukkansu da rarrashinta kan bakomai aka musu ba tayi hak'uri basai anyi mata ba.

Saidai fur Haneepha taqi yarda saima qara volume na kukan nata da tayi..😳

Sam ADAMS baya san kukan Haneepha Dan haka sai kawai ya biye mata yace doctor Aryan ya ibi nata jinin ya gwada da nasan.

Aiko Cikin rikicewa NUFAISAT ta goge gumin daya wanke mata fuskar tace... "Haba my luv kabarta basai ammata ba.
Ai Haneepha najin hakan taqara tab'arb'arewa da kukan...
NUFAISAT taja numfashi haka kawai taji gabanta na fad'uwa. Saboda tasan idan doctor Aryan yagwada jinin Haneepha dana ADAMS gaskiya akwai matsala.. 😒

Murmushi ADAMS yayi dace mata.. Karki damu my luv. bari yayi mata kinsan Haneepha da rikice idan ba'a mata ba har dare kuka zatata mana yau..

Gyad'a masa kai NUFAISAT tayi dacigaba da goge gumi..

Haka tana ji tana gani doctor Aryan ya ibi jinin Haneepha ba abin ta hanasa ba..

Shi kansa doctor Aryan ya girgiza da ganin sakamakwan da binciken ya nuna masa na Haneepha ba jinin ADAMS bace😊..

Dan haka Sanda yayi gwajin sau uku yaga duk abu d'aya sakamakwan yake basa. Sannan ya hak'ura da fitowa daga wajen gwajin jikinsa a sanyaye ya miqama Adams takaddar gwajin nasa da Haneephan..

Tunda Adams ya fahimci Haneepha ba y'arsa bace ya zuba Haneephan ido zuciyarsa na bugawa.

Canko sai ganinsa a qasa sukayi.. NUFAISAT da doctor Aryan sukayi kansa suna masu kiran sunansa..
Bashi da damar amsawa dan yarigada ya sume..



Minti goma tsakani Adams ya farfad'o da kallan NUFAISAT yace... "Wannan ma kina da sani akai..
Saurin girgiza masa kai tayi alamar aa hawaye na zubo mata tace.... "Banda da sani akan wannan sam
Shima hawayen ne yazubo masa yace.. Nagodema Allah daya saka mukazo da Haneepha har hakan tafaru..

NUFAISAT taudhat tacuceni.. Ta ha'inceni.. Duk halaccin danayi mata sanda ta munafunceni. Ashe abinda tagayamin ranar farkon amarcina da ita qarya ne..
Allah Kasan nakamu dasan wannan yarinya Haneepha Allah ka sassautamin.
"Amiin.. NUFAISAT da doctor Aryan suka ce.

Ahankali ya tashi da saukowa daga gadan da doctor Aryan yasashi sannan ya karb'i makullin motarsa gun NUFAISAT yace su tashi suje gida..
Haneepha ta kalli ADAMS tace.. "Dady baka rungumeni kayimin kiss d'in ba..
Rintse idansa Adams yayi cikin wani hali ya rungumeta dayi mata kiss d'in..
Doctor Aryan ya dafa kafad'arsa yace.. "Kayi aiki da hankali abokina. Tunda kaga lokacin dakasan hakan akan Haneepha lokacin ne kake da arziqin su Khalit harsu uku..
Dan haka pls kanutsu sosai wajen yanke hukunci...
Murmushi kawai Adams yayima masa da ficcewa daga d'akin yana cema NUFAISAT susamesa a mota..
Haka da damuwa NUFAISAT sukabi bayansa..


Tuqi kawai Adams yake amma hankalinsa ya tafi kan tunanin wane hukunci ya dace yayima TAUDHAT..

Ahaka suka iso gidan jiki a sanyaye..
Direct part d'insa Adams yayi ya d'auki takadda da biro ya rubutama TAUDHAT saki har uku..


Itako tana zaune a falan nata zuciyarta cike da mamakin ina Adams ya d'auki NUFAISAT sukaje.. Saiji kawai tayi wayarta na ringing.. Bak'uwar number ce. Dan haka saita d'auka a yatsine..

"TAUDHAT nice me magana..
"Wake nan.
"Hajjiya Rukayyat kishiyar sirukarki.
"Ayya. Sannu Hajjiya. Dafatan dai Alkairi ne yasa kika kirani..
"Ai tunda kikaga ban tab'a kiranki ba. Yadace kigane wannan kiran ba alkairi bane agareki
"Ko.
"Kwarar
"To ina jinki..
Murmushi Hajjiya Rukayyat tayi da qara bajewa kan kujerar falanta tace.. "Dama na gaya miki saina baqanta rayuwarki kan abinda kika min ko. Toh yau ranar tazo dan ba abinda zai katangeki ga haukacewa yanxu...
Murmushi TAUDHAT tayi da faɗin.. "Lalle kanki ya kulle. Dan ina tabbatar miki har qarshen rayuwata bazan tab'a yin hauka ba.
"TAUDHAT kenan. Zaki gani yanzu a kwaryarki. Danni Hajjiya Rukayyat ban tab'a d'aukar alqawari naqi cikawa ba. Dan haka kibaza ido yanxu d'an zukuluzu zai baiyana agareki.. Hajjiya Rukayyat na fad'in hakan ta kashe wayarta da sheqewa da dariya..

Sororo TAUDHAT tayi da wayarta a hannunta. Kuma daidai lokacin ADAMS ya shigo falan nata..
Ahankali ya miqa mata takaddar hannunsa me d'auke da sakin dayayi mata. Tako karb'a cikin sauri da wareta dan taga me ta kunsa..

Agigice tatashi da kallansa tace... "Wai ni TAUDHAT kasaka ADAMS.😳
Murmushi yayi mata da cewa.. "Eh. Na sake ki saki uku TAUDHAT. Sannan ki tattara kayanki a yanxu ki barmin gidana. Sannan nasan kinsan muslinci yaban Haneepha ko..
Dan haka ke d'aya zaki fitta batare da ita ba..

Cikin matuƙar gigicewa tace "Kan uba. Kutumar uba. Durin uwa.😊 NUFAISAT ce ta gaya maka Haneepha ba y'arka bace ko..
Lalle tunda tayi sanadin datse igiyar aurena tsakanina dakai Wallahi sainayi mata abinda har tamutu bazata tab'a mantawa dani ba...

ɗauketa da wani matsiyacin mari ADAMS yayi..
Kanfin tadawo daga hayyacinta ya qara bata wani..
Nan take ta kwalla wata muguwar qara sakamakwan ganin wani jibgegen aljani da tayi a gefanta yana zaro mata ido kamar zai cinyeta. Sannan ya watsa mata wani abu kamar qasa ajikinta. Ai nan take taji kamar an zuba mata wuta.
Wannan shine yasata kwalla qara ba marin da Adams yayi mata ba..

Nan tafara cire d'an kwaninta tare da fara cizge gashin kanta tana cewa shikenan na haukace.
Zuba mata ido ADAMS yayi ganin kamar da gaske abinda take fad'a na shirin faruwa da ita..
Daidai nan NUFAISAT tashigo falan saboda ihun da TAUDHAT d'in tayi..
Ai NUFAISAT naganin abinda takeyi cikin rashin fahimta tace... "TAUDHAT kidena cizgar gashinki mana. Kokinyi hauka ne..
Kallan NUFAISAT d'in tayi idanta ya juye ya zama ja tace. "Nayi hauka NUFAISAT.. Na haukace. ADAMS ya sakeni bayan baqar wahalar dana sha wajen bin malamai da bokaye akansa... Sannan Hajjiya Rukayyat ta haukatar dani dan nayi mata asiri takwanta jinya tsawan shekara biyu. Yanxu kema zokimin naji dad'i dan kema nasaka malamina ya bata miki ni'ima dan kawai Adams ya tsaneki.... Takai qarshen zancenta da nufo NUFAISAT d'in..
Ai cikin sauri NUFAISAT tayi tsalle d'aya ta maqalqane ADAMS tana ihun wai ya kalli idan TAUDHAT tazama mayya😁...



Afuwa sis hajjaju🙏🏻 ga LEEKITAN ZUCHIYA kema naki ne. Ki gaidamin da Habibat kice ina santa...

Nagaida y'an hannuna🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻luv u ❤❤❤❤
[8/2, 7:13 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.. *Viawattpad@rahamanalele*

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 27☆



Qara qalqale NUFAISAT d'in ADAMS yayi cikin matuqar mamakin abinda TAUDHAT d'in take fad'a..
Itako NUFAISAT Yanxu tagane cikin hauka TAUDHAT d'in tayi maganar.

Cikin tsawa ADAMS yace da TAUDHAT d'in.. "Idan kika kuskura kika tab'amin mata Wallahi saina miki dukan mutuwa..
Ai TAUDHAT najin hakan sai tatsaya cak da fashewa da kuka...
Da sauri NUFAISAT tasake ADAMS tayi waje da gudu ADAMS yabi bayanta da kulle TAUDHAT d'in..
Hankalin NUFAISAT atashe yake matuqa...
Nan tahau safa da marwa a d'akinta tana mamakin abinda yasami TAUDHAT d'in. ADAMS ya bata labarin shidai yana bata takaddar saki tahau yimai sambatu. Sannan ya qara dace mata takwantar da hankalinta komai zaizo da sauri.
Nan NUFAISAT tabashi labarin abinda tasani tsakanin Hajjiya Rukayyat d'in da TAUDHAT d'in.. Sannan taqara mai da janta wajen boka da ita TAUDHAT d'in tayi...
Sosai ADAMS yayi mamakin wannan lamari. Anan ya rungumi NUFAISAT d'in dajin qarin sanda da qaunarta aransa..
Nan yakira mama Mahaifiyar TAUDHAT dasu Dadynsa ya gaya musu gafa abinda yake faruwa....

Koda sukazo gidan Hankalin Dady dana Amminsa ya tashi matuqa.
Mamah ko mahaifiyar TAUDHAT d'in sam bata wani damu ba. Cewa tayi dama haka qarshen mutane irinsu kenan yake zuwa.. Dan haka ADAMS yasata amota akaita gidan mahaukata. Karya wani saka lamarin aransa bare ya damesa. Dan alhakin mutanan dake kanta koyasa ayi mata wani temako cikin gidan nasa baza awani ci nasara ba.
Dan haka maza yanxu yasa akaita can gidan mahaukata..

Aiko ADAMS yabi abinda maman nata tace... Dan haka saiya dubi TAUDHAT d'in yace.. "Duk da na sakeki TAUDHAT kije ki qarasa rayuwarki nayafe miki duk abinda kikayi min.
NUFAISAT ma ta kalleta da hawaye tace.. "Nima na yafe miki TAUDHAT Allah ya baki lafiya..
Mamanta ma tace "Nima haka..
Abin gwanin ban tausayi. Dan Sai dariya TAUDHAT d'in take musu alamar haukar tagama shiga jikinta..😭

Haka ADAMS yasa masu tsaransa sukaita can gidan mahaukatan sannan su tsaya tsayin daka su cika komai na abinda masu kula da lafiyar irinsu suke buqata suyi musu kana su dawo. Nan suka amsa masa da ladabi suka taficce da TAUDHAT tana ihu da kiran sunan Hajjiya Rukayyat da ADAMS d'in da mamanta harda NUFAISAT..



Kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya Ammin Adams take gayama maman TAUDHAT na tayi hak'uri ta rungumi qaddarar da Allah ya aiko mata akan yar tata tilo...
Murmushin yaqe kawai maman TAUDHAT d'in tayima Ammin da cewa bakomai ai rayuwa haka take. Aduk yanda ka d'auketa haka zata zo maka. Jan hankalin da zatayi shine dan Allah idan da masu hali irin na TAUDHAT suyi gaggawar komawa ga Allah tunkan rayuwarsu ta wulaqanta idan sukazo gangara. Wallahi rayuwar bata da tabbas. Idan yau mune gobe bamu bane. Gashi dai kowa yaga farkwan TAUDHAT kuma kowa yaga qarshenta. Wannan kad'ai ya ishi mutum ishara. Bokaye da malaman tsubbu ba abinda suke iya yima mutum sai kaishi ga halaka.
Wallahi jama'a boka da malaman tsubbo manyan maqiyinku ne dan jefaku suke ga halaka suna baku biyan buqatarku nad'an wani lokaci.
Ni wannan abun ma yana bani mamaki.🤔 Tayaya zakaje wajen annamimai irinsu neman biyan buqata bayan ga ALLAH wanda yayika.. Wanda ya halicceka yayi maka komai na rayuwa sannan yace karoqesa zai biya maka buqatarka amma ka bijirema maganarsa kaje wajensu sannan kace qarshenka zaiyi kyau.. Lala lala🙁. Wallahi qarshenka-ki bazaiyi kyau ba

Yanxu ku duba NUFAISAT... Bata zuwa wajen irinsu neman biyan buqata ita Allah kawai tasa agaba... Ya hanata Haihuwa😭 amma hakan baisata kauce masa ba.
Tana jin dad'in rayuwarta. Tunda ya bata lafiya ya bata kwanciyar hankali. Ya bata soyayyar miji. To itako mezaisa tayima Allah budulci taje wajen waninsa neman wani abu bashi ba. Mutane wallahi muyima kammu tanadi agidan lahira. Mudena biyema san duniya muna jefa kammu ga maseefa. Tun anan gidan duniya bamu tare da kwanciyar hankali hakama agidan lahira bamu ba samun rahamar ubangiji..😭😭😭😭😭


Haka maman TAUDHAT tatafi gidan nata zuciyarta da sanyi dan taji d'ad'in sanyayyun kalaman da Ammin Adams tagaya mata..


Maman TAUDHAT d'in na tafiya Dady ya kalli Ammi dace mata suma ai saisu koma gida ko..
ADAMS ya gyara zama a falan TAUDHAT d'in dake duk anan suka taru yace da Dadyn nasa... "Dama ina san nagaya muku wani batu kuma..
Ammi tace "yauwa bamuji dalilin sakin da kayima TAUDHAT d'in ba tunkan tayi haukan..
Kama hannun Ammin tasa yayi ya kwashe duk abinda NUFAISAT tayagamai akan MUSLEEMA na matarsa ce kuma su Khalit yaransa ne. Sannan da sanin da yayi na Haneepha ba y'arsa bace. Da sakin dayayima TAUDHAT d'in sanadin hakan..

Dady Ammi sun girgiza dajin wannan batu...
Sunji mamaki matuqa.
Nan Dady yasa yaje ya kira masu su MUSLEEMAN su gansu.

NUFAISAT tace aa ya zauna bara taje ta kirasu..
Aiko nan taje shashin dasu MUSLEEMAN suke
Tagansu jugun jugun da alama sunfahimci wani abu na farawa agidan..

Su Khalit da Kahlil Rahma da Haneepha ko sai wasansu suke.
Nan NUFAISAT tasakar musu murmushi da gaya musu iyayan ADAMS nasan ganinsu yanxu a shashin TAUDHAT..
NUFAISAT na fad'in musu hakan tahad'a kan yaran tace subiyota tabasu minti.
Nan suka bi bayanta da murna.
Suma su MUSLEEMAN bayansu sukabi da tunanin Allah yasa ba wani abu sukayi ba..


Dake MUSLEEMA ce a gaban YAWO tana shiga falan YAWO tabiyo bayanta..
Nan YAWON idanta ya sauka akan Ammin Adams..
Ai a furgice Ammi tatashi da nuna YAWO tace.. "YAWO.. 😳
Cikin sarqewar murya da mamaki itama YAWON tace.. "RAHMA..😳

Ainan Ammi tazube qasa sumammiya..
ADAMS yashiga zuba mata ruwa cikin tashin hankali..
Shiko Dady zubama YAWO ido yayi yana tuna itace mahaifiya ga Ammin Adams..
Wacce sukasha nema ashekarun da suka gabata..

Bayan Ammi ta farfad'o kuka tasaka da tashi ta rungumi YAWO tana cewa.. "Haba mahaifiyata menayi miki arayuwa kika gujemin.
Kin hanani ganinki. Sannan kin hanani sukuni. Kwanciyar hankali nutsuwa duk na rasasu sanadinki.
Sanda nasaka araina baki raye sannan na samu nutsuwa..

Share hawayenta YAWO tayi da bata labarin dalilinta na barin BASA garin Jos sukazo gwambe.
Anan take cigaba da bata labarin mutuwan yayanta Musa da samuwar y'arsa MUSLEEMA da sukayi. Sannan taqara mata da labarin Auran ADAMS da MUSLEEMA data musu.. daidai wahalar da suka sha kafin su qara ganin Adams d'in akaro na biyu..😭

Jan numfashi Ammi tayi dace ma Yawon...
"Wahalar ku taqare YAWO. Dan MUSLEEMA d'an uwanta ta Aura. ADAMS D'ANA NE YAWO..

Da mamaki YAWO ta kalli ADAMS da sakar mai murmushi tace.. "Ashe ba banza ba naji qaunarka da sanka a zuciyata. Sannan MUSLEEMA takafe kan kai take so.
Murmushin shima ya sakar mata da kallan MUSLEEMA wacce tayi saurin sunkuyar dakanta qasa tana wasa da awarwaran hannunta.. Yace.. "Nima ganin farko dana muku kan titi naji zuciyata tana san rayuwa daku.
Wannan dalilin yasani tambayarki meyake damun MUSLEEMAN lokacin da take a sume. Nagodema Allah dayasa mutanan nan suka min dukan dana rasa tunanina na fad'a hannunki kika bani Auran qanwata har hakan tafaru
Sannan ina qara godema Allah dayasa nake rayuwa da matata NUFAISAT.. Wacce ta kasance daban acikin mata..
Wallahi YAWO idan har MUSLEEMA bazatabi NUFAISAT a zamansu da zasuyi ba zan iya barin MUSLEEMAN na rungumi yarana na rayu ni kad'ai da NUFAISAT d'in..

Murmushi YAWO tayi dace mai.. "Wallahi baka nan Allahn ka nanan bamu da abin yabo sai matarka NUFAISAT..
Tunda nake arayuwata ban tab'a tunanin zanso wata y'a mace har cikin jinina bayan MUSLEEMA sai NUFAISAT..
ADAMU ina san NUFAISAT kuma ina bayanka kayanke duk wani hukunci dazaka yanke akan MUSLEEMA idai har zata takawo ma NUFAISAT d'in wani wargi....

Murmushi NUFAISAT tayi da zuwa wajen MUSLEEMA takama hannunta da cewa.. "Zan rayu dake qanwata rayuwa irinta yaya da qanwa.. Ina sanki saboda san da kika nunama ADAMS a Ruga. Ina qaunar y'ay'anki dan Allah badan san da nake miki ko nake ma ADAMS ba.
Saboda idan naso su dan ADAMS wata rana baya nan.
Idan naso su saboda ke wata ranah bakya nan.
Yau naqara ganin ishara agun abokiyar zaman TAUDHAT.. Dan haka dan Allah ina rokwanki daki saka Allah azuciyarki mubama mijinmu Farin ciki da kwanciyar hankali...
Kallanta MUSLEEMA tayi hawaye ya zubo mata ta rungumi NUFAISAT d'in tace... "Aunty zan biki. Wallahi zan biki. Ke uwace agareni yanzu. Sannan abokiyar zama. Auntyna. Wacce zanna gayama damuwata.. Haka kawai naji sanki azuciyata. Haka kawai naji qaunarki azuciyata. Haka kawai naji ina san nayi rayuwa dake..
Uwa uba nasan bazan tab'a samun wani Farin ciki tsakanina da mijina ba idan har ban biki nasaka azuciyata zan rayu dake da amana da gaskiya ba.
Aunty ina sanki dan Allah kiyarda aranki haka ne..

Murmushi NUFAISAT tayi da cewa.. "Nima ina sanki MUSLEEMA. Allah ya shige mana gaba akan dukkanin al'amuranmu..
"Amiin.. Dukkansu sukace..
Sannan Dady yaqara sakama NUFAISAT albarka. Ya rungumi yaran MUSLEEMA jikokinsa yayi musu addu'a sannan suka d'an tab'a hira kad'an inda Ammi take cewa yanxu Adams yasa masu kwasar kaya suzo su kwashe kayan TAUDHAT sukaima Mahaifiyarta ayau.
Sai gobe ayima MUSLEEMA d'an gyare gyare ya saka mata komai na rayuwa saita koma d'akinta. Tunda ba wani batun gyara Aure tsakaninsu dan har yanxu tana nan a matsayin matarsa dan bata kai iya adadin da za'ayi musu gyara ba...
Nan ya amsa mata da to insha Allah zaiyi yanda tace...


Da MUSLEEMAN su Dady suka tafi gidansu..
Dan Ammi tace tana san tad'an tab'a hira da ita kafin tashiga d'akin nata..

Sai gidan ya kasance daga NUFAISAT sai Haneepha da Adams sai masu hidima..

Anan ADAMS yasa masu kwashe kaya sukazo suka kwashe kayan TAUDHAT tas ko tsinke basu gari ba sukayi gidan maman nata dashi
.
Tun alokacin aka fara gyaran shashin TAUDHAT d'in...


Komawar su Ammi gidansu ko abin daya faru shine. Dady nayin ido hud'u da Hajjiya Rukayyat ya danqara mata saki uku..
Ai yana danqara mata nan tafad'i sumammiya..
Dama lokacin qanwarta na gidan. Nan Dady yace tafitar masa da ita daga gida..
Sannan zai turo musu da kayanta tas..
Aiko hakan ce tafaru..
Dan qanwar tata na tafiya da ita asibiti Dady yakira masu kwashe suka kwashe kayanta tas zuwa gidansu..

A asibitin cewa sukayi b'arin jikinta ne ya shanye.
(Rahama nalele tace Toh ALLAH ya bata lafiya✋🏻)



NUFAISAT rungumar Haneepha tayi awannan dare suka sha baccinsu.
ADAMS na kallansu yace da NUFAISAT tasan fa bai iya kwana shi kad'ai ba.
Tace yau dai saidai yayi hak'uri dan bata tab'a jin qaunar Haneepha aranta irin nayau ba.
Shuru yayi mata.. Dan abin gwanin ban tausayi ne..
Yasaka aransa zai riqe Haneepha kamar yanda ya faro.. Dan dama yana santa yana qaunarta..
Dan haka bin bayan NUFAISAT yayi ya kwanta tana jinsa taqara rungume Haneephan a gabanta.
Saiya sakar mata kiss awiya da cewa "Ina sanki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login