Showing 63001 words to 66000 words out of 81675 words

Chapter 22 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

bata jiba bata gani ba. Har yanxu yau kusan shekara biyu kenan ba'a sake mutumin ba. Yana can gidan yari ana ganamai azaba.
Kudai Allah ya temake ku sai kuyi Maza kuqara gaba. Dan yanzu lallabawa zanyi na mayar mata da kin k'ofar nan karta gane.
Ga number na wata nasan wata ranah zaku nemeni.
Karb'a MUSLEEMA tayi.
Sannan YAWO tayi mata godiya sosai suka d'auki hanya. Ita kuma Hafsan takulle ƙofar da komawa cikin gidan da sand'a


Sam su MUSLEEMA basu san inda suke jefa qafarsu ba. Sudai saibin titi suke suna tafiya da addu'a.

Ahaka sukaga wani layi suka Shiga. nan sukaga wani gu da alama wajen me saida balangu ne. To wajen yad'anyi duhu anan suka shinfid'a zaninsu suka zazzauna da rungumar yaran dansu bacci ne a idansu.
Har aka kira sallar asuba idansu YAWO garau yake.
Suna ganin mutane suna wuccewa zuwa masallaci har aka sauko akan idansu.
Haka sanda gari yayi haske har mutane sun fara yawa sannan suka tashi daci gaba da tafiya.

Rahma ce tasa musu kuka ita abata abinci.
Nan suka tsaya wajen wata mata me saida koko da k'osai. YAWO ta durqusa taroketa taba yaran kokon da k'osai d'in basu da kud'i idan tana buqatar sumata aikin kud'inta zasu mata.
Kallansu sosai matar tayi kana ta tab'e baki tace Nanawa zata basu
YAWO tafad'a mata sannan tabasu. Haka suka ibi ruwa a gun matar suka wanke musu baki da burushinsu da makilin Suma suka wanke nasu. sannan suka ba yaran koko da k'osan kana suka roketa dan Allah tanuna musu gidan da zasu Shiga suyi salla.. Daqer matar tanuna musu wani gida ba nata ba. Dan bataji aranta tayarda dasu ba.

Matar gidanku me kirki kuwa. haka tabasu ruwa sukayi sallar sannan suka fitto lokacin harsu Rahma sun gama cin k'osan da kunun.
Sai suka tambayi matar wane aiki zasu mata na kud'inta.
Tace ita kawai tabasu dan Allah ne. Dan haka su d'auki yaransu su qara gaba. Haka suka mata godiya suka tasa yaran agaba suka fara tafiya suna tambayar mutane LEEKITAN ZUCHIYA..


"Dan Allah malam katemaka idan kasanshi. Sunan damu muka rad'a mishi shine Ahmad. Amman sunanshi na Ainihi LEEKITAN ZUCHIYA. Ance mana likitocin zuciya sunfi yawa anan garin na kaduna ne shiyasa mukazo ko Allah zaisa adace. YAWO tafad'ama wani mutum hakan da suka taresa..
Kallansu yayi a nazarce kana yace.. "Gaskiya ban sanshi ba. Kuma garin kano yafi cikin garin nan likitocin zuciya. kawai wanda ya gaya muku ya fad'in muku hakan ne danya baku wahala.. Yana fad'a mata hakan ya wuccesu.

MUSLEEMA ta zauna kan wani d'an dandamali anan kan titi bakin wani layi tana me kallan YAWO tace da ita. "Wallahi nagaji YAWO. Yunwa nakeji. Gashi qirjina zafi yake min. Yana min wani abu kamar soya haka ga zafi kamar ZUCIYATA zata fitta....
Itama Yawo zuwa tayi gefanta tazauna yaran suka tsaya gabansu tace. "Hak'uri zakiyi MUSLEEMA mu qara gaba ko Allah zai had'amu dame saida abinci kici ko yunwace
Shuru MUSLEEMAT tayi. jin yanda yanxu gabanta ya shiga bugawa fat fat fat... Aiko dai dai lokacin ADAMS ya faka motarsa agefan titin. Amman tatsallakensu MUSLEEMAT d'inne. Yana tare da Yusuf ne Wanda yaje har office d'insa ya d'aukosa dan ya duba masa kakarsa Hajjiyansu. Yusuf d'in yayi yayi da ita Hajjiyan nasu kan tayarda yakaita asibitin kamar yanda ya saba kaita tace ita sam yau batasan yakaita yaje dai ya d'auko mata ADAMS d'in tasan zaibar duk abinda yake yazo ya dubata ai.
Shine fa Yusuf yanxu yaje yasa ADAMS d'in agaba kan suje ya dubata.

Ahankali ADAMS ya kalli Yusuf yace.. "Kayi hak'uri d'an uwa. Yau dai d'aya na tsaya gefan titi dan amsa waya.
Murmushi Yusuf yayi da cewa.. "Haka tsarin yake ai. Dama ai ganganci kakeyi da kake d'aga waya kana tuqin. Fatana dai Allah yasa ba maiyarka bace takiraka taja mana lokaci.
Murmushi ADAMS yayi da cewa "kamarko kasan Ita d'ince. Yafad'a yana me d'aga wayar daci gaba da cewa... Ina cikin k'oshin lafiya my luv.

NUFAISAT dake tsaye a kitchen d'inta tana yanka kub'ewa dan yau ADAMS d'in yace mata tuwo yake san ci da ranah. kasancewar yau itace dashi ma'ana tashiga girkinta.

Ajiye wuqar dake hannunta tayi tare da tab'e baki tace.. "Nasan kana cikin k'oshin lafiya mijina. Tunda tunkan kafita nake binka da addu'a. Kuma nasan bazata fad'i qasa banza ba. Kawai haka kawai naji gabana yana fad'uwa yanxu. Shine na kira ka dan naji lafiyar zuciyarka. babu mamaki ko zuciyar taka tana dab da karb'ar wani saqo ne shine nake san jan kunnanka dan Allah karka bari ta amshi sakwan soyayyar wata y'a mace...

Hak'ik'a ADAMS yana jin NUFAISAT da kalamanta amma idansa nakan MUSLEEMA yana me qare mata kallo from up down. Kallo na qurilla. Tunda idansa yakai kanta wasu jijiyoyi acikin kansa sukaso fara aiki. Saidai dake yana jin muryar NUFAISAT d'in sai hakan yaqi ba jijiyoyin damar aikin yanda ya dace.

"Kamar nasanta.
Ya faɗi hakan a bayyane batare da yasan ya fad'i ba
Cikin nutsuwa NUFAISAT tace.. "Ita wah🤔..
Ahankali yacire wayar tashi daga kunnansa yamaida kallansa kan wayar.. Shi sai yanxuma ya tuna Ashe waya suke da NUFAISAT. Dan haka cikin sauri ya maida wayar kunnasa da cigaba da cewa. "Kiyi hak'uri my LUV na Shiga wani yanayi ne.
Waro ido😳 NUFAISAT tayi da cewa. "Na Shiga uku ni NUFAISAT. Kardai har zuciyar taka ta karb'i sakwan.
Murmushi ADAMS yayi da faɗin. "Kwantar da hankalinki matata. Dan ba wani sak'o da zuciyata zata karb'a imba naki ba.
"Naqi yarda da abinda kace min a wannan lokacin. B'cos baka tab'amin qarya ba.
"Haka ne my LUV. Kuma bazan fara miki yau ba. Zan gaya miki idan nadawo gida.
"Yanxu bazaka gayamin ba.
"Muna kan hanya ne nida Yusuf zanje duba Hajjiyansu. Pls ki barni kar kisa kaina ya kulle na kasa komai dan Allah.
Murmushi tayi da cewa "Kanka bazai kulle ba mijina bare yasaka kasa komai. Na Barka saika dawo luv u.💋
Murmushi kawai yayi da ajiye wayar ya qara maida kallansa ga MUSLEEMAT tare da tab'a Yusuf wanda yaketa danne dannan waya yace dashi... "Kaga wata Baby mekyau🧕🏻. Nutsu dakyau ka qare mata kallo tatara duk wani abu damu maza muke buk'ata agun mace..
Murmushi Yusuf yayi idansa nakan MUSLEEMAT d'in yace. Saidai hannunta na dafe da zuciya.
"Eh nanma na lura kamar tana da matsala da zuciyartata. dan idan kaqara kallan gefan wiyanta dakyau zakaga alamar tashin wata jijiya wacce nake kyautata zatan akowane lokaci ciwan zuciya zai iya kamata. Dan wannan jijiyar alamace tafara bayyanar ciwan

Jan numfashi Yousuf yayi da cewa "Wai dama waya kakeyi d'azu ko kallan yarinyar mutane. Dan naga kayi saurin gane komai atare da ita cikin lokaci k'ank'ani..
Murmushi ADAMS yayi da bashi amsa. "Kasan ko'a skull nafika gane abubuwa cikin sauri. Kuma karkace na shagala da yawa. Dan kasan san mata ba d'abi'ata bace.

Juyowa Yusuf yayi yana harararsa da cewa. "Wato magana zaka gayamin.
ADAMS ya qara yin murmushi da cewa. "Harma na gaya maka mai ai. In banda iskanci kasan dai neman mata baya gabana
Kaine dai wahalalle daka dami zuciyarka saika had'u da wacce tacika sharid'anka..
"Naji dan Allah. Wannan d'inma dan tayi yarinya ne. Bazata isheni watayawa da yaw ba. Da Wallahi yau saina baka kunya na nemeta da aure in kashe bakin gorin da kakemin akoda yaushe.

Tada motar ADAMS yayi yana cewa. "Dako ka huta wallahi..
Daidai nan kamar ance MUSLEEMA tad'ago kanta saiko tasauke akan gefan fuskar ADAMS...

Azarane tatashi har tana mangare Khalit dake gabanta ta kwalla ihu tana nunama Yawo ADAMS faɗi take "Wallahi shine. Shine YAWO. Shine acikin motar can.
Wani saurayi ne yazo wucce yaji abinda take fad'i. Sai ya kalli motar ADAMS dake tafiya ya dawo da kallansa kan MUSLEEMA da galla mata harara yace.. "Shine wah.
Da sauri MUSLEEMA ta qarasa gun saurayin tace. "Shine mijina Wallahi mujina ne dan Allah kasan shi ne.

Kallan raini yayi mata da qare mata kallo daga sama har qasa yace. "Gaskiya ke y'ar rainin hankali ce. ADAMS LEEKITAN ZUCHIYA ne mijinki. Ke kinsan waye shi afad'in garin nan kuwa. Wani babban mutum ne me arziqi. Gashi Doctor gashi d'an kasuwa. Kafin ki gansama kuzanta sai kina da hanya. Dan yau baki gansa da masu tsoro ba shine zaki wani ce mijinki ne. Mijinki a ina kina kicaka dake haka. Dubeki fa kamar wata almajira. Ke idan kikaci karo da Matansama kikace ke matarsa ce wallahi sai sun sa and'aureki d'aurewar dahar ki mutu bame kunceki. Shashasha wawiya almajira kawai...
Ai MUSLEEMA bataji qarshen zancensa ba hannunta dafe da k'irji tafad'i sumammiya sakamakwan qara ganin motar ADAMS da tayi tana nufosu..
Dama zagawa ADAMS yayi da motar tashi dan cikin layin dasu MUSLEEMA suke zaune zai Shiga kasancewar nan ne layinsu Hajjiyansu Yusuf d'in da suke san zuwa dubata.

Jan tsaki saurayin yayi da wuccewarsa abinsa yana tafiya yana sambatu daga ganinsa kasan akwai abinda yake damunsa kamarma dai abuge yake.

Hankalin YAWO ya bala'in tashi. Nanta jawo MUSLEEMA jikinta tana mata fifita da fad'in. "Ki tashi MUSLEEMA kinga halin da muke ciki dan Allah ki tashi.
Dai dai nan ADAMS ya qaraso da motarsa dan yin kwana ya Shiga layin. Ahankali ya tsaya da motar tare da zuge gilashin b'angaransa ya kalli YAWO da cewa.. "Sannu Baba meyasameta.
Ai da sauri YAWO takallesa tana had'a ido dashi tunaninta ya tsaya cak....
San da ADAMS ya qara maimaita tambayarsa Sannan tunaninta ya dawo. Hawaye ya zubo mata tace dashi. "Yanxu tafad'i d'an saurayi. dan Allah katemaka min ita kenan gareni..
ADAMS ya kalli MUSLEEMA dake hannunta kamar bata da rai. Kana ya kalli yaran nata da suka zuba musu ido shida Yusuf. Saiya fitta daga motar Yusuf ya biyo bayansa. Ahankali ADAMS ya d'auki MUSLEEMA Yusuf ya bud'e mai gidan baya yasata.
Sannan ya kalli YAWO da cewa. "Kushiga muje asibiti.
Da sauri yawo tashige ciki da yaran. Yusuf ya koma wajen zamansa yana cewa. "Mujuya kawai adubata ma dawo ka duba Hajjiyan namu..
"Toh. ADAMS yace mai jiki babu kwari dan haka kawai yaji jikinsa ya mutu da ganin yaran MUSLEEMA.
Shi idanma idansa ba gixo yake masa ba zai iya cewa yaran na kama dashi.

Shima Yusuf yaga kamar amma sam wani abu bai dirsu a zuciyarsa ba.
Suko yaran kallan ADAMS kawai suke zuciyarsu na raya musu ayya basu san wannan mutumin ba.
Yawo ko gabanta fad'uwa yashiga yi. Yayinda hankalinta duk ya tashi da ganin Adams d'in. Dan ganin ya qara kyau sosai. Ga wani kwarjininsa daya maketa. Ita tsoroma taji tace tasanshi bare har takaita da cewa ya Auri jikarta harda yara uku. Wayyo Allah ya kawo mata sauki cikin lamarin..



Awannan lokacin TAUDHAT na tare da malamin nata sun gama tsula tsiyarsu. Dan cema ADAMS tayi ya sauketa agidansu tana da maganar da zatayi da mamanta.
Toh shinefa daya tashi fitta office d'azu da safe ya sauketa.

Shine yana tafiya tayi wajen malamin nata karb'ar maganin mata. Shi kuma yace mata saiya jita.

"Dan Allah kamin had'i na musamman. Dan naga kan ADAMS bai dena rawa akan NUFAISAT kwanan nan ba. Ka duba yau zai Shiga girkinta sai wani nishad'i yake. Ina jinsafa yana cemata tayi masa tuwo ta turamai office shi zaici yau da ranah.
Kumafa karka manta idan da nice nayi masa tuwo sam bazaici ba.. TAUDHAT ta fad'inma malamin nata hakan da damuwa.

Murmushi malamin nata yayi da shafan gefan fuskarta yace.. "TAUDHAT kina da futuna. Nina rasa me kike gani agun wannan kishiyar taki da kike kishi da ita.
"Kai bazaka gane bane. Yanxu dubamin kaga me yake tafiya a tsakaninsu.
"Toh.. Yace mata da wargaza qasarsa yana Zane Zane cikin gwanancewa.
Can ya d'ago ya kalleta a furgice. Sai kuma yaci gaba da zane zanen nasa.
Sanda ya gama tsaf ya ture farantin qasar tasa gefe yace da ita.. "Tabd'ijan.. Lalle ambar baya da qura..
"Ban gane me kake nufi da ambar baya da qura ba.

"Ina nufin NUFAISAT da ADAMS ba wani abu na tashin hankali agaresu. Qara san junansu suke kamar yanda kika sani.
Baya da quran da kikaji nafad'i ko shine Wallahi ga wasu yara nan kyawawa na mijinki ADAMS har uku. wata qaramar yarinya ce tahaifa masa su. sam shi bai samma yaransa bane..
Haka ita yarinyar ayanzu bata cikin hankalinta.

😳😳😳 Inda ace kawunan TAUDHAT uku ne ba shakka da saita waro dukka idanunta dasu.
A razane. A furgice. A haukace tadafe qirji da cewa.. "Kutumar uba. Ban gane me kake nufi ba. Ka fahimtar dani na fahimta. Wallahi kwakwalwata ta hautsine.. Isma'in ina san nayi haukafa..

"Ki kwantar da hanlinki yanxu ki koma gidan naki ki gano mana komai. Danni nayi bincike akan nasan komai. Saidai banga komai d'in ba. Yanxu saikin gano mana wani abu zan iya baki haske.
Da sauri TAUDHAT tatashi da saka kayanta ta d'auki yajarta ko sallama batayi masa ba taficce daga d'akin nasa hankalinta amatuqar tashe...



🤔🤔🤔🤔🤔 na gaida y'an hannuna



[7/28, 4:18 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

http://hausafulaniwriters.blogspot.com
” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 25☆


Koda ta iso gidan bataga kowa ba alamu sun nuna ba wani ma abinda ya faru. Nan takira malamin nata tace bataga kowa ba. Yace tabari Adams d'in ya dawo tukunna...



Su ADAMS ko bayan sun isa asbitin duba MUSLEEMAT yahauyi. Inda ya tabbatar tana d'auke da ciwan zuciya. Sosai yashawo kam matsalar yana me mamakin yanda tana qaramar yarinya haka takamu da ciwan ZUCIYAR

Ahankali ya kalli yawo dace mata. Bara suje ya duba kakarsa. Yana nufin Hajjiyansu Yusuf.
Bayan sun dawo ne yana zaune kan kujerarsa a office d'insa sai kawai ya shiga tunanin meyajama MUSLEEMA ciwan ZUCIYA tana qaramar yarinya haka.
Shuru yayi dajan numfashi ya kira ma'aikaciyarsa yace takira masa kakar yarinyar daya duba d'azu. Cikin ladabi ta amsa mai da kiran YAWO.
Bayan YAWO tazauna ya kalleta anutse da cewa.. "Baba ina san nasan sunanki.
"Sunana YAWO..
"Wannan yarinyar dana dubata y'arki ce ko jikarki.
"Jikata ce.
"Ina iyayenta.
"Atakaice dai yanxu ita marainiyace. Danni yara biyu gareni. Rahma da Musa. Kuma duk na rasasu. Yazu haka dai ita kad'ai taragemin da yaranta.
Waro ido ADAMS cikin mamaki yace da ita. "Kina nufin way'ancan yaran ita ta haifesu.
YAWO ta d'aga mai alamar tabbatarwa hawaye na zubamata tace. "Y'an uku ne su. Wata ranah wani yazo rugarmu da matsalar d'aukewar tunani. Ita ce tafara ganinsa. Sai me rugar nawa yasa d'ansa doctor yayi mai binciken lafiyarsa. Bayan yagane yasamu d'aukewar tunani. Sai muka saka masa suna Ahmad kasan cewar bamu san sunansa da inda ya fitto ba.
Bayan d'an me Rugar namu ya dawo dashi daga asibitin nashi. Sai jikar tawa tanuna qauna agareshi. Zai zauna wajen me rugar tamu. saitace ita tana san nakawosa gidana yazama yayanta.
Haka na yarda da abinda tace dan baqaramin so nake mata ba.
Ahaka ahaka soyayya tashiga tsakaninsa da ita. Taqi wanda suke da alk'awarin Aure. Tace shi take so. Nan banyi cikakken tunani ba. Banyi tunanin bansan daga inda ya fitoba. Banyi tunanin waye shi ba. Banyi tunanin ko sunansa bamu sani ba. Kawai saina duba nutsuwarsa da kyawun halinsa. Da ladabi da biyayyar da yake min. Kawai saina aura masa ita. Watansu tara tasamu ciki. Shine tahaifi way'annan yaran y'an uku.. Bayan wasu lokaci sai wanda yake da niyar Auranta dafarko wanda suke da alqawarin Aure dashi saiyaja shi wannan mijin nata daji ya makeshi da sanda.
Anan dai muka nemesa muka rasa..
In takaice maka shidai wanda ya makesan shine wanda yazo ya bamu labarin shine sanadin b'acewarsa.
Shine mukaxo garin kano nemansa dan nan yace mana ya turasa.

Gaban ADAMS ne ya fad'i sakamakwan tunanin dayazo masa kwakwalwa amma danya tabbatar da tunanin nasa saiya kalleta a nazarce yace da ita.. "Yanxu ina ne rugar taku.
Kallansa yawo tayi da tunanin tagaya masa gaskiya ne kodai tad'an jinkinta taga iya gudun ruwan lamarin. Gaskiya ita tsoran ADAMS takeji. Sam bata tab'a tunanin ganinsa da zatayi akaro na biyu zai kasance mata haka me matuqar kwarjini da kamala ba. Idan tace zatayi saurin gayamai lamarin qila yaqi yarda da ita. Koma yayi mata wata fassarar. Gaskiya bazata gayamai yanxu ba. Saidai zatasan yanda zatayi su rayu dashi. Daga nan idan ya fara sakewa dasu saita gaya mai gaskiyar lamarin.
Dan haka gyara nutsuwarta tayi da cemai. "Rugarmu nacan garin JOS basa.

Jan numfashi ADAMS yayi da cewa. "Gaskiya kinyi kuskuran bashi jikarki bayan kinsan baki san daga inda ya fito ba.
Sannan kuskure na biyu da kikayi shine na baro Rugarku da kukayi kuka fito yawan nemansa.

Yanxu dai ina buqatar sanin wata damuwa ce tasa ita jikar taki shiga cikin wani hali dahar ya haifar mata da ciwan ZUCIYA haka...

"Sanshi da qaunarsa ne ya haifar mata da hakan. Tana matuqar sanshi da qaunarsa. Dan kowane lokaci zancenta shine. Kullum cikin kuka take.

Jan numfashi ADAMS yayi da cewa "Toh nidai yanxu nayi niyar temakwanku. Inasan naji wane irin temako kikesan nayi muku.
"YAWO tashere hawaye cikin matuqar Farin ciki tace.. "Kayarda damu kan bazamu cuceka ba. Kakaimu gidanka matsayin y'an aiki ga matanka. Sannan dan Allah kabama yaranta kulawa kamar kaine mahaifinsu. Dan bani san sutaso da rashin soyayyar mahaifi agaresu.

Shuru ADAMS yayi da tunanin shi tunda yaga yaran qaunarsu tashigesa. Gaskiya wannan karan saidai Dadynsa yayi hak'uri dashi yabarsa ya raini yaran daba nasa ba.

Ahankali yace da ita. "Indai wannan ne insha Allah bazai zama da matsala ba. Zan nemi amincewar mahaifina yanxu naji tabakinsa. idan ya amince min shikenan.
Godiya YAWO tamai sosai..
Anan yakira Dadyn nasa a waya yace dashi. "Dan Allah Dady kamin afuwa ina san rainan wasu yaran wata yarinya da kakarta. Ina san basu kulawata. Dan Allah Dady karkace aa.
Shuru Dady yayi. Lokacin yana wajen shaqatarwar gidan nasa yana karanta jarida. Ahankali yace mai.. "Na amince amma ka kula dakyau. Dan kasan yanxu mutane babu yarda...
"Insha Allah Dady zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login