Showing 69001 words to 72000 words out of 81675 words
d'akin zuciyar cike da baqin cikin ganin yaran MUSLEEMA.
Nan tahau safa da marwa afalanta tana cewa.. "Shegun yara sai idanuwa kwala kwala kamar na mayu. Ga fari kamar y'an shan jini. Ga kyau kamar d'awisu.🤣
Haka tadinga sambatunta kamar tab'abb'iya. daga qarshe dai tayanke shawarar zuwa wajen bokanta kan adawo da Haneepha daga skull..
Ko qaryar data saba shararama Adams idan zata wajen malaminta batayi ba tazari gyale da iban kud'i tahad'a da kin motarta sai daji..
Tana fitta ko wani saurayi yazo ya kwashi su Khalit yakaisu skull d'in da Haneepha take zuwa. Dake had'e da madarasa ce skull d'in nan da nan komai ya kammala na zuwa skull d'in su Khalil d'in.
Dan nan take skull d'in tabayar da uniform nasu har na madarasa ad'inka musu. Nan saurayin ya dawo dasu daba YAWO tabbacin gobe idan yazo d'aukar Haneepha zai tawo da uniform nasu asa musu ya tafi dasu. Dan agoben akesan sufara zuwa.
Godiya YAWO da MUSLEEMA sukamai..
NUFAISAT tayanke shawarar gobe zataje kasuwa da MUSLEEMA dan tafara aiwatar da udirinta akanta.
Nan taqara duba account nata taga tana da wadatattun kud'i sai tayi hamdala ga Allah tana rokwansa daya bata damar aiwatar da komai cikin nasara. Sannan yacire mata jin kishi da baqin hali ko hassada. Kana tashafa addu'arta dajin wani shauqi me saka zuciyata cikin sukuni..
TAUDHAT ko tasamu bokan nata yana da baqi sosai. Amma haka ta fad'a turakar tashi kuma ya saurareta dan shima dama yayi missing nata..
Sanda ya gama surkullansa ya d'auko wani magani ya bata yace tasama MUSLEEMA a abinci ita da yaranta. Yana tabbatar mata idan sukaci nan zasubi duniya ba Wanda zai qara ganinsu bare ya kawo labarinsu.
Aiko nan TAUDHAT ta karb'a da bashi kud'i yace sam tariqe kud'inta yafi buqatar jikinta akan kud'in..
Nan dai takwanta yayi yanda yaga dama da ita kusan awanni. Asannan ne yabarta tasamu dawowa gida..
Ai tana dawowa gida tadafa had'add'iyar jalof da kifi ta barbad'e maganin aciki. Da nufin takaima su MUSLEEMA..
Saidai kan takai musu sanda takira malaminta da farin ciki take cewa... "Toh naje gun bokan nawa har yabani magani nasama su MUSLEEMAN a abinci yace suna ci zasubi duniya kuma ba Wanda zaisan inda suke har qarshen rayuwa.
Jan numfashi malamin nata yayi da cewa. "Dama nasan sai kinje wajensa. Bazaki tab'a hak'uri ba. Toh wallahi nayi bincike basu bane zasubi duniya kece zakibi duniya. Dan haka ina shawartarki kafin ki aiwatar da udirin kije ki nemi yafiyar mahaifiyarki dan Wannan asirin da kika mata ya karye d'azu d'azun nan ajikinta. Sakamakwan temakwan da maman kishiyarki NUFAISAT tabata. Dan taje tagaya mata matsalarta tsaf. Ita kuma tasa wani malami ya b'ata abinda kika mata shekara da shekaru. Yanxun nan naga hakan nake qoqarin kiranki sai gashi kinkirani.
Sannan ki kawomin yata. Karsai kinbi duniyar nazo karb'a yazama hajadi....
"Me kake san cewa. Kana nufin idan sunci abincin ni zambi duniya su suzauna saboda nice naci abincin..
"Ina nufin kome zaki musu bazai kamasu ba. Idan kuma kika matsa komai dawowa kanki zaiyi.
"Ban yarda ba. Dan ina ji ajikina nice dacin galaba akansu.
"Haba TAUDHAT. Ya kamata ki gane qaunar ki nake har cikin zuciyata. Wane malami ne yake gayama miki gaskiya tsagwaranta imba niba. Wallahi abin dana gaya miki idan har baki bishi ahankaliba haukacewa zakiyi..
"Haukacewa. Haukacewafa kace. Waini d'in kake cema zan haukace.
To canja tunaninka. Dan ba wani asirin dazan yima wani ko wata dazai dawo kaina har nayi hauka.
"Ba mamaki qila akan MUSLEEMA da yaranta qarshenki yake san zuwa TAUDHAT....
Saboda haka kiyi duk abinda kike sanyi kiyi na barki lafiya. Amma kafin nan kikawomin y'ata da hannunki dan Wallahi yanda banyi auran nan ba ko sama da qasa zata had'e saina karb'i yata agun mijinki Adams. Danko gawarki nagani saiya bani y'ata b'cos kinfi kowa sanin yanda nake qaunarta. Shiyasa nake qara jaddada miki daki kawomin y'ata tun da wuri....
"Da Allah dakata Isma'in. Kama dena batu akan Haneepha. Dan Haneepha y'ace ga ADAMS. Kaima kasan muslinci ya bashi ita...
"Wato TAUDHAT baki sanni bane.
"Zan sanka tunda ina darai da lafiya.. Tana faɗin hakan takashe wayarta da mamakin yanda asirin da tama mamanta ya qarye..
Ahankali ta d'auki abincin tanufi shashinsu MUSLEEMA.
Lokacin NUFAISAT na tare dasu. Tana nunama MUSLEEMA yanda ake dressing d'in kayan yara.
Da nutsuwa TAUDHAT ta'ajiye musu abincin agefe ta harari inda NUFAISAT d'in take tace da Yawo. "Gashi abinci nakawo muku kuci kuji irin nawa girkin..
Da murmushi yawo tace.. "Toh angode Allah ya saka..
Har takai ƙofar fitta tajuyo da qara kallan YAWO tace.. "Kuci fa.
"Insha Allah zamuci yanxu kuwa. YAWO taqara bata amsa da kulawa
Sanda NUFAISAT tatabbtar tatafi Sannan tace da MUSLEEMA. "Kar kuci kuzubar a shara. Badan ina zarginta ba. Saidan hankalina bai kwanta da abincin ba..
Ba musu MUSLEEMA tajuye a baqar leda kana taje tasaka a sharar...😁
ADAMS ko daya tashi daga office gidansu ya nufa. Kasancewar jiya baisamu yaje ba.
Anan yake qara gayama Dadynsa ya kwantar da hankalinsa yayaba da hankalinsu YAWO. Alamu sun nuna mutanan arziqi ne.
Sanda ADAMS ya tabbatar Dadyn nasa ya gamsu sannan yaje gun Amminsa itama ya kwashe labarin komai ya gaya mata.
Da jin daɗin temakwan da yayi musu Ammin nasa ta kallesa da cewa.. "Gayamin sunansu.
"Ita dai yarinyar sunanta MUSLEEMAT sai kakarta YAWO. Sai yaran MUSLEEMAN Khalit da Khalil & Rahma..
Shuru Ammin tayi cikin tunani. Can taqara cewa. "Kuma kace fulani ne ko.
"Murmushi yayi da bata amsa... "Eh fulani ne. Saima kinga yaran ita MUSLEEMAT d'in suna kama dani sosai. Wallahi saikace nine ubansu.
Bara naje gida dare yayi kuma gashi ina jin yunwa.
Jan numfashi Ammin tayi da cewa.. "Kona zubo maka abinci ne.
"aa barshi. Karki had'ani fad'a da ita😄
Murmushi tayi da cewa.. "Wacece acikinsu.
Tashi yayi da sakar mata kiss ahannu yace. "NUFAISAT..
"Wato har tayi nesa yanxu a girki dazaka k'i cin nawa ko.😀
"aa wasa nake miki Ammina. Kingama na zauna zubomin naci kawai😃.
Murmushi tayi da cewa. "Nagodema Allah data kware yanxu. Allah ya qara had'e kanku maza jeka bana san kana yawo da yunwa.
Murmushin shima yayi mata da sallama ya fitta daga falan nata suka d'auki hanyar gida..
Suna isowa shashin su MUSLEEMAT yayi.
Nan yaga MUSLEEMAN da Rahma suna kallo. Da alama YAWO da su Khalit sunyi bacci.
Ahankali takemai sannu da zuwa da gayamai YAWO dasu Khalit sunyi bacci.
Dajin dad'in yanda tasake da gidan nasa yayi mata sallama daniyar ficcewa daga falan..
Ai cikin sauri tatuna tana san yimai godiya dan haka cikin sanyin murya tace... "Nagode da cika maganarka da kayi d'azu da safe YAYANA.
Juyowa yayi da kallanta ya d'aga mata gira alamar me take nufi.. Ganin hakan sai tacigaba da cewa.. Ina nufin wajen sakasu amakaranta dakayi.
Murmushi yayi da harararta yace... "Idan kika qaramin godiya akan wani abu dazan miki ko nayima yarana saina sab'a miki.
Cikin shagwab'a tace.. "Afuwa YAYANA. Wallahi na tuba bazan sake ba.
"Idan kika sake fah.
Shuru tamai.
Sai yaci gaba da cewa.. Ke da kanki nakesan kigayamin wane hukunci ne yadace dake.
Jan numfashi tayi da cewa "Saika dena kulani.
"Shikenan. Yanxu saikin sake ki gani a kwaryarki. Gud9t
Yana faɗin hakan ya ficce daga falan...
_Wallahi Yayana ina MASEEFAR SONKA_ tafad'i hakan aranta tare da tashi takulle musu kofa...
Ya samu NUFAISAT kamar yanda yasaba ganinta cikin tsafta. Bayan sunyima junansu wlcm part na TAUDHAT ya nufa. Ba lefi yaga tasake ba kamar yanda yabarta da safe ba.
Anan yasakarma Haneepha kiss ya koma shashinsa yayi wanka dama NUFAISAT tashirya masa komai na abinda zaici.
Dan haka yana yin sallah yahau cin abincinsa.
Anan NUFAISAT take gayamai gobe zataje kasuwa da MUSLEEMA..
TAUDHAT har kwanciyar bacci taji shuru su MUSLEEMA na tare da lafiya.
Dan bala'i haka takasa nutsuwa qarfe goma sha d'aya da rabi taje ta bugama su MUSLEEMA kofa.
Nan taga MUSLEEMA ce ma tabud'e mata kofar dan har alokacin basuyi bacci ba ita da rahama.. A rikicewa take tambayar MUSLEEMA waiko sunci abincin data basu d'azu.
Nan ko MUSLEEMA ta bata tabbacin sunci har suna Santi..
Da mamaki ta dawo d'akinta tana tunanin ita dai tunda take da bokan nata bai tab'a bata abu tayi taga sab'anin abinda yace mata ba.
Nan alokacin takira malaminta tace bataga komai daya faru dasu MUSLEEMAT ba. Kodai zancenshi haka yake.
Murmushi yayi dace mata TAUDHAT kinqi gane gaskiya nagaya miki. Dan duk inda zaki saidai kawai suci kud'inki.
Shuru tayi bayan ta kashe wayar. Tunani tashiga kodai taqara komawa wajen bokan natane.
Sai wata zuciyar tace mata tadai d'an jinkirta taga gudun ruwan lamarin
Washe gari haka MUSLEEMA taqara taya NUFAISAT had'a breakfast..
bayan ADAMS ya fitta NUFAISAT saurin gama shirya d'akinta tayi. Saita tasa MUSLEEMAT agaba sukaje kasuwa inda tazab'an mata kayan make-up dasu kayan gyara jiki irin na mata kala kala masu kyau. kana suka nufi wajen atamfofi fashion masu kyau tasai mata kusan kala talatin tare da su les material. Daga nan wajen telanta suka wucce ya gwada MUSLEEMA tace mai tana san kayan dukka su kammala nan da sati d'aya. Pls ya rabama yaransa aikin dan suyi sauri.
Nan ya tabbatar mata insha Allah zai kawo mata kayan bazai qara ko kwana d'aya ba.
Nanko NUFAISAT tabasa kud'in d'inkinsa cif bata rage masa komai ba suka dawo gida.
Godiya ba irin Wanda MUSLEEMA batama NUFAISAT ba. Ganin akwalla kud'in data kashe mata yau zaikai dubu d'ari biyu. Duk da cewa dama kana kallan NUFAISAT kasan taci tatada kai amma abin a jinjina mata ne wannan siyayyar datai mata ai..
Haka yawo ma tadinga gode mata.
Sanda NUFAISAT tanuna musu b'acin ranta kana suka hak'ura suka dena yimata godiyar..
Alokacin NUFAISAT d'in tafara koyama MUSLEEMA yanda ake make-up na zamani.
Aiko dake kwakwalwar MUSLEEMAN abud'e take nan tafara gane komai..
Zuciyar TAUDHAT ko tayanke mata shawara kan taqara komawa wajen bokan nata. Dan hausawa nacewa kanufi cimma burinka da zafi zafi yafi kabishi da sanyi sanyi .. Still yau d'inma haka taficcewarta batare data gayama Adams ba..
Saidai koda taje gun bokan shima bata tabbaci yayi kan tayi hak'uri Kawai da lamarin. Idan kuma tana ganin bazata iya hak'urin da lamarin ba. Toh ta lura da lokacin da MUSLEEMA take al'ada. Tasan duk yanda zatayi takawo masa tsumman da take amfani dashi alokacin kota kawo masa wani dai abu dayake da jinin al'adar tata..
Da damuwa TAUDHAT tadawo gida.. Tana saqa tataya zata gane MUSLEEMA tana al'ada bare takawoma bokan abinda ya shaifi jinin nata..
Dan dai tayanke shawarar zata sakama MUSLEEMAN ido sosai har tacinma borinta..
_________
Bayan sati biyu zanso me karatu yaga yanda MUSLEEMA tacanja.
Tacanja kamar ba MUSLEEMAN ruga ba..
Dan mayukan da NUFAISAT tabata dan tadinga amfani dasu sun goge fatarta sunmai da ita gwanin ban sha'awa. Dama yanxu take kan cikowa dan haka data fara samun gyara dacin abinci me gida jiki nan taqara murmurewa.
Haka yaranta ma gwanin ban sha'awa. ADAMS san yaran yake kamar me. Wannan ma ya qara baqanta ran TAUDHAU.
Musamman yanda taga NUFAISAT tana zagewa akan lamarinsu. Yanda ta maida su y'antattu kamar tasan yaran ADAMS d'in ne.. Wannan abu na k'ona ran TAUDHAU matuqa.. (Batasan NUFAISAT tasan komai fiye da saninta ba😂)
Dake yau LAHADI ne ADAMS yana dawowa gida da wurri. Dan haka sai NUFAISAT tasa MUSLEEMA tayi wanka tayi makeup.
bayan tafito daga wankan wasu riga da siket na atamfa NUFAISAT ta d'auko mata. Kayan yana d'aya daga cikin wanda tad'inka mata.
Ba qaramin karb'arta atamfar tayi ba. Dan ita kantama NUFAISAT santa taji sha'awarta. Nan tabata turare me sanyin qamshi d'aya daga cikin way'anda take sawa.
Nan MUSLEEMA ta saka...
NUFAISAT takalleta da nutsuwa tace.. "Yauwa yanxu bazai wcce minti goma ba zai shigo. dan haka ina buqar kisan duk yanda zakiyi ya ganki.
Na tabbatar zaiji wani abu aransa. pls kifa nutsu dakyau dan bani san asamu matsala.
Murmushi MUSLEEMA tayi dace mata. "Karki damu Auntyna. Insha Allah komai da kika tsaramin yana nan a kwakwalwata..
"Masha Allah. Yanxu ni zanyi wajen shaqatawar gidan nan. Nasan komai zai faru akan idona. Danta k'ofar baya zai shigo. Dan Allah ki ankare dan Adams daban yake acikin maza.
Murmushi MUSLEEMA taqara yimata da d'aga mata kai alamar taji..
Aiko NUFAISAT na barin wajen saiga Adams ya dawo..
Da nutsuwa ya fitto daga motarsa yana mejin dad'in yanda NUFAISAT ce dashi.
Shi kawai yana rayuwa da TAUDHAT ne badan tana gamsar dashi abubuwa da dama na rayuwar aure ba. Dan nesa ba kusa ba NUFAISAT tafita sanin abubuwan da suka dace..
Yana wannan tunanin ne yaci karo da MUSLEEMA.. "Subhanallah.. Shine abinda yace. Dan sunbigi goshin juna.
Ahankali cikin sanyayyiyar murya MUSLEEMA tace.. "Dan Allah kayi hak'uri YAYANA bansan kana tawowa ba daban tawo gabaki d'aya ba..
Lumshe ido ADAMS yayi. Shifa ya lura kwana biyun nan MUSLEEMA na canjawa. Dan fatarta ta goge ga wani kyau da take qarawa. Sannan uwa uba Shifa yana jin wani iri sosai idan magana tana shiga tsakaninshi da ita
Yau kuma gashi yaji qamshin d'aya daga cikin turaran da NUFAISAT take sawa ajikinta..
Wai me yake faruwa ne.. Ya tambayi kansa..
Bud'e idansa yayi ahankali ya sauke akan dara daran idanunta kamar madara yana me cigaba da qare mata kallo daga har qasa. Tayi mai kyau sosai ga gashinta yasha gyara. Wallahi jiyayi kamar ya rungumeta..
Cikin wani hali yace. "Na hak'ura..
MUSLEEMA najin hakan taratsa tagefansa ta wucce. Saiko yabi bayanta da kallo cikin mamakin had'uwar datayi...
"INA SANTA.... Ya fad'i hakan abayyane ba tare dayasan ya fad'i ba... Yana juyowa danci gaba da tafiyarsa kawai sai yaga NUFAISAT tsaye!!! nannad'e da hannu tana kallansa.
Nan yahau kame kame yana cewa.. "Umm amm dama... Kasa cewa komai yayi dan haka sai kawai ya nemi wucce NUFAISAT d'in dan Wallahi wata kunyarta ce ta bala'in kamasa..🙈
Ainan cikin sauri NUFAISAT tasha gaban sa da cewa. "ɗan jini kaɗan mana malam..
Tsayawa yayi batare daya kalleta ba. Ganin hakan saitaci gaba da cewa. Kace kana santa ko..
Kallanta yayi ahankali da girgiza mata kai alamar aa...
Murmushin yaqe tayi mai daci gaba da cewa.. Hmm. Kasandai y'ar d'akina ce. Dan haka yanxu saika bada dubu d'ari saboda wannan furucin da kayi...
Cikin marairaicewa ya had'a hannuwansa biyu 👏🏻 alamar tayi hak'uri bazai sake ba.
Tab'e baki tayi dacigaba da cewa..
Bayan kabada kud'in daga baya sai muyi ciniki kawai nabaka auranta.
Cije bakinsa yayi cikin matuqar jin kunyar yace.. "Zan bada. Amman kafin nan muje falanki kiji wani abu.
Gyad'a masa kai tayi alamar suje...
Bayan sunje sakata yayi kan kujera da durqusawa gabanta ya kama dukkanin hannayenta yace.. "My luv wallahi akwai matsala babba.. Dan tunda nayima yarinyar nan kallan farko naji wani abu ya minsini zuciyata...
Magana ta gaskiya zuciyata na tsumuwa idan magana tashiga tsakanina da ita..
Gashi ita matar aure ce.
Bai dace naji hakan akanta ba... Kawai ni yanxu na yanke shawarar zan kaisu gidansu momy dan kare kaina ga fad'awa ga halaka.. Saboda yanxu haka da naji qamshin wani turaranki ajikinta jinayi kamar na rungumeta..
Waro ido NUFAISAT tayi😳..
Cikin sauri yacigaba da cewa.. Wallahi gaskiya na gaya miki dan kinsan ban iya yimiki qarya ba.🙂
Shuru NUFAISAT tayi tana tunanin tagaya masa gaskiya ne yanxu kodai tabari sai nan gaba.
Idan tagaya masa yanxu gaskiya tatemakesa da ita kanta dan bazai kwashe mata su ba.
Idan kuma taqi gaya masa tasan tunda ya furta zai kaisu wajen su Dady to saiya kaisu.
Dan haka Ahankali taqara rike hannunsa fiye da yanda shi ya riqe matan tace.. "Ka godema Allah ya Mijina daya had'aka dasu MUSLEEMAT har yabaka ikwan temakwansu kakawosu cikin gidanka.
Kasan da cewa MUSLEEMA matarka ce ya Mijina
Kasan da cewa yaran MUSLEEMA yaranka ne ya mijina
Kasan da cewa ganinka da MUSLEEMA tayi shiyasata sumewa har katemaketa
Kasan da cewa sanadin sanka da qaunarka shine silar kamuwa da ciwan zuciyarta
Kasan da cewa labarin da YAWO tad'an gutsira maka da cewa wani ne ba wanin bane kaine wanda tunaninka ya d'auke har tabaka auran MUSLEEMAN..
Cikin zubar hawaye NUFAISAT takwashe komai ta gayama ADAMS kamar yanda MUSLEEMA tagaya mata..
Shuru ADAMS yayi saboda jin yanda kansa yake juyama..
Ahankali yasaki hannun NUFAISAT ya tashi da komawa kan kujera hankalinsa tashe.
Lalle Allah shine Allah. Bai tab'a tunanin hakan zata faru dashi arayuwa ba.
Wai ya rayu a ruga. Sannan har kiwo yayi. Sannan yayi Aure har da raban y'ay'a uku...
sannan tunaninsa ya dawo baisan yayi hakan ba.
Wannan kad'ai ya isa mutum ishara...
Sosai yayi nisa cikin tunani. sam baiji abinda NUFAISAT take cemai ba. Naya ya kwantar da hankakinsa..
Sanda tatab'a shi da miqa masa madara me sanyi sannan ya dawo daga duniyar tunanin daya fad'a..
Jiki asanyaye ya karb'i madarar yasha kad'an da tashi da niyarsa nasan ficcewa..
Shan gabansa NUFAISAT tayi da riqe qugu tayimai fari da ido tace dashi.. "Sam bazaka fitta ba saika gayamin me zuciyarka tashirya maka. Dan bamuyi da MUSLEEMA zan gayama kowa ba..
Murmushi yayi da rungumarta yace... "Kinyi kyau sosai matata.. Sannan kinyi arayuwa..
"Ba wannan na tambayeka ba. Kawai kabani amsata.
"Dama part nawa zanje nayi wanka daga nan saina fara shawarar da zuciyar tawa..
"Nifa ban yarda ba. Kawai ka gayamin..
"Wallahi NUFAISAT kina da futuna. To dama zuwa zanyi na kwashe yaran naje asibiti ayimin gwajin jininsu da nawa.
Idan naqara tabbatarwa saina Nazo wajen YAWO na tuhumeta kan meyasa tab'oye min komai tunda farko...
Murmushi NUFAISAT tayi da kallansa tana cewa.. "Gud... naji dad'i sosai. Saidai yau lahadi baku zuwa asibiti kai da doctor Aryan.
"Zan kirasa yanxu muhad'u ai.
"Bara naje na d'auko gyalena to saina rakaka..
Jan hancinta yayi cikin matuqar santa da qaunarta. Yace "idan bake bazan iya rayuwa ba.
Kiss tasakar mai da cewa. "Wayace maka nima idan bakai zan iya rayuwa...
Murmushi ya sakar mata..
Bayan tad'auko gyalan nata direct shashin su MUSLEEMA sukayi...
ADAMS ya qara kallan MUSLEEMA mamaki cike tam azuciyarsa wai ita d'in matarsa ce..
"Kuzo muje kumana rakiyar unguwa..
NUFAISAT ta katse masa tunani da faɗin