Showing 48001 words to 51000 words out of 81675 words

Chapter 17 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

ADAMS ya nufi gidan nasu cikin sauri yana atunanin anya kuwa zancen da yaran suka gayamai gaskiya ne..

Aiko ya tabbatar. Jiyayi kamar yasa ransa ame dan Farin ciki.
Yawo ta kalli ADAMS tace.. "Kaga ikwan Allah ko. Dama na gaya muku kudena biyema y'an asibitin nan wajen haihuwa. A kwai sinadarai namu na gargajiya irinsu ganyayyaki itacuwa ingantattu da muke zuwa daji muke iboma me ciki take sha.
haka zakaga ta haihu sumul da ita. Bata tare da wani ciwo ko kad'an.. Yaranta suzo duniya jikinsu luwai luwai gwanin ban sha'awa dashi.
Murmushi ADAMS yayi baice mata komai ba. Dan yasan Yawo wajen musu idan akan ciki ne. Shi kuma gani yake kamar ya dace idan Mace nada ciki taje doctors su dubata. Saidai yanxu ya qara tabbatarwa Allah ne kawai me karewa.

Har kwana hud'u da haihuwan amma sam yaran basu da kuka basu da wani matsala.
Sai shan nonon uwarsu suke me gard'i da lafiya. Saboda sinadaran da Yawo take bata dan qarama nonon inganci..


Ranar suna raguna uku da shunuwa d'aya aka yankama yaran.
Yawo tace idan bamma Y'ay'an MUSLEEMA ba banga y'ay'an wanda zamma ba.
Dan haka ko d'ari ne ayanka dabbobin arziqinsu ne.
Jin hakan yasa ADAMS murmushi yace mata aa raguna uku shanuwa d'aya sun isa..
Tace to badamuwa.

Y'an tattun suna aka sama yaran kamar... Musu da Aliyu sai qaramarsu Rahma...

Wannan suna ya tara mutane ba d'an kad'an ba.
Saboda bajintar da Yawo tayi asunan bad'an kad'an bane.
Haka shima Adams ana saura kwana biyu suna sanda ya saida saniyarsa irin way'anda Yawo take basa yaba usman kud'in yace dan Allah yaba matarsa tashiga kasuwa takwaso masa rugunan yara da atamfofi masu kyau irin na mejego..

Wannan yasa sunan MUSLEEMA ya zarce dukkan wani sunan yara da akeyi a rugar..

Sunan dai kam ya zama sunan kwatance...
Dan kowa yaci shinkafa da nama san ransa.
Wannan shine kawai abinda akayi asunan kuma ya qayatar ya gamsar da al'umar rugar...

Matar Usman kasance warta doctor itama kamar mijinta data zo sunan sanda takeb'ance da MUSLEEMA ta duba gabanta tatabbatar bata samu qari ba sannan hankalinta ya kwanta..
Saidai tayi mamakin yanda bataje asibiti ko sau d'aya ba Amma cikinta ya rayu da lafiya. Gashi itama da lafiya ga yaranta gwanin ban sha'awa.
Duk da haka sanda tabama yaran kulawa irin tasu ta likitoci.





____________________________
San duniyar nan haka ADAMS ya d'auka ya d'ora kan MUSLEEMA da yaranta..
Yara suna rayuwarsu rayuwa me inganci.
Usman da matarsa yaran sun shiga ransu hakan yasa suke zuwa suke ba yaran kulawa irin tasu ta likitoci acewarsu bai dace su zauna haka ba kulawar likitoci ba...






***************
Ayanxu shekarar yaran biyu da wata d'aya..
Yaran sun taso gwanin ban sha'awa abinsu.
Ga surutu ga wayo..
Idan kagansu Sai kace sunkai shekara uku.
Saboda girmansu da lafiyar da suke tare da ita....
Da kanta MUSLEEMA take kaisu wajen malam jauro d'aukar karatun Alqur'ani me girma.
Zanso gaji yanda suke d'auke komai akansu idan an biya musu..


Yau take Asabar tun safe
MUSLEEMA taji gabanta na fad'uwa haka kawai..
ADAMS na lura da canjin yanayinta dan haka bayan sun idar da karyawa ya kalleta da cewa.. "Na lura yau tunda kika tashi baki da kuzari..
Jan numfashi tayi da kallansa shima tace.. "Eh wallahi. Haka kawai naji gabana na fad'uwa kamar zan rasa wani abu me mahimmanci arayuwata.
"Niko kinga bani jin komai. Dan haka kishare dan ba mamaki ko alkairi ne yake san zuwa gareki.
Murmushi Yawo tayi da cewa.. "Eh nima fa haka nake ji araina haka kamar wani abu zai faru damu..
"Haba Yawo kema da tsufanki zakina fad'in hakan danki tsurar min da mata. Kunga nima fa shuru nayi. Dan Wallahi yanda kukeji haka nima nakeji..
Da marairaicewa cikin shagwab'a MUSLEEMA tace.. "Bana san nayi rashin koma wane irin abu ne haka arayuwata.
Dan Allah mijina katayani da addu'a.
Kama hannunta yayi cikin so da qauna yace. "Baki da matsala da hakan matata.
Fatana yanxu ki kwantar da hankalinki dan ba abinda zaki rasa..
Murmushi kawai tasakar mai.
Yawo ta girgiza kai. Tana tuna wane irin so ADAMS yakema MUSLEEMA ne..
Ahankali tatashi daqer tabar musu wajen. Saboda ciwan da yake damunta na duk jiki. Wanda yake haka ga kowane mutum idan ya d'auko hanyar tsufa.
Ganin hakan yasa ADAMS jan matarsa d'aki dama yaran nasu suna makarantar malam jauro..

Acan uwar d'aga ya ritsata yana cewa.. "Ban tab'a jin muguwar sha'awa irin tayau ba..
Kallansa dayi da muradi tace.. "Nima haka YAYANA..

Sun faranta ran juna kamar bazasu bar juna ba.
Tana qirjinsa yake cewa.. "Maganar gaskiya qanwata ina jin wani iri araina yau kamar yanda kika fad'a d'azu.
Kallansa tayi da Qara shige masa tana me fad'in. "Nidai koma dai miye Allah kabarni da mijina da yarana da kuma kakata..
Shafata yahau yi da yana amsa mata da "amiin..

Lokacin da suka fitto Yawo bata nan da alama ta fitta ne..
Suna jin dad'in yanda suke wanka a tare.
Kuma sun lura kamar idan suka keb'e da juna da ranah Yawo shiga makwafta take..
Hakan ne yake basu damar yin wankan tare da ranar ma

Da gaske Yawo bar musu gidan take..
Saboda tana jin kukan MUSLEEMA idan suka keb'e da juna.
Ta tabbatar ADAMS ya gama samun MUSLEEMAN ne shiyasa koyaushe cikin yimai ihu take.. Ba dare ba ranah..
Toh abin naba Yawo kunya🙈 shiyasa take barin musu gidan. Gwara da daddare tayi bacci wani lokacin bata jinta. Dan idan kaji tajita da daddaran to dama ciwan qafarta ne ya dameta ya hanata bacci shiyasa take jinta. Allah yasa yaran a d'akin Yawon suke kwana ba'a d'akinsu ADAMS d'in ba. Dan inda ace a d'akin su Adams d'in suke kwana ba makawa tashinsu MUSLEEMA zata dingayi da ihun nata idan abin ya ciyota.🙈

Shiko ADAMS tun abin nata na bashi kunya kar Yawo tajiyota har ya cire kunyar ya ajeta gefe tunda ya fuskanci kamar halittartace haka.🤣

Ga ita MUSLEEMAN ko
bata san Ashe Yawo tana jin kukanta da ihunta haka ba. Shiyasa bata tab'a tunanin denawa ba.


Haka suka saka ruwa sukayi wankansu. Wannan ranah duk jikinsu a sanyaye yake. Haka ADAMS ya shafi gefan faskar MUSLEEMA yace.. "Bara naje wajen shanu na duba lafiyarsu na dawo ko.
Kallansa tayi cikin so da qauna tace.. "Ka kula da kanka YAYANA karka bari wani abu yasamar min kai.
"Zan kula miki da kaina qanwata fatan kema kijimin da kanki.
Ahankali tamatsa jikinsa tasakar mai kisa a baki tace.. "Zan kula ma da kaina..
"Kinyi alqawari..
"Nayi maka mijina..
Qara shafar fuskarta yayi da sakar mata murmushi ya fitto daga d'akin..
Yazo zai fitta waje kenan sukaci karo da Yawo. Tace. "Har kafito zaka daji ne.
"Eh amman ina jin yanxu zan dawo dan ina jin kamar zazzab'i ne yake san kamani.
"Toh kadawo kawai ka kwanta mana. Idan kaji dama dama ka fitta anjima.....
Kan ADAMS yayi mata magana saigasu Khalit da Khalil da Rahma sunshigo (dake haka ake kiransu. Wannan ma malam jauro ne yake kirasu da hakan. Wato Musa shine Khalit. Aliyu Kuma Khalil. Shekenan sai Yawo tafara kiransu da hakan shine ya bisu dan Rahma ita ba'a mata wani inkiya ba.)
Wata Rabi ce a makwaftansu take dawowa dasu idan MUSLEEMA takaisu.

Da Farin ciki sosai ADAMS yake d'aukarsu. Idan ya sauke Wannan saiya d'auki wancan.
Suko sai murna suke dan baqaramin San uban nasu suke ba..

Sanda ya koma gidan ya zaunar dasu sannan yama Yawo sallama yana cewa gwara yaje dai ya duba tabbobin yaga ya suke idan yaso ya dawo ya kwantar.... Jin hakan yasa tamai fatan dawowa lafiya....


Saidai ADAMS baiyi nisa a tafiyarsa ba Iro da wasu abokansa uku suka taresa wai yaje inji malam jauro..
Har ADAMS yayi haryar gidan Malam jauro d'in sai Iron ya dakatar dashi wajen cewa ai baya gida kadaixo muje daji acan yake yaje sassaq'o wani magani ne.
Jin hakan yasa ADAMS binsu da zuciya d'aya


Sai tafiya suke cikin daji can Adams yace "Wai har ina malam d'in yake ne.
Shuru sukamai. Ganin hakan saiyaja bakinsa yayi shuru sukaci gaba da tafiya..
Dake Iro tashin wajen ne. Yasan lungu da sak'o na dajin. Dan haka nan kusa suka kusa b'ollowa titi.
Ahankali Iro ya fara dawowa baya da baya dayima d'aya daga cikin abokan nasa nuni da ido wai ya wuccesa. Aiko cikin sauri abokin nasa ya wuccesa saiya kasance yana gabansu su suna bayansa..
Da haka da haka Iro ya koma baya can ya kasance shine a qarshensu suna gaba yana binsu a baya..

Aiko ganin ADAMS ya tattara hankalinsa kawai a gabansa. Sai ko Iro ya d'aga sandarsa sama 🙄 ya sauketa a ƙeyar ADAMS. Saiji kake gubbb😳.....

Ai nan take ADAMS yaji kansa nayi masa hajijiya. Bai samo nutsuwarsa ba Iro ya qara sakar masa wata sandar awajen.. Aiko wannan karan sai zubewa qasa ADAMS yayi warwar alamar sumewa.. Dan bugu ne na shammata. Kuma na mugunta. Sannan nasan illatarwa..

Dariya Iro yayi da cewa.. "Dama nayi ma ZUCIYATA Alqawari bazan tab'a garinka kaci gaba da rayuwa da MUSLEEMA ina gani ba.
Nayi alqawarin saina maka illah. To gashi ka gani...

Sanda ya gama duk iskancinsa sannan suka kinkimesa sukayi titin dashi... Basu qarasa titin ba suka ajiyesa dan hutawa
Suna cikin hutawar ne zai sukaga wata mota tatsaya wani na miji ya fitto daga motar da mata biyu suna masu duba motar...
Can sai sukaga matan sun fara nufo inda suke da gorar swan water a hannunsu.
Kan suyi wani qoqari na b'oye ADAMS kar matan su gansa saiya kasance har sun iso wajen nasu. Lokacin Yayi daidai da rungume Adams da Iro Yayi
D'aya daga cikin matan tace dan Allah ku temaka mana da ruwa musama motarmu..
Kan subata amsa d'ayar tabigi kafad'ar wacce tayi maganar tace.. "Kinga salma wannan mutumin baya miki kama da LEEKITAN da yake duba momy wanda take gaya mana ya b'ata shekarun baya...
Qura ma ADAMS ido wacce aka kira da salma tayi. Can tace. Kuma fa suna kama. Saidai wannan yad'anyi baqi da rama.
"Nima abinda magani kenan. Waccan yafi wannan fari da gogaggiyar fata Wannan kuma Yayi baqi da siranta.. D'ayar tafad'i hakan danuna tabbaci
Salman tace... "Niko mema sunan wancan d'in...
"Ni dai nafi saninsa da LEEKITAN ZUCHIYA kamar yanda momy take fad'a yafi duba ZUCIYATA akan kowa b'angare na jiki. Bacin hakan bansan ainiyin sunansa ba. Kinga munemi abinda zamu nema gunsu lokaci na tafiya.
Jan numfashi salman tayi da qara kallansu tace.. "Dan Allah kuna da ruwa..
Girgiza mata kai iro yayi alamar basu dashi.
"Toh yanxu a ina kuke ganin zamu samu
"Gaskiya bamu sani ba. D'aya daga cikin abokan Iro yace da ita hakan
Ganin hakan sai suka tafi dan su gayama saurayin da suka fitto tare dashi daga cikin motar wanda ya bud'e murfin gaban motar yana dubawa.
Ahankali ya kallesu yace dasu aina samu ruwan. Sukace a'ina ya samu. Nan yake gaya musu Ashe yana dashi a bayan but na ledar pure water. Sukace toh yanxu gyaran me yakeyi. Yace kawai yana dad'a duba motar ne bawai badan tana da wata matsala ba. Jin hakan sai yasa suka shige cikin motar shima ya rufe murfin gaban motar yashiga ciki sukayi gaba abinsu..

Iro ya kalli abokansa yace "Yanxu ya zamuyi dashi ne.
"Kawai mubarshi anan.. Inji wani daga cikinsu.
Iro yace.. "Kai baka da kai. Idan muka barshi anan wani na temaka masa ya farfad'o zai iya gaya masa inda yake. Kaga shikenan ya qara dawo mana ruga kenan. Kawai mu jira wata motar Lodi wacce zata gari me nisa saimu biya direban yakaishi can. Idan ya tashi duk wanda zai gayama daga Rugar malam jauro yake baza'a kallesa ba. Dan ba wanda ya Santa a garin. Kunga shikenan zaiyi hakuri ya kama wata rayuwa. Ni kuma na aure MUSLEEMA..
Sun yarda da shawarar tasa..
Dan haka suka zauna awajen sunata hirarrakinsu. Suna kallan motoci na wuccewa daga nesa. Tunda su motar Lodi suke nema tazo..🤔
Suna nan a haka saiga wani me motar Lodi zai wucce.. Ai da sauri Iro yaje ya taresa.
Direban ya zaci kayansa ne wani ya kunce ya fad'i. Saida ya tsaya yaga tsab'anin hakan
D'an tsohu ne direban. Irin tsofaffin y'an iskan nan. Dan kana masa kallo d'aya zaka san d'an bariki ne.
Gashi ya bugu alamar yasha kwaya tamai karo kamar yanda suka saba sha.
Da wani yanayi ya kalli Iro yace.. "Kai Yaro menene dalikinka na tareni..
Iro ya kalli bayan motarsa da take abud'e hanhai kamar ta d'aukar gawa. Sai kullun kayayyaki da suke cikin buhu burjik alamar lodi. Saiya dawo da kallansa garesa Yace.. "Dan Allah wane gari zaka.
Direban yace.. "KANO na nufa...
Da sauri iro yace.. "Dama ko wani d'an uwanmu ne zashi KANON gashi can. Dan Allah sai musamaka shi abaya cikin kayanka. Kana zuwa saika saukesa..
Direban ya kalli Iro a wulaqance yace. "Ban gane kusamin shi cikin kayana kamar wani kayan wanke ba. Shi bashi da rai ne daba zai hau da kansa ba sai kun sashi...
"aa ba wai haka bane yana da ciwan bacci ne. Yanxu baccin yayi.. Ga wannan dan Allah katemakemu musa maka shi.. Iro ya fad'i hakan da miqara masa kud'i har naira dubu uku..
Kunsan direbobin nan da san kud'i. Bare wannan dayake a make. Ainan da nan ya amsha kud'in yana cewa kusashi.
Nan take Iro yakira abokansa dasu tawo da ADAMS d'in.
Cikin sauri ko suka kinkimosa suka kawosa nan.
Haka suka temaka ma iro suka sashi cikin kayan lodin nan cikin hikima wanda kana gani zaka zaci bacci ne ya d'aukesa. Dan sun ajiyesa da tsari..

Suna gama sashi suka cema direban sun sashi. Nan ko yaja motar shi abinsa.
Iro da abokansa suka sheqe da dariya suka koma cikin dajin dan nufar Rugarsu...



Lokaci lokaci sojoji masu tsaran hanya suka cema direban daya d'auki ADAMS d'in.. Shiko wannan baccinsa yake abinsa.. Direban ya kan basu amsa da cewa. Eh yayi bacci..

Lokacin dayaga yafara nufo kano tsayawa yayi anan d'an wani daji ya fitto ya karema Adams kallo yadai tabbatar babu numfashi atare dashi. Aiko saiya saukesa ya barsa nan bakin titi yana cewa "Y'an iska qilama matacce suka samin dan nashiga uku.
Haka direban nan yayi gaba abinsa yabar Adams anan yashe...

Minto goma tsakani wani Alhaji yazo wucce da motarsa me d'an kyau haka shi da yaransa da alama suna kan hanyarsu ta nufar wani gari ne. Sai kawai yaga ADAMS a yashe kan titi.
Nan ya yatsaida motar tashi suka fito shi da d'ansa dan ganin abin mamakin waye haka akan titi..
Suna zuwa alhajin nan ya qarema ADAMS kallo ya tabbatar lalle wannan idan ba doctor ADAMS bane LEEKITAN ZUCHIYA ya tabbatar d'an uwansa ne.
Dan haka yasa d'ansa ya temaka mishi su sashi cikin motarsu. Suna mamakin ya akayi yake kwance haka a gefan titi inda babu kowa agun haka. da alamama ko rai yayi halinsa.
Fatansu dai yanxu su isa garin nasu na kaduna su kaishi asibiti suji yana da rai koko baya dashi dan sunji jikinsa bai sake irin na mamaci ba ..

Cikin ikwan Allah sun iso garin kaduna lafiya basu zarce ako Ina ba sai'a wani asibiti wanda ya amsa sunansa new yan hospital.. Anan masana sirrin lafiya suka shiga caje ADAMS. Nanko suka gano yana da matsala babba. Suna tunanin tunaninsa ya tab'a d'aukewa a baya. Yanxu suna fatan idan ya tashi farfad'owar tunanin nasa ya daidaita..

Jin hakan da alhajin yayi sai kawai ya kira Dadyn ADAMS a waya dake amininsa ne yace mai dan Allah yazo nan asibitin yaga wani mutum me kama da ADAMS nasu. Shifa yana ginin kamar Adams ne mah.
Ai Dady najin batun abokin nasa ya tashi zunb'ur daga falansa ya saka takalmi ko bin kan d'aya daga cikin matan nasa baiyi ba ya ficce daga gidan sai asibitin...
Dady Suma yayi dayaga ADAMS. Dan babu wani canji da ADAMS zai samu a rayuwarsa wanda zaisa Dady ya kasa gane shi..

Bayan ya farfad'o kuka ya sake yana me hangen ADAMS ta jikin window saboda likitocin sunqi yarda ya qara zuwa ga ADAMS a karo na biyu dan karya qara sumewa..
Dady yasha kuka dan yacire tsammanin qara ganin ADAMS d'insa...

Dady ya tabbatar ma da abokin nasa Adams ne ba wani ba..
Anan abokin nasa yake basa labarin yanda akayi yaga ADAMS d'in. Da bayanan da likitoci suka fad'a akansa..
Jan numfashi Dady yayi. Ya tabbatar Allah shine me iko.
Dama saidai idan ADAMS baya cikin tunanin shine zai iya d'aukar way'annan shekaru batare da yayi waiwayen gida ba...
Anan Dady yakira su Ammi ya gaya musu Amman Yace karsu gayama su NUFAISAT har saiya farfad'o.. Ammin Adams bata tab'a jin labari me dad'i irin nayau ba...
Jin dad'in nata yaqara tabbatuwa ne lokacin data hangi ADAMS d'in tajikin window ita da Hajjiya Rukayyat....




🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻
Me karatu idan kayi tunani ya kamata kasan koda ADAMS ya farfad'o bazai iya tuna wata rayuwa yayi da wata MUSLEEMA ba..
Koda zai tuna wani abu tunanin zai dinga masa wasa ne kamar yayi mafarki ne ya tashi. Kuma mafarkin bazai nuna mishi komai yanda zai ankare ba.

Sannan kunsan ambar baya da q'ura tafannin su MUSLEEMA..

Kuci gaba da bina a LEEKITAN ZUCHIYA inda zamuga wacece cikin matan Adams take da mallakin wannan sunan abakinta na LEEKITAN ZUCHIYA ina zata ganshi ya gyara tunaninta..🤫
[7/17, 3:49 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 21☆


Zama Amminsa tayi tana me godema Allah daya bayyana mata d'an nata..

Hajjiya Rukayyat ko haka kawai sai taji bataji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login