Showing 60001 words to 63000 words out of 81675 words

Chapter 21 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

duk abinda yake buqata dancin.
Sai ya kirata yana tambayarta a ina take kwana.
Kallansa tayi dakyau tana nazarinsa can tace mai miye had'insa da inda taje kwana
Murmushi yayi mata idansa qir akan qirjinta yake bata da cewa. Kawai yana san sani ne. Idan bazata gaya masa ba yaje gun Yalwa tagayamai.
Sanda ta galla masa wata muguwar harara kana tace mai ashagwan taje kwana.
Yaji dad'in hakan sosai dan b'aro b'aro taga ya saki dariya yace mata zai dawo wajenta anjima.
Bata gane me yake nufi dazai dawo d'inba haka tashige abinta ta barsa.

YAWO jikinta kwana biyu babu lafiya komai daurewa kawai takeyi saboda aikin datake bana wasa bane
Hakan yasa yau qarfe goma:pm ta kwanta.
MUSLEEMA ko sai sha d'aya da rabi tasamu kanta.

Qarfe d'aya na dare kowa yayi bacci cikinsu.
Almajiran suna tacan waje suna baccinsu Ammanfa ahakan gadi sukema Yalwa na kaya.
Su Yawo ko suna tacan ciki.
Amma dan tabar shed'ananci haka shegen mutumin nan ya ratsa kowa yaje har inda MUSLEEMA take yahau shafata.
Dake baccin ya fara cin qarfinta sam bata fara jin wani abu ajikinta ba.
Motsinsa ne ya Rahma tashi dake tana kusa da MUSLEEMAN ganin mutumin saita hau jan rigarsa tana mama kitashi ga wani yana tab'aki
Sam MUSLEEMA bataji ba.
Sanda shegen yayi nasarar damke na fulaninta ya fara cirosu tare da daneta iyakar qarfinsa sannan MUSLEEMA tafarka da wata shegiyar qara.
Ai sanda dukkansu suka farka.
Ganin abinda yake faruwa sai Matan sukaja tsaki kowaccensu takoma baccinta dan Wannan su aganinsu ba bakwan lamari bane.
Mazan dake wajen ko tunaninsu d'aya daga cikinsu ne ya afkawa MUSLEEMAN kamar yanda idan wani cikinsu yaji lalurarsa yake afkawa duk wacce yaso amatan kuma komin ihunki saiya biya buqatarsa sannan zai barki.
Toh tunaninsu ko hakan ne. Duk da kowa acikinsu idansa akanta yake. Ganin Yanxu tafara bunqarowa.

YAWO taya MUSLEEMA ihun tayi. Amma sai taga kowa cikinsu ya sharesu.
Nan tanufi inda kayan aikin Yalwa suke ta rarumo muciya aiko tasauke masa a baya.
Lokacin bakinsa nakan san Shiga kan na fulaninta.
Aiko jin hakan afurgice ya saketa YAWO ta qara shinfid'a mai a kafad'a ainan ya taso da zafin nama ya mangare YAWON tazube qasa sannan ya taka hannunta da qarfin tsiya ya fuzze muciyar. Sannan ya qara nufar MUSLEEMA ganga ganga wacce tayi nasarar gyara rigarta. Aiko nan ya kwasheta abinka da ririya. Nan tazube qasa tim. yako bita ruf ya rufeta kamar matarsa yana kici kicin lalle saiya cinmma burinsa akanta.
Kuka wiwi MUSLEEMA take yi tana yimai ihu da yakushinsa da cizansa amma ina burinsa dai yacimma burinsa.

Daqer YAWO ta qara tashi kasan cewar ba qaramar mangare yayi mata ba. Haka tadaure taje ta qara rarumo farantin tangaras ta rutsa masa aka....
Wannan karan yayi qarya wajen cigaba da aiwatar da kudirin nasa Dan haka ba shiri ya tashi ganin yanda kansa yake fitar da jini.
Sanda ya qara mangare YAWO kana ya ficce daga shagwan..
Sai a lokacin almajiran suka gane ba d'aya daga cikinsu bane.

Matan ko mita suka dingama MUSLEEMA wai tashiga hakk'insu ta hanasu bacci miye danta barshi yayi amfani da ita. Ai wannan ba wani abu bane. Amma dan tsabar mugunta ta wani hanasu bacci bayan ba lokaci suke samu nayin baccin ba.
Dan wasu acikinsu da qarfe hud'u na asuba suke tashi d'ora abincin safe.
Tomiye danta barsa yayi abin aina d'an wani lokaci ne.
Ba kunyar YAWO ba jin tsoran Allah haka suka dingama MUSLEEMA Wannan masifar..

MUSLEEMA ko tattara kan y'ay'anta tayi ta rungumesu tana kuka suna tayata abin tausayi.
Itama Yawon hawaye takeyi
Wannan dare dai basu iya rintsawa ba.

Washe gari da kuka MUSLEEMA tace da YAWO.. "Dan Allah yawo mubar wajen nan. Dan suna shirin ketamin hakk'in aureta. Sun kulla aniyar cin mutuncin aurena. Zasu wulaqanta min igiyata.
Wallahi YAWO ina san mijina ina san ya ganni batare da wani yayi masa illa cikin Soyayyarsa ba.
Kimin rai ki amincemin mubar wajen.
"Toya zanyi MUSLEEMA. Ai barin wajen nan ya zamam mana dole dan zan iya jure wahala amma bazan iya jure aci mutuncinki ba.
Jin hakan yasa hankalin MUSLEEMA kwanciya.

Yalwa na fitowa qarfe takwas na safen wata qawarta Hajjiya batula tazo gareta karb'ar kud'inta da wata mata takawo mata jiya danta ajiye mata.
Nan Hajjiya Batula tayi ido hud'u dasu Khalit da Khalil & Rahma.
Nan tagigice ta kalli Yalwa daniyar cewa wani abu saiga MUSLEEMA da YAWO sun iso wajen.
MUSLEEMA ta durqusa da cewa. "Dan Allah Aunty Yalwa kimana hakuri zamubar aiki anan. Saboda abinda ya faru jiya damu... Nan YAWO takwashe komai tagaya mata. Ta qara da cewa "Kiyi hak'uri Yalwa ki yafe mana kud'in da kike binmu bashi wanda bamu qarasa aikin dan biyanki ba.
Nan hankalin Yalwa ya tashi. Danta gane kamar yanda tayi harsashe idan tamallaki MUSLEEMA zata qara samun kwastamomi. Toh haka abin ya kasance. Dan MUSLEEMA nafara bama munan nata abinci saita lura wasunsu jikin MUSLEEMAN ne yake sasu dawowa washe gari ko basuyi niyar dawowa ba. Tunaninsu ko zasu cimma burinsu.
To tayaya zatayi ta rabu dasu haka cikin sauqi. Dan haka cikin b'acin rai ta kalli yawo dakyau tace... "Ke tsohuwa ba inda zaku har sai kunyi min aikin kud'ina. Dan ba haka mukayi daku ba. Tayaya zan ciyar daku da way'ancan yaran naku masu cin tsiya sannan na baku aran kud'i yanxu kuzo kuce min wai inyi hak'uri zakubar aiki nayafe muku kud'ina. To wallahi baku isa ba. Dan sai kunbiyani kud'ina. Saboda lokacin dake kikazo kikamin y'ar murya akan na ranta miki kud'i zakiba MUSLEEMA taje can gari nemo mijinta ba wanda yasani dan haka babu batun hak'uri ko yafiya anan zaku zauna kuyimin aikin kud'ina iyeeee...

Galla mata harara MUSLEEMA tayi da cewa. "Lallema matar nan baki da imani. Kina gani za'aci mutuncin aure. Za'aci mutuncin soyayyata. za'aci mutuncin shinfid'ar mijina amma kike magana akan wai saimun zauna hakan tafaru dan kawai munci kud'inki wanda bai taka kara ya karya ba..
Kallemu sama daga qasa muba matsiyata bane. Qaddara qaddara qaddara ce tasa kika gammu nan cikin garinku gabanki muna sunkuyar dakai dan muyi miki aiki kibamu abin zamuci. Banda haka ba abinda zaisa muyima wata mata kamarki aikatau.
Dan haka kwantar da hankalinki ina dai dubu d'aya ce Yanxu saura kud'in da kike binmu. Zan biyaki kafin fad'uwar rana kwana ne dai bazamu qarayi cikin wannan akurkin naki ba...

Ba Yalwa ba hatta YAWO sanda tayi mamakin maganar da MUSLEEMA tagayama Yalwan. Dan aqalla Yalwa ta haifi MUSLEEMA.

Yalwa gyad'a kai tayi tace.. "Hmm d'an Adam butulu. Tokije duk inda zaki kije ki nemomin kud'ina sannan kizo ki kwashi y'ay'anki da kakarki kubarmin akurkin nawa tunda ke matsiyaciya ce.

Girgiza kai Hajjiya batula tayi cikin jin dad'in faruwar yanayin. Yanxu take da damar dazata cuka maganarta ko zatayi tasiri.
Dan haka salta kalli MUSLEEMA tace "Y'ata zonan ba haka za'ayi ba.
Zo nan kigayamin wacece ke...
Da kuka MUSLEEMA ta qarasa gareta takwashe komai tagaya mata.
Duk da cewar Hajjiya Batula shed'aniya ce sanda ta tausayama MUSLEEMA. Saidai duk da haka zataso burinta ya cika akan yaran MUSLEEMAN dan haka saita kalli YAWO tace...
"Ayya ai mutanan kirki sun mutu a garin Kano. Dakin sani daba nan kike nufo ba.
Sannan gaskiya Baba kinyi kuskuran bama shi LEEKITAN ZUCHIYAN jikarki MUSLEEMA.
Yanxu shawarar dazan baku d'ayace. Shine zai iya yuhuwa shi direban ba garin kano ya kawosa ba.
Dan haka ku canja gari ko Allah zaisa ku dace.
Amma idan kunga zaku iya bina ni ina garin KADUNA ne da zama. Kuma kunga zai iya yuhuwa direban garin kaduna yayi dashi ba nan garin kano ba.
Tunda kunga duk hanyar d'aya ce.
Idan kun yarda dama ni nazo nan Kano siyan kaya ne jiya. Idan kunga ba damuwa kuzo muje garin Kadunan kuyi sati d'aya a gidan nawa lokacin kun huta. daga nan saiku fara neman LEEKITAN ZUCHIYAN. Tunda kunga likitocin zuciya sunfi yawa a garin Kaduna. Ina kyautata zatan zaku samesa acan d'in
Kunga shikenan saina bama Yalwa kud'inta wannan na bata fisabidillahi ne na temakeku.
Saidai zaku dinga min aikin gidana har lokacin daza kuga LEEKITAN ZUCHIYAN shikenan fa idan kun amince. Danni nayi niyar temakwanku ne tsakani da Allah ganin likitocin zuciya sunfi yawa a garin na Kaduna...
Ai dajin hakan MUSLEEMA tace. "Na amince Aunty Allah yasaka. Haka YAWO mah tace ta amince.
Jan numfashi Hajjiya Batula tayi da cewa. "To kuje ku had'a kayanku da kan yaran ga motata can kusaka kayanku kafin na gama da Yalwan.
Aiko kicin jin dad'i suka koma ciki dan aiwatar da abinda tace musu.

Yalwa takalli Hajjiya Batula tace "Nasan dai badan Allah kike san zuwa dasu garin na Kaduna ba.
Tace "Eh magana ta gaskiya naga yaran MUSLEEMAN zasuyi daraja da yawa ne.
Sannan daga ganinsu basu da hankali.
Banda haka me zaisa kakar tata tabama wanda bata san daga Inda ya fitoba jikarta. Sannan dan rashin dabara sukama suzo garin kano batare da sunsan inda zasu dosa ba.
Kawai magana ta gaskiya anan naga zanyi kud'i sosai da yaran nan idan na siyarma da Ahaji bala su.
Murmushin mugunta Yalwa tayi da cewa.. "Dan Allah albarkacin rashin kunyar da MUSLEEMAN tamin ina rokwanki da ALLAH kuna zuwa kisa a fiffille musu kai🤣
Dariya Hajjiya Batula tayi da fad'in.. "Kai Yalwa baki da mutunci. Ai ki kwantar da hankalinki tunda sukacemin su fulani ne naji na tsanesu. Kin manta kishiyata bafulatanace ta kwacemin miji. Aitun daga lokacin natsani duk wani bafulatan mutum dan babu mugu kamarsa.
Yanxu dai ga dubu ishirin kiyi harkar gabanki da ita.
Idan mun had'u na qara miki wani abun koda yake kema ai kin kusa fad'owa hannu adinga damawa dake.
Yalwa tace. "Eh duk da haka wallahi baki isa ba. Koki bani duba hamshin ko yanxu na tona miki asiri agunsu.
Sanin halinta shiyasa Hajjiya Batula qara mata sukayi sallama.

Motar tata kad'al idan ka kalla ta'isheka tabbatarwa Hajjiyan me kud'ice.

Cewa tayi MUSLEEMA takoma gaba tabar YAWO da yaran a baya zasufi sakewa.
Aiko hakan MUSLEEMA tayi.
Hajjiya Batulan tashiga mazaunin direba tajasu da gaske garin na kaduna tanufa dan acan d'in gidan nata yake...



By AUNTYN LUV😍😍😍
[7/26, 1:00 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R ®
http://hausafulaniwriters.blogspot.com
” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 24☆

Sun d'an sha tafiya sannan suka iso wani katafaran gida.
Tun daga bakin get YAWO da MUSLEEMA sukasan hajjiyan tajik'u da naira.
Nan ma'akatanta biyu mata suka hau zube mata suna masu yimata Barka da dawowa.
Tunda MUSLEEMA da YAWO suke aduniya basu tab'a zatan zasu Shiga gida irin wannan ba. Duk da cewa bawai gidan ya taka kara ya karya bane. aa gida ne dai me kyau amma ko kwatan kwatan kyau baiyiba a irin jerin gidajen masu kud'i.

Yanxu dai gasu afalan gidan sai raba ido suke inda ɗaya daga cikin masu aikin takawo musu abinci me rai da lafiya.
Shinkaface da miya da had'in salat da nama manya manya. Ga drink da ruwa susha duk wanda sukaga dama.

Haka sukayi nak Hajjiya Batula takallesu da murmushi tace bara tayi musu jagora I zuwa inda zasu dinga kwana.
Da murmushin godiya sukabi bayanta har takaisu wani d'aki me kyau da tsari.
Gadone lafiyayye ad'akin da durowarsa sai toilet. d'akin dai ba lefi yayi kama dana saukar baqi.

Haka su MUSLEEMA sukayi sallah tayima yaranta wanka da canja musu kaya suka d'an kwanta saboda gajiya.
Basu suka tashi ba saican kusan magrib. Haka sukayi salati da godema Allah daya kawosu hannun wannan mata me kirki. Dan tunda suka baro Rugar malam jauro basu tab'a baccin kwanciyar hankali cikin lokaci kad'an haka ba.

Haka da sukayi sallar isha haka me aikin nan taqara basu abinci har cikin d'akin da suke.
Sukaci suka qoshi kamar d'azu suka qara meqewa suka kwanta.

Sam Hajjiya Batula Bata bi takan su cikin daran da udirinta ba. Saboda tana so susake da ita tayanda zata aiwatar da udirin nata da hikima.
Haka yasa tadinga kyautata musu. Ba dare ba ranah harna tsawan sati d'aya kamar yanda tagaya musu saisun huta saboda jikin YAWO da bata jin daɗinsa kana saisu fara fitta neman ADAMS dan idan suka fitta ne take da damar cimma burinta akan yaran.

Ayau d'inne kwanansu bakwai dan haka sai murna Hajjiyan take tana Allah Allah gobe tayi dan agoben ne su MUSLEEMA da YAWO zasu fara fitta neman ADAMS LEEKITAN ZUCHIYAN nasu.

Hafsat sunan d'aya daga cikin y'an aikin Hajjiya Batula itace taji tausayin su MUSLEEMA data nemi yau subata labarinsu sukako bata.

Taji tausayinsu matuqa musamman ma datasan k'udirin Hajjiya Batula akansu.
Saboda itace idan hakan tafaru ma'ana idan Hajjiyan tazo da mutane irinsu irin hakan. itace take jan hankalin yaran takaisu can bayan gidan Hajjiyan wajen wata k'ofa da aka fitar da yaran da Hajjiya Batulan take siyarwa. Sai wani alhaji bala yasa yaran amota yayi gaba dasu. Shikenan duk bala'in duniya da za'ayi yaranka sun tafi kenan. Dan ita Hajjiya Batula zata nuna ai tana tare daku masu y'ay'an. Kawai dai yaran sun fitta waje ne wasu suka sacesu. Dama garin Kaduna ai garin mayune.🤪 yanxu ne dai abin yayi sauqi.

Ahankali Hafsat ta kalli YAWO da MUSLEEMA tace dasu.. "Zan gaya muku wata gaskiya saboda yanda naji tausayinku araina. Hak'ik'a da kunsan wajen wacce kuke hannunta ayanzu. da baku yarda kun biyota ba.
Hajjiya Batula wata shahararriyar shed'aniya ce. Bata da aiki saina sato yaran mutane tana saidama manyan mutane suna kud'i dasu.
Ta gayamin gobe zaku fara fitta neman LEEKITAN ZUCHIYA dan haka agoben naja hankalin yaranki ke MUSLEEMA nakaisu wajen Alhaji bala.
Idan kuka dawo sai nace muku ai kuna fitta yaran suka saka kuka shine na bud'e musu get suka biyo bayanku dan atunanina tunda naga bakuyi nisa ba nasan zakuji motsinsu a bayanku. Kai batama yanda za'ayi kuna fitta na bud'e musu get kuce baku gansu ba..

Idan kunqi gamsuwa da wannan hujjar Hajjiya Batula tasan abubuwan da zata gaya muku dole sai kun yarda kun gamsu yaranku b'ata sukayi. Sannan zata b'ata muku tunani wajen yad'awa gidajen rediyo da talabijin wajen cikiya sam bazaku kawo cewar itace tasace muku yara ba.
Idanfa kuncire zoton ba itace tasace muku y'ay'aba. Idanko kunsaka mata gaba kan itace tasace muku y'ay'a Wallahi makaku zatayi agun bokanta ya rufe muku baki.

Waro ido waje😳 MUSLEEMA tayi jin abinda Hafsat ke faɗi.
Ai ba shiri tararumo yaranta ta rungumesu cikin matuqar tsoro kamar ance mata yanxu ne za'a rabata da yaran.

Cikin kuka ta kalli Hafsat d'in tace.. "Yanxu ya za'ayi mu ficce daga gidan nan. Wallahi ina san yara na ina san yaruwa dasu ina san ubansu ya gansu ina san rayuwa dasu da ubansu.😭
Jan numfashi Hafsat tayi da cewa. "Agaskiya yanxu kuna cikin bala'i. Saboda yanxu kuna tashi kuna cewa zaku fitta daga gidan nan da yaran nan wannan saurayin me bama fulawa ruwa bazai tab'a barinku kufitta ba. Dan yasan nufin Hajjiya akanku.
Nan zaiyi babakere a get yace saiya kira Hajjiya idan tace abarku ku ficce toh. Idan yaji sab'anin hakan bazai barku ba.
Kuma Hajjiyan na zuwa farko tambayarku zata farayi mezaisaku tafiya batare dakun gaya mata ba.
Daga lokacin da kuka fara mata kame kame daga wannan lokacin kunjefamu nida abokiyar aikina a bala'a.
Saboda zatace mungaya muku wani abu Wallahi daga yau mumbar numfashi aduniya. Dan kashemu zatasa ayi.
Saboda da mu uku ne masuyi mata aikin. Sai d'aya data gane me take aikatawa saita gudu garinsu dan acewarta a imani irin nata babban kuskure ne dasa hannunta adinga kashe yaran mutane.
Wallahi ina gaya muku har garinsu Hajjiya Batula tasa wasu sukaje suka kashe Balkisu bazamu tab'a mantawa ba dan agabanmu tayi waya tana jinjinama way'anda sukayi kisan. Sannan taja kunnanmu wai muma idan muka fad'ama wani abun da takeyi bama muba har iyayenmu saitaga bayansu..

Wallahi nima raina basan wannan aikin yake ba. Lokuta da dama idan ina aikatawa kuka nakeyi cikin dare kan Allah ya fitar dani daga gidan nan lafiya😭
Dan ni aikin su wanke wanke nazo mata kuma haka iyayena suka turoni nayi. Saidai basu san abinda nake aikatawa ba. Hafsat takai qarshen zancenta da zubda hawaye

Goge gumi YAWO tayi da tashi arikice take cewa. "Bar kuka y'arnan yanxu ba lokacin kuka bane. Innalillahiwainna'ilaihirraji'un.
Wannan ba gidan zama bane. Keko yarinya meyasa baki fad'in mana hakan tuntuni ba.
Goge hawayenta Hafsat tayi da cewa.. "Kwantar da hankalinki YAWO zan fitar daku daga gidan nan ta k'ofar da ake fitta da yaran da take satowa. Amman sai cikin dare yayin da qafa ta d'auke.
Dafatan kingane.
"Nagane y'ar nan.

"Toh yanxu kusake karku nuna kunsan wani abu bare tagane.
"Insha Allah bazamu nuna wani abu wanda zaisa ta ankare damu ba. MUSLEEMA tagaya mata hakan da qara qanqame yaranta.

Godiya sosai YAWO tama Hafsat. Kana Hafsat d'in ta fitta daga d'akin nasu cikin sand'a takoma nasu. Kasancewar tara har da rabi tayi:pm.

Su MUSLEEMA ko sam basu kwantar da haqarqarinsu ba. Dan tsoro ya cika zuciyarsu. Haka suka had'a kayansu gefe d'aya jira kawai suke dare yayi Hafsat tayi musu dagoran fitta.

Har qarfe biyu na daran idansu qir yake. Rahma na bayan yawo. Yayin da Khalil yake bayan MUSLEEMA. Haka d'auki Khalit ma tarungume duk da sun fara nauyi da wayo. ita dai awannan lokacin bataji nauyinsu ba.
Aiko Ahankali Hafsat tatuto ƙofar tasu tayi musu nuna da hannunta su biyota.
Cikin sanda haka Allah ya basu sa'a suka ficce ta k'ofar da Hafsat tagaya musu.
Sanda suka fitta. YAWO takama hannun Hafsat tace "Yanxu bazakizo mu gudu dake ba.
Murmushi Hafsat d'in tayi da cewa. "Kiyi hakuri YAWO nafiki san nabar gidan nan. Ina san iyayena araye wannan yasa nake har yanxu agidan. Indai addu'a na magani insha Allah zan fitta daga gidan.

"Tome yasa bazaku kai qararta gun hukuma ba. MUSLEEMA tace da Hafsan hakan
Murmushi Hafsan tayi da bata amsa da.. "Wata rana wani mutum ya tab'a zuwa da y'an sanda yace tasace miki d'a. Haka tarufe idanta tace ita bata sace mishi d'a ba.
In takaice muku tunda tamaka mutumin akotu wai yayi mata qage da sharri akan abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login