Showing 21001 words to 24000 words out of 81675 words

Chapter 8 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

jiya Marwanatu y'ar aikinta tagaya mata kamar maman TAUDHAT tana taro. Sai momyn take ce mata ba yanda za'ayi maman TAUDHAT tayi wani taro batare data gaya mata ba. Saboda ko babu komai ai akwai hakk'in makwaftaka da mutunci.. Qila dai ko qawayen TAUDHAT ne suke kawo mata ziyara.

Tuno hakan da mommy d'in tayi sai yasa ranta b'ata taga kamar abinda maman TAUDHAT d'in tayi mata kamar bai dace ba. Idan tayi duba da irin zaman amanar dake tsakaninsu. Hmm mutum kenan.

NUFAISAT ko bayan ta gayama mommy d'in tasu kira Zainab yayarta tayi itama ta gaya mata komai
Wannan karan taga tashin hankalin Zainab d'in. Dan ce mata tayi gobe itama zata gida su had'u acan.
Toh NUFAISAT tace mata da kashe wayan.
Sanda tayi sallah raka'a biyu taroki Allah daya sassauta mata lamarin sannan tasamu nutsuwa.
Kiran asiya tayi tace taje babban falo ta kwaso kayan breakfast d'in datayi d'azu taba masu so takai yakan kitchen dan Allah ta wankesu.
Cikin ladabi ta amsa mata da toh.



Sai wajen qarfe Tara da rabi na dare Adams ya dawo gidan. Saboda bai tashi da wuri a asibitin nasu. Sannan ya biya gun iyayansa ya gaishesu kamar yanda ya saba. Koda ya murd'a kofar NUFAISAT akulle yajita. Haka daya duba tacikin babban falan nasu ma tasaka key
Dan haka murmushi yayi kawai dajin rashin jin dad'i aransa dan wallahi ya dawo da muradin San ganinta da sakawa aransa sai sun daidaita shi da ita cikin daran nan. Dan bai saba fad'a da itaba. Jinsa kawai yake wani iri haka. Zama yayi afalan ya dinga kiranta bata d'auka ba. Haka yayi hakuri dayin part d'insa yayi wanka da canja kaya ya nufi part d'in TAUDHAT
Ba lefi shashin Nata yana tashin qamshi amman baiji kamshin ya ratsa ba kamar yanda yake jin na NUFAISAT
Anan falan ya tarar da ita tana kallo hankali kwance. Aiko tana ganinsa tatashi da tsayawa dana sakar mai murmushi cikin nuna jin dad'inta da ganinsa da tayi.
K'arasowa yayi gareta da rungumarta yace... "Nayi farin ciki da ganinki cikin kwanciyar hankali
Qara kusanta kanta garesa tayi da cewa.. "Nafi kowace mace farin ciki awannan lokacin saboda naga mijina ya dawo gida cikin k'oshin lafiya
"Gaskiya na dawo cikin k'oshin lafiya ammafa Zuciyata babu dad'i.
Nan take tazare jikinta daga nasa tace.. "Ayya.. Har yanzu Aunty NUFAISAT bata gane qaddarace ta had'ani dakai ba.
"aa bance miki. Kawai ki share zancen nan. Komai zai tafi daidai insha Allah.
D'an b'ata fuska tayi alamun nuna damuwa. Ganin hakan da yayi saiya qara janta jikinsa da cigaba da cewa. Ban yarje miki kisaka wannan lamarin cikin ranki ba. Saboda bana san natsinci kaina cikin matsala biyu gatata gataki. Dan Allah ki sake nasamu nutsuwa agunki. danna tabbatar natamma na d'an wani lokaci ne..
Jin hakan sai yasa TAUDHAT sakin murmushi tace.. "Muje dining kaci abincin dana girkama. "Kamar ko kinsan tun break d'in danayi d'azu banci komai ba. Saidai kamar bai dace kifara girki tun yanxu ba.
"Duk abinda zanyi wanda zai zama farin ciki agareka bana duba dacewa. Kawai Zuciyata gaya min take nayi shi.
Gaskiya yaji dad'in amsar data bashi hakan yasa ya kama hannunta sukayi dining d'in yana me gaya mata suna ci zasu kwanta dan haka kawai yake jin gajiya yau.
Murmushi tayi mai kawai da fara zuba mai abincikan datayi mai tana sakawa aranta saita kwace zuciyar Adams ya dena damuwa da wata NUFAISAT...

Itako NUFAISAT tana jin dawowarsa da ganin kiran da yake mata taja tsaki da cewa "Allah kasaka min. Tana fad'in hakan taja bargo abinta.. Asuba tagari ADAMS TAUDHAT & NUFAISAT 😍

Rahma Nalele Auntyn luv. Ina gasuwa y'an hanuna🙌🏻


[6/26, 8:17 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 13☆


Koda wasa washe gari NUFAISAT batayi tunanin ta had'a musu breakfast ba. Qarfe takwas daidai tagama dukkanin abinda zatayi tashiga wanka.
Bayan ta fito daga wankan tad'auki wayarta taturama da Adams text message kad'an haka👌🏻. Kana tagyara kanta nan tafito fes da ita. Doguwar riga tasaka me kalar ja. Ta yane kanta da d'ankwalin rigar da saka takalminta med'an tudu.
Sannan ta d'auki wayarta da key d'in motarta tama masu yimata hidima sallama ta ficce daga gidan.. Bata dire ako ina ba sai'a gidansu.
Da Dadynta taci karo lokacin dazata shiga falan nasu. Ya kalleta ad'an nazarce yace.. "Mamana kece agidan haka da sassafe. ( dake da haka yake kiranta kasancewar sunar mamansa yasa mata )
Turo baki tayi da durqusawa tace.. "Ina kwana Dady. Murmushi yayi da bata da amsa da. "Lafiya lau. Saidai baki ban amsata ba mamana.
Qara turo baki tayi da cewa. "Momy ce tace nazo saboda na gaya mata ADAMS ba wata bace wacce ya Aura face TAUDHAT aminiyata. Dady ADAMS bai kyauta min ba Sam.
Wallahi ban hanasa Aure ba. Saboda nasan dalilinshi nayin hakan. Sannan duk mata ta gari idan tana San taqara samun kusanci da ubangijinta to ya zaman mata dole tayima mijinta biyayya taso abinda Allahn ya halatta mishi da yayi. Sannan tadinga bashi gudun mawa idan taga zai kauce hanya.
Dady kun bani tarbiya wacce nataso akanta har ake sha'awata dan ita.
Saidai ina ganin kamar bazan iya yima Adams biyayya ba ayanxu. Dan ina mishi kallan munafuki azzalimi wanda ya aikata abinda bai dace ba.... Taqarashe maganar tata da sakin kuka.
Murmushi Dadyn nata yayi da cewa aransa.. Mata mata halinsu sai su. Banda haka miye abin tada hankali dan kawai mijinki ya Auri aminiyarki.
Afiliko ce mata yayi. Tashi mamana kukan ya isa haka nan. Muje falo
Haka tatashi tabishi har falan nasa. Anan yayi mata nasiha da nuna mata wannan ba komai bane. Ita dai ta riqe sirrin gidanta. Taci gaba dayi mai ladabi da biyayya. Wallahi komai zaixo mata da sauqi idan har tasaka Allah agabanta...
Godiya tayima Dadyn nata sosai sannan ta nufi gun momyn nata lokacin tana kan sallaya da alama warha tayi.
Tana jiranta ta idar d'inne saiga Zainab yayarta taxo. Aiko nan tatashi ta rungumeta sai yaxo da dai dai da lokacin da mommy d'in nasu tashafa addu'ar da takeyi...
Aiko bayan sun gama gaisawa NUFAISAT ta gyara zama tabasu kaf labarin abinda ya faru...
Ran mommy ya b'aci amman bata nunama NUFAISAT d'in ba
Zainab kam tausayin y'ar uwar tatane ya kamata.
Mommy tayi shuru tana nazari can tace da NUFAISAT d'in... "Ki bud'e kunnanki da kyau ki saurareni kiji abinda zan gaya miki.
Tattaro dukkan hankalinta NUFAISAT tayi tana sauraranta..
Mommy taja numfashi daci gaba da cewa.. Sirrin zama da kishiya uku ne NUFAISAT.. Nafarko kisaka aranki zaki zauna da ita tsakaninki da Allah. Bazaki munafunceta ba. Bakuma zaki cutar da ita wajen aikata mata wani mugun abu ba. Sannan bazaki danne mata hakk'inta ba.
Na biyu . ki rungumi danginta da y'ay'anta da qawayenta runguma ta tsakani da Allah wacce babu batun kai qararta ga d'aya daga cikinsu ku zauna kuna munafuntarta. Saboda duk yanda kikai da abinki saiya koma mata kunnanta wata ranah..
Karkisa aranki zaki cutar da y'ay'anta agaban idanta ko'a bayan idanta. Dan bakisan alkairin dake tafe dasu ba. Ko wata rana sune zasu temakeki. Koki mutu suna masu yi miki addu'a. Ki riqesu amana ba ruwanki da nuna musu wani hali na mugunta.
Na uku shine uwa uba..
Kisa aranki bazaki dena yima mijinki ladabi da biyayya ba dan kawai ya aurota. Ya zamana lokacin ne zaki ninka ladabin da kike masa da zak'ulo duk wani abu da kikasan zai faranta ransa
Ya kasance kowane lokaci cikin bincike kike akan San sanin me yafi so. Meyafi d'aukar hankalinsa. Meyafi tafiya da tunaninsa. Meye idan kika masa yake tsayawa aransa wanda idan ya kalleki zaisa ya sakar miki murmushi.
Idan kika san way'annan saiki kasance cikin yimasa su. Gefe guda kuma kina yaqi da zuciyarki wajen San zak'ulo abinda idan kika masa zai bashi mamaki.
Idan kika gama karantar way'annan saiki koma lura da abinda bayaso. Idan kika gama lura da abinda baya so. Sai kiyi yaqi da zuciyarki wajen nisantar wannan abun..

Wannan shine sirrin zama da kishiya. Kinga baki nuna mata baqin hali ba. Baki cutar da ita ba. Baki danne mata hakkinta. Baki aikata mata wani mugun abu. Ke kawai mijinki shine agabanki ba kishi da ita. Toki saiki gayamin ta inda zata fiki kwanciyar hankali acikin gidan...
Magana ta qarshe dazan gaya miki NUFAISAT itace. Bana San wasa da sallah. Lokacin sallah nayi kitashi kije kiyi. Dan duk macen da take yin sallah akan lokaci wallahi tafi qarfin kishiyarta tako ta ina..
Sannan duk sallar da zakiyi idanga rokwan Allah ya cire miki kishin abokiyar zamanki. Sannan ya fifita qaunarki acikin zuciyar mijinki
Yasoki ya qaunaceki fiye da kowace y'a mace afad'in duniya dama gidan lahira.

Amatsayina na uwarki mahaifiyarki ban yarje miki ki sararama TAUDHAT wajen kishi akan abinda Adams yake so ba
Na baki dama kije ki kwace mijinki agun TAUDHAT ki nuna mata ko babu haihuwa bazaki tab'a wulaƙanta agun mijiki ba.
Ki nuna mata ita da banza duk d'aya kika d'aukesu
Ki nuna mata ita bata kai kiyi kishi da ita ba
Ki nuna mata Adams naku ne ku biyu amman kece abar qaunarsa...

Toh saiki tambayeni. Tayaya zaki nuna mata dukkanin way'an nan abubuwan.
Ta hanya d'aya ce itace HAKURI da nazari wajen yanke hukunci
Na sanki da San fad'an gaskiya atake idan aka miki abu. Saidai kisani Yanzu dole ki koyi yanda ake danne abu. Koda kin ganshi gashi gaskiya ne kuma ke aka cuta saiki share nunu sam abinda aka mikin bai dameki ba.
Dan idan kikayi hak'uri ga wanda yake sab'a miki wallahi wata rana shida kansa zai zauna yayi tunani da nazari akan ya dace yadena miki abinda yake miki...
Ki iya kirsa da kisisina da basarwa akan komai da zakiyi agidanki. Ammafa me kyau banda mara kyau.
Sannan kisa aranki raguwar mace itake kuka da buri da fad'ace fad'ace idan anyi mata kishiya.
Kedai kisa aranki abokiyar zamanki ba abar tsoranki bace.
Ki riqe Allah duk abinda zakiyi kiyi damunsa
Wannan itace nasihata agareki. Kuma itace gaskiyar dazan gaya miki. Kuma daga yau bazan qara zama dake irin wannan dan kinrasa yanda zakiyi da kishiyarki ba....
Mommy na kawowa nancikin zancenta taja numfashi da d'auke kallanta daga kan NUFAISAT d'in taciga da cewa. Naji kince text message kika masa wajen wajen gaya mai zaki nan gidan. Kuma bai turo miki amsa ba kawai kikayo gaban kanki kika tawo ko....
D'aga mata kai NUFAISAT tayi jiki asanyaye.
Ganin hakan yasata murmushi taci gaba da cewa.. Kishi da tsanar TAUDHAT yana neman ya canjamin ke NUFAISAT a lokaci d'aya
Hmm ba komai. Idan kikayi abinda nace miki zanga aikinsa ajikinki. Idan kuma naga akasarin hakan. Zaki ban mamaki dan zan d'auka da gaske TAUDHAT tafi qarfinki. Ta gaske tsoranta kikeji. Da gaske takwace miki farin cikinki
Wallahi NUFAISAT idan naga hakan atare dake da baqin cikinki zan mutu...
Da sauri NUFAISAT ta kalleta.
Aiko mommy d'in ta gyad'a mata kai alamun tabbatarwa. Kana taci gaba da cewa. Ki tashi kije gidanki ki gyara kanki da ingantattun magungunan mata da kayan marmari. Ki wadata kanki da qamshi da kuma d'akunan ki. Kici gaba da koyan girki agun y'ar uwarki. Kisa aranki kina da Allah baki da damuwa da albarkacin manzan Allah. NUFAISAT tashi ki tafi gidanki Allah ya miki albarka ya d'oraki akan mijinki da abokiyar zaman naki. Zan bama Y'ar uwarki Zainab magungunan gyaran jiki anjima saita kawo miki gobe..
Tashi NUFAISAT tayi hawaye na zubo mata tayimusu sallama da ficcewa daga gidan.
Da kallan tausayi mommyn tabita dashi kana ta kalli Zainab dake kuka tace "miye naki na kuka kuma.
"Momy ina kukan rashin adalcin da TAUDHAT tama NUFAISAT ne. Sannan tausayin NUFAISAT d'in ya kamani. Sannan godiya nake ga Allah daya bamu iyaye kamarku....
Murmushi mommy tayi da tashi tana nad'e sallaya dace mata. "Naji futan Dadynku bara na kirasa nagaya masa zani unguwa. Kinga kanki tashi daga office nagama had'a mata komai da komai. Sai kawai ki biyo ki karb'a idan Allah ya kaimu gobe kya bata kamar yanda nace mata..
Toh Zainab tace mata tare da share hawayenta ta d'auki jakarta da key na motarta tanufi wajen aikinta.



Lokacin da sakwan NUFAISAT ya iske ADAMS shida TAUDHAT suna kan dining yana cin breakfast d'in da tayi mai.
_Na tafi gidanmu ba wani jimawa zanyi ba._
Wannan shine sakwan data tura mai.
Murmushi ADAMS yayi dajin takaicinta. Kana ya ture wayar gefe yana me sanyin sauri ya gama yaje ya sameta. Dan baya San kiranta TAUDHAT ta ankare da wani abu
Saidai kanya ida gamawa yaji tashin motarta.
Sanda ya rintse idansa dan takaici.
TAUDHAT ko duk ta fahimci NUFAISAT ce ta fitta tsaresa tayi da ido tana me tambayarsa ko wani abu ne ya shigar mai ido.
Bud'e idan yayi da sakar mata murmushin yaqe batare dayace mata qala ba.
Sanda ya gama ne ya sakar mata kiss a kumatu da d'aukar jakarsa ya ficce daga falan. Ai tana jin fitansa da masu tsaran nasa tafad'a tunanin me NUFAISAT tafutayi da sassafe haka. Ganin takasa ba kanta amsa sai kawai ta saka wani layinta cikin wata qaramar wayarta takira wani malaminta akan ya duba mata ina kishiyarta taje yanxu da safen nan. Murmushi ya mata da cewa su TAUDHAT yau an tuna damu. Yaushe kikayi Auran da har kike magana akan kishiyarki baki bamu labari ba
Da murmushin yaqe tabashi labarin yanda akayi tasamu Adams d'in kana ta qara mishi da cewa ita dai yanxu ya gano mata me NUFAISAT tafuta yi
Sanda yayi mata kirari kafin yace zai duba mata takwantar da hankalinta. Saidai koya duba bazai gaya mata sakamako ba sai indai tazo garesa.
Waro ido TAUDHAT tayi da cewa "Ina matar aure me zan maka idan nazo. Murmushi yayi da bata amsa... "Lalle TAUDHAT. Mata nawa ne suke da Aure amman suke cigaba da abinda sukeyi.
Gaskiya bazaki samu nasara akan kowane abu daga gareni ba har sai idan zaki dinga zuwa ina d'anaki. Dan yanxu kika gama bani labarin yanda kike sakarma da boka jikinki.
"Kaga da Allah dakata. Me zakace akan boka. Naga ai duk aikinku d'aya ne dashi. Kawai shi yana amsa sunansa na boka ne kai kuma d'an iskan malami.
Sheqe mata da dariya yayi da cewa. "Ya San ranki mutuniyata. Kawai malama idan zakixo kizo kawai. Idan bazakizo ba kisha zamanki
"Zanzo amma gaskiya sai nakai kwana bakwai d'ina kafin nan na lashe amarci na. Dan bazan Bari kalashi tanadin da nayima mijina nan kusa ba. Dan haka ka adana binkikenka akan udirin nawa idan nazo ka gaya min komai... Tana fad'in hakan bata jirayi cewarsa ba ta kashe wayartata danya bata haushi. Gashi bokan nata baya da waya bare takirasa taji ina NUFAISAT d'in taje...
Kwantawa tayi tana tuna yanda Adams yake da dad'in mu'amala.
Komai nashi daban yake. Dole mace taso shi dan yana da abubuwan da za'a soshi dansu.
Duk yawan bud'e idanta afannin karuwanci da iskanci taga Adams oganta ne ta wannan fannin. Saboda yasan kan mace fiye da tunaninta. Wannan kad'ai ya isa yasa NUFAISAT hauka akansa. Dan itama taji abinda NUFAISAT d'in take ji akansa.
Nan tunaninta ya fara juyewa akan gaskiya itace tadace da Adams ba NUFAISAT ba.
Kuma dole NUFAISAT tabar mata Adams taje can tanemi wani mijin ta aura😌. Dan bazatayi sake da duk wani abu da yake dashi ya mazana su biyu ne ita da NUFAISAT suke da mallakinsa ba.. Haka dai tadinga sak'a sharri aranta har taji lokacin da NUFAISAT d'in tadawo.


Yarda wayarta da key na motarta NUFAISAT tayi akan gadanta. Kana tad'an zauna agefen gadan tana me nazarin maganganun da momyn nata tayi mata..

Sai yanxu kanta ya bud'e tagane wasu abubuwa dadama. Sam idan kirsa na magani bai dace tafito ta nunama TAUDHAT tsana haka afili har ADAMS ya gani ba..
Idan zata nuna mata ya dace ta nuna mata ita da ita ne. Saboda idan ta nuna hakan ita TAUDHAT d'in kwantar da Kai zatayi agunsa.
Kuma tasan halin mijinta sarai dasan abashi kulawa da tattalinsa. Duk da bai cika d'aukar iskancin mace barkatai ba.
Toh mezai hana ta danne zuciyarta tayi kamar batasan ya Auri TAUDHAT ba. Idan ya ficce sai suci junansu ita da ita.
Murmushin jin dad'i NUFAISAT tayi saboda tanad'e komai na makaman yaqi da TAUDHAT akan duk abinda zata zo mata dashi. Sai tayi nazari kafin ta yanke mata hukunci. Ta saka aranta Wallahi bazata tab'a barma TAUDHAT d'in shi ba..
Dan haka yamma nayi tashirya kanta kamar yanda tasaba. Sam bata kulle kofarta kamar yanda takeyi a kwanaki biyun nan ba

Aiko da misalin qarfe shidda da rabi tana kitchen tana had'a complex taji qamshin mijin nata ya daki hancinta. Bata juya ba dan tana da tabbacin shine ya shigo kitchen d'in...
ADAMS dake bakin kofar kitchen d'in shigowa yayi yana jin dad'i aransa na ganinta da yayi. Gaskiya yayi missing d'inta sosai. Da'ace zata gane ko kad'an baya jin dad'in TAUDHAT da mu'amala da ita.. Da Ita kawai yake san rayuwa dajin dad'in mu'amala. yasan da zatafi kowa jin d'adi. Saidai bazai iya gaya mata ba. Ita da kanta zata gane hakan. Dan shi ya dad'e da yima zuciyarsa hud'uba akan taji maganganun kowa akan soyayya saidai tafi d'aukar na NUFAISAT da mahimmanci. Dan da ita yafara soyayyar. Wannan dalilin shiyasa duk yake jinsa wani iri idan yana kallan TAUDHAT tana zuba masa kalaman soyayya. Shi dai bazaice bata iya ba. Amman yafi jin na NUFAISAT fiye da nata aransa. Kodan yanxu ya fara sabawa da ita ne ta wannan fannin🤔.....
A hankali yaje ya rungumi NUFAISAT d'in ta baya yana ne sauqe ajiyar zuciya. Cikin wani salo yake shaqar qamshinta yana cigaba da sauke ajiyar zuciyar..
A hankali NUFAISAT tafara juyawa garesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login