Showing 36001 words to 39000 words out of 81675 words
tadinga cinye masa lokaci duk ran da yake a d'akinta..
Saiya fuskanci NUFAISAT tafara fushi dashi
Dako yayi duba sai yaga duk ran girkin TAUDHAT baya fitta da wurri yayin zuwansa office..
Dan har sama da awa d'aya yake qarawa asaman yanda yasaba fitta..
Sai NUFAISAT tafara tunanin ko yafara gajiya da ita ne. Saboda ganin da tayi ita baya kaiwa tsawan wannan lokacin a d'akinta saina TAUDHAT d'in
Dan haka sai kawai tahau fushi dashi
Idan yazo da safen zai mata sallama saitaqi bud'e mai kofa
Dan tasan koya shigo cikin sauri sauri yake ficcewa wai yayi latti. Takance mishi tome yake tsayawa yi duk ran da yake d'akin TAUDHAT d'in dahar lokaci yake tafiya mishi haka..
Baya bata wata cikakkiyar amsa..
Wannan dalilin yasa tadena bud'emai ฦofar kwata kwata
Toya gama fahimtar da biyu TAUDHAT take mishi hakan. Daya lura sosai ya gane raina mishi hankali take da zummar batajin dad'in jikin nata toh shine yayanke mata ranar ya gaya mata ta nutsu baya san iskancin banza da hofi. Kota manta shi doctor ne. Yasan yanayin me ciwo yasan yanayin wanda yake da lafiya.. Dan haka ta nutsuwa tadena b'ata mishi lokaci idan zai fitta office. Duk abinda zatamai tamai da dare idan ya dawo gareta..
Toh tunda ya mata haka saita dena mai hakan
NUFAISAT Kuma tadena kullemai ฦofar tata.๐
ADAMS ya kanyi murmushi da cewa aransa mata halinsu sai su..
Hajjiya Rukayyat ko tasama zuciyarta hak'uri tana nan tana jiran lokaci yayi tatashi taci uban TAUDHAT
Mommy kullin kiranta ga NUFAISAT nasiha da jan hankali ne.
Zainab tayi nasarar koyama NUFAISAT duk abin daya dace na fannin girki atak'aice..
*******
Da misalin qarfe hud'u4 na yamma TAUDHAT tatashi da nak'uda...
Ba shiri takira Adams awaya. Yace bata gayama NUFAISAT bane.
Tace wai takira number nata akashe.
Da sauri shi ya kira sai kuma yaji a kunne. Cikin saurin yake gayama NUFAISAT d'in taje part na TAUDHAT ta temaka mata da had'a kayan Baby gashi nan zuwa wai nak'uda tatashi mata ne..
Cikin tausayawa ko NUFAISAT taje gareta.. Aiko tsameta tana jin jiki sosai.
Nan tatambayeta inda tasa kayan baby bako musu ta gaya mata..
NUFAISAT na had'a komai saiga Ammi tazo dan Adams d'in ya kirata ya gaya mata.
Haka dai Ammi tadinga bata temako irin nasu na manya har sa'adda Adams d'in ya iso
Nan suka shigar da ita mota sai asibi....
TAUDHAT ba ita tasamu kanta ba sai wajen qarfe tara na dare. Inda tasamu Haifo Baby girl.. Bebinta mace kyakkyawa da ita fara soll
Dangi kowa sai murna yake da zuwan wannan jinjira..
Sanda ta kwana aka sallamota b'cos bata tare da matsala
Sosai TAUDHAT ta yarda dangin Adams suna san ganin jininsa.
Shuru tayi kawai tana saka dama ace namiji ta haifa...
Mamanta ta kirata akan zata aiko mata da kayan data siya mata dan asaka akayan suna..
Nan take ta dakatar da maman wajen gaya mata karta aiko mata da masu araha. Tabarshi ita tayima kanta kaya na gani na fad'a
Shuru maman nata tayi.. Itafa har yau bataje gidan nasu ba.. Dan tunkan bikin Adams d'in da TAUDHAT d'in rabanta da gidan NUFAISAT d'in
Amman ko kad'an TAUDHAT bata damu da taje d'in ba..
Dan haka ita sai tayi aiki da hankali ana kwana uku da haihuwan taje gidan nasu amman a d'akin NUFAISAT tatare.
NUFAISAT d'inko taji dad'in hakan. Dan har labarin yanda auran na ADAMS da TAUDHAT d'in sanda maman tagayama NUFAISAT. Bayan kuma abinda TAUDHAT d'in take mata
Sanda NUFAISAT tayi kuka. tace narasa wanda ya b'atama TAUDHAT tarbiya..
Mama dai shuru tayi mata dan ji take dama NUFAISAT d'ince y'arta
Ganin irin dad'ewar da maman tayi a part d'in NUFAISAT d'in sai TAUDHAT ta balbale maman da fad'a lokacin da taje part d'inta
Wai akan wane dalili zataje part d'in NUFAISAT ta zauna
Ai wannan munafunci ne. Dan haka karta qara zuwa mata gida dama ai ba gayyatarta tayi ba bare tazo ta nunama duniya bata qaunarta kishiyarta take qauna dan tsabar munafunci...
Ran mama yayi matuqar b'aci nan take taji LAMARIN Y'ar tata ya isheta haka. Dan haka saita kalleta cikin matuqar b'acin rai...
Tace "TAUDHAT Ni kike gayama haka.
Aiko TAUDHAT ta galla mata harara tace... "aa da iska nake badake ba. Kinsan ai mu d'ari ne acikin d'akin dazaki wani ce dake nake.
Tashi mama tayi da yafa gyalanta tace.. "Har abada bazan qara zuwa inda kike ba TAUDHAT.. Haka ni bazan hanaki zuwa inda nake ba saidai ni bazan qara zuwa inda kike ba... Maman na kawowa nan a zancenta ta ficce daga bedroom na TAUDHAT d'in tama y'an barka na falan nata sallama sannan taje gun NUFAISAT tayi mata sallama NUFAISAT ta bata turare da atamfa biyu. Nan tamata godiya sannan tabar gidan dajin haushi da tsanar y'ar tata...
Ranar suna yarinya taci Sunan maman TAUDHAT d'in.. Wato HAFSAT.
Dan Adams Sunan Amminsa yaso sawa sai Ammin tace ya saka Sunan maman TAUDHAT d'in..
Bai san dalilinta nayin hakan ba.
Haka aka saka ma yarinyar sunan..
TAUDHAT ansamu abinda akeso dankam tasamu kaya kasancewar ADAMS me bayarwa ne hakan yasa kowa yake san yayi masa bajinta.. Anyi bidiri bired'e awannan suna
Dan qawayenta tantiran y'an iska sanda sukazo mata..
Kallo d'aya NUFAISAT tayi musu gabanta ya fad'i.. Dan ita ko'a mafarki idan akace mata TAUDHAT zatayi aminta da waฦดannan qawayen zata qaryata.. Amma gashi dake ba'a shedar mutum gashi nan tagani a zahiri...
Baqin cikin da TAUDHAT taso taga NUFAISAT aciki ranar sunan nata sai taga Sam bata tare da wannan baqin cikin.. Dan Sai warwala takeyi abinta tana Shiga tana fitta hankalinta kwance.. *(Yo Allah yaga zuciyarta ya kuma dafa mata*)
Saiya kasance TAUDHAT d'ince kicin b'acin rai dan haka kawai taji ranta baya mata dad'i. *( duk abinda zakayi idan ba dan Allah zakayi ba na banza ne. Kuma ALLAHN bazai baka yanda kake so d'in ba)*
Wasu matan masu jego suna barin miji agun abokiyar zamansu bisa al'ada...
Amman rashin barin shiyafi alkairi ga maso jegwan dan sune da riba.
Akwai wani d'umin juna na qara so da shak'uwa dayake samuwa yayin da me jego takwanta gado d'aya da mijinta da abinda ta haifa..
Wannan dalilin yasa masana sanin SOO da qauna basa barin matayensu dan suna jego. Haka Matan masana sanin K'AUNA basa tab'a yarda su yada mazajensu yayin da suke jego.
Duk da cewa ba wai wani abu bane zai faru tsakaninsu.
Kawai ana buqatan sudinga jin d'umin junan nasu ne..
TAUDHAT bata san da hakan ba. Amma ADAMS yasan da hakan.
Saidai dama ita TAUDHAT ko kad'an bataji aranta zata iya barma NUFAISAT Adams har na tsawan wata da kwana goma ba..
Wannan dalilin yasa tayanke hukunci akan koda Adams yazo mata da zancen tabarshi gun NUFAISAT zatace mishi bata yarda ba..๐ก
_(Toh tama kwantar da hankalinta inji Rahma Nalele)_
Dan a washe garin ranar sunan dama itace da girki.
Dan haka Adams yazo gareta dan su kwana
Amma me. Sam taqi ta kula da jikinta yanda ya dace dan yana daga nesa da ita yake jiyo qarnin jininta
Dan haka yace mata dama yazo ne dan ya tayata kwana sanadin yanda take jego basai tazo garesa ba..
Amman tunda har yanxu qarnin jininta bai rabu da ita ba zaije part d'insa. duk sa'adda ya d'auke tamai magana.. Tace mai toh ammadai ba da NUFAISAT zai dinga kwana ba ko.
Murmushi yayi mata da mamakinta yace. Ko kad'an. Kamar dai yanda suka saba hakan ne zaici gaba dayi musu..
Murmushi tayi batare da tace mai komai ba
Ganin hakan yasashi ficcewa daga d'akin dan qarnin ya ishesa
Hakance ko ta kasance. Yana bama kowa hakk'inta na kwananta kamar yanda ya saba.
Ran girkin NUFAISAT yana manne da ita ran na TAUDHAT kuwa saidai ya rungumi filo
Ahaka TAUDHAT tayi arba'in amman duk da hakan sanda Adams ya qara mata kwana biyar kafin ya kulata ta fannin kwanciya...
**********
Komai yayi daidai dan Haneepha yarinyar tasu (deke haka suke kiranta dashi). Tayi wayo ayanxu Dan shekaranta d'aya yau. gudunta take yi ko'ina ga baqin magana..
NUFAISAT duk da tasan ba y'ar Adams bace hakan baisa taji wani abu naqin ciki akan yarinyar ba..
Dan sosai take qaunarta..
Tun TAUDHAT na hanata y'ar hardai ta hakura tafara bata. Dan ba qaramin cin ubanta Adams yayi wata ranah
Da yayi mantuwa ya dawo d'auka yaji TAUDHAT d'in tanama NUFAISAT gori akan haihuwa dan kawai taje tace tabata yarinyar tamata wasa..
Ran Adams bai tab'a b'aci irin na ranar ba..
Anan yayima TAUDHAT d'in saki d'aya yace tatattara tatafi gidansu ya saketa. Sannan ya kuma kwace y'ar yaba NUFAISAT ita
Hankalin TAUDHAT ba qaramin tashi yayi ba daqer da sid'in goshi Amminsa da Dadynsa suka samu kan Adams d'in ya dawo da TAUDHAT d'in
Dan maman TAUDHAT d'in da TAUDHAT d'in tazo mata da maganar ko kallanta batayi ba.
Dan tana nan da jin haushinta na wulaqancin data mata kafin sunan haleephan
Hakan ne yasa TAUDHAT jan tsaki taje tasa su Ammi agaba da magiya shine dalilin da yasa suka samu kan Adams d'in ya maida ita..
Tana dawowa ko NUFAISAT taje tabata y'ar tata. Da cewa wallahi TAUDHAT kibi duniya Ahankali idan da kara da mutunci baici ace kinyimin gori akan haihuwa saboda wannan Y'ar taki ba. Nasani kin sani ba y'ar Adams bace. Ta wani ce can daban Amman sabo mugun baqin halinki kina neman rasa igiyar auranki akan baqin tunaninki...
Dalla mata harara TAUDHAT d'in tayi da fizge yartata..
Tunda daga ranar bata qara hana NUFAISAT yarinyar ba. Idan har NUFAISAT d'in tazo d'aukarta zata bata ita..
Kawai shed'an ne yake yawo akan TAUDHAT dan sarai tasan NUFAISAT bazata cutar mata da Y'a ba...
******
Ayau ne Hajjiya Hadiza tagaji dacin kud'in Hajjiya Rukayyat. Tasaka aranta zata nema mata magani na Gaskiya
Dan takai shekara d'ayan da kusan rabi fiyema da haka shuru
Sai dad'in baki da take mata
Toh yazu gata gaban wani malami tagaya masa matsalarta ya bata magani yace taje tabata tasha sannan ta shafe mata jiki dashi...
Aiko tunda tazo tayi mata haka cikin iko na Allah saiga Hajjiya Rukayyat tatashi..
Kwananta uku da dawowa normal taje wajen bokanta akan ya haukatar da TAUDHAT
Aiko nan yake gaya mata aiki akan TAUDHAT ba qaramin abu bane..
Dan wani malaminta nayi mata aiki
Saidai idan tana san ayi mata wani abu toh tayi qoqarin kawo mishi jinin al'adar ita TAUDHAT d'in da ruwan ni'imarta
Hankalin Hajjiya Rukayyat ya tashi
Anan taqara tabbatarwa lalle dole TAUDHAT tacika mata baki.
Amman ba komai idan kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu had'u ne.
Wallahi tasha alwashin zaita wargaza rayuwar TAUDHAT..
Lokacin da TAUDHAT taji tashin Hajjiya Rukayyat d'in ji tayi kamar taji hauka
Nan takira malamin ta yace takwantar da hankalinta dama haukatata tasoyi. Amman ai tana dashi. Kawai taci gaba da lura mishi da y'arsa...
Jin hakan yasa hankalin TAUDHAT kwanciya kamar tsumma aranda..๐
โ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ป "Stop.. Ya kamata NUFAISAT TAUDHAT ku tsaya a haka... Naje can qauye nagano MUSLEEMAT... Nice Rahma Nalele ce me fad'in๐
Junior RAMADAN dake gefena yace "Ya kamata kam my Aunty. Yanxu kin shiryane nakai ki can qauyen cikin daqiqa biyu..
Murmushi nayi da cewa. "Aiya kamata ADAMS yayima su NUFAISAT sallama me tsayawa arai.
Yace "kuma fa haka ne..
๐๐๐๐๐
๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ปNa gaida y'an hannu na๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐ฏ๐ปโโ
[7/9, 2:44 PM] ยฎ๐ณโพโผโชofficial Auntyn Luv.: `โยด-`โยด-
โโหโขโโข
ยธโโโยชโ_โพ`โโข
โ *.ยธยธ.*โ *.ยธยธ.*โซ*.ยธยธ*โ *.ยธยธ.*โซ.ยธยธ.*โ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.ยธยธ.*โซ*.ยธยธ*โ ยธยธ.*โซยธ*โ *.ยธยธ.*โซ*.ยธยธ*โ
`โยด-`โยด-
โโหโขโโข
ยธโโโยชโ_โพ`โโข
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. โพโขRahma Muh'md Rufa'i Nalele..โ
*ยฉ REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM๐*
โWe the best โ
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
โ ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
[email protected]
โpage 18โ
Dalilin dayasa ADAMS yake tare da masu tsaro shine... Ashe shekarun baya tunda ya fara tashen kud'i sai mahassada suka sashi agaba.
Sam baza'ace gasu ba.
Saboda sunqi fitowa su nuna kansa bare ad'au hukunci akansu.
Wata rana yana dawowa daga wajen kasuwancinsa. Dan ranar bata zuwa asibiti bace agaresa. Haka wasu mutane suka taresa suka mai dukan mutuwa.
Sanda ADAMS ya shafe wata d'aya yana jinyar kansa.
Haka daya tashi bayan kwana uku da tashin nasa still suka qara taresa suka dad'a mai irin wannan dukan.. Suna gayamai Wanda yasa ogansu wannan aikin rayuwarshi yake so. Su basuso su kashesa saboda alkairin daya tab'a yima ogansu. Suna bashi shawara yabar garin Kaduna ya koma can wani gari da rayuwa...
Wannan karan sanda ya kai wata biyu kafin yasamu kanshi.
Shiga tunani yayi sosai wajen tuna kalaman da suka gaya masa yayin da suke mai wannan duka. Shi sam baisan waye wannan ogan nasu da yake san rayuwarshi ba..
Haka kazalika bai tab'a ganin fuskokin masu mai dukan ba. Dan idansu arufe yake ba wata alama da suka bari yanda zai ganesu...
Wannan yasa hankalin Dadynsa ya tashi yace dole ya dinga yawo da masu tsoro..
Da Adams yama Dadyn nasa musu akan me zaisa ko'ina zashi sai yayi yawo da masu tsoro. Shi baya sha'awar hakan sam. ALLAHn daya yisa shizai karesa.. Ba qaramin yaqi Dadyn yayi dashi ba kafin ya yarda ya samu matsaron lafiyar tashi. Sai Allah ya had'asa da nagari wanda sam basu da niyar cin amanarsa. Saboda yanda suke tunanin zai kyautata musu sai sukaga aihar ya zarce hakan wajen kyautata musun.. Dan haka sukaqi bama wanda yake san ganin bayan nasa had'in kai. Dansu sun sanshi sarai sundai k'i gayama ADAMS d'in ne saboda sun gaya masa yanda suke da ilimi wajen saran lafiyar mutum zasuyi amfani da wannan ilimin nasu wajen gujema duk wani hari dazai kawo ma Adams..
Dan haba bazasu gayama ADAMS ba. Dan sunsan zai d'auki mataki ne. Kuma kunga su shikenan fa sun rasa wannan garab'asan da suke samu agunsa ba..
Sannan sunyi ilimi da Allah zasu tsare lafiyarsa dayakar qarfinsu da aiki da iliminsu...
Wannan yasa mekaratu yake ganin Adams da masu tsaro tun farkwan fara karatunshi....
*******
Yana breakfast a falan NUFAISAT Yayinda Haneepha take kan cinyarsa sai zubamai surutu takeyi irin na yara..
Sam hankalinsa baya kanta yana kan NUFAISAT da tayi tagumi kawai saboda maganar daya gaya mata tun shekaran jiya na wai zaiyi tafiya...
D'an shafan gefan fusakarta yayi cikin so da qauna yace.. "Haba my luv. Wai miye ne haka. Ke dazaki bani qarfin gwiwar zuwa amma saiki jefa kanki cikin tunani dan kisa ZUCIYATA rawa ko..
Kallansa tayi cikin damuwa tace.. "Wallahi ba haka bane mijina. Kawai dai kasan baka tab'ayin tafiya bane kabarni haka
Murmushi yayi da cewa.. "Kwana hud'u nefa kawai zanyi. Kuma ya kamata kibani qarfin gwiwa dan nagaya miki waye Ibrahim agaremu.
Ibrahim shine wanda mukayi skull kaf dashi. Kawai bamu cika shiga harkarsa bane nida Yusuf saboda halinmu ya bambanta da nashi..
Ko yaushe yana san jammu cikin al'amuransa mune dai muke kauce masa. Amman yanxu ya dace mununa masa bama qinsa mununa masa farin cikinmu akan abinda ya samesa na alkairin nan.
"Toh shi kenan dama haka kawai ne naji gabana na fad'uwa akan tafiyar sam bana san kayita Wallahi. Bana so. amma tunda ka kafe Allah yakaika lafiya ya dawo min dakai lafiya..
"Yauwa matata dama hakan nake sanji daga gareki.
Yana gamawa ya sauke Haneepha da rungumar NUFAISAT d'in ya b'ata lokaci sosai yana kissing d'inta kamar bazai barta ba. Can dai ya barta da nufar part d'in TAUDHAT itama dai tanuna mai bata san tafiyar amman tunda yana so itama tanai mishi Fatan alkairi...
Tabbas shima yaji wani iri lokacin daya shiga motar tashi dan ganin yanda jikin NUFAISAT yayi sanyi.. Haka ya sakar mata murmushi yace direban nashi yaja motar..
Haka sufa ficce dashi daga gidan yana me d'agama Haneepha hannu alamun bye bye...
Direct gidansu yayi.. Nanko yagasu Dady da Amminsa cikin damuwa. alama tanuna suma hankalinsu bai kwanta da tafiyar tashi ba...
Ibrahim abokin Adams da Yusuf ne..
Sam halinsu yasha bambam da nashi. Wannan dalilin yasa ba kowa bane yake yarda ma abokinsu ne. Saboda yanda suke guje masa sam basu san wuld'a dashi tunda suka dawo daga karatu daga waje..
Katsam acikin satin nan saiya kirasu yake gaya musu ya bud'e wani asibiti nashi na qashin kansa a garin da mahaifiyarsa take jahar Gwambe.
Amman dan Allah kar suce mai basu suzo ba dan yana san yayi walimar bud'e asibitin tare dasu.. Walimar biyu ce. Data ranar jumma'a data ranar lahadi.. Kuma yana san dukka ayi dasu.
Sunji kunyarsa sosai hakan ne yasa suka amsa masa dato zasuzo kuma za'ayi komai dasu...
Tunran alhamis Yusuf ya tafi dan lokacin jikin Dadyn Adams bai gama warwarewa ba kasancewar yayi zazzab'i kwana biyu da suka wucce..
Hakan yasa Adams yace yaje shi yaxo ran asabar yasamu walimar ta ranar lahadin
Haka ko akayi nan Yusuf ya tafi..
Kuma har ya tabbatar mishi da cewa ya sauka lafiya dake tafiyar jirgi ne.
Toshi haka kawai Adams ya tsinci kansa dasan tafiyar mota..
Danya ankawo masa wata fitacciyar mota me inganci wacce tazarce kowace mota cikin motocinsa a kud'i... Dan haka sai yaji yana san tafiya da motar..
Kuma baya san tafiya da maso tsaran lafiyansa.
Dayake gayama su Dadynsa da Amminsa sai hankalinsu ya tashi sukace basu yarda ba
Dan basu manta yanda aka mishi lokacin baya da yake yawo shi kad'ai ba
Murmushi yayi dace musu haba dai. Yanxu koma waye maqiyin nasa ai yaci ace ya haqura ya dena bibiyarsa tunda yanxu rabansa dashi kusan shekaru takwas kenan.
Jin hakan yasa hankalin nasu kwanciya.. Amma yanxu ganin da gaske tafiyan zaiyi sai kuma sukaji tashin hankalin ya dawo musu...
Murmushi ADAMS yayi dan ganinsu cikin damuwa. Haka ya kalli Dadyn nasa yace.. "Dama Dady nazo muku sallamar ne..
Murmushin yaqe Dadyn yayi masa dacewa.. "Anya bazan hanaka tafiyan nan bako ADAMU
Da sauri Adams ya qara tsaida idanta akan na Dadyn nasa yace... "Dan Allah karka hanani Dady.. Bafa wani abun dazai faru. Kawai addu'arku nake nema nasan idan har kukamin bazata fad'i qasa banza ba..
Jan numfashi Amminsa tayi da cewa toh Allah ya saukeka lafiya ya dawo mana dakai lafiya.. Sannan ka kula da hanya kasan ba sanin wajen kayi ba..
"Insha Allah Ammina
Kuma ai kinga tare da Sunusi zamu dan yaje gwamben kusan sau biyar tunda acen Mahaifinsa yanxu yake da zama.
Dan haka baza mu sami wata matsala ba
Jin hakan yasa hankalinsu kwanciya amman duk da hakan sunso da ace girgi yabi. Da hankalinsu yafi kwanciya...
Haka yayi musu