Showing 57001 words to 60000 words out of 81675 words

Chapter 20 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

mijina ne shi. Yana nan wani fari kyakkyawa haka me yawan murmushi dasan tsafta...
Sheqe mata da dariya mutumin yayi tare da way'anda suke wajen. Nan ran YAWO ya b'aci ta kallesu da takaici tace.. "Haba yaran nan daga tambayarku sai kuhau yima mutane dariya.
"Mutumin ya kalle da cewa. "Kema tsohuwa da girmanki zaki tsaya biyema shirman jikarki. Fisabidillahi a'ina zamusan wani waishi LEEKITAN ZUCHIYA. Kuma gashi wai kyakkyawa me san tsafta da murmushi.
Yanxu idan ke mukama wannan tambayar fisabidillahi zaki bamu amsa.
"Me zaisa bazan baku amsa ba yaran nan. Idan nasan shi gaya muku zanyi idanko ban sanshi ba banga dalilin da zaisa na tsaya yi muku dariya ba.
Dariyar suka qara bushe musu da ita. Kana ya bata amsa da.. "Tomu bamu san wani waishi LEEKITAN ZUCHIYA ba. Kuje can gaba wala'Allah zakuci karo da Wanda ya sanshi..
Hawaye ne ya zuboma MUSLEEMA. Nan YAWO tatab'ata tana meyi mata nuni dasu qara gaba..


Afuwan masoyana LEEKITAN ZUCHIYA naku ne.. 😍kuci gaba da bibiyata akansa
[7/23, 10:30 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 23☆


Haka suka qara gaba inda suka had'u da wani masifaffan tsoho ya kalli Yawo kallan wani iri haka yace. "LEEKITAN ZUCHIYA kowa kuke cewa. Yanxu ni a'ina zan sanshi. Da Allah ku qara can gaba qila kwa gansa.
Haka YAWO da MUSLEEMA suka dinga yawo suna neman ADAMS da bashi suna LEEKITAN ZUCHIYA amma basuci karo da wanda yace ya sanshi ba.
Duk sunsha ranah. Musamman kunsan garin kano da zafin ranah. Haka suka zauna bakin shagwan wani mutum me saida kayan provision dan ganin akwai wani me soya indomie da kwai. Haka suka bashi kud'i ya had'a musu yanda zai ishesu.
Bayan sun gamaci ne suka fara tunanin inda zasuyi sallah. Bama wannan ba a'ina zasu samu wajen kwana.
Wani saurayi ne yazo wuccewa Yawo takirasa take tambayarsa dan Allah a'ina zasu samu d'akin haya na sati biyu. Su baqi ne suna neman wajen kwana ne.
Kallan tsaf saurayin yayi musu kana yace suna da kud'i ne.
Nan YAWO tace mishi eh suna da shi.
Ai dajin hakan saurayin yace suzo zai kaisu wajen Hajjiya ladi tana da d'akuna acikin gidanta sannan tana bada haya yana tabbatar musu sun sami gidan haya me kyau dan ko'ina a gidan me kyau ne sosai
Haka YAWO da MUSLEEMA da yaranta sukabi bayan mutumin nan yakaisu gidan Hajjiya ladi dake unguwar bacirawa.

Hajjiya ladi shahararriyar shed'aniya ce. Kaf way'anda suke haya a gidanta gogaggun y'an iska ne karuwai. Shi dai wannan mutumin shiyake kawoma Hajjiya ladi mutane musamman way'anda idan ya lura basusan kan gari ba. To idan ya kai mata su yakan dawo da daddare yayima mutunan dai daya kawo mata sane wato sata. Sam bashi da wani aiki sai hakan.

Dan haka da suka isa gidan Hajjiya ladi kallansu tayi da kyau taga dai basu da fuskar mugayan mutane sai tace subata dubu talatin..
Ai nan YAWO ta zaro ido tace. "Haba keko baiwar Allah kiji tausayinmu mu baki dubu goma saboda muma bada hakan mukazo ba. Munzo da kud'i da yawa saidai munci karo da y'an fashi sun yashe mana me yawan. Nan YAWO takwashe komai tagayama Hajjiya ladi.
Azahirin Gaskiya Hajjiya ladi ta tausayama MUSLEEMA dan ganinta qaramar yarinya.
Saidai taji haushin YAWO over dan inda itace bazata tab'a Aurama ADAMS jikarta ba. Saboda bata san waye shi ba. Bata san daga inda ya fito ba. Haka kawai dan gwaninta saita kama ta bashi jikarta dan toshewar basira..
"Toh ai shikenan. Allah ya rufa asiri. Kidai bada dubu Ishirin kiyi wata d'aya. Idan wata d'aya yayi saiku fitta kubani d'akina idan kuma zaku qara biya saiku qara zama har Allah yasa kusami shi LEEKITAN ZUCHIYAR naku.. Hajjiya Ladi tafad'i hakan da wani tab'e baki.
Godiya YAWO tamata ta fito da kud'in ta qirga tabata. Sannan tamaida kud'in cikin y'ar lalitarta cikin wani d'an qaramin buhu duk wannan mutumin yana kallanta.
Haka Hajjiya ladi tayi musu jagora zuwa wani d'aki haka. Eh dai bashi da wani matsala. Dan akwai ledar d'aki cikinsa da wata yololuwar katifa da fillo..
Haka MUSLEEMA ta share d'akin tas tasaka musu kayansu a gefe sukayi sallah kana suka fara tunanin me zasuci na dare.
Anan kusa da gidan Hajjiya ladi akwai wata mata Yalwa me saida abinci safe da rana da dare tana da ma'aikata da dama. Matar ta'iya abinci sosai shiyasa mazaje masu aji daji da kansu da mata masu aji suke zuwa wajenta cin abincin nata.

To gurinta Hajjiya ladi ta nunama su MUSLEEMA da suka tambayeta inda zasu sami abinci.
Kallan farko da Yalwa tama MUSLEEMA taji aranta dama tazama meyi mata aiki. Dan taga yarinyar tana da diri sosai zata qara ja mata Hankalin maza kwastamomi. Gashi ta mallaki duk wani abu da mazan suke so agun mace.
Dan haka da fara'a ta kalli MUSLEEMA tace.. "Daga ina kike yarinya.
Nuna mata gidan Hajjiya ladi MUSLEEMA tayi tace.. "Daga nan gidan nake..
"Ikwan Allah. Meya kawoku gidan.
Dake MUSLEEMA ahannu take burinta mutane su dinga sakewa da ita dan tadinga fad'in musu buqatarta na neman ADAMS ko Allah zaisa wani yace mata yasanshi. Nan tabata labarin abinda ya kawosu gidan.
Sosai Yalwa me abinci ta tausayama MUSLEEMA tace. "Aiko nayi mamaki danaji kince daga gidan Hajjiya Ladi kike. Ganin da nayi kamar kina da nutsuwa.
"A nazarce MUSLEEMA tace.. "Meyasa ki fad'in hakan.
"Eh gani nayi gidan karuwai ne.
Waro ido waje 😳 MUSLEEMA tayi da cewa. "Gidan karuwai. Toh aimu ba karuwar bane. Meyasa wannan mutumin ya kawomu gidan.
"Nima mamakin danaji kenan. Karfa wani abu ya dameki dan zaman naku ai na wani d'an lokaci ne.
Murmushin yaqe MUSLEEMA tayi mata. Da miqa mata kud'i ta had'a musu abincin da MUSLEEMA tace mata tanaso..

Aiko MUSLEEMA na dawowa ta gayama YAWO agidan karuwai suke.
Ran YAWO baiyi mata dad'i ba. Amma data tuna zaman nasu na d'an wani lokaci ne sai Kawai ta share. Kula dai da yaran MUSLEEMA zatayi sosai dankarsu b'ata musu tarbiya.
Sosai yawo tayaba abincin Yalwa

Cikin dare da misalin qarfe goma sha biyu na dare wannan mutumin daya kawo su YAWO ya lallab'a ya tura d'akin dasu yawon suke yashige. Dake sun kashe kwan wuta da d'an hasken wayarsa ya dinga lalubar inda zaiga inda yawo tasa sauran kud'in nan. Aiko yaci sa'a. 😳 nan cikin kayan su Khalit yagani. Ahankali kamar yanda yake tafiyar da motsin nasa ya d'auke kud'in gabaki d'aya. Har zai fitta saiya dawo ya sakama musu d'ari biyar a inda dai ya d'auki kud'in.
Kana ya ficce daga d'akin ahankali cikin jin dad'in yanda basu sakama ƙofar sakata ba kamar yanda yayi zato.

Washe gari da safe YAWO ta tambayi Hajjiya ladi kan inda zasu samu ruwan wanka. Hajjiya ladi ta cokaro d'an kwali gaba tace da ita Hita zaku sayo da d'an bokati da soso dakomai na buqata. Harda furko da gawayi kudinga yin abinda kukeso. Kamar yanda kukaga kowa nayi. Dake ku baqi ne kikawo kud'in naba almajirin gidan nan yaje ya suyo muku

Toh YAWO tace mata da dawowa d'akinsu. Anan tahau neman kud'in nasu tanema sama ko qasa babu ko sisi sai d'ari biyar.
Hankalin YAWO dana MUSLEEMA ya tashi nan suka fara hargitsa kayansu waiko zasu gani. Amma babu kud'in nan nasu ba dalilinsa.
Hawaye ya zuboma MUSLEEMA ta d'ora hannu aka tace "YAWO mun shiga uku. Yanxu waye zai bamu kud'i. Can y'an fashi sun amshe manyan kud'ad'an. Nan kuma gashi an yashe mana Sauran.
Sam YAWO bata iya ba MUSLEEMA amsa ba. Dan hankalinta ya tashi matuqa.
Da muguwar damuwa taje tana gayama Hajjiya Ladi sufa basuga kud'insu ba.
Dariya Hajjiya Ladi tasheqe musu dashi tace. "Ban gane bakuga kud'inku ba. Kun bar ƙofar taku a bud'e ne.
"Eh abud'e muka barta saboda nayi nayi na kulle na kasa.. YAWO tabata amsa da damuwa.
Qara dariya Hajjiya Ladi tayi tace.. "Shege d'an malam. Ai gaya muku ne banyi ba na sha'afa. Wannan mutumin daya kawoku jiya ai tantagaryar b'arawo ne.
Idan ya kawamin mutane irinku way'anda basu san gari ba. Zuwa yake daga baya yayi musu sane wato sata.
Dan haka sai kuyi hakuri.

YAWO ta waro ido tace. "Muyi hakuri muci me kenan. Yanxu tunda kin sanshi nezai hana ki had'amu dashi yabamu kud'inmu
Kallan raini Hajjiya ladi tayi mata da cewa. "Tabd'ijan. Ai sai dai kuyi hakuri dan Wallahi tunda d'an malam ya sace muku kud'in ban yatafi kenan har abada. Toni yanzu ma a ina zanga d'an malam. Dama idan ya aikata irin wannan nemansa ake a rasa sai ya daidaici mutanan sun tafi yake dawowa yaban labarin yanda yayi satar.
Kinga tsohuwa kibar batun d'an malam yanxu kikama abinda zai fishsheku
"Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un. Shine abinda YAWO ta fad'i.
MUSLEEMA ko sai hawaye take tana hararo mezai faru dasu gaba yanzu tunda ba kud'i.


Da d'ari biyar d'in MUSLEEMA taje tasiyo musu hitar d'ari da hamsin da buredin d'ari biyu. Da Lipton na ishirin da sikarin arba'in dake da sauran canji ahannunta na jiya data siya musu abinci saita had'a tasiya musu soso da sabulu harda man shafawa tadawo gidan lokacin akwai wuta. Hajjiya Ladin ce dai tanuna musu yanda ake amfani da hitar har tabasu aran bokatin ta da kofuna. Kafin almajirin data aika ya kawo musu nasun. Dan MUSLEEMA tabata sauran kud'in dan taba almajirin yasai musu bukati d'aya da kofuna uku harda lokali d'aya da buta. Shine taba almajirin yasiyo musu.

Haka YAWO tayi wanka MUSLEEMA ma tayi tayima yaranta. Sannan suka sha ruwan Lipton d'in da buredin.

Suna gama sha ko MUSLEEMA tasaka yaranta agaba YAWO na binsu dama Hajjiya ladi ta had'asu da wani almajiri dan haka nan suka Shiga gari neman ADAMS.
Duk inda sukaje sai ammusu dariya. Wasu su tausaya musu Wasu kuma suga ganganci irin na Yawo data ba ADAMS MUSLEEMA bayan tasan bata san kowa nasa ba bata san waye shi ba.

Haka suka dawo gidan lilis da gajiya. Gajin yunwa gashi basu da ko sisi. Abin gwanin ban tausayi.
Suna gani Hajjiya Ladi tasaka abincinta agaba ta zauna a tsakar gidan tacinye ko kwad'an batayi musu tayi ba. Dan tasan idan tayi musu tayin wallahi ci zasuyi dan tasan sarai yunwa sukeji.
Khalil ya kalli MUSLEEMA yace. "Mama yunwa nake ji. Khalit ma yace "nima yunwa nakeji mama.
Hawaye ya zuboma MUSLEEMA tace.. "Kuyi hakuri Yanxu zan nemo muku abinci.
YAWO ta share hawayan da itama ya zubo mata tace. "Gwara musan yanda zamuyi mu basu abinci MUSLEEMA. Tunkan wannan acicin tatashi kinga dai yanda tayi baccin da kukan yunwar.
"To yanzu YAWO ya zamuyi.
"Muje wajen me abincin nan na roketa tabamu bashi mubasu daga baya masan yanda zamuyi.

Haka ko suka nufi gun Yalwa me saida abinci suka gaya mata buqatarsu har suka qara mata da cewa sace musu kud'insu wani yayi.
Yalwa tayi murmushi tace. "Hmm yanxu idan na baku ya zakuyi anjima.
Kawai dai ga shawara idan kunga zaku iya.
"YAWO tace idan tayi mezai hanamu iyawa
"Yauwa tsohuwa temakwanku zanyi. Kinga ke saiki dinga min wanke wanke da shara. Ke kuma MUSLEEMA saiki dinga zuwa kina bama mazage abinci. Amma cikin nutsuwa yanda zakina jan ra'ayinsu kamar yanda akeyi.
YAWO tace.. "Yanxu idan muka yarda da hakan yaushe zamu samu lokacin dubawa shi LEEKITAN ZUCHIYAN.
Yalwa taja numfashi tace. "Sai MUSLEEMA tadinga zuwa da safe nemansan har zuwa ranah. Daga lokacin da yamma tayi saitazo tajimin da kwastomumina har zuwa sha d'aya na dare.
Idan kun yarda to zan dinga baku abinci safe da ranah da dare sannan zan dinga baku naira d'ari. ammafa ba batun biyanku albashi kamar yanda nake bama y'an aikina duk sati.. Danku nayi muku babban temako ne..
Saidai idan zaman namu ya d'ore nan da wata uku zan iya baku kud'in da zaku koma garin na gwambe
Da sauri sukace mata sun yarda.
Aiko nan tacika musu abinci suka dawo gidan sukaba Khalil da Khalit sukaci Suma sukaci sannan suka ragema Rahma kan tatashi..


****
Sai rayuwar tasu ta kansance haka. Kullum idan sun tashi wanka sukeyi YAWO tana tasa Khalit da Khalil zuwa gun Yalwa me abinci su hau yimata aiki kamar sauran ma'aikatan nata. MUSLEEMA Kuma tashiga gari neman (ADAMS) LEEKITAN ZUCHIYA..

Safe da ranah MUSLEEMA neman ADAMS tasaka agaba. Kullum cikin kuka take musamman idan tatambayi wasu mutanan suka sakata a gaba da dariya.
Duk sallar da zatayi addu'a take tana kuka kan Allah ya had'ata da LEEKITAN ZUCHIYA.

Ayanxu dai satinsu d'aya kenan
Yau tun asuba kan MUSLEEMA yake mata ciwo. Lokaci lokaci kuma takanji qirjinta nayi mata zafi musamman wajen da ZUCIYA take amsar sak'o. Haka daddafa tashirya qarfe tara ta fitta kamar yanda tasaba ita da almajirin dake mata rakiyar dan neman LEEKITAN ZUCHIYA.

Sunyi tambayoyin da dama bataci karo da wanda yace ya gane kwatancen nata ba.
Sai kawai tazauna kan wani dakali tad'ora hannu aka tarushe da kuka.
Fad'i take a bayyane. "Meyasa kamin haka Abban Khalit. Meyasa kamin haka baban Khalil. Meyasa kamin haka YAYANA. Meyasa kamin haka LEEKITAN ZUCHIYA.
Kamanta cewar ka b'ata tunanina. Kamanta cewa kadasamin qaunarka azuciyata. Kamanta cewa bana ji bani gani akan sanka da qaunarka.
Meyasa kake wahalar da ruhina. Meyasa kake wahalar da tunanina. Meyasa kake wahalar da zuciyata. Harshena. Gangar jikina. Kafafuna. Ya dace kaji aranka kayi rayuwa dani. Ya dace kaji aranka ina nemanka. Ya dace kaji aranka kana da yara dani. Ya dace kaji aranka akwai wata meyi maka wani SO wanda yafi qarfin akirashi da MASIFAR SO.
Haka tadinga sambatu tana kuka wiwi mutane na kallanta wasu suji tausayinta su tsaya tambayarta idan tayi musu shuru su qara gaba. Wasunsu ko koda sunji tausayin nata basa mata magana suke wuccewa.
Wani tsoho ne ya nace saiyaji abinda yasata kuka haka. Nan tagaya masa. Ya tausaya mata nan ya bata shawara tunda sunan ya had'a dangantaka da likita mezaisa bazataje asibitoci taga ko zata ganshi acan ba.
Aiko taji dad'in shawarar daya bata.
Haka suka dawo gida tagayama YAWO.
Washe gari yawo tabata d'ari biyar irin d'ari d'arin da Yalwa take basu. Haka suka tari kekenafaf zuwa asibitin Aminu kano.
Taci sa'a wata doctor salma taji tausayinta dataji labarinta. Dan haka nan tasadata da hotunan doctors Amman bataga ko me kama da idan Adams ba.
Tunkan tabar asibitin tafara kuka.

Washe gari haka Yalwa ta ranta musu dari biyar ta nufi asibitin murtala. Nan kam tad'an sha wahala kafin wani Dr Ahmad ya fahimceta.
Shima ya nuna mata manyan doctors nanma ko me irin qeyar Adams MUSLEEMA bata gani ba.
Still haka tabaro asibitin da kuka.

Haka akwanakin nan tadinga ziyartar asibitoci amma shuru kake ji.

Haka ta tabari tadena bin asibitocin badan ta hak'ura ba. Saidan babu kud'in zuwa gunsu.
Dan Yalwa tace bazata qara ara musu ko sisi ba. Tunda kud'inta yakai duba biyu da d'ari biyar akansu.
Gashi MUSLEEMAN ba dawowa take da wuri ba. Sai kusan bayan isha. Dan haka idan zata tsaya tayi mata aiki tatsaya tayi mata aiki. Sannan tasan inda zataje ta biyata kud'inta.
Yawo ce tace tayi hak'uri zata dinga dawowa akan lokaci batun kud'i kuma tadinga cirewa aduk rana cikin d'arin da take basu.
Wannan yasa Hankalin Yalwa kwanciya..

Toh MUSLEEMA tadena dadewa wajen yawan neman ADAMS saboda dukar Yalwa.
Saidai yanxu tafara fuskantar wata matsala kamar haka wajen aikin nata.

Idan tazo kawowa Mazajen abinci saisuta kallan qirjinta da qugunta.
Suna janta da hira.
Sam bata san hakan b'cos tana ganin ita matar aure ce.
Duk da cewar hijab take sawa amman hakan baya hanasu qin kallan way'annan abubuwan biyun ba.

Gashi duk da saida dare take dawowa hakan baya hana mazan dake suwa wajen karuwan gidan Hajjiya Ladin binta da mayataccen kallo
Itadai jifansu take da addu'a dan tasan itace makaminta

Dan akwai ranar da wani ya tab'a fad'o musu d'akin nasu yana me san fad'ama MUSLEEMAN haka dai Allah ya kare
Saidai daga ranar suka koyi iya rufe d'akin nasu..




________
Yau tun safe Hajjiya Ladi tabasu notis kan kud'insu ya qare wata d'ayan da sukayi da ita ya qare dan haka su tashi mata daga d'aki zatasa wata budurwa aciki. Dan gashi tabata kud'inta cif cif dan haka su tattara inasu inasu su qara gaba

Kuka MUSLEEMA tasama Hajjiya Ladi tace.. "Dan Allah ki temaka mana kiqara mana lokaci zamu biyaki kud'inki.
Tace.. "Bazai yuhu ina ganin kud'i ahannu nabar budurwar nan ta tafi da kud'inta bayan ku babani zakuyi yanxu ba
Wallahi Saidai kuyi hakuri inda ace d'akunan basu cika ba dana qara muku lokacin.

Ba irin magiyar dasu MUSLEEMA basuma Hajjiya ladi ba kan ta barsu tace basu isa ba.
Haka suka d'an kwashe kayansu sukaje gun Yalwa me saidai abinci.
Anan Yalwa tace idan sunga zaku iya kwana cikin y'an aikin da suke mata aikatau a shagwan abincin nata to ga waje nan su ajiye kayansu.
Idanko sunga bazasu iya ba. To ita bata da wani waje da zata sasu.
Dan gidanta d'aki d'aya ne tayimai rufi daga shi sai bayan gida ai gashi nan dai sunga gidan ajikin shagwan nata.
Shuru sukayi mata dan a y'an aikin nata harda maza almajirai.
Kuma duk balagaggu ne.
Amma da sukaga gefan matan daban na mazan daban dansu mazan a barandar waje suke kwana. Matan ne aciki Suma irin yaran nan ne way'anda iyayansu suke koransu kai da duhun jahilci ko yaran da basu da yanda zasuyi.

Haka dai YAWO tacema MUSLEEMA su yarda.
Haka suka yarda tunda ba yanda zasuyi.
Sunyi kwana d'aya lafiya lau dai.
Ayau na biyun ne MUSLEEMA tazo kawoma wani alhaji abinci kamar yanda yasaba zuwa kullum ci qarfe tara na dare.. Yana d'aya daga cikin mutanan da suke bin qirjinta da kallo.
Hakan ne yasa ta tsane shi. Harta juya zata tafi ganin ta shirya mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login