Showing 6001 words to 9000 words out of 81675 words
"Wake nan..😳 Wai kana nufin TAUDHAT...
ɗaga mata kai yayi yana kunshe muguwar dariyar dataxo masa..
Aiko turmuƙe fuska tayi kamar zatayi kuka tace... "Dan Allah kabari... Kaima kasan abune bame yuhuwa ba..
Nasan ko'a mafarki TAUDHAT baza tataɓa zama kishiyata ba..
"Ko..... Ya katseta da faɗin hakan yana me cigaba da cewa... Amman kinsan da cewa TAUDHAT tana matuƙar sona..
Jan numfashi NUFAISAT tayi da cewa. "Na lura yau sokake ka zautar dani da zolaya...
Kaga zomuje na shayar dakai dannaga a kwaɗaice kake dasu... Ta ƙarashe furucin nata tana me karɓar ledar dake hannunsa da kama hannun nasa tajashi bedroom ɗinsa
Buɗe mata kayan sanyin yayi su ice-cream ɗin tasha San ranta...
Kana ya fara sarrafata yanda yakeso...
Sanda ya tabbatar yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali kana ya maƙaleta yana juya na fulaninta cikin bakinsa yana jin daɗi..
Sanda ya ɗauki lokaci ahakan kana ya bar matasu ya rungumeta yana ce da ita... "My luv. Ina samun dukkanin wani farin ciki daga gareki
Sannan a iya sanina ba ma'Auratan da suka kaimu fahimtar juna..
Dan kina san abinda ni nake so
Haka kaza nika nima Ina san abinda ke kike so.
Duk da cewar nasan kishiya da zafi take..
Ina baki haƙuri wajen gaya miki dazanyi cewar ina San zan ƙara Aure.....
Sosai yaji bugawar da girjinta tayi.... Sakamakwan dama a ƙirjinsan take..
ƙokari tayi dan ta raba kanta da ƙirjinsa Amman saiya ƙara ƙamƙameta..
Shuru na wani ɗan lokaci... Zuwa can ya fara jin zubar hawayenta a ƙirjin nasa
Cikin wata siririyar muryar tace dashi... "Me zaisa ka ƙara Aure...
"Zan ƙara Aure ne saboda ina San na faranta ran iyayena
Ko Allah zaisa nasamu rabo...
Bayan hakan ina addu'a akan Allah yasa wacce zan Auran ta iya girki...
Dan ina San mace wacce ta'iya. Nasha gaya miki batun yau ba.
Sannan bawai zanyi Auran bane danna musguna miki
Zanyine kawai dan farin cikin iyayena da kuma kwad'ayin samun wacce ta iya girki... Danna San zamammu da TAUDHAT na wani ɗan lokaci ne.
Kasancewar Dole tazama matar wani.
Idan hakan ta kasance yazanyi... Ya faɗi hakan yana me kallan fuskarta daci gaba da cewa.... Nayi nayi dake akan ki daure ki d'an iya. Amman kinqi
Toh ya zanyi dake my luv....
Kuka take sosai. Dan baqamin shiga tashin hankali tayi ba
Tasani.. Mijin nata me magana ɗaya ne.. Kuma duk abinda zai gaya maka gaskiya ne
Tasan tsakaninta dashi ba batun wani ƙunbiya ƙunbiya
Duk abinda yace mata zaiyi zaiyi ne kawai
Wannan yasa tafara jin tausayin kanta
Dan tasan zamani ya lalace... Batasan wazai kawo mata ba
Tasan yana dasan yara.
Shin idan yasamu daga wajen kishiyar tata wane baƙin ciki zata kwasa....
Cikin kuka tace dashi.. "Yanxu awane matsayi zaka barni...
"Wallahi bazan taɓa canja miki matsayin da kike dashi a cikin zuciyata ba...
NUFAISAT umarni nake baki akan bana San naga wani tashin hakanlinki akan Auran nan
Sannan bana San naga kin canja daga abubuwan da kike min
Hakan zai iya tunzura zuciyata
Dan kinsan baki isa dakatar dani daga ƙin aikata hakan ba
Kinfi kowa sanin magana ɗaya nake dake. Wacce ta kasance bata wasa ba.
Ina San ki saka aranki abokiyar zaman ki zata iya zuwa miki a kowane lokaci
Daga ƙarshe ina Sanki. Kuma bana tunanin zanso wata Y'a mace KAMAR yanda nake sanki..
Jan numfashi tayi cikin cigaba da kukan nata tace dashi... "Zanbi umarninka Ya mijina.. Dan abinda ya kawoni kenan gidanka...
Saidai yanxu ina buƙatar kaɗaici
Dan Allah kabarni naje bedroom nawa na kwana..
Murmushi kawai yayi da saketa ta sauka daga gadan da suturce kanta har takai ƙofa yace da Ita "dakata
Tashi yayi shima da sitirce gabansa yaxo gabanta da kama fuskarta yace... Dawai ina San ki tayani wankan ne kamar yanda kika saba.. Ya fad'i hakan yana me janye hannunsa
Share hawayenta tayi dayi mishi Murmushin yaqe tace... "Toh muje..
ɗaukarta yayi kamar wata baby ya nufi toilet d'in da Ita KAMAR yanda yasaba mata
Akan idansa tayi wankan tsarkin. shima yayi..
Sannan sukabi da wankan sosu da sabulu
Kamar yanda tasaba temaka masa. Hakan tayi..
Bayan sun fitoh ne dukkaninsu jikinsu d'auke da tawul. Ya kalleta yace.. "Da'ace kamar yanda kike bani kulawar nan Idan mun kusanci juna wajen yin wanka. Da'ace hakan kike bani kulawa Idan kina tare da TAUDHAT dana qara sanki da qaunarki....
Dan sosai nake jin takaicin yanda baki San kulawa dani Idan kina tare da TAUDHAT..
Abin na d'auremin kai Idan kina bani kulawa bayan idanta
Kawai dai magana d'aya anan itace.. ina San kulawa akowane lokaci koma kina tare da waye..
Murmushin k'arfin hani tamai da cewa... "Ayanxu zan kula sosai ya Mijina..
Kama fuskarta yayi ya fara aika mata da wani make✔.. Kiss. Wanda yake tafiya cikin wani salo
Sanda yay mata San ransa kana ya barta yana mece mata.. "Zanso ki sami kaɗaicin da kika nemi alfarma akansa..
Murmushin dai taƙara sakar masa da cewa... "Nagode...
Tana fad'in hakan taficce daga d'akin
_yau rana d'aya kacal.. Kin raba shinfid'a dani NUFAISAT.._
Ya fad'i hakan aransa
Kana ya zauna yana tunanin maraicin dazaiyi yau
Dan yasaba da d'umin jikinta yayin baccinsa...
Shuru yayi... Zuwa can ya canja kaya da shinfid'a dadduma ya fara aikin bada lafula. Yana gaisar da ubangijinsa
Itako Sanda ta tabbatar da cewar ta kulle ƙofar bedroom natan.. Sannan ta zube a gadanta tarushe da wani uban kuka wiwi..
Ta sani... Mijinta na matuƙar santa.. Kuma ayanda take kyautatama iyayansa baici ace su mata haka ba.😭
Har shekara nawa tayi da Auran da zasuce ya qara Aure dan kawai bata haihu ba..
Abayyane take cewa.. "Wai meyasa mutune suke haka ne
Meyasa Ammee zakimin hakan
Me yasa. Meya Dady zakamin haka..
Shin bakusan Kishiya da zafi da ciwo take ba..
Ji nake kamar nayi hauka..
Ba qaramin kuka taci ba.
Candai daga bisani dataga kanta na Sara mata alamar zata cutar da kanta.. Sai kawai tatashi tayo alwala tahau lafula.. Tana rokwan Allah akan ya biya mata buqatarta na yasa Auran karya zama tashin hankali agareta
Allah yasa yinshi shine farin ciki agareta
Allah yasa hakan ya zama alkairi agareta
Allah yayaye mata baqin cikin duniya dana lahira.
Allah ya BATA DAMAR B'OYE KISHINTA agun amaryar da shi kansa uban tafiyar...
Haka tadinga addu'a kamar bazata dena ba..
Sannan kuma tadawo tafara karanta Qur'ani
Sanda taji idanta na rufewa sannan ta kwanta
Aiko bacci me nauyin gaske ne yayi awan gaba da ita...
Shiko Sam bai iya wani baccin kirki ba
Dan tunda yake da NUFAISAT wani abu bai tab'a shiga tsaninsa da Ita sun raba shinfid'a ba
Wannan dalilin yasaka ya kasa baccin kirki..
[29/04 12:05 pm] 🔳◾◼▪💙: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 06☆
Asuba nayi kamar yanda tasaba... Watoh bayan kammala sallar asubarta.. Tana shiga toilet d'insa da nata ta wankesu
Bayan ta fitto tayi shara da saita saka turara nan zakaji ko ina ya d'auki ƙamshi
Kana tayi wanka sai tatarama ogan nata nasa ruwan wankan
Kasancewar baya dawowa daga masallaci har sai gari yayi haske...
Hakan yake bata damar kammala way'annan ayyukan saidai kawai ya dawo ya ganta fes Ita da dakunanta...
Toh yau abin yaxo da wani saban salo..
Kasancewar tatashi da wani yanayi ba kamar yanda tasaba tashi ba
Saidai tagodema Allah daya amshi addu'arta... Dan bata tashi da muguwar damuwar nan da mata ke tashi da Ita lokacin da mazajensu suka gaya masu zasu qara Aure ba...
Hakanne mah. Ya bata damar tagama komai kamar yanda tasaba..
Yanxu haka tana tsaye a kitchen d'inta ne..
Lokacin bakwai dai-dai.. Alokacin kuma take sakaran dawowar Mijin nata daga Masallacin
Dama shine yake dafa musu Lipton da soya musu kwai da sauransu..😂
Shine yau take San gwadawa.. Taga zaiyi dad'in da yake musu..
Saka ruwa tayi da d'an jefa citta dasu kanunfari ta cika ruwan..
Nan tatsaya har ya tafasa ta juye a fulas.. Sannan ta fasa kwai guda shidda tasaka magi dunƙule shima guda shidda...
Sannan takad'a ta soya..
D'aukar wayarta tayi takira yayarta Zainab akan tagaya mata yanda ake had'a farfesun kaza...
Da iya adadin magin da zata sakama kaza d'aya
Dariya Zainab tayi mata
Da cewa.. "Ina y'an aikinki suke.. Larai da Aseeya.. Kikara larai tayi miki mana...
Kamar NUFAISAT zatayi kuka tace da Ita.. "Kisan bana sakasu aikin daya shafi shashina. saidai imbanda lafiya..
Aikin su shine kawai su dafa nasu daba ma'aikatan gidan..
Bama wannan ba. Shi Wanda zanyi dominsa baci zaiyi ba..
Ko kin manta yanda nasha wiya wajen cusa masa San cin girkin TAUDHAT
Kinsan Daga na Ammeensa saina nata Yanxu kawai yakeci
Jan numfashi Zainab tayi da cewa.. "Toh meyasa yau kikesan kiyi masa da kanki..
Bayan nasan shine yake had'a muku breakfast..
"Ki bari kawai y'ar uwa.. Ina San ganinki pls idan kin tashi daga office yau
Ina san gaya miki wani abu..
"Ok.. Zainab tace da ita.. Sannan tagaya mata yanda zatayi..
Cikin iko na Allah ko sai tayi dai-dai da yanda tagaya matan...
Dan duk gidansu Zainab ce kawai tayo momynsu wajen iya girki..
Shidai ADAMCY daya dawo yayi mamakin ganin NUFAISAT a kitchen.. Bama wannan ba. Mamakinsa yafi tsayawa akan yanda yake jiyo ƙamshin farfesun kaza..
Yasani wannan aikinsa ne na safe 😂
Murmushi kawai yayi da girgiza kai yayi part d'insa yana dad'a jin mamakinta..
Dan yafi kowa sanin koda wasa NUFAISAT bata shiga kitchen dasunan wai tashiga dan yin girki..
Wato Kishiya ba abinda bata saka mata...
Haka yata surutansa a ZUCIYA.. Har yayi wanka da saka kayansa ya feshe jikinsa da turaransa me maƙalewa azuciya..
Kana ya nufi wani shashi na gidan nasa Wanda yake basa damar ganawa da baƙinsa..
Watoh tunda yau ta kasance asabar.. Baya zuwa asibiti ranar asabar da Lahadi
Kawai yana zuwa kasuwancinsa ne.. Amman kafin nan yana ganawa da talakawa way'anda basu dashi wajen temaka musu daga ƙarfe takwas da rabi zuwa ƙarfe goma..
Toh da zaran ya gama dasu d'inne yake dawowa ga matarsa yaci breakfast d'in daya had'a musu. Kana ya nufi wajen kasuwancin nasa...
Toh yau ƙarfe takwas ya nufi shashin dayake ganawa dasu...
Kasan cewar yau Matar gidan tatashi da himma😀 ta canjesa wajen girka musu abin da zasuci.
_Hmmm yau zaici girkin NUFAISAT_ ya fad'i hakan aransa..
Itako bayan tagama jitayi jikinta ya dauki ƙamshin girkin.. Hakan yasa taqara shaqa wanka tayi shigarmu irinta hausawa. Inda tasaka wata doguwar rigar atamfa... Kasancewar kalan ja da bak'i ne saiya haskata... Ba abinda zai baka sha'awa sai d'aurin data kafa... NUFAISAT nada kyau naban mamaki.. Macece so sweet.. Abin San kowane namiji.. Matsalarta biyuce inji ADAMCY.. shine bata masa shagwaɓa yanda zatana tsuma zuciyarsa.. Kasancewarsa d'an luv.. Sannan bata iya girki ba..
Waƴannan sune matsalar agun ADAMCY..
Falo tadawo duk ƙamshi ya rufeta.. Anan ta zauna ta d'auki wani littafin sister Rahma Nalele me suna *YA FARU AKAN KAINA* daniyar San karantawa..
Saidai kash.. Bai cancanta amatsayinta na wacce akace za'ama kishiya zuciyarta tabarta haka kawai ba..
Dan haka kasa karatun tayi.. Tayi shuru kawai da afkawa cikin kogwan tunanin ya zatayi da ganin mijin nata da wata mace.. Tafi kowa sanin waye shi.. ADAMCY daban yake acikin mazaje... Komai ya iya.. Bataga abinda ADAM bai iya ba..
Yanxu duk abinda yake mata haka zaima wacce zai Aura.......
Jitayi an shafi gefan fuskarta.. Koda ta d'ago da kan nata ADAM d'in tagani.. Aiko nan ya sakar mata Murmushi yana me cewa.
"Nasan tunanina kikeyi. Banda abinki waya isa ya kwace miki ni.. Ƙaryar wata mace takwace miki ni uwar ƴaƴana..
Sanyayyan Murmushi tasakar mai da cewa.. "Har yau nakasa gane yanda akeyi kake gane tunanina...
"Saboda nine me GYARA TUNANIN NAKI..
Ina mamakin yanda kike manta cewar zuciyarki da tawa abu d'aya ne..
"Idanko haka ne. ya dace tunaninmu shima ya kasance abu d'aya..
"Tabbas.. Ya bata amsa da fad'in hakan. Yana me cigaba da cewa. Ƙamshi ya dami hancina.. Zan rigaki zuwa dining fah😀
Dad'i ya cika zuciyarta.. Tatashi ahankali daniyar zuwa ga dining d'in.. Shi kuma ganin hakan yasa shi rungumarta ya d'ago da fuskarta izuwa kallansa yana cewa... "Anya akwai ranar da zatazo nadena ganin kyen fuskarki kuwa..
Lumshe ido tayi da bud'ewa Ahankali tace.. "Ranar na zuwa.. Dan gashi nan alamun sun fara bayyana Yanxu...
"Toh gayamin.. Ina alamun suke..
"Banda hakan. Mezaisa ka ƙara Aure..
"Izuwa gaba zanji ba dad'i idan kika ƙara alaƙanta maganar Aurena cikin maganata dake..
Shuru tayi najin wani iri.. Wai ADAM wane irin mutum ne.. Tafad'i hakan aranta.. D'an qara tsaida kallanta tayi akansa kad'an tace.. "Insha Allah bakina bazai qara gangancin furta wata kalma dangane da Auran naka ba...
"Dts gud my sweetheart.. Nasan kina San mijinki... Kina kuma tsoran wata ta mallake miki shi. Kina san ganin kin haihu dashi.. Kina fatan kasancewa dashi har iya qarshen rayuwa.
Ina sanki NUFAISAT. Adai yanxu yanda nake jin ZUCIYATA!!! Bana tunanin zanso wata mace!! Kamar yanda nake qaunarki..
"Da'ace zai kasance har iya qarshe rayuwa zakaji hakan aranka ba iya yanxu ba. Dana tabbatarmah da kaina!!! Nayi dace duniya walahira
Cikin wani hali ya bata amsa da cewa. "Todai a'iya yanda nake jinki araina.. Ina tabbatar miki da cewar.. Kice afarkwanfarko cikin matan dazan rayu dasu cikin Auratayyata.
Zatayi magana sai yayi saurin had'e bakinsa da nata Yana me juya harshensu cikin wani hali..
Sanin makomarta Idan tabari ya d'auki lokaci ahakan yana me mata kiss d'in.. Shiyasata yimai cakulkulu tana me kyalkyalewa da Dariya...
Aiko nan take yasake yana cewa... "Watoh kinyimin hakan dan nabarki ko
"aa... Kawai gani nayi kana shirin cinyemin baki nah🙃
Da Murmushi yace "aiko da gaske wata ranah zan iya cinye miki shi.
Dariya taqarayi da kama hannunsa suka nufi dining tana cewa.. "Naka ne Mijina. Kayi duk yanda kaga dama dashi... Dan bani fatan naga ranar dazaka dena nunana qaunarka garesa
Murmushi yayi dai dai lokacin daya zauna tana qoqarin zubamai farfesu... Bayan tagama ta tura mai kwan data soya had'e da had'a mai komai Wanda ya dace dashi.
Sannan ta zauna itama ta d'an saka nata agaba cikin tsoron Allah yasa bata kwafsa ba..
Shuru ADAMCY yayi lokacin daya kwurb'i ruwan Lipton din data samai dan baya shansa da madara..
Eh.. Tayi qoqari ba lefi. Duk da cewar tamanta da abu biyu.. Wato ganyan na'a na'a da ganyen giris..
Yaji ba dad'i lokacin daya kai warnar kwan nan bakinsa..
Dan magi yayima kwan yawa over
Gashi ta kafesa da ido..
Kawai jira take taga me zaiyi
Ganin da tayi ya rintse ido sanadin kai wainar kwan bakinsa.
Tasan Daurewa kawai yayi ya had'iye..
Zai qara tayi saurin riqe hannunsa Kamar zatayi kuka take cewa.. "Ban sanka da fulako ba.. Alamu sun nuna banyi abinda ya dace ba.. Idan nayi duba da yanda ka rintse idanka yayin had'iyewa.
Shuru yayi mata..
Ganin hakan yasa tad'an gutsiri kad'an takai bakinta.... Aiba shiri tadawo dashi.. Dan magin yayi yawan dazai iya yima mutum illah..
Shuru tayi da sunkuyar da kanta..
Bai mata magana ba ya jawo farfesun kazar yakai bakinsa yana addu'ar Allah yasa tayi dai dai ashi..
Aiko addu'arsa ta karb'u.. Dan yayi dai-dai irin kadaran kadaham d'innan..
Dan haka ya zage yaci sosai..
Bayan ya gama ya kalleta kad'an dayin Murmushi dan har lokacin bawai ta d'ago da kan nata bane..
Kan natan yana qasa da alama ma kuka takeyi..
Jawo biran dake jikin rigansa yayi da wata y'ar fefa. Nan yayi mata wasu rubutu kad'an ya ajiye mata... Kana ya tashi da d'aukar laptop d'insa da wayoyinsa ya ficce daga falan yana addu'ar fita daga gida...
Sanda taji tafiyansa shida maso tsaran nasa. Sannan ta d'ago da kanta ta sauke akan farar takaddar daya ajiye mata..
Ga abinda yace..
_Da'ace haka kike min tun da farko dana qara sanki da qaunarki.. Gaskiya ban taɓa cin farfesu me dad'in Wanda naci yanxu ba. Dan haka ina sauraran qaracin wani irinsa da rana idan zan samu.._
_Kisani Yanxu bana San naqara cin girkin TAUDHAT.. Idan kika bari wani ko wata ya qara saka miki hannu akan abinda zanci daga gareki!!! Lalle zanji ba dad'i. Zanji kamar kin munafunceni. Zanji zafinki sosai. Aqarshe koda kinyi nadama. Bazan kalleki ba.._
_Ina sanki matata.._
_Kidena wannan kukan da kikeyi.. Dan zai iya ɓatamin farin cikina ayau..._
_Sannan ki qara nutsuwa sosai wajen saka magi akwai. Dan idan kikaci gaba da sakawa da yawa kamar hakan... Lalle bazanƙici ba. Saidar cuta takamani.. Dan ayanxu nayima zuciyata alƙawarin duk abinda kika dafa zancishi ko Yaya yake.._❤
Jan numfashi NUFAISAT tayi da sakin Murmushi.. Abayyane take cewa.. "Bazan qara barin TAUDHAT tayima girki ba Ya Mijina.
Yanzu