Showing 15001 words to 18000 words out of 81675 words

Chapter 6 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

gaban motar tana me kallansa da cigaba da cewa. Nasan dai ba abinda zai kawoka ƙofar gidamu adaidai wannan lokacin imba wani abu me mahimmanci ba. Allah dai yasa qawata tana lafiya. Danna farajin fad'uwar gaba.
"Ai dole kiji hakan. Dan kina San aure mata miji. Wato TAUDHAT Nazo miki da wata magana me mahimmanci.
"Kafin ka Sanar min da maganar ina San naji batun lafiyar qawata. Dan wallahi da gaske zuciyata tasaka tsayuwa waje d'aya. Sannan meyasaka cemin zan aure mata miji.
"Tana cikin k'oshin lafiya. Dan tacemin mah in gaya miki ki kula dani sosai. Dan idan nakoma mata gida rai b'ace saita hukuntaki.
"Masha Allah. Naji dad'in yanda take cikin koshin lafiya. Batun zan aure mata miji fah.
"Shine ya kawoni. Kuma ina San kima abin kyakkyawar fahimta.
NUFAISAT tafi saninki fiye da kowa arayuwarta. Sannan tana sanki fiye da kowa a qawayenta. Hakan yasa nazo da k'okwan barana akan kiyarje min na Aureki matsayin matata ta biyu dan nasan idan kece kika zamo kishiyarta bazaki tab'a bata matsala ba. Amma fa idan kin yarda dan babu dole aciki. Kawai farin cikin matata nake nema.
Jan numfashi TAUDHAT tayi kamar gaske tace. "Idan har dai NUFAISAT ta amince zan aure ka Adams. Saboda katara duk wani abu da y'a mace take fatan samu agun mijin auranta.
Ina sanka Adams. Amman dan qawata nake sanka. Inasan inciga da raya mata wannan San nata acikin zuciyarka. Dan bana sha'awar wata can tazo ta b'ata mata gininta....

"NUFAISAT bata San ke nayanke shawarar aura ba. Bare har aje batun amincewa. Taqi bani damar na gaya mata hakan. Hakan yasa ban takurata ba. Dan nasan idan taganki matsayin abokiyar zamanta zataso hakan kuma zatayi farin ciki sosai.
Murmushin mugunta TAUDHAT tayi dayimai wani kallo qasa qasa tace.. "Idan ko haka ne nayarda da Auran ka. Ko yanxu kace a d'aura wallahi nabaka goyan baya.
Murmushi yayi da cewa. "Ina San kiyimin iso wajen mama acikin daran nan
Haka ko tamai iso wajen mama.
Hankalin mama ya tashi sosai da buqatar da Adams yazo mata dashi.
Dan tanuna mai hakan bai dace ba sam. Bai dace ya Auri TAUDHAT ba kuma yana Auran NUFAISAT
Nutsuwa sosai Adams yayi yabata hujjojinsa nasan yin hakan kafin tayarda.
Sun yanke shawarar limamin unguwar shi zai bada Auran TAUDHAT d'in. Kasancewar basa da kowa masu ganin mutuncinsu
Adams yaji dad'i sosai. Dan haka acikin daran bai duba qurewar lokaci ba ya nufi gidansu.

TAUDHAT Adams na fitta ta rufe mahaifiyarta da masifa wai akan me zata nunama Adams bai dace ya aureta ba
Wannan wane irin baqin ciki take mata.
Ita dai mama shuru tayi mata hakan yasa ta qare mata rashin kunya ta nufi d'akinta da mafificin farin cikin burunta ya kusa cika


Adams ya tadda Dadynsa na qoqarin kwantawa. Anan ya zayyane masa komai kuma Dadyn yayi farin ciki da hakan. Yace Allah ya kaisu gobe ya qara nazari akan lamarin. Toh yace masa ya nufi gun Amminsa. Saidai ita Ammi yana gaya mata komai yaga jikinta yayi sanyi bata wani nuna farin cikinta ba.
Shidai ahaka ya lallab'a yabarta lafiya dan yasan idan ya d'auki lokaci agunta ba makawa saita kawo mishi dalilinta na rashin nuna farin cikin nata. Kuma ya saba bin abinda take so. Yanxu saita canja mishi ra'ayi. Kuma abinda bayaso kenan akan wannan lamarin. Dan yana ganin Auran TAUDHAT shine mafi ALKAIRI agaresa da kuma matarsa NUFAISAT.
Da farin ciki yakai gidansa lafiya lokacin qarfe goma sha d'aya na dare. Tun NUFAISAT nasaran dawowarsa hardai ta hakura bacci yayi awan gaba da ita

Shiko ganinta tana bacci hankali kwance sai kawai yayi wanka da gabatar da lafula kana yabi jikinta ya kwanta anan taji ajikinta yada dawo. Dan har ta bud'e ido Amman bata nuna mai ta farka ba.
Tunani kawai takeyi akan yanxu sai sha d'aya zai dinga dawowa. Hmm Allah ya sanyaya zuciyarta..

Wàshe gari bata nuna mai komai na dad'ewar da yayi jiya ba. Sam baiga wani alamu na b'acin agareta ba.
Hakan yasa yaji dad'i sosai harya tafi office da nutsuwa. Amman ta gayamai zata gida tagaida momynta
Ya amince mata dan yasan tana buqatar tattaunawa da mahaifiyartata akan lamarin Auran nasa dan tabata shawara. Kuma yana da tabbacin zata bata shawara tagari dan yafi kowa sanin halin momynsu nata wajen nutsuwa da hankali sanin ya kamata da hak'uri...


Aranar qanin Dadynsa dashi Dadyn kansa sukaje nemammai Auran TAUDHAT d'in. Dan Dadyn yayi tunani yaga dacewar hakan. Kuma wani iko na Allah ko kad'an abinciken dayasa amai akan TAUDHAT d'in ansamu kyakkyawar sheda akanta. Sam basuci karo da mummunar sheda akanta ba..
Wannan dalilin yasa suka kai sadaki awashe garin ranar. Sannan suka buqaci da asaka ranar d'aurin aure nan da sati d'aya☝🏼..

Murna wajen TAUDHAT ba'a magana
Sai bayan kwana biyu Adams ya gayama NUFAISAT Auran nasa nan da kwana biyar
Duk da taji fad'uwar gaba amma bata nuna masa ba. Ita yasa agaba sukaje manya manyan boutique suka had'o lefe na kerema sa'a. Dan Wannan tsarin Amminsa ne tace mai yaje da NUFAISAT susuyo komai. Duk abinda ta d'auka ta d'aukarma amaryar. Hakan yasa komai bibbiyu NUFAISAT take d'auka. Ba lefi sun samu akwatina shidda shidda ammafa manya manyan...😨

Qanwar Hajjiya Rukayyat da qawayenta ne sukaje gidansu TAUDHAT sukakai lefan awashe gari.
Anan Hajjiya Rukayyat taja TAUDHAT gefe tana kitsa mata wasu kalamai kamar haka..
Kasan cewar bokanta ya bata tabbaci akan bazata samu nasara akan NUFAISAT ba. Saboda tana da qarfin imani. Zadai ta iya cin galaba akan TAUDHAT. Ya bata wani magani yace taba TAUDHAT d'in cikin wani abun ci. idan har taci bazata tab'a haihuwa da Adams ba. Idanko ta haihu da Adams toh wallahi cikin wani ne bana Adams ba
Wannan dalilin yasa Hajjiya Rukayyat ta dafama TAUDHAT kaza da maganin tabata yanxu amatsayin wai kyautarta na maganin mata. Har tana qarama TAUDHAT da qarya wai shi tabama NUFAISAT shiyasa Adams yake qaunarta kamar ransa. Aiko jin Hakan nan take TAUDHAT ta miqe agaban Hajjiya Rukayyat tacinye kazar nan harda sid'e flasks.
Dariyar mugunta Hajjiya Rukayyat tayi da jinjina kishi irin na TAUDHAT
Hmm tab'e baki tayi da cewa aranta.. tunda buqatata tabiya banda matsala dake..
Dan haka da farin ciki sosai Hajjiya Rukayyat tadawo gida tana bama Ammin Adams da Dady labarin karramawar da mama mahaifiyar TAUDHAT tayi musu. Sosai tanuna taji fad'in zuwanta gidan.
Jin hakan yasa Ammi da Dady jin dad'i sosai



Gobe ne d'aurin aure dan haka Adams yasa akazo aka canjama NUFAISAT wasu abubuwan d'aki
Duk da cewar shashin amaryama shiyayi mata komai Amman hakan baihana idan kashigo shashin NUFAISAT kaga nata yafi baka sha'awa da birgewa ba.
Ita amarya nata shashin komai Skye blur ne.
Yayinda komai na NUFAISAT ya kasance ash color n black
Gidan ya qara fitowa fiye da tunanin me tunani.
NUFAISAT ta kalli ADAMS da kulawa tace. "Gabe zaka zama ango Amman banji kana maganar yin wasu bidi'o'eh da shagalewa ba
Murmushi ya sakar mata da bata kiss a wiya yace. "Amaryama tabuqaci ayi hakan amman nace mata banda ra'ayi. Saboda bani San nuna miki d'okina.
Saidai yau sunyi walima da qawayenta har nayi mamakin yanda baki halacci wajen ba kamar yanda tace min
Murmushi NUFAISAT tayi da cewa. Ba'a gayyaceni ba. Hasalima bansanta ba. Aganina abu me wiya ne zaisa taganni wajen. Gaskiya naji haushin kawo maka wannan qarar tawa da tayi.
"Toh ai gani nayi Ku qawayene. Ai basai ta gayyaceki ba.
Zadai tazama y'ar uwata idan tashigo gobe. Dan bazan barta a matsayin qawa ba. Kaga mubar batun nan mubarma goben kawai haka kawai naji bana jin dad'i azuciyata.
Dake dama suna zaune ne akan kujerar falo saiya janyota jikinsa ya rungumeta dan ya hango bama baman kishi b'aro b'aro a tattare da ita.
Dan haka yau baija da nisa ba. Yashiga lallab'ata. Shi sai Yanxu ma ya tuna ai batasan TAUDHAT zai aura ba.

Washe gari asabar NUFAISAT da yayarta Zainab da sauran y'an uwanta harda momynsu dake wayayyiyar macece tazo gidan haka suka saka NUFAISAT agaba suka dinga mata nasiha dajan hankalinta akan ta qara hak'uri akan komai karta saka damuwa akan zuwan wannan amaryar tata.
Aiko da misalin qarfe gamo sha d'aya aka d'aura auran ADAMSY da TAUDHAT...

Kowa ya watse a gidan yazamana shuru daga NUFAISAT dake shashinta sai y'an aiki dake shashinsu sai amarya TAUDHAT dake nata shashin.
A haka Adams ya dawo shida masu tsaransa da abokanayansa biyu wato Yusuf da wani wai shi Suleiman
B'angaran NUFAISAT suka nufa nan suka ganta afalo cikin kyakkyawar shiga ta doguwar rigar less jah. Ya haskata sosai abinka da fara.
Tashi tayi tana musu barka da zuwa cikin yaqe...
Da wani hali suke gaisawa da ita suna masu kiranta da uwar gida ran gida. In bake ba gida. Murmushi kawai tayi musu da kama hannun mijinta tana mece musu dasu tashi aje rakiyar da ita zuwa d'akin amaryar...
Ta basu mamaki sosai haka taja mijin nata gaba Yusuf da Suleiman sukabi bayansu Adams na qara janta jikinsa yana kuma hango farin cikin dazai ganta aciki idan taga TAUDHAT ce amaryar tata...

Hmm😌 masu karatu yake nan..
By Rahma Nalele Auntyn luv
[6/21, 9:11 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 11☆


Sunsami TAUDHAT d'in akan gadanta kanta lullub'e da mayafi. NUFAISAT ta zauna kusa da ita da kama hannunta ba tare data bud'e mata fuska ba tace. "Aminci agareki ya y'ar uwata. Yau gaki agaidan mijina matsayin matarsa ta biyu. Ina rokwanki da Allah daki d'aure kiba mijina kulawar data dace. Wallahi ina San farin cikinsa. Allah ya bamu zaman lafiya da rayuwa me d'orewa.😀
TAUDHAT batayi magana ba. Amman tad'an motsa alamun tajita.
Ganin hakan yasa NUFAISAT sakar mata hannu da tashi tama abokanayen nasa sallama ta ficce daga d'akin
Tana fitta Yusuf da Suleiman suka ma TAUDHAT nasiha kana itama suka ajiye mata kaza da madara kamar yanda suka ajiyama NUFAISAT suka fito suma daga d'akin
A can waje Yusuf ya dingama Adams tsiya akan yadai bi TAUDHAT a hankali danyaga har wani rawar kai yakeyi.
Adams yayi murmushi da cemai. Haba dai rawar kai. Sai kace wani saban shiga. Bana tunanin zatazo min da wani abu wanda NUFAISAT bata zomin dashi ba. Kudai kawai kujira gobe. Koma miye zaku gani akan fuskata dan kyakkyawan amarci baya b'oya..
Dariya suka sheqemai da ita kana suka shine motocinsu damai sallama megadi ya kulle gida.
Part d'in NUFAISAT Adams yayi. Amman yana murd'a kofar tata saiya jita a kulle. Ahankali yashiga bugawa yana kiran sunanta amma shuru wai malam yaci shirwa. Haka ya koma part d'in TAUDHAT lokacin tana toilet da alama alwala takeyi. Hakan yasa ya zauna jiranta yana tunanin meyasa NUFAISAT kulle mishi kofa ba tare da sun yima junansu sai da safe ba.... Fitowar TAUDHAT ne ya katse mai tunanin. Ya kalleta da murmushi yace. "Amarya kinsha qamshi. Dafatan kina tare da alwala mu gabatar da sallar godiya ga Allah daya bamu damar zama ma'aurata.
Da matuqar farin ciki tace.. "Dama banyi isha bane shine nayo alwalar.
"Toki gabatar kafin nan na shirya saimu gabatar da wannan.
Toh tace mai ya ficce ita kuma tacanja kaya zuwa wata doguwar riga ta bacci. Kana ta saka hijab ta gabatar da sallar i'sha'in.

Yana zuwa room nasan yayi wanka da qara d'auro wata alwalar ya canja kaya shima zuwa na bacci duk NUFAISAT ta tsaya mishi arai.
Dan haka kwanciya yayi agadansa yahau kiran number nata. Saidai ya kira yafi sau goma amman taqi d'aga wayar. Nanko take hankalinsa ya tashi ya nufi part d'inta yana bugawa da kiran sunanta. Bata bud'e kofar ba. Saidai yaga shigowar message d'inta cikin wayar tasa.
Hakan yasa ya dena buga kofar ya shiga duba abin data rubutomai kamar haka.
_Haba mijina. Bayan ina tare dakai. Kawai bazan iya jure ganinka kazo yimin sallama zaka gun tawa bane. Hakan yasa na kulle kofata. Kuma idan na d'auki wayarka kuka zan fashe maka dashi wannan dalilin yasa naqi d'aga wayanka. Kaganni nan ina cikin koshin lafiya. Aci amarci lafiya da qanwata. Saidai Karka wahalar da ita. Dan bazan jure zuwa yin jinya da safe ba😌._

Murmushi ADAMS yayi da mamakinta. Kai shiyama kasa gane wane irin kishine da ita. Yau tanuna gobe kuma kaga kamar bata da matsala da dashi. Da wani hali ya tura mata da... _Allah ya barni dake matata. Wallahi zanyi maraicinki sosai cikin wannan dare. Kasancewar shine na biyu atarihin rayuwarmu da muka tab'a raba shinfid'a._
Yana tuna tura mata da hakan yabar ƙofar ɗakin nata.
Akan sallaya yaga TAUDHAT tana zaman jiransa yace da ita.. "Amin afuwa nabar amarya da jiran ango
"Batun afuwa babu tsakaninmu. Nasan dai akwai abinda ya riqemin kaine. "Kwarar kuwa yanxu tashi mu gabatar da sallar..
Haka tatashi suka gabatar da sallar
Yayi musu addu'a da tambayarta yanda take wankan tsarki tako gaya masa. Yaji dad'in haka. Sosai.
Haka yasa mata kaza a gaba da madara yace ta daure suci.
Ba wani kunya can tasake sukaci suka koshi. Kana labari ya canja.
Dan koda wasa Adams baiji aransa zai iya tsallakema TAUDHAT wannan dare batare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba.
Ya jata jikinsa yana aika mata da wasu sakwanni. Yana me jin dad'in yanda doguwar rigarce kawai a jikinta.
ADAMS gwanine qajen iya sarrafa mace. Danko a wasan ni ya barki bazaki tab'a San yabar rayuwarki ba.
Yasan kan mace fiye da komai arayuwarsa. Yasan yanda zai sarrafaki kimanta duniyar da kike.
Sannan idan yagane inda kikafi mutuwa agun yakan iya b'ata lokaci wajan ganin ya qara b'ullo miki da wata hanyar da zatafi wacce kikafi sani wajen mutuwa akanta.
Lamarin yana tsuma TAUDHAT sosai fah.
Dake tayi shaye shayen maganin mata hakan yasa Adams yaji dad'inta sosai.
Saidai hankalinsa ya tashi sosai dayaga ƙofar bashi bane ya fara bud'eta.
A hankali ya tashi da zama gefan gadan ya sauke kallansa akanta bayan komai ya wakana. Yasani ya bata wahala sosai. Dan yasan ba kowace mace bace wacce zata iya dashi imba NUFAISAT ba. Saidai TAUDHAT tabashi mamaki. Bayan yanda kofa take bud'e harda wasu salo data kware wajan nuna masa su.

D'an tashi tayi a hankali ta jingina da bangwan jikin gadan nata ta kallesa kad'an ganin ita kawai yake kallo saita sadda kanta qasa tace dashi.. "Kamin rai Ya mijina. Nasan na b'oye maka shi. Abun ya faru ne wata ranah danaje bikin wata qawarmu. Lokacin da aka tashi daga bikin. Sai wasu samari suka buqaci dana shiga motarsu suragemin hanya. Har nayi musu musu amma saboda nacinsu da qaddarar da take kaina saina shiga motar tasu. Adams ban tashi tsintar kaina ba sai a wani gida cikin wani d'aki kan gadan wani. Yana d'aya daga cikin SAMARIN dake cikin motar da suka d'aukoni. Yana gefena lokacin dana samu kaina. Anan nagane yayi min b'arna yayi min illa ya rabani da mutuncina da kimata. Nayi kuka nayimai Allah ya isa amman da dariya yabini da ita. Daga wannan ranah nake cikin kunci amman na kasa gayama kowa. Duk da cewar naje asibity an tabbatar min da lafiyata qalau bana tare da wani ciwo. Amman hakan bai sani nasamu nutsuwa ba. Dan nasan zan fuskanci qalubale agidan aurena.
Wannan dalilin yasa nayi saurin amincewa da auranka dan nasan kai kad'ai ne wanda zaka iya rufamin asiri ka rayu dani cikin aminci batare da nuna min tsana ko tsangwama ba. Da TAUDHAT tazo nan azancenta sai kawai tarushe da kuka kamar gaske☹

Shuru Adams yayi dajin tausayinta. Hakan yasa ya rungumeta da lallashinta akan tayi shuru insha Allah bata da matsala dashi.
Amman zai ibi jininta gobe dan yaje asibiti ya tabbatar da lafiyarsa.
Ba qaramin jin dad'i TAUDHAT tayi ba.
Dan batayi tunanin shirin nata zaiyi tasiri agunsa nan take haka ba.

Shiko Adams har a zuciyarsa yayarda da abinda tace mai. Hakan yasa yacire duk wani mugun tunani akanta da wani mamakinta dayaji yanzun yasaka aransa zai rayu da ita dan ya tabbatar ba qaramin lada zai samu agun Allah ba.

Haka ya tsaftace kansa itama ta tsaftace kanta. Ta koma da kwantawa shikuma yahau yin nafula da qara godema Allah akan al'amuransa. Saidai yaji ya qara San NUFAISAT aransa dan koba komai shine dai ya bud'eta aleda. Sannan uwa uba tafi TAUDHAT dadin harka. Duk da cewar yaji dad'in TAUDHAT d'in. Amman gamsuwar tashi yafi jinta agun NUFAISAT. Gaskiyama babu had'i
Haka kafin ya bar kan sallayar sanda ya tura ma da NUFAISAT message akan takula sosai da kanta. Babu wata y'a mace daza tasha gabansa akanta. Wallahi yanxu ya qara tabbatar da hakan.
Yana tura mata ya tashi da tashin TAUDHAT yana ce mata tatashi suje bedroom nasa su kwanta bazai iya kwana a d'akinta ba. Dan bai saba da hakan ba
Ba musu tabishi d'akinsa suka kwanta yana me rungumarta saboda sabo da yayi da NUFAISAT...

NUFAISAT ko tunda tasama ƙofarta key. Tayi sallar i'sha fad'awa tayi a gadanta kawai tana tunani barkatai akan yau ba ita ba kwana da mijinta. Zaije ya kwana da wata ba ita ba. Ya dinga mata abinda yake mata. Ai bata ankara ba!!! Wani kuka me ciwo ya kufce mata. Nan tadinga yi tana sambatu.
Tana jin bugun kofarsa na farko bayan ya raka abokanayen nasa amman taqi bud'emai. Dan wani haushinsa ne yazo ya rufeta. Gani take baiyi mata adalci ba
Tana jinsa yabar wajen
Haka kiranta daya dingayi awayama tana kallan wayar tayi burus da ita. Daya dawo ne yana qara buga mata kofar saitaji sanyi azuciyarta tatabbatar ya damu da ita. Hakan yasa ta tura masa da text message har yake bata amsar nan ta d'azu
Ganin ya qara turo mata da wani text d'in kusan biyu na dare hakan yasata ganewa komai ya wakana tsakaninsa da amaryar..
Hawaye me zafi yashiga bin kuncinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login