Showing 66001 words to 69000 words out of 81675 words

Chapter 23 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

kula. damma naji ajikina basu da niyar cutar dani.
Murmushi Dadyn yayi da cewa.. "Kadai ka kula da kanka da matanka.
"To nagode Dady sainazo.
Yana fad'in hakan ya kashe wayar da kallan YAWO yana cigaba da cewa. "Yace ya amince min.
Sosai YAWO tanuna Farin cikinta da qara yimai godiya. Kana ya bata umarni kan taje can waje wajen jira idan yaje ya duba MUSLEEMAN yaga tafarfad'o zai gaya mata..
Toh tace mai da matuqar jin dad'i...


Qarfe biyu NUFAISAT ta aikomai da tuwansa datamai. Kad'an yaci yabama YAWO sukaci da yaran.


Sai kusan qarfe biyar da rabi MUSLEEMA ta farfad'o..
Dake YAWO ta roqi Adams lokacin daya kawo musu tuwo tace mai yabarta tazauna a d'akin da MUSLEEMA take dan tana san ta farfad'o akan idanta. Ya amince mata da hakan badan suna yin hakan ba.
To shine lokacin da MUSLEEMAN ta farfad'o Yawon tana d'akin.
Dan haka cikin sauri YAWON tabata labarin yanda akayi bayan sumewarta. Sannan taqara mata da cewa karta tab'a gayama ADAMS cewa ita matarsa ce koda ya tambayeta yanxu. Ita dai duk abinda zaice mata tajishi kawai. Dan tana san tasan yanda yake rayuwarsa kafin subashi gaskiyar labari....
Kallanta MUSLEEMA tayi da cewa. "Indai zan qara rayuwar Aure dashi akaro na biyu zanyi duk abin da kikace. Sannan na godema Allah daya baiyana mana shi cikin sauqi.😀
Kan yawo tabata amsa saiga ADAMS d'in ya shigo d'akin.. Nan YAWO tashiga gayamai yanxu tafarka.
Murmushi yayima YAWON saita futa daga d'akin shi kuma yaja kujera Ahankali ya zauna daf da MUSLEEMA yana qarema fuskarta kallo yace.. "Mema sunanki.
Cikin sanyin murya gabanta na fad'uwa tace.. "Sunana MUSLEEMA.
" MUSLEEMAT. Ya maimaita sunan da cigaba da cewa.. Suna me dad'i. Yanxu me yake damunki.
"Ba abinda yake damuna.
"Har tunanin mijin naki.
Kallansa tayi da d'aga masa kai hawaye ya zubo mata tace.. "Eh har shi.
"Zan iya roqar wata alfarma agareki...
D'aga mai kai tayi alamar eh...
Yaci gaba da cewa. Zan d'auke ki matsayin qanwata idan har zaki iya cire damuwar mijinki aranki. Dan ina san naci nasarar bama zuciyarki kariya..

Murmushi tayi dinful nata ya losa tace.. "Nayi maka alqawari idan har ka'iya rik'eni da gaskiya. Ka'iya bama zuciyata kulawa da amana. Zan cire duk wata damuwa daga zuciyata na fuskanci sabowar rayuwa.
"Mijinki ya tab'a gaya miki cewa muryarki na dadad'i.
"Bashi da abin fad'a wanda ya wucce yaban duk wata halitta tawa.
"Toki kula da kanki. Dan yanxu zaki fara sabowar rayuwa. Bani fatan naqara ganinki kwance a wannan gadan dan matsalar ZUCIYA. Zan riqeki da gaskiya da amana qanwata. Zan baki kulawa fiye da yanda Yaya yake bama qanwarsa..
Ahankali ta sakar mai murmushi shima ya sakar mata. Sannan yace tatashi taci abinci ga toilet nan tayi sallah yanxu zaizo su tafi. Sunansa ADAMS..
Toh tace mai. Zuciyarta nasan tajita jikinsa. Ga qamshinsa me gyara tunaninta. Tana matuqar san mijinta..

Har yakai qofa tace da shi.. "YAYANA baka temaka min natashi ba.
Ahankali ya dawo da tsayawa gabanta yace. "Ba cemin kikayi yanxu baki jin ciwan komai ba.

Gabanta ne ya fad'i. Bata fatan ya futa batare dajita jikinsa ba.
Gaskiya qauna da SO da zafi suke azuci...
A shagwab'e kamar zatayi kuka tace mai.. "Na faɗin maka hakan ne kafin nagane qafata tana da matsala..
"Kina nufin bazaki iya takawa ba.
"Idan dai naganni a bayi na sakama qafar tawa ruwa me sanyi zata tashi. Dan dama tasaba yimin hakan... Takai qarshen zancen nata da shagwab'ewa. Abin gwanin ban wani iri haka👌🏻.
D'aukarta yayi ahankali yakaita toilet d'in sannan ya fito dajin dad'in yanda tafara saurin sakewa dashi.
Murmushi yayi aransa yana fad'in koma waye mijinta sosai yake shan fama da shagwab'arta..😂

Bai wani dad'e a office d'in nasa ba. ya kulle dan shidda har ta gota. Nan yasa masu tsaransa su kwashi kayansu MUSLEEMAT susa a shara...
Haka su MUSLEEMA sunaji suna gani aka saka kayansu a shara.
Saidai suna cikin tafiyar tasu suka biya wani saban biotic d'in Adams d'in daya bud'e anan ya ibamma MUSLEEMA kaya sunkai 20. Haka Khalit da Khalil ma & mamansa Rahma. Dan harya fara kiranta da mamansa. Dayaji sunan Amminsa take da shi.

Haka direct suka iso gidansa.
NUFAISAT taci adonta cikin riga da wando jajaye. Tayi kyau sosai.
A nazarce take qarema su MUSLEEMA kallo dayi musu sannu da zuwa. Sanda takawo musu ruwa da drink kana ADAMS ya mata nuna data biyosa shashinsa..

Dan haka saita cema su MUSLEEMAN tana zuwa.

Da mamaki akan fuskarta take tayasa rage kayan jikinsa dace mai... "Mijina suwaye way'an nan.
Jawota jikinsa yayi ta zauna kan cinyarsa saiya shiga bata amsa da... "Wasu y'an uwanki ne my luv. Dan Allah kiji tausayina ki tayani cika alqawarin danayi musu.
"Na kasa gane inda zancenka ya nufa.
"Bini Ahankali mana my luv aizan gaya miki komai..
Shuru tayi zuciyarta na bugawa.
Ahankali ya qara jawota jikinsa dakyau ya kwashe komai ya gaya mata..
Sanda ta nutsu sosai kana ta kallesa da cewa. "Nayi alk'awarin zan tayaka cika alk'awarinka mijina. Saidai bazan b'oye maka ba. Gabana ya fad'i lokacin dana d'aga ido na kalli MUSLEEMAT. Jikina ya bani zuciyarta tana d'auke da wani sak'o..

Jan hancinta ADAMS yayi da fad'in "Kawai ki gayamin mekikejin tsoro.
"Ina jin tsoran kar nasake da ita tazo ta auremin kai. Kamar yanda TAUDHAT tayimin.
"Kina san dawo da hannun agogo baya my luv. Kince min kin gane manufata na auran TAUDHAT danayi. Ya kamata kibar batun TAUDHAT. Sannan batun da kike akan wannan Babyn tayimin qarama ASO. Tayaya zan fara iyawa da ita idan na auretan.
Ya dace ki gane kece da ZUCHIYAR ADAMS har abada.
Kece me iyawa dashi har abada
Kece wacce ya fara so da qauna arayuwarsa....

"Kaga naji naji. Takatseshi da fad'in hakan. Tana me cigaba da cewa. Saidai katabbatar duk ran danaga MUSLEEMA tazama mata agareka zan d'auki hukuncin daya dace akanka. Sannan duk abinda nace awannan lokacin saika yishi..

Murmushi yayi da manna mata kiss💋 yana cewa "Na yarda...
"Ba yarda kad'ai ba. So nake ka d'aukimin alqawari.
"Na d'aukar miki alqawarin bani ba Auranta...
Tashi NUFAISAT tayi daga jikinsa fuskarta cike da murmushi ta manna masa kiss da cewa. "Idanko ka kuskure zaina yanka kowa ya rasa🙅🏻‍♀..
Waro ido ADAMS yayi😳 da cewa. "Yankawa fa kikace.
Da dariya sosai tace mai. "Eh. Kuma sai kana bacci zan yanketa fil🙈
Murmushi yayi dan ganin yanda taqarashe maganar tata da rufe idanta alamar taji kunyarsa. Kana ya tashi da qarasowa gabanta. Ya zare hannayanta daga fuskar tata yace... "Idan kika yimin hakan kinsan bani ba qara rayuwa. Magana ta gaskiya my Luv. tunda nake arayuwata ban tab'a d'aukar alqawari na tsinci kaina cikin fad'uwar gaba ba sai yau. Gaskiya wannan alama ce na akwai kuskure cikin alqawarin dana d'aukar miki yanxu..
Dan Allah kiba zuciyata nutsuwa kiyi hak'uri da wannan alqawarin. kiciresa daga zuciyarki kisa aranki tamkar ban d'aukar miki shi ba dan Allah..

Kama fuskarsa tayi da hannu biyu tana cewa. "Ai tunda naganta nasan akwai wani abu Wanda zai faru dani akanta nan gaba. Walau ni ko wani nawa.
Ina ganin akanka ne abin zai faru shiyasa naji araina.
Kawai na share nabarma Allah ikwansa. Zan kuma karb'i duk qaddarar dazata sameni sanadinta. Zan karb'a da hannu bibbiyu... Tana kawowa nan azancenta tarungumesa. shima rugumeta yayi cikin matuqar MASEEFAR SONTA..

Daqer ta kwaci kanta agunsa takoma wajensu YAWO.
Nan takaisu wani shashi na baqi agidan.
Falo ne da bedroom me toilet acikinsa
Ba komai a falan saisu TV da kafet da kujeru. Sai bedroom d'in shi kuma set d'in gado ne.
Bayan sun saka kayansu a durowa abinci me rai da lafiya NUFAISAT takawo musu
Nan YAWO tama NUFAISAT d'in godiya sosai.

Haka kawai NUFAISAT taji tana san YAWO da MUSLEEMA da yaranta
Nan tarungume yaran tace tara tabasu abincin nasu da kanta.
Murmushi MUSLEEMA tayi mata dan itama taji santa aranta sosai.
Ahankali taje ta durqusa a gabanta tace da ita. "Aunty dan Allah zaki d'aukeni matsayin qanwarki. Wallahi tallahi haka kawai naji ina sanki.
Sanda NUFAISAT tagama ba Khalit abincin da takai mai baki Sannan ta kalli MUSLEEMAN tace da mata. "Kawai kin rigani fad'a ne.
Zan d'aukeki kamar qanwata idan har kika sakemin way'annan yaran suka zama kamar nice mamansu...
Murmushi taqarayi da qarasa matsowa kusa da ita tace.. "Aunty na baki su. Dama yaranki ne. Kawai ni na Haifa miki sune..
Ahankali NUFAISAT ta kalleta. Nan take taqara jin qaunarta aranta Amman tashare da cewa. "Idanko haka ne zanyi saurin y'antaki cikin ZUCIYATA. Musamman idan kika kasance meyimin ladabi da biyayya..
"Aunty na d'auki alqawarin zanyi duk abinda kike cemin.. idan dai bazai sab'awa Allah da manzansa ba.

"Yauwa my sister yanxu kiyi wanka bara na kawo miki kayan bacci kisa dan kifi samun nutsuwa.
YAWO ma tayi. kiyima yaran Sannan ku kwanta. Na tabbatar zakufi samun nutsuwa...
"Toh MUSLEEMA tace mata.
Nan NUFAISAT taje ta kawo mata kayan bacci. Kana tayi musu sallama takoma shashin mijinta.
Lokacin bata samesa ba. Da alama yayi shashin TAUDHAT ne

Eh yana falan TAUDHAT dan duba lafiyarsu kamar yanda yasaba idan ya dawo yake shiga d'akin wacce bata da girki dashi dan duba lafiyarta.
Haneepha na jikinsa tana murnar ganinsa yake ba TAUDHAT labarin su MUSLEEMAT. Da yanda ya d'auki aniyar temakwansu.
Gumi ne yaketa tsattsafoma TAUDHAT. Hankalinta ya bala'in tashi da labarin da yake bata. Duk sai tanemi nutsuwarta tarasa...
"Wai meyake damunki ne naga kikata had'a gumi. Da alamama kamar kina cikin damuwa.
A furgice ta kallesa da gyara nutsuwarta tace da shi.. "Bansan me zance maka ba. Haka kawai naji hankalina bai kwanta dasu ba.

D'aga Haneepha yayi daga kan cinyarsa ya zaunar da ita kan kujera sannan ya qarasa gaban TAUDHAT da kama hannunta yace.... "Kar wani abu ya dameki. Hankalina ya kwanta dasu dari bisa dari. Dan haka kema ina san hankalinki ya kwanta dasu. Dan bazasu cutar miki da miji da qawarki da y'arki ba.😀
Murmushi tayi mai da d'agamai kai.
Ahankali ya sakar mata kiss a goshi da sakin hannunta ya sakarma Haneepha ma sannan yabar d'akin..
Ai yana futta TAUDHAT tatashi a rikice takira malamin nata da gaya masa komai.. Sannan taqara da cewa "Pls kasan yanda zakayi yanxu kajefemin bakinsu dukkansu. Tayanda bazasu tab'a gayama wani komai ba. Sannan ina san ganin bayan yaran. Dan Wallahi idan suka taso tawa taqare. Pls kayi wani abu akai yanxu....
"To ki kwantar da hankalinki kibani minti biyar zan kiraki yanxu..
"Toh tace mai da kashe wayar. Tana me safa da marwa cikin matsananciyar damuwam.

Canko bayan ya gama binciken nasa nan ya kirata dace mata.. "Gaskiya akwai matsala TAUDHAT..
Dan ainiyin fulanin daji nesu.
Ba wani abu dani zan iya yimusu. Saboda ita kakar tata tarigada ta dafa kanta da maganin tsari kala kala. Hakama tajiqa jikar tata da maganin bana wasa ba. Sannan suma yaran tunda sukazo duniya ta wankesu da ganyayyakinsu irin na fulani Wanda duk maseefar me jifa da matsafi da maye bai isa yaci yaran nan ba.
Sannan ita kanta uwar tasu yarinyar tana da ibada.. Sosai takema yaran nata dan Allah ya kare mata su.
Agaskiya TAUDHAT kifita daga harkar muta nan nan. Dan duk inda zakije bazaki samu galaba akansu ba.
Iya gaskiyar kenan dazan gaya miki itace tunda kikaga basu gayamai gaskiyar lamarin ba. To kibarsu ahakan. Ki dinga yimusu kirsa da kisisina yanda zasubar gidan wannan itace mafuta agareki...
"Kaga da Allah malam dakata. Naji duk abinda kace. Harsai yaushe zanta zama da maqiyana kana gayamin nabarsu bazan samu nasara akansu ba.
To bari kaji... zanje wajan bokan dayayi sanadin aurena da Adams yayimin maganin wannan matsalar
"Ba wajen boka ba. Kowajen wa zakije bazaki samu nasara akansu ba. Kuma na gaya miki iya gaskiyar ne kasancewarki uwar y'ata bani san kije kisha wahala. Tsaki TAUDHAT taja da kashe wayar tayi jifa da ita. Ranta abala'in b'ace.
Haneepha na kallanta tace.. "Momy malaminmu na islamiya yace babu kyau zuwa gun boka..
Galla mata wata muguwar harara TAUDHAT tayi da cewa. "Dan ubanki angaya miki gunsa zanje.
Shuru Haneepha tayi. (Kar me karatu ya manta Haneepha bata wucce shekara shidda ba idan ma takai. Amma take gayama uwar tata hakan.)


Shiko ADAMS rungume matarsa NUFAISAT yayi sukaji dad'insu abinsu. Sam basu da wata matsala.

Washe gari da safe NUFAISAT taje suka gaisa dasu YAWO.
MUSLEEMA tace zata raka NUFAISAT kitchen tatayata aiki.
Aiko NUFAISAT taji dad'in sake irinna MUSLEEMA.
Dan haka tare suka had'a kayan breakfast d'in.
Taba MUSLEEMA nasun takai nasu dining tajera ita da gwanin nata.

Suna breakfast d'in ne ta kalli ADAMS da cewa. "Saidai kamin afuwa. Dan MUSLEEMA tatayani had'a wannan breakfast d'in. Fatan kayafemin.
"Nayafe miki matata. Kuma dama tunda kika bata matsayin qanwa agarki dole nayi hakuri da duk wani abu dazan samu daga gareki naci Dan nasan dole tatemaka miki.
"Nagode mijina. Dafatan komai yayi zamzam.
"Sosai mah. Dan karna yaba ne ki zargeni shiyasa yin shuru. Dannaga lokacin da kuke aikin tare.
"Yabi abinka ai qanwa ce agareni.
Murmushi yayi mata da shafar gefan fuskarta..
"Ina sanki da yawa matata
"Gaskiya da fahimtar juna ce takaimu har iyanxu a SO Mijina. Nima ina san ka.😍


Koda yaje gun TAUDHAT dansu gaisa har a lokacin bata tare da nutsuwarta.
Nanma sanda ya qara tabbatar mata Bafa wani matsala mutanan arziqi ne. Sannan ya nufi gunsu MUSLEEMAT d'in...

Bayan sun gaisa da Yawo Ahankali ya kalli MUSLEEMA ya amsa gaisuwar da take masa a shagwab'e. shagwab'ar tata tana shigansa da zafi fah😒..
Da sanyin jiki yake cema YAWO "Zan turo salim qanina yakai yaran nan skull da islamiya anjima. dan bani san ganin yara haka ba karatu.
Godiya yawo tamai sosai sannan ya kalli MUSLEEMA tasakar mai murmushi shima ya mayar mata kana ya ficce daga d'akin zuwa motarsa.
Nan masu tsaran nasa sukayi gaba dashi..


Bayan NUFAISAT tagama komai na gyaran d'akinta saka Asiya tayi takira mata MUSLEEMA.
Bayan MUSLEEMAN tazo janta wani d'aki tayi suka zauna takira sunanta a nutse.
Nan MUSLEEMA ta kalleta da amsawa.
"Ina san kigayamin ainiyin labarinku. Dan zuciyata taqi gamsuwa da labarin da kakarki YAWO taba ADAMS akanku. Idan har kina san zama dani na amana to kiban labarinku na gaskiya..
Shuru MUSLEEMA tayi mata. Ita dai tun ganin farko taji tana san NUFAISAT d'in. Kuma taji aranta zata iya gaya mata komai na rayuwarta....
Qara kallan NUFAISAT d'in tayi da fashewa da kuka tace.. "Aunty kiyi hak'uri dajin labarinmu. Komai gaskiya YAWO tagayama Adams. Kawai dai ta boye wasu abubuwan ne.

"MUSLEEMA ina san sanin labarinku. Bazan iya hak'uri dashi ba..

Sanda MUSLEEMA tayi kukanta san ranta NUFAISAT bata hanata ba. Sannan takwashe labarinsu kaf ba abinda tarage tagayama NUFAISAT d'in.. Sannan taqara ta cewa.. "AUNTY MIJINKI ADAMS SHINE MIJINA UBAN ƳAƳANA. Wallahi Aunty ina matuqar laba'in sanshi kiyi hak'uri..

"Innalillahiwainna'ilaihirraji'un. Shine abinda NUFAISAT tace kanta na tsarawa. Nan tatashi taji jiri na ibanta.
Ai MUSLEEMA bata ankareba sai ganin NUFAISAT tayi ta zube qasa sumammiya..

Nan hankalin MUSLEEMA ya tashi. Gashi ba abin takira yawo YAWO ba. YAWO tasan tagayama NUFAISAT d'in komai.
Dan haka kitchen ta nufa ta ibo ruwa tadinga yayyafama NUFAISAT har Allah yasa NUFAISAT farfad'o..
Nan NUFAISAT taja numfashi duk da haka kanta bai dena Sara mata ba..
Nan hawaye ya shiga zubo mata.
MUSLEEMA da itama hawayen takeyi takama hannun NUFAISAT d'in tace.. "dan Allah Aunty karki nunama YAWO na gaya miki komai dan Allah..

Murmushi NUFAISAT tayi dace mata.. "Karki damu
MUSLEEMAT. Albarkacin qaunar da kika nunama ADAMS zan sadaki dashi cikin hikima. zakiji dad'insa fiye da yanda kikaji a rayuwar da kukayi a Ruga..
Saidai kimin alqawarin zaki kiresa amana. Kiza kik'eni amana.
"Aunty wallahi bani da mugun hali. Auntyna zakiji dad'ina. Aunty kece nake san kiriqeni amana. Aunty idan kin rikeni kamar qanwa zanji dad'in rayuwata. Bazanyi rashin uwa ba. Bazanyi rashi a maraici ba.

Rungumarta NUFAISAT tayi na d'an wani lokaci. Kana tace mata.. "Yanxu zaki fara sabuwar rayuwa. Zan fara gyaraki kafin nagayama Adams d'in komai. Idan kuma YAWO ta rigani shekenan kinga saidai kawai a gyara muku auranku.
"Aunty ina sanki Wallahi...
"Nima ina sanki Qanwata.

Sanda suka qara fahimtar juna sannan MUSLEEMA taje shashinsu.
NUFAISAT tayi murmushi da sakawa aranta zata riqe MUSLEEMA tsakaninta da Allah. Koda kuwa zata cutar da ita. Dan santa na hak'ik'a ne yayi ram da zuciyarta...


Follow me on wattpad @Rahamatnalele
Sadaukar da wannan shafi gareki ummu bashir nagode sosai da qaunar da kikemin cikinmu MARUBUTA. Ina sanki daji dake.. luv u 2 sister

Nagaida y'an hannuna🙏🏻
[7/31, 1:04 AM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Yanxu zaku iya following nawa a wattpad.* @Rahamanalele

” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 26☆

Ga TAUDHAT ko MUSLEEMA na komawa shashinsu. tafito daga part nata dayi nasu MUSLEEMAN..

Da mutuntawa YAWO take gaishe tana amsa mata daqer kamar ansata dole. Dama ita MUSLEEMA kallan farko datama TAUDHAT d'in nan tagane itace matar Adams d'in ta biyu..

Da izgilanci TAUDHAT take qare musu kallo musamman MUSLEEMA da yaranta. Sai zuwa can taja tsaki tace. "Dama kune y'an aikin da Adams ya kawo jiya.
Murmushin yaqe YAWO tayi mata da cewa.. "Eh mune y'ar nan. Kina buqatar muyi miki wani abu ne..

"Ba Sunana y'ar nan ba Baba. Kamar yanda kukazo aiki da Hajjiya ya dace kikirani.
"Toh Hajjiya kiyi hak'uri.
Tsaki taqara jah. Kana tace. "Amma wannan shine karanku na farko azuwa aiki ko.
Shuru YAWO tayi mata.
Saiko MUSLEEM ta karb'e maganar cikin sauri da cewa. "Eh wannan shine karanmu na farko. Allah yasa ba lefi mukayima Aunty NUFAISAT matar gidan ba...

Harara TAUDHAT ta galla ma MUSLEEMAN da faɗin. "Ce miki akayi NUFAISAT ita kad'aice matar gidan.
Murmushi MUSLEEMA tayi mata da cewa. "Ai mun d'auka ita kad'ai ce matar gidan.
"Toh mu biyu ne. Ita NUFAISAT ni kuma TAUDHAT.. Dan haka daga gobe zaku fara yimin aiki..
YAWO tace.. "Toh Allah ya kaimu darai da lafiya...
Tsaki taqara ja batare datace komai ba ta ficce daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login