Showing 51001 words to 54000 words out of 81675 words

Chapter 18 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

daɗin bayyanar ADAMS ba.

Dady ko sallar godiya ga Allah yake tayi dan ba qarya yaji mafificin Farin ciki sosai da yanda ADAMS ɗin ya bayyana.

ADAMS bai samu kansa ba sanda yakai kwana uku kana ya samu kansa.
Lokacin daya bud'e idansa qarema ɗakin dayake kallo ya fara yi. Yana tunanin meya kawosa asibiti haka...
Dake shigowar doctor Suleiman kenan wanda yafi bashi kulawa sai yayi murmushi dace mai. "Masha Allah. Allah abin godiya. Wlcm da tashi.
Murmushi ADAMS yayi masa da faɗin. "Yauwa. meya kawoni asibiti haka.
Murmushi doctor Suleiman ya qarayi yace.. "Bara dai na kira maka iyayenka sai kaji daga garesu. Amman kafin nan ɗan bani dama na qara tabbatar da lafiyarka..
Murmushi ADAMS d'in yayi mai kawai.
Ganin hakan saiya fara dubasa dakyau ya tabbatar yanxu bashi da wata matsala sai ɗan ciwan kai dayace mai yana damunsa.
Magani ya basa da ficcewa ya gayama su Dady ya farfad'o. Ainan take sukayi ciki da murnarsu. Dady ya kama hannunsa yana nuna masa zahirin Farin cikin da yake ciki.
Yace dashi. "Yanxu Ina ne yake kama ciwo my son.
ɗan ɓata fuska ADAMS yayi da cewa. "Kai na ne dai kawai.. Wai Dady meya faru dani ne aka kawoni asibiti.
Shuru Dady yamasa. Sai Amminsa ce ta amshi zancen da cewa. "kai zamu tambaya meya faru dakai. Amma ba yanzu ba sai mun koma gida.

Sun ɗan jima suna hira. Can dai ADAMS ya kasa haƙuri yace. "Ammi ina NUFAISAT da TAUDHAT ne & my daughter Haneepha..
"ADAMS kayi haƙuri mu koma gida mana. Yanzufa ka tashi ya dace kabama kanka lokaci ko kaɗan ne. Ta gayamai hakan da damuwa
Shuru ADAMS yayi. Yanxu jikinsa ya fara basa akwai wani abu da ya faru wanda basu san su gaya masa..

Haka zuwa can yamma bayan likitocin sun tabbatar da bashi da wata matsalar daza tasa su riƙesa sai kawai suka bashi sallama.
Adams yayi mamakin yanda ba asibitinsu aka kaishi ba.


Mamakinsa ya qara tabbatuwa ne lokacin da suka isa gidansa. Yaga canji dadama agidan. Dan Dady tun randa yaga ADAMS ɗin yasa aka fara gyaran gidan nasa. Anyi saban fanti anyi gyaran sauri dai gaskiya ba lafe gidan ya qara kyau. Anan yake sanar da masu tsaran Adams ɗin cewar anga Adams ɗin
Shiyasa yanxu da sukazo gidan sai shigowa suke suna masa barka da dawowa.
Shi dai amsawa kawai yake yi amma azahiri bai san meyasa suke mai barkan ba..

Lokacin daya shiga toilet wanka matsama kansa yayi da tunani yana san tuno wani abu. Amma sam bai tuno komai ba.

Bayan ya fitto yana shafa mai da alamama kayan shafe shafen nasa sabbine ne aka saka mai awajen. Murmushi kawai yayi yana tuna NUFAISAT dan itace ta fad'omai. "Wai suna ina ne.. Yayi furucin abayyane.
Sauri sauri gudu gudu haka ya gama kintsa kansa ya dawo falan nashi inda su Dady suke jiransa..
Anan sukace ya gaya musu bayan tafiyarsa garin gwambe meya faru dashi...
Ai dajin haka nan take ya fara tuno abin daya faru..
Sanda ya gaya musu komai wanda y'an iskan yaran nan suka masa.
Sannan yaqara da cewa.. "Wallahi Dady bayan hakan bansan kuma meya faru dani ba. Sai yanxu dana tsinci kaina a asibitin da muka dawo yanzu..

Jan numfashi Dady yayi sannan shima ya kwashe duk yanda al'amuran suka faru dasu anan..
Sosai ADAMS yayi mamakin abokin nasu Ibrahim. Ya tabbatar da lalle mutum abin tsoro ne. Amma banda haka hujjar dashi Ibrahim ɗin ya bayar wai akanta yake neman rayuwarsa sam ba abar dubawa bace awajensa shi.
Dan gani yayi ai ɗaukaka awajen Allah take kuma mutum baya tsallakema arziƙinsa

Hankalin ADAMS ya tashi sosai dajin yanda ya ibi shekaru masu tsawo haka. Gashi shi ya kasa tuno komai bare ya gaya musu gashi gashi ga rayuwar da yayi.. Saidai ya dace ya koma inda aminin Dadyn nasa ya tsinceshi yaga ko akwai wanda ya sanshi agun...

Nan dai yaci abinci me rai da lafiya wanda Amminsa tasa laraba me aikinta tayi masa tun sa'adda ya farfad'o.
Sanda ya gama ci take gayamai yau yaci girkin ƴar aiki. Da mamaki yake kallan Ammin tasa da cewa dama ba ita ce tayi mai ba. Hajjiya Rukayyat tace yi shuru dai kawai dan yau kaci girkin ƴar aiki..
Murmushi shida Dady da Salim sukayi.
Anan Dady yake cemai bara yaje gida ya kira iyayan matan nasa NUFAISAT da TAUDHAT dan agyara musu auran nasu..

Komai yayi daidai inji ADAMS.
Karb'ar wayarsa yayi gun Amminsa ya kira Yusuf awayar yake cemai... "Kai gauro ban mutu ba. Dena nemana nadawo gida cikin hankalina😂..
Yusuf dake kan gadansa damuwar kakarsa ta ishesa kan saiya nemo matar aure sai ganin kiran ADAMS ɗin kawai yayi awayarsa. Da matuqar mamaki ya amsa kiran yana addu'ar Allah yasa yaji muryar ADAMS d'in.. Aiko yana jin muryar tashi ya tatashi zumbur dace mai.. "Alhamdulillah.. Allah na gode maka daka dawomin da aminina ɗan uwa na. ALLAH kabarni dashi ko'a gidan ALJANNAH NE...
Dariya ADAMS yayi da faɗin. "Wato saida na ɓace kasan mahimmanci na agareka ko.
Yace "kamarko kasani ɗan uwa. Yanxu dai kana ina ne wallahi na zaƙu najika na ganka ko Farin cikin nawa yayi low.
"Saidai yayi hai✋🏻. Dan daga lahira nake magana dakai..😂
Dariya sukayi gabaki ɗaya.. Adams yana meci gaba da cemai yazo gidansa ya samesa yana so yaje yaga ƴan matansa wato NUFAISAT da TAUDHAT

Ai ba shiri Yusuf ya fito daga ɗakinsa direct ga motarsa ya nufa bai tsaya ako ina ba sai'a gidan ADAMS. Anan ko falansa ya gansa ya rungumesa suna masu jin daɗin ganin juna.
Sanda ADAMS ya bashi labarin komai. Sannan shima Yusuf yace. "Wallahi na shiga damuwa daban ganka a garin gwambe ba. Haka nashiga tashin hankali da Ibrahim yake bayanin wai shine wannan maqiyin naka me neman rayuwarka.
Wato ADAMS wallahi yanxu mutum tsoro yake ban. Shiyasa naqi yarda da kowa tun bayan ɓatanka bani da aboki. Yanxu naji mafificin Farin ciki sosai dana tsinci muryarka cikin wayata. Dole na qara Alwala nayi salla danna godema Allah daya qara haska fuskokinmu gani gaka...
Qara rungumarsa ADAMS yayi dan ga zahiri nan na damuwar rashin nasa ta bayyana ajikin Yusuf ɗin danya rame sosai gashi bashi da kuzarin da yake dashi kamar yanda ya sanshi.
Ahankali yace dashi. "Har abada bazan samu abokin gaskiya kamarka ba Yusuf. Wallahi ina sanka ina qaunarka kaci gaba da suna da amana nima zanci gaba dasanka da amana.
"Baka da matsala da hakan ADAMS. Yanxu dai ina muka nufa. Sannan banga su Dady ba.
"Eh su Dady sunyi gida. Yanxu dai rakani wajen matana zakayi naga awane yanayi suke. Duk da na samu labari agun Dady kana kulamin dasu sosai. Wannan ma yasa nake san qara gode maka..
"karka damu da wannan ma. Dan Idan baka waje komai naka abin dubawa nane. Haka nasan idan nima bana waje komai nawa abin dubawarka ne. Yanxu muje Kagansu hankalinka ya kwanta. Dan naga har wani rawar kai kake...
Murmushi ADAMS yayi da dakar kafaɗar Yusuf d'in Suka ficce daga falan...
Da sauri masu tsaransa sukazo dan bud'e musu mota sukaisu inda zasu.
Dakatar dasu ADAMS yayi da cewa.. "Yanxu na gane maqiyin nawa me neman rayuwata. Zanyi zama daku ran lahadi in sallameku dan dama nifa ba wani san yawo daku nake ba.
Cikin sanyin jiki suka kallesa da cewa. "Bamu fatan barinka oga. Saboda kai mutum ne. Kasan darajar ɗan Adam. Gashi abinda kake bamu yana wadatamu da iyalanmu. Idan har kace baka san kulawar da muke baka bazamu tab'a samun wanda zai dinga biyanmu yanda ya dace ba..
Jan numfashi ADAMS yayi da cewa... "Toh naji. Kudai had'a kanku ranar lahadi kusameni. Sannan yanxu dai bani buqatar kuyimin rakiya.
Toh suka cemai saiya shige motar Yusuf ya jasu..

Suna zuwa unguwar sukaga TAUDHAT ta fitto taci kwalliya ita da yarinyarta Haneepha.
Waro ido ADAMS yayi ganin yanda tayi ƙiba komai na jikinta ya cika tam tam. Ta qara wayewa da ganinta kasan tana jin daɗin rayuwa..
ADAMS yace. "Wow Hankalinta akwance.

"Kuma fa kwanan nan tafara qibar nan. Cewar Yusuf.
Tsaki Adams yaja da cewa. "Karka wani kareta malam. Yana faɗin hakan ya fitto daga motar sosai jikinsa yake fudda qamshin turaransa..
ƙamshinne ya bugi hancin TAUDHAT ta ɗago da saurinta dan jin wane mahalukin ne ya mallaki ƙamshin ADAMS...
Ai tana haɗa ido dashi tawancakalar da jakarta da wayarta kobi takan ƴarta Haneepha batayi ba ta daka wani tsalle saigata a ƙofar gidasu. Da sauri tashige cikin gidan nasu tana maida numfashi. Tunaninta gamo tayi. Dan yanxu tagama tunanin ADAMS d'in shiyasata tunanin ko wannan aljani ne.

Murmushi ADAMS yayi danya lura ta tsorata dashi ne.
Ahankali yaje ya kama hannun Haneepha tare da rage tsawansa yace da ita. "Haneepha kin gane ni. Shuru tamai tana me qarema fuskarsa kallo. Can tace. "Na ganeka kana kama da Dadyna na photo. Sai dai Dadyna ya fika fari.
Murmushi ADAMS yayi da manna mata kiss a goshi. Yace. "Nine Dadynki kawai nayi rashin lafiya ne yasa nayi baqin. Amman Farin nawa zai dawo nan kusa kinji..
"Toh Amma me yasa ka gudu ka barni baka zuwa guna. Kullum mamana ce take kaini skull kai baka kaini.
"Ba guduwa nayi ba. Nace miki bani da lafiya ne amma yanxu na samu sauqi kullum zaki dinga ganina kinji.
ɗaga masa kai tayi. Alamar taji..
D'auko jakar TAUDHAT d'in yayi da wayarta yaba Haneephan yana cigaba dace mata
Yanxu jeki gayama mamanki tafito..
Ai da gudu tayi cikin gidan tana cewa mamah mamah kifito ga Dadyna..

Kama hannunta TAUDHAT tayi da cewa. "Ya kama hannunki. "Har kiss yamin Dadyn. "Toh jeki gun mamah zanje ni gunsan.
Toh Haneepha tace mata tanufi gun mama dake zaune kan taburma tana cin burabisko..

Da qarfin hali TAUDHAT ta fitto tana qara had'a ido da ADAMS ya galla mata harara.
Sanda ta iso garesa yace mata. "Wai da ɗazu ina zaki kikaci wanka haka.
Kallansa da sauri tayi yanxu ta tabbatar da cewar shine. Cikin matuqar Farin ciki sosai tace.. "Wayyo Allahna wai da gaske Kaine agabana. Harfa na cire tsammanin ganinka.
Wayyo Allah abin godiya. Gaskiya naji mafificin daɗi da sanyi sosai. Kamar na rungumeka saidai gamu akan titi🙈.
Murmushi yayi da cewa "baki dai so hakan ba. Yanxu kaimu muga Mamah idan naganta anjima idan Aka dawomin dake kyayimin yanda kikeso tunda yanxu kin kasa.

Murmushi tayi da shigewa gaba tana cewa. "Muje kawai..
Haka tana gaba suna binta abaya har zuwa cikin gidan nasu.
Mama murmushi tayi mai da nuna mishi Farin cikinta Sosai na ganinsan da akayi. Har take qaramai ai bata dad'e dayin waya da Dadynsa ba yake gaya mata bayyanarsa.
Tana kyautata zatan anjima ma zaiso kan batun komawar TAUDHAT..
Murmushi ADAMS yayi suka tashi dayi mata sallama kan zasu shiga cikin gidansu NUFAISAT..
Nan taqara sakin fara'a dayi musu fatan alkairi.

Bayan sunfita ne TAUDHAT taja tsaki dacema Maman nata.. "Ke dai mamah bazaki dena munafunci ba. In banda munafunci Ashe d'azu da Dadyn ADAMS d'in kike waya shine kika kasa sanar dani angansan sanda yazo sannan nake sani...
Kallanta maman tayi kawai dan yanzu lamarin TAUDHAT d'in ya dena bata mamaki Sam...


Su Adams ko gidansu NUFAISAT suka shiga... NUFAISAT ɗin na barandarsu ta sama da wani littafin AUNTYN LUV tana karantawa me suna *ABU KAMAR WASA FAH* jaruman cikin labarin suna burgeta hakan yasa take tare da nishaɗi..
Ji tayi ajikinta kamar ana kallanta. Saita maida kallanta inda tafi tunanin daga nan ake kallan nata... Aiko sai ganin masoyin nata tayi shida Yusuf jikin motar mummy ɗinta....
Nan tatashi da yar da littafin tana me murza idanta danta tabbatar da gaske mijin nata ne abin alfaharinta..
Murmushi ya sakar mata da dafa Yusuf dan ta tabbatar dashi ɗin ne..
Aifa ƙafa me naci ban baki ba. Nan tasheqo da gudun gaske ta sauko qasa mummy dake falo tana yankan farce fad'i take "ke lafiyarki kike gudu haka.. Sam batabi ta akanta ba sanda tayi waje lokacin yayi daidai da ware mata hannunsa da yayi alamar ta rungumesa. Dama itama niyarta kenan. Ai zafin nama taje ta rungumesa.. Fad'i take. "Mijina ka dawo gareni. Mijina ne wallahi. Mijina ne Yusuf ba kowa ba. Mijina ne na tabbatar. Mijina ne naji ɗuminsa. Mijina ne shine wallahi... Saka mata hannunsa yayi a bakinta alamar tayi shuru danin yanda take a rikice .. Aiko shurun tayi idanta cikin nasa. Cikin sanyayyiyar murya yace.. "Bazan iya rayuwa babu ke ba! dan ina tabbatar miki ko mutuwa ce tazo d'aukata rokwanta zanyi ta had'a dake. Saboda ina san kabarinmu suyi makwaftaka da juna...
Tunda nadawo haiyacina farkwan tunanina kece my LUV.
Dan haka ki nutsu da kyau matata danki qara gaya min naji sanyi araina. Madallah. Yanzu gaya min ya kikaji da kika ganni...

Jan numfashi tayi
"Komai ma naji mijina. Na rikice matuqa da ganinka. Dan Allah kayima zuciyata gata kada ka qara aikata wannan babban lefi agareta.
Na shiga tashin hankali. Na shiga ɗimuwa sosai dana rasaka. Ashe da gaske kaine ganina. Dana rasa ganinka kowa haushin kallansa nake ji.. Ashe da gaske kaine jina. Dana rasa muryarka. Kowa jin muryarsa nake kamar maɗaci. Ashe da gaske kaine gangar jikina. Dana rasa ɗuminka rashin lafiya baibarni ba sai yanxu dana jini jikinka. Nayi missing abubuwa uku arayuwata. Wanda tunda ka ɓace har yau mummy da Dady wany'anda suka isa dani fama suke dani akansu.
Sun kaini asibiti yafi sau nawa akan hakan.
1 Bana cin abinci yanda ya dace. B'cos idan nasaka agabana kai nake tunani. 2 Bana bacci yanda ya dace. B'cos idan na kwanta kai nake tunani. Bana cika magana da kowa. B'cos daikai kaɗai na iya hira..
Meyasa hakan ta faru dani. Saboda karigada ka ɓata masu tarbiyar ƴa...
B'cos daka baka auranta kacanja musu duk wani abu da suka raineta dashi.
ADAMS kaine rayuwata. Nayi alqawarin bazan tab'a bari wani namiji ya raɓar maka jikina ba idan har na rasaka arayuwa saidai na mutu babu aure... NUFAISAT takai ƙarshen zancenta da zubo da hawaye..
Ahankali yahau lashe mata su. Cikin matuƙar so da ƙauna
"Ina sanki matata. Ina qaunarki matata. Ina fatan zarce kasancewa dake har agidan ALJANNAH....
Kai bakinta tayi cikin nasa ta aika masa da wani shu'umin kiss.... Cikin matuƙar buƙata yaso gyara mata mazauni a qirkinta wajen san su kasance da jin ɗumin bakin junansu. sai dai Yusuf ya katse musu jin dad'in nasu wajen cewa.... "Na farko agidan surukai kuke. Bacin nan saiku ɗan jin kirta agyara muku auranku...
Denawa NUFAISAT tayi cikin jin kunyarsa. Sai dai duk da haka sanda ts qara bajewa a qirjinsa tana lumshe ido da kallan Yusuf tace.. "Dole surukan su mana uziri..
Murmushi yayi da cewa.. "Kimana iso wajen momy kawai mu gaisheta idan yaso kwaci gaba..
ɗago da kanta ADAMS yayi da cewa.. "Kiyi haƙuri matata ganin yanda ya katse mana qauna...
"Da wani hali tace mai.. "Ba batun haƙuri kawai ka hukunta shine abun da zaifi.
Murmushi yayi da faɗin "Yusuf ne fa..
Itama murmushin tayi da bashi amsa da. "Tona nayi hak'uri.
"Yauwa masoyiya maza rakamu gun mummy itama taganni ta tabbatar.
Murmushi ta qara mai...

Hannunsa cikin nata haka suka shige gaba Yusuf na binsu a baya da murmushi akan fuskarsa dan Sosai suka birgesa. Har jin wani abu yayi aransa yadai yi addu'ar Allah ya kawo mai masoyiyarsa suma suyi rayuwa fiye da yanda ADAMS yake da NUFAISAT😄...

Sun gaisar da mummy inda tanuna Farin cikinta sosai da bayyanar ADAMS ɗin..
Haka suka baro gidan zuciyar ADAMS cike da buqatar kasancewa da NUFAISAT.


Da misalin qarfe takwas na dare iyayan nasu suka tattauna kan batun komawar su NUFAISAT d'in.. Bayan sunyi abin daya dace ADAMS yaso aranar akawo maisu. Saidai dole yayi haƙuri ya barma gobe. Aiko da misalin qarfe goma sha biyu TAUDHAT ta koma d'akinta. NUFAISAT ko sanda takai hud'u saboda shirye shiryen da mummy da Zainab suka tsaya yi mata..


Da misalin qarfe tara na dare ne yake tare dasu a falan nasa bayan ya gama gaya musu iya abinda yasani akan dukan da y'an iskan nan suka masa..
Nan yake tsokanarsu wai daga d'akin wayake ne kafin b'acewarsa.
TAUDHAT tayi kicin kicin tace a ɗakinta yake.
NUFAISAT ɗaure fuska tayi dan tasan kwanan shi d'aya a ɗakinta bai cikace mata na biyun ba yayi tafiyar.
Dan haka saita ɗaure fuska batace komai ba.

Ganin hakan saiya kalli TAUDHAT ɗin yace.. "Tunda yanxu sabuwar rayuwa zamu fara. Aisaina fara daga kan uwar gida nasan hakan duk bazai zama da matsala bako.
Kunyarsa ce tasa TAUDHAT ɗin cewa. "La wasafa nakeyi. Dama ban gama shirya maka kaina ba. Dan haka har azuciyata na amince kayi ko kwana nawa ne aɗakin ƙawata..
Kallan qasan ido NUFAISAT tayi mata Jin tana san sashi nishaɗi da makirci irin yace ita ɗin nan me haƙuri. Sai kawai NUFAISAT ɗin tayi saurin cewa.. "Ai kinsan kece ƙarama dan haka naci girma nadai barshi ya fara yin kwana biyun aɗakinki dan nasan wannan ba wani abu bane.. Saidai zarcewane bazan iya jurewa ba. dan nayi missing abubuwa masu mahimmanci agaresa wanda duk baccin duniya idan zanyi idan banji shi ahannun damana yana yimin su ba bana samun wannan nutsuwar da kowace mace take samu idan ta rufe idanta dan san yin baccin...
Harara TAUDHAT ta galla mata batare da ADAMS ya ganta ba. Itako NUFAISAT saita ɗaga mata gira alamar zamu ɗora daga inda muka tsaya...

"Toh yanxu dai kowaccenku ta barma ƴar uwarta ni ko. Shikenan ni zan yanke hukunci. Zan fara daga kanki NUFAISAT. Idan nayi kwana biyun na koma ga TAUDHAT ɗin..
Dan haka hira ta ƙare zanje na watsa ruwa...
Tashi TAUDHAT

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login