Showing 33001 words to 36000 words out of 81675 words
falan ya juyo da kallansa gareta yaci gaba da cewa... Ki fara neman canjin daga yanxu. Dan idan na dawo girkin naki naji canjin..
Tashi tayi a hankali tazo gabansa jikinta a sanyaye cikin wata murya tace mai. "Zan iya fitta unguwa yau..
"Zaki iya fitta akone lokaci banda dare kuma aduk lokacin da kikaso indai akan matsalar ne..
Murmushi ta sakar mai da cewa. "Nagode.
Shima Murmushin ya mayar mata da rungumarta ya sakar mata kiss a kumatu da d'ayan gefan kumatun kana ya ficce daga falan.. Ko shashin TAUDHAT baiyi ba ya shige mota masu tsaran nashi suka jashi.
Sanda sukayi nisa a tafiyar ne sannan ya tuna da TAUDHAT d'in saiya kirata awaya kan tayi mai uzuri ammishi kiran gaggawa ne.
Sanda ta magantu dan ganin da tayi yau lahadi ne kuma har ya iya ganawa da masu neman temako gunsa. Ya kuma qara komawa ga qawarta NUFAISAT amman ita ya kasa tsayawa ganinta koda na minti biyu ne..
Hakuri ya bata da cewa tamai uziri hakan bazata qara faruwa ba..
Tayi mai uzirin sannan tabishi da kalamai..
Murmushi kawai yayi da kashe wayar..
Itako NUFAISAT dafe kanta tayi cikin damuwa tana tunanin meyaja mata haka..
Can dataga tunanin bazai bata shawara ba dan haka sai kawai takira asiya da larai kan su qarasa mata aikin ta zata fitta ne.....
Aiko nan suka mata aikin cikin gaggawa sun fahimci tamatsu dasan tafitan akan lokaci..
Haka kawai suke jin tausayinta. Dan ganin yanda TAUDHAT ta aure mata mijin nata. qawarta aminiyarta..
Sun rasa ya akayi hakan ta faru.
Sudai suna Santa da qaunarta dan macece ita agaresu me kulawa da kyautata musu. sam bata y'amatarsu...
Suna gama yimata ta kulle shashinta sai gidansu..
Cikin nutsuwa ta zayyane ma mommy nata komai
ba wani batun kunya taqara da cewa.. "Nifa ina tunanin TAUDHAT tayi wani abu ne fitanta ranar mommy. Dan aranar yace yaji canji agareta..
"Idan ma tayi wani mugun abin ne kanta tayima bake ba.. Dan yanzu zanje na nema miki qaiqayi koma kan masheqiya kisha da Lipton insha Allah komai zaizo miki da sauqi..
Da murmushi NUFAISAT ta sakarma mommy d'in kiss a hannu tace.. "Nagode mommy..
"Ba komai ki jirani gun Hajjiya shuwa zani na ganta dashi da yawa satin daya wucce..
Dake acikin layin nasu ne Hajjiya shuwan take hakan yasa mommy d'in batafi minti goma ba tadawo da wani koren ganye shar adake..
Nan ta had'a mata Lipton tasaka mata maganin tabata tasha. Sannan ta kulle mata sauran tace taje dashi gida tasha na kwana uku insha Allah komai zaizo mata da sauqi
Saidai koda Adams ya dawo girkin NUFAISAT abin bai canja zani ba...
Aiko NUFAISAT na gane hakan ta fashe da kuka..
Bata kira mommy natan tagaya mata ba. Sai ta duqufa kaima Allah kukanta..
Ahaka Sanda suka shafe kusan wata uku da kwanaki ba abinda ya canja
Dan Yanxu ko kad'an Adams ya dena daurewa yana amfani da NUFAISAT d'in
Sam ya dena kulata ta wannan harkar..
Dan idan ya kulata gabansa zafi yake mai kamar ya saka kansa a rami me zafin wuta
Dan haka saiya denayi da ita ya kama kansa ran girkinta..
Tun abin na damun NUFAISAT har yazo ya dena damunta. Amman ganin da tayi sunfara d'aukar watanni nan hankalinta ya tashi dan koba komai ai ita mutum ce. Tana buqatar kulawar mijin nata..
Duk da cewar ko kad'an bai canja mata ba akan komai. Amman yanda wani lokacin yake juya mata qeya wajen kwanciya ai dole yafi d'aga mata hankali. Gashi taqi qara zuwa ta gayama mommy d'in nata. Ko zainab taqi gayama.
TAUDHAT tasamu yanda take so. dan wani ji da ita Adams yakeyi kamar ya cinyeta..
Dan kam yana samun yanda yakeso agunta.. Shiyasa yake yaqice damuwar rashin samun NUFAISAT da batayi akan hakan.....
Hajjiya Rukayyat tananan yanda take. Dan Hajjiya Hadiza sai shafe mata jiki take da jiqakken ararrab'i a zunmar shine maganin da bokaye suke bata.
Hajjiya Rukayyat bata wani damu ba dan tunda Hajjiya Hadizan tagaya mata babban bokansu yace bazata samu lafiya ba saita d'auki shekara d'aya ahaka ana shafe mata jinkinta da maganin da Hajjiya Hadizan take shafeta dashi Sannan zata samu lafiya.
Wannan yasa tasama kanta hakuri har izuwa lokacin daya iban mata..
Ammi na kallansu dan kotace ga wani agwada mata Hajjiya Rukayyat bata yarda dan Hajjiya Hadiza ta hure mata kunne akan karta yarda a mata amfani da wani magani. Dan bokan yace kar'a had'a mishi maganinsa dana wani..
Yau mommy takawoma NUFAISAT ziyara.
NUFAISAT tayi murna sosai. Sai ajima mommy d'in nata take Wannan ta ajiye mata wancan agabanta..
Komai dai Sanda mommy ta cakala dan nacin NUFAISAT d'in
Sunsha hira sosai har mommy d'in ta buqaci da NUFAISAT takaita shashin TAUDHAT su gaisa.
Nan take gaya mata ai tun safe fitan Adams itama ta ficce daga gidan bata san ina taje ba..
Mommy tace.. "Bakwama junanku sallama ne..
NUFAISAT tace "Munayi. Yanxu ne dai daga baya bamama junan namu saboda ita ta faro hakan. Nima saina kasance idan zan fitta bana yimata.
"Toh hakan bashi da kyau NUFAISAT. Idan batayi miki ba ke duk sa'adda zaki fitta kiyi mata..
"Toh mommy na gode.
"Ba komai. Saidai naga alamu sun nuna kamar har yanxu kina da damuwa.
"Eh ina da ita gaskiya mommy. "Toh mecece damuwar.
"Akan dai wacce muka tattauna dake ne watan nin baya
Shuru mommy tayi.. Sai zuwa can tace. "Wai kina nufin wannan qaiqayi koma kan masheqiyar dana baki baiyi miki ba..
D'aga mata kai NUFAISAT tayi.
Hakan sai yasa mommy Jan numfashi da mamakin y'ar tata. Ganin yanda tad'auki wannan watannin ahaka..
Can taqara Jan numfashi taci gaba da cewa.. Aida kinyi min magana dabaki kai iyanzu da matsalar ba.
Dan duk cutar da take damun bawa idan ya duba qur'ani maganinta na nan
Dan haka ki kwantar da hankalinki. Zanje wajen malam me y'an makaranta nasa shi ya rubuta miki suratul maryam da suratul Alrahama insha Allah ni'amarki data dawo za kuma kisha mamaki
Murmushi NUFAISAT tayi mata dan taji dad'in hakan sosai
Nan mommy tayi mata nasiha sosai dace mata idan suka kammala rubutun zata turo mata dashi..
NUFAISAT tace mata toh.
Mommy d'in tafitoh kenan zata shiga motarta saiga TAUDHAT nan tadawo daga anguwar tata..
Aiko da sauri tayi parking ta fito daga motar tata tagaida mommy d'in..
Da murna sosai mommy d'in ta amsa mata. Kana ta shige part d'inta
Ita kuma mommy d'in ta shige motarta tatafi..
Ashe TAUDHAT d'in tana cikin farin ciki ne yau. Dan bata dena sheqa ayarta da malamin nata ba..
Kwatsam yau taje garesa dan ya bata wasu magungunan mata shine yake gaya mata anya ba ciki bane da ita.. Ai dajin haka tace mai ya duba mata.
Abincikensa na duba ya gane mata da gaske tana da cikin.. Ta kalle shi da murna tace.. mai yanxu zan fara rainan d'an malam bana mijina ba. Kai amma wannan tsinanniyar mata tacuceni..
Dariya malamin nata yayi mata kawai batare daya ce komai
Shine da take kan hanyarta na dawowa gida ta biya wani qaramin asibiti kan amata gwajin ciki dan Allah
Suma sun tabbatar mata tana d'auke da ciki..
Toh wannan farin cikin ne yasata fittowa da sauri ta gaida mommy d'in NUFAISAT tayi part d'inta d'azu
Sai juyin jin dad'i take afalo tana murnar yau dole Adams ya nunama NUFAISAT iyakarta.. Tana San kwana dashi kuma gashi ba girkinta bane..
Shine take San yanxu ta kirasa tagaya masa cewar tana da ciki. Dan idan dare yayi ta kirasa tamai qaryar bata jin dad'i dan Allah yazo ya tayata kwana.. Tasan tunda yana san haihuwa bazai mata musu ba. Qilama ko gayama NUFAISAT d'in bazaiyi ba zaizo gareta da sauri...
Dan haka da sauri sauri tahau kiransa yana d'auka tace mai.. "Ako da yaushe fatan alkairi nake agareka...
Jan numfashi yayi dace mata "Nagode qawarmu. Ya akayi ne.
"K'aramin labari ne. Amman bansan ko awajenka babba bane..
"Toh gayamin. ina jinki.
"Dama ciki ne dani...
Murmushi ADAMS yayi da fad'in. "Mun gode Allah
Tabbas awaje qaramin labari ne. Agun iyayanmu kuma babban labari ne..
Zanso ace da zaki iya kizo asibitinmu yanxu na tabbatar da hakan da kaina...
Duk da taji ba dad'in yanda yace awajensa qaramin labari ne amman hakan baisa tanunamai ba. Dan cike da murna tace mai gata nan zuwa..
Tana isa Adams ya tabbatar da hakan.. Saidai yayi mamakin zuciyarsa dabaiji wani cikken shauqi a cikinta ba..
Dan yayi tsammanin duk lokacin dayaji matarsa nada ciki zaiji mafificin farin ciki. Sai kuma yaga abin ba haka bane..
Wata zuciyar ce mishi tayi kodan ba NUFAISAT bace..
Haka dai ya nuna jin dad'insa ba wani can ba. Dan azahiri ma ita TAUDHAT d'in tafishi zumud'i..
Haka tadawo gida da d'an damuwa dan yanda tayi tunanin zai haukace mata da murna sai taga baiyi mata hakan ba.
Dan haka sai takira malamin nata tagaya mai wai bataga wani farin cikin Adams akan cikin ba
Dariyar mugunta yayi mata da bata amsa.. Haba TAUDHAT. Kema kinsan mutane d'ai d'ai kune matansu suke musu irin hakan sununa farin cikin su nan take
Amman wasu basa jin shauqin hakan aransu tunda ai ba jininsu bane.
Haka dai zasuji farin ciki dan sun kasance sune mazan nasu. Amman Sam basa jin irin sosai d'innan..
Yanxu TAUDHAT ta fahimta. Amma taso daya nuna farin cikinsa da yawa da abin zaiyi mata dad'i sosai
Tana kashe wayar dashi Ammi takirata dayi mata murna ita da Dady
Da daddare ne da misalin qarfe gama sha d'aya da rabi na dare lokacin NUFAISAT na jikin Adams har sun fara bacci sai kiran wayan TAUDHAT ya shigo wayar Adams d'in bayan ya d'auka ne take cemai. "Mijin Qawa bana jin dad'in jikina Sam bana jin dad'insa...
Da damuwa Adams ya tashi kad'an yace.. "Meyake damunki.. "Gashi nan dai kamar zazzab'i ne da ciwan kai harda amai da ciwan baya. Ga ciki na na juyamin kamar zai fitta. Abin dai gashi nan babu dad'i Sam. Dan ALLAH kazo ka kwana dani ko zanji dad'i. Wallahi duk a tsorace nake gani nake kamar mutuwa zanyi acikin daran nan.
Saurin qarasa tashi Adams yayi da janye NUFAISAT daga jikinsa yace.. "Gani nan..
Har yakai kofa NUFAISAT tace mai "lafiya.. me yake faruwa naji kamar kana waya da TAUDHAT cikin wani hali.
"Eh wai batajin dad'i ne. Kuma wai cikin kamar zai fitta.
Waro ido NUFAISAT tayi gabanta na fad'uwa tace.. "Wane ciki kuma.
Dafe kansa Adams yayi da cewa.. "Kinga na manta in gaya miki. Ai tana d'auke da Ciki har na tsawan wata biyu..
Jan numfashi NUFAISAT tayi cikin mamaki tatashi da fad'in. "Muje. Allah yasa karya fittan..
Haka ko suka nufi shashin TAUDHAT d'in sun sameta a can bedroom lullub'e cikin bargo.
Adams ya yayeta dace mata sannu...
Nanta amsa daqer.. Saboda b'acin ran dataji naganin da NUFAISAT yazo.
Nan ya fara duba jikinta baiga wani abin tashin hankali ba.
Hakan yasa shi cewa.. "Jikin da sauqi ashe.. Shine kika wanibi kika rikitani
Da Sanyin murya tace.. "Bakaga yanda yayi min d'azu bane..
"Toh Allah ya sawake ya bada lafiya
"Amiin tace..
NUFAISAT tace.. "Allah ya bada lafiya. Na tayaki murna sosai Y'ar uwa Allah ya saukeki lafiya..
Da baqin ciki tace mata Amiin
Sai sukayi shuru dukkansu kawai suna masu kallanta.
Gaskiya Adams bazai iya kwana da TAUDHAT ran girkin NUFAISAT ba.
Dan yayi mata alk'awari bazai nuna mata wani hali akan samun cikin da wata matarsa zata samu ba..
Dan haka yace da TAUDHAT.. "Zamuje mu kwanta tunda jikin da sauqi basai an tayaki kwanan bako
"Zanso hakan idan za'a tayani gaskiya. Danni nasan abinda nake ji..
Cikin sauri NUFAISAT tace. "Kaga kaje ka kwanta nina kwana da ita.
Kamar ya dalla ma NUFAISAT mari haka yaji. Saboda baiji dad'in hakan.
Shi bazai iya kwana haka batare dajin d'umin d'aya daga cikinsu ba. Kuma ya lura tsaf futuna TAUDHAT takeji Wallahi ba wani abinda yake damunta.
B'cos ba wani alamar komai na ciwo ajikinta..
Ahankali ya ficcewa daga d'akin yana cema NUFAISAT d'in.. "Hakan yayi..
Yana fitta NUFAISAT ta kulle kofar da zama gefan gadan tana meyi mata kallan tausayi.
Aiko nan take TAUDHAT d'in tatashi da cillar da bargwan jikin nata ta gallama NUFAISAT harara tace. "Ke kam ke kam wannan akwaiki da baqin hali
D'an kwanan dazaki bar shi yayi anan shine abin baqin cikin naki da zakiyi saurin cewa ke zaki kwana dani. Idan kin kwana dani me zakimin..
Kingafa lafiyata qalau. Ba abinda yake damuna.
Kawai Babyn cikina ne yake san jin d'umin babansa..
Da mamakinta NUFAISAT tace "Ikwan Allah.. Wai yaushe zaki dena san kanki da yawa ne TAUDHAT..
Toh har ki mutu baza kiji dumin Adams ranar girki na ba. Dan haka kinga tafiyata..
Kumama tsaya... Da kike maganar Baby nasan jin d'umin jikin ubansa. Ai saikije can wajen wanda yayi miki Cikin yaji d'uminsa dan ba abinda momy Rukayyat bata gayamin ba.
Kasan cewar kar tafito tace kece kika kwantar da itan nan asirinki ya tuno shiyasa tayi gum da bakinta dan bata san asirinta ya tonu. Dan idan naki ya tono itama nata dole ya tonu. Wannan dalilin yasa ta gayamin duk abinda ya faru tsakaninki da ita
Tace duk ran da kika fito kikace kina da Ciki ba Cikin ADAMS bane Cikin wani ne can. dan ita tasan abinda tayi miki. Dan haka tace idan kinfito kince kina da ciki na tona miki asiri nace ba cikin Adams bane.. Sai dai Na gaya mata bazan iya hakan ba.
Saboda Allah na ganinki ni bazan tona miki asiri ba. Amman nasan komin daran dad'ewa shiALLAHN zai tona miki asirin..
Wannan yasa nacika da mamakin dayanzu yake gayamin wai ai kina da ciki. Nayi mamaki sosai dan banyi tunanin zaki iya aikata hakan da gaske da auranki ba..
Dan abin da mamaki matuqa yanda kike da auranki da mijinki dan neman duniya ki iya zuwa wajen wani qatan gard'e ya danqara miki ciki kizo kuma kina pretending kan na mijinki ne..
Nasan komai akanki yanxu TAUDHAT. Dan haka sai gayama wanda bai sani ba kina da cikin Adams. Amma nikam kar nake ganinki. Dan haka kishiga taitayinki ki fitta daga idona karki qara gigin shiga min hakk'i ran girki na akan wannan shegen cikin...
Dan zan miki rashin mutuncin dahar ki mutu ba'a tab'a yi miki irinsa ba..
Sannan ina nemamma momy Rukayyat afuwa kije can wajen bokan naki kice yayi hakuri ya karya wannan mugun asirin da kikayi mata.. Idan fa kinga zaki iya. Idan bazaki iya ba! ba dole dan tsakaninku ke da ita..
Da matuqar mamaki TAUDHAT take kallan NUFAISAT.. Cikin borin kunya tace da ita.. "Kimma kanki gata dabaki ce komai akan cikin nan ba..
Dan wallahi da kince dasai kinga abinda zai faru dake..
Dallah mata harara NUFAISAT tayi da cewa. "Angaya miki tsoranki ne yasani in cewa komai. Ko an gaya miki ina jin tsoran kiyimin wani abu ne..
Kawai dai naga dama ne na qashin kaina nace bazance komai ba. Dan bansan me Allah yake nufi da hakan ba..tana fad'in hakan ta bod'e kofa ta ficce daga d'akin...
Cije yatsa TAUDHAT tayi cikin matuqar baqin cikin yanda NUFAISAT tasan komai...
Adams yayi murnar ganin NUFAISAT dan sai juyi yake ya kasa baccin. Duk dako ba wani abu bane zai shiga tsakaninsu.
NUFAISAT ce mishi tayi TAUDHAT d'in ce tamatsa mata kan tatawo dan zata iya kwana mah ita kad'ai dan taji jikin da sauqi
Jinta kawai yayi dan dama alamu sun nuna mai lafiya lau take
Na gaida ku y'an hanuna...👐🏼👐🏼👐🏼
[7/6, 11:50 AM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
[email protected]
☆page 17☆
Washe gari mah gar Adams yaga TAUDHAT..
Yace da ita.. "Wow kice jiki Alhamdulillah..
Murmushi tamai da cewa "Masha Allah..
Kwana uku da zuwan mommy ta aikoma da NUFAISAT rubutun suratul maryam da suratul Alrahaman.. Wanda aka wanke da ruwan kankana..
Aiko tunda NUFAISAT tasha taji tanata zuba. Nan murna ta cikata hankalinta ya kwanta.
Ita da kanta ta nemi mijin nata. Ya kalleta sosai zaiyi magana amman ta hanasa tana cewa "yau nice da ranar..
"Kwananki ne kiyi duk yanda zakiyi dani.. Ya fad'i hakan da murmushi akan fuskarsa. Sannan yaci gaba da cewa.. Amma Allah yasa an samu canji.. Ya fad'i hakan da wani hali..
Fari tamai da ido da cewa.. "Tunda yau kaga hakan. inama kaina fatan alkairi kawai.
Ai dajin hakan yayi saurin rungumarta. cikin farin ciki da jin dad'i dan wallahi duk da yana jin dad'in TAUDHAT sosai yayi missing d'in matar tasa..
Tabbas ya tabbatar tadawo normal
Dan yajita yanda ya dace.
Yaji dad'inta fiye da jin dad'in dayake samu agun TAUDHAT ayanxu..
Komai yayi daidai yanxu. Dan NUFAISAT matsalarta takau..
Sam ayanxu ta rage jin tsanar TAUDHAT aranta. Sannan tasaka aran nata zamanta da ita na wani d'an lokaci ne. B'cos duk ranar da Adams ya san ita wacece cikin dake jikinta ba nasa bane. Tasan bazai qara rayuwa da ita ba
Ita kam ko ajikinta Dan sai rainan cikinta takeyi yana girma dajin wani san shi cikin ranta.
Sam bata dena sheqe ayarta da malamin nata ba.
Haka tasaka aranta zatayi hakuri ta zauna da NUFAISAT tunda ba yanda zatayi da ita.. (TAUDHAT kenan)
Adams bashi da matsala takone b'angare.
Dan baisama zuciyarshi matsalar ba
Duk wani abu da TAUDHAT zatayi danta fake da cikinta dan ya nunama NUFAISAT wani hali toh yayi fatali da wannan abun.
Shi mamaki mah take bashi idan tana irin hakan. Dan Sam baiyi tsammanin hakan daga gareta ba.
Shi yama aureta ne dan yasan ita bazata nunama NUFAISAT d'in wani hali irin hakan ba
Amman sai gashi tana sai lalle saita nuna mata...
Shine tun da ya fuskanci hakan ya taka mata birki shi da ita.
Dan tun ranar da NUFAISAT tayanke mata bata qara gigin aikata mata hakan ran girkinta ba
Amman idan itace da ADAMS d'in tata ja mishi lokaci yayin dazai fitta tace nan na mata ciwo can na damunta. Bata jin dad'in komai. Ire Iran way'annan abubuwan dai. Haka takeyi dan kawai