Showing 24001 words to 27000 words out of 81675 words

Chapter 9 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

ta rungumesa tsam. Dan nan take taji abinda takwana biyu bataji shi ba. Wato d'umin mijin nata. A hankali taji ranta na mata dad'i dasan su kasance ahakan.
Shima yaji mafificin dad'i da hakan data mai. Kamshinta kawai da yayi sabo dashi yana saukar masa da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Cikin sanyin murya tace da shi. "Kayima Zuciyata illa da yawa mijina. Tunda karaba fatata dajin d'uminka kullum. Karaba idanuna da San ganinka cikin dare kullum. Karaba kunnena da sauraranka kullum. Kagayamin wane hukunci ya dace dakai
Murmushi ADAMS yayi da d'ago da hab'arta yace.. "Wallahi ganinki yanxu da nayi ji nake kamar na cinyeki d'anye. Dan komai naki nayi missing d'inshi da yawa my luv.
Dan Allah matata kiyima Zuciyata gata kidena kullemin kofa.
"Yanxu ka gayamin hukuncin daya dace na yanke akanka.. Wato zan hana ganinka da zuciyarka ganina. Zan hana kunnuwanka da fatar jikinka saurarona da jina...
"Haba matata dan Allah kimin aikin gafara wallahi bazan qara yimiki wannan kuskuran cikin hankalina ba. Nayi nadama nayi dana sani nayi Allah wadai da wannan tunani nawa daya kitsamin na rasa wacce zan auro miki sai TAUDHAT..
"Kadena Allah wadai da tunaninka mijina. Dan abinda kayi shine ya dace dani. Shed'an ne ya shiga Zuciyata har yakaini dayi muku wannan borin.
Sanda naje gun mommy na tabani haske akan manufarka da dalilinka da kuma nufinka.
Nagode Allah daya bani kai amatsayin mijina mesan ganin farin cikina akowane lokaci.
Tabbas kayi gaskiya TAUDHAT itace ta dace da zama abokiyar zama. Agareni. dan baza tata aikatamin abinda bai dace ba
Haka nima nasanta bazan tab'a aikata mata abinda bazai dace ba.
Na yarda da TAUDHAT yanxu mijina d'ari bisa d'ari. Kuma ina San rayuwa da ita rayuwa tahar abada.
Yanxu muje na ganta na kama hannunta na gaya mata ita qawata ce kuma y'ar uwata ce har yanxu. Fatana takulamin dakai kamar yanda nake kula dakai..

Qara rungumarta yayi dan yaji dad'in bayanan nata. Ya tabbatar mahaifiyarta uwace dan ta'iya gyara masa gida..

Ahankali ya fara neman bakinta amma taqi dana nuna masa yanxu ba lokacinta bane lokacin TAUDHAT ne dan haka ya kula..
Baiji abinda ta gaya masa ba. Dan bai barta ba sanda yaji bakin dakyau...
Aiko tana manne ajikinsa suka nufi part d'in TAUDHAT d'in zuciyarta na bugawa dan baqaramin tsanar ganin TAUDHAT d'in take ba.
Aha dai suka samu TAUDHAT d'in a falo taci riga da wando kayan sun matseta ainun dan komai nata ya bayyana ya fito fili qara qara.
Hankalin NUFAISAT ya tashi matuqa😨 danta tabbatar lalle TAUDHAT so take ta kwace mata mijinta acikin lokaci qanqani tabarta can baki sake tana kuka da ihun aminiyarta ta cutar da ita ta aure mata miji.
ADAMS ko dagaske har cikin ransa kwalliyar TAUDHAT d'in ta birgesa amman yaga saurinta nayin hakan. Dan NUFAISAT sanda tayi sati biyu kafin tafara saka mai qananun kaya. Koda yake zamanine yazo da hakan. Dan kullum dad'a wayewa ake. Nan ya qara kallanta dakyau Saiya fad'a tunanin dukfa da hakan idan da kayan ne ajikin NUFAISAT ya tabbatar saiyafi d'aukarta. Saboda tad'anfi TAUDHAT abubuwan d'aukar hankali.
Ita kuma TAUDHAT ganin NUFAISAT da murmushi gata kuma manne jikin Adams ba qaramin fad'uwar gaba taji aranta ba. Nan take ta dibibice dan ranta b'aci yayi ainun.
Ba qaramin yaqi da zuciyarta NUFAISAT tayi ba wajen cewa.. "Nagode ma Allah dayasa nasameki cikin koshin lafiya haka. Takai qarshen zancen nata da sakarma Adams kiss a gefan kumatunsa shima ya sakar mata cikin kulawa kana ta zare jikinta daga nasa taje takama hannun TAUDHAT d'in daci gaba da cewa... Dama nazo nakama hannunki ne nanemi afuwarki daga takaicin dana nuna miki akan kyakkyawan udirinki na auransa da kikayi wajen San faranta min. Nagane gaskiyar mijina nufinsa akanki na aurokin da yayi. dan haka dan Allah kicire komai aranki kici gaba da d'aukata a matsayin qawa aminiya y'ar uwa. Dan muhad'u mu bama mijinmu farin ciki me d'orewa.
Kallan Adams taudhat tayi da maida kallan nata ga NUFAISAT tace "La.. karki damu. Ai dama nasan da wuri zaki gane manufarmu....
Galla mata harara NUFAISAT tayi tunda ta fahimci ta juyama Adams baya bayi ganinta sai tayi saurin bata amsa da cewa.. "Ina jin dad'in yanda kike da sauqin kan nuna komai ba komai bane
Cikin muryar qasa qasa TAUDHAT tace mata. "Hmm.. Wane saban shiri ne kuma wannan. NUFAISAT ta wurga mata kallan tsana itama cikin muryar qasa qasa tace.. "Irin shirin da kika d'auki lokaci kinayi wajen aure min miji.
"Idan ko haka ne kidena yinsa tun yanxu dan bazaki iya irinsa ba!
"Na rigada na shirya makaman yak'i dake taudhat. Wallahi ko'ana ha maza ha mata saikin gane ADAMS na irinmu ne mu kad'ai ba irinku karuwai mushirikai ba.
"Ni kuma saina nuna miki da irinmu ya dace bada irinku shashashai banzaye dolaye ba
"Idan da gaske na riqi Allah ke kuma kin riqi boka zanga tsakanin nidake wayake dacin galaba..
"Kasancewar ni ce nake fuskantar mijinmu ayanxu na lura ya fara zargin wani abu muke kullawa akansa. Dan haka ki adana kalamanki yanxu idan gobe tayi bayan ya fitta zanzo shashinki kifad'i maitarki ni kuma na baki amsarki
"OK. Ina nan ina jiranki me zuciyar maciya amana....
Kan TAUDHAT ta batama NUFAISAT amsa sai Adams yace.. "Wai me kuke fad'ama junanku ne haka naji kuna magana qasa qasa da alama akaina kuke maganar...
Murmushin yaqe TAUDHAT tayi da saurin figge hannunta daga na NUFAISAT tana niyar bashi amsa sai NUFAISAT tayi saurin juyawa garesa tace. "Hud'uba nake mata akan takulamin dakai. Dan idan tabarmin kai haka ba kulawa zan hukuntata irin sosai d'innan. Shine fa take ban hakuri... taqarashe maganar da kallan TAUDHAT d'in tana cigaba da cewa. Ko ba haka bane.
D'aga mata kai TAUDHAT tayi da cewa. "Haka ne man. hmm haka.
Murmushi ADAMS yayi da qarasowa ya kama hannun NUFAISAT ya sakar mata kiss da cewa.. "Nagode matata. Sannan kulamin da kanki. Ina miki fatan ALKAIRI akan kitashi lafiya.
Mayar mishi da kiss d'in tayi itama a hannunsa tace... "Tare dakai mijina. Kana taje ta rungumi TAUDHAT dacigaba da cewa.. Tare dakema Yar uwata... Tana fad'in hakan ta ficce daga d'akin tana jin wani iri aranta
Ko ba komai taji dad'in aranta. Yanxu ta fahimci agaban kowa Adams zai iya bata kulawa. Kuma Wallahi saita nunama TAUDHAT iya karta.

Adams ko part d'insa ya nufa yana me cema TAUDHAT gaskiya Kinyi kyau sosai Qawarmu. Zanso nayi wanka na biya kud'insa
Murmushi baqin ciki tayi da bashi amsa da cewa. "Nagode mijin qawa...
Har yakai kusa da part d'insa ya juya da kallansa gareta da cewa.. "Wato baza'a canjamin suna daga mijin qawa na koma wani ba ko.
"Toh ai sunan daya dace dakai ne.
"Kuma fa haka ne. Tunda NUFAISAT tace kuci gaba da d'aukar junanku kamar yanda kuke dah.
Kici gaba da kirana da mijin qawa. Zanci gaba da kiranki qawarmu. Zataci gaba da kiranki y'ar uwa. Ki had'amin komai na abinci dan nadawo da yunwa sosai.
Murmushi tayi dace masa "Toh..

Yana shigewa part d'in nasan tasakar mai harara da cewa. Ba kana rawar kai wai kai ka shirya da matarka ba. Wallahi duk sainayi maganinku....


Kuyimin afuwa y'an hannuna. Bana jin dad'i ne shiyasa kuka jini shuru. Sosai nagode da kulawar da kuka bani sisters🙋🏻‍♀ MUSLEEMAT na zuwa gareku cikin wannan labari nawa😌
[6/28, 11:46 PM] ®🔳◾◼▪official Auntyn Luv.: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 14☆



Da b'aqin ciki ta nufi dining dan had'a masa abincin

NUFAISAT ko zama tayi afalanta tasauke numfashi sannan ta nufi toilet tayo alwala da gabatar da sallar Magrib...

Washe gari da misalin qarfe takwas da rabi Adams ne ya gama shirinsa nasan zuwa ga asibitin nasu
A hankali ya kalli TAUDHAT dace mata. "Ki duba yanda kwanaki suke shigewa. Mutane na cigaba da aikata abinda sukeyi. Wai yau idan Allah ya kaimu dare kwanan mu hud'u kenan da aure..
Murmushi ta sakar mai da cewa. "Eh wallahi. Allah dai yasa mu dace.
"Amiin
"Gaskiya kayi kyau mijin ƙawa..
Kallan kansa yayi da d'aukar jakarsa yana me cewa. "Nagode ƙawarmu ya fad'i hakan da ficcewa daga falan nata ya nufi kofar da zata sadashi da shashin NUFAISAT cikin sauqi.
Hard'e ya ganta akan kujera taci uban ado kamar ba NUFAISAT d'insa ba.
Dan gani yayi tayi irin wannan adan da matan yanxu keyi wajan fitar da tsarin jagira me kyau.
Ga wani salan d'aurin d'an kwali datayi me d'aukar hankali. Falan sai qamshi yake zubawa me tafiya da zuciyar masoyi.
Riga da siket ne ajikinta y'an kanti. Sun matseta da fitar mata da tsarin halittarta. Kalan kayan milk colour ne. Gaskiya matar tashi tayi mai 💯. Hakan yasa yaqi qarasawa cikin falan ya tsaya cak da sakar jakarsa ya ware hannuwansa alamar tazo garesa. Aiko da gudu taje ta rungumesa tana me sakar mai kiss a baki.. Fad'i take. "Gaskiya na zaƙu kadawo gareni naji d'umin jikinka da kyau mijina.
"Kwantar da hankalinki my luv. Dan saura kwana uku kacal nadawo gareki.
"Ina sanka mijina. "Ina ƙaunarki matata...
Sun d'an b'ata lokaci suna masu shaƙar ƙamshin juna tare da ɗumin jiki. Kana sukama juna sallama cike da qauna..
TAUDHAT naganin fitar Adams tafito da sauri dan zuwa shashin NUFAISAT
Saboda ta kwana da abinda ya faru tsakaninta da ita jiya. Sam bata wani bama Adams kulawa cikin daran nasu na jiyan ba. Saboda tsabar tunani.

NUFAISAT na k'ok'arin neman inda tasa wayarta saiji tayi kawai an banko mata kofa alamar wanda yazo garetan afusace yake.
Ta d'aga kai taga TAUDHAT ce. Aiko nan take ta b'ata fuska dace mata. "Haba malama miye haka. Ya zaki shigomin falo kamar wata y'ar arna babu sallama sannan afusace. Idan fad'a kikayi da Mijinki ko kin samu sab'ani da masu aikin gidan nan naga bai dace kizo ki sauke akan ƙofata ba.
Galla mata wata muguwar harara TAUDHAT tayi da cewa. Idan fatanki inyi fad'a da miji dan kiji dad'i ne to kisa aranki wannan ranar bazata tab'a zuwa gareni da Adams ba
Sab'ani ko da ma'aikata saidai ke kisamu dasu keda kika sakar masu. Dan wallahi ko baqi nayi basu ba samun sab'ani da ma'aika. Bare ni matar gida aisai kawai kiga babusu agidan nasa an koresu.
Mezai kawoni shashinki idan ba kece kika ja nazo ba. Idan kin manta ne nazo muyi magana akan maganganun da mukayi dake jiya

"Ayya kice da abin kika kwana aranki.
Kinga ko duk da nice na tsokano zancen amman ban kwana dashi arai ba. kiyi hakuri na manta ashe haka nan ayanxu gari banza bazaki iya zuwa shashina ba saboda cin amanar da kikayi agareni.
Yanzu dai gayamun meke tafe dake. Dan da gaske ayanzu na manta kalaman dasuka shiga tsakanina dake awannan lokacin.
Murmushin baqin ciki TAUDHAT tayi da cewa... "Nima ayanxu na manta. Kawai dai bari naja miki kunne akan ADAMS. Ya dace ki gane ayanxu Sam bai dace dake ba. Dani TAUDHAT ya dace. saboda nice zan iya d'aukar kowane abu idan yaxo dashi. Kasancewar nafiki sanin abubu dadama. Ina baki shawara datun wuri kinemi takaddar sakinki agunsa kije can kisamu daidai dake tunkan nafara nuna miki TAUDHAT d'in da kika sani da! Ba itace yanxu agabanki ba.
Kallan raini NUFAISAT tayi mata da sheqewa da dariya tace... "Ikwan ALLAH. Idan daranka bazaka dena ganin daqiqai aduniya ba. Idan daranka zakaga abubuwa dadama na faruwa. Idan da ranka zakasha kallo inji malam bahaushe. Nufaisat na kawowa nan azancanta. ta tsaida dariyarta da kama gudunta ta kafe TAUDHAT ƙirr da ido taciga da cewa... Toke yanzu in banda daƙiƙanci ya samu zama a kwakwalwarki yaushe zaki dubeni sama da qasa kice wai ban dace da Adams ba. Naga nafiki wayewa tunda nafiki ilimi da sanin abinda yadace me hankali ya aikata ma d'an uwansa musulmi. Ma'ana bazan tab'a cutar da mutumin daya bani gaskiya da amana ba. Bazan tab'a cin amanar wanda yayarda dani ba. Bazan tab'a aikatama wanda yasoni tsakani da Allah da wani abu wanda zai d'aga mishi hankali ba..
Naga nafiki komai wanda maza keso ajikin y'a mace. Ma'ana nafiki kyan fuska. Nafiki kyan sura. Nafiki kyan mazaunar da nonuwa masu kyau nad'aukar hankalin maza. Uwa uba na fiki kyan hali halin da Allah keso manzan Allah keso ki gayamin ta inda kikafi dacewa da ADAM wanda ni NUFAISAT y'ar gaban goshinsa ban dace dashi ba
Sannan da kike wani maganar zaki nunamin TAUDHAT d'in dana sani da zaki nunamin ba itace yanxu agabana ba. An gaya miki ban dad'e da canja miki matsaya bane akan sanin danayi miki da dana yanxu.
Da nasan TAUDHAT d'in dana sani kamulalliyace wacce tasan abinda ya dace da ita. Me sona me nuna min qauna agaban kowa.
Yanxu kuma ta canja kamar yanda yanayi yake canjawa takoma karuwa me bin bokaye da malamai tsubbu ta kuma muguwa maciyiya amana.
Tayaya kike tunanin zanci gaba da barinki awancan matsaya dana barki dashi azuciya tunna k'uruciya. Bakiyi tunanin zan canja miki matsayi saboda canjin da nagani zahiri agareki ba
Toki kama kanki tunkan dare yayi miki dan tun ranar da kika kaini wajen boka da nuna min malami ne. Tun daga Wannan ranah nasaka azuciyata TAUDHAT d'in dana sani ba itace yanxu ba.
Saiyakasance daga ranar dana gane kice kishiyata nacanja nima nazama wata NUFAISAT wacce keda kanki zaki furta nan gaba ba wacce kika sani bace.
Sannan da kike cewa naje nanemi takaddar sakina a wajensa naje can nanemi daidai dani. To ADAMS shine daidai dani. Ko an gaya miki ina d'aya daga cikin jerin matayen da suke barma karuwai mazajensu ne.
Wallahi idan ni banje nace yaban takaddata ba ke zakije kice mai ya baki taki saboda qarfinki da zanfi akan komai..
Ya kamata kigane lokacin dazan iya baki yaxo qarshe dan haka kifitarmin daga d'aki saboda y'ar uwata Zainab zatazo ina San nayi mata wani abu wanda zatasa abakinta. Kinsan yanxu NUFAISAT ta iya girka fiye da tunaninki.
Murmushin takaici TAUDHAT tayi. Wato NUFAISAT batasan wacece ita ba. Rai bace tace da ita.. "Ke kin isa ki jefeni da mugayan kalamai sannan na futta daga d'akinki batare dana mayar miki kona d'auki fansa ba.
NUFAISAT tayi mata kallan tsana tace. "Na k'ara miki lokaci to. Kina da damar mayar min koki d'auki fansar...
Ai NUFAISAT bata ida zancenta da numfashi ba TAUDHAT ta ɗauketa
da wani shegen mari... Cikin b'acin rai saboda jin wata sabowar maguwar tsanarta da taji tsanar datafi tako yaushe muni..
Cikin matuk'ar mamaki tayi saurin dafe kuncin tana tare da cewa.. "TAUDHAT ni NUFAISAT ni kika Mara..😨
Girgiza mata kai TAUDHAT tayi da murmushin mugunta tace.. "aa.. Kawai dai na maimaita miki irin wanda mijinki yayi miki ne agabana. Saboda na lura idan haukarki tatashi sai'an tab'a lafiyarki kike dawowa cikin hankalinki. Saidai zanso kikoma gefan kujerarki. B'cos idan kin tashi sumewa ki sume kan kujerarki. Saboda ayanxu bame rikicewa wajen San ki farfad'o saidai ki wucce daga nan idan kuma kina da nisan kona ki farfad'o da kanki. Oho na manta kince zainab zatazo idan tazo tatemaka da yayyafa miki ruwa wajen farfad'owan......
Aiko itama TAUDHAT d'in bata ida zancen nata da numfashi ba NUFAISAT ta ɗauketa da wani masiyacin mari... Wanda hakan bai isheta ba sanda taqara mata da wani. Daga ƙarshe kuma ta rufeta da duka tana cewa bara na nuna miki cikakkiyar haukan...
Lokaci d'aya fad'a ya kaure tsakaninsu..... Dai dai da lokacin da Asiya me yima NUFAISAT hidima tashigo falan ita da Zainab yayar NUFAISAT d'in.
Hankalin Zainab ya tashi matuqa dan ita macece wacce bata saba da ganin fad'a haka manya dasu ba...
Duk yanda sukaso ita da Asiya su rabasu amman abin yaci tura.
TAUDHAT ta d'auki wata kwalba ta turare ta rotsama NUFAISAT agefan ka🙆🏻‍♀..
Ai daga nin haka cikin Zainab ya d'uru ruwa... Bata San lokacin data danna number na Adams ta gaya mai gashi NUFAISAT da TAUDHAT suna fad'a zasu kashe junansu ba...
Zuwan Adams office d'insa kenan yaji wannan mummunan labarin abakin TAUDHAT...
Ai ba shiri ya fitto daga office d'in ya shige mota da tsawa yake cema direbansa yayi sauri yanxu ya maida shi gida...

NUFAISAT najin azabar rod'a mata kwalbar da TAUDHAT tayi nan taje tararomo wata bishiyarta dake gefan TVstan d'inta tanufo TAUDHAT da ita gadan gadan da nufin ta caka mata aciki kasancewar bakin bishiyar yayi sirisiri tsini tsini haka. amman TAUDHAT ta kauce aiko sanda NUFAISAT ta caketa agefan mazauninta... Nan ko jini ya fara fitta daga wajen kamar yanda jini ya wanke fuskar NUFAISAT...
Ai bashiri Zainab da Asiya suka kwalla qara da rabtaba salati suna masu neman akawo musu agaji. Dan ahakan ma ba denawa sukayi ba..
Dan NUFAISAT yar da bishiyar tayi da niyar cakamo wiyan TAUDHAT saidai kamar TAUDHAT d'in ta ankare nan ita tafara kamo wiyan NUFAISAT suka zube kan tiles duk jini ya b'ata musu jiki... Dai dai nan Adams ya sawo kai cikin falan dan anan yaji hayaniyar...
Taqer ya iya rabasu ransa yayi matuqar b'aci basoda yanda jini ke fitta daga jikinsu amman dan bala'i basu sararama junansu ba.... (Shed'an la'ananne daya had'a futunar yana gefe yana musu dariya.)
_Allah ka karemu daga sharrinsa Ameen_

Haka Adams ya danne zuciyarsa yasamu suka lallab'asu suka shiga cikin mota harda shi direban yajasu yana cema Zainab dan Allah tad'an jirasu yanxu zasu dawo.. Toh tace mai cikin damuwa.

Dr Aryan ne dai ya dubasu..
NUFAISAT tasha nani wajen saman kunnanta Yayinda TAUDHAT tasha gyara a gefan mazauninta
Adams baice musu komai ba. haka suka qara shiga motar wannan karan shiya jasu.

Ababban falan nasu ya had'asu yana me tambayarsu meya tayar musu da wannan futunar..
Duk shuru suka mai. Ransa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login