Showing 48001 words to 51000 words out of 155647 words

Chapter 17 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

465

tunanin mai email d'in nima, saiku fara bincike akan mutane 5 d'innan daya turo mana numbers nasu, kasanarma fharuk sukula sosai, idankuma sukaimin wasa nadawo office tabbas zand'auki mataki akan kowa".
" tom shikenan, ALLAH yasa mudace".
"Ameen, yamaganar yaran da aka kama agidannan?".
" yes sir! Suma muna bincike akansu, amma bamu matsantaba sosai, muna jira saika dawo kan aiiki, mun dai kaisu d'akin duhu".
"Ok, kubarsu saina dawo d'in".

Sund'an k'ara tattunawa akan aikin.
Daga baya kuma suka koma tsokanar juna irinna abokai, abinma dariya yabama Aysha, wato idan ana fagen aiki babu wasa tsakaninsu, saidai girmamawa juna, idan kuma aka dawo fannin abota saikaga an canja, afirar tasune ya khaleel yake sanarmasa bashida lfy, nandai taheer ya jajanta masa, harya juyo yana tsokanar Aysha, wai kodai ciwon angon NATA Na wayaune dan a k'ara masa Hutu yasha amarcine?, batadaice komaiba sai murmushi Dan kunyar taheer d'in takeji.
Yace, "su shirya weekend d'innan insha ALLAH zasu kawo musu ziyara suda matansu, dama sund'an basu iskane susha amarci.
Ya khaleel yace, " ALLAH yakawoku to, muna zuba idanu".
''Insha ALLAH zamuzo".

Taheer yad'an dad'e agidan kafin yamusu sallama yatafi.


Cikin matuk'ar farinciki Aysha ta turama Anty meerah sak'o, wai sunci nasara, aikinsu yayi, harma su ya khaleel sun kama k'awar Anty glory Ruth.
Meerah tayi farinciki sosai, Dan kullum burinta dama bai wuce ta rusa k'ungiyar su glory ba..
Meerah ta tabbatar ma Aysha tashirya gobe idan ALLAH ya kaimu zasuzo musu sallam, Dan jibi jirginsu zai d'aga zuwa Canada, dama Dady da maheer tun washe garin d'aurin aure suka koma, maheer zai fara exam ne a school, dady kuma saboda aiki.
Ya naufal kam akwai aikin daya rik'esa anan Nigeria, shiyyasa su meerah suka tsaya jiransa.
Cikin d'oki Aysha tace, "ALLAH ya kaimu lfy Anty meerah na".
Meerah tayi dariya, "oh ke lil sholyna, har yau dai ba'a canjaba, k'uruciya fal ciki, ya khaleel na hak'uri dai".
"Kai Anty meerah, saikace wata jinjira?". 'Tayi maganar a shagwa6e'.
Cikin dariya meerah tace, "sai anjima, kigaida boss".
Bata jira cewar Aysha bata ta yanke wayar.
'Yar dariya Aysha tayi itama kawai, tana fad'in " I love you Anty meerah na, kina sakani farinciki wlhy, ked'in tadabance atarihina=?
?.




___________________________
Alhmdllh ya khaleel sauk'i yasamu, harma yad'an fita iya nan tsakar gidansu yanashan iska, Aysha data kammala gyara ko ina na gidan nasu, tasaka turaren wuta ko ina yad'auki k'amshi, komai tanayinsa cikin nishad'ine, saboda d'okin zuwansu meerah gidan, ga mama zata dawo yau.
d'akinta tashige domin yin wanka tacire kayanta, tad'aura guntun towel, tana tsaye gaban madubi tana tura sak'o ta email d'insu na sirri gasu ya khaleel, sai zabga murmushi takeyi.
d'agowarnan dazatayi suka had'a ido da ya khaleel ta madubi, yana tsaye a bayanta.
Kawai saita fasa k'ara saboda tsoratar datayi.
Cikin sauri ya tallafota tafad'o jikinsa, wani mugun bugu zuciyar Aysha keyi, babu abinda take ambata sai innalillahi wa'inna'ilairraji'un, shikenan k'aryarta ta k'are, inhar ya khaleel yaga email d'innan nasune, cikin dabara tasaki wayar ak'asa, tasaka k'afarta ta shureta kamar bata ganiba, wayar tashige k'ark'ashin gadonta.
Shikam tana rungume ajikinsa, idonsa kan bak'inta daketa motsi babu magana.
Batareda sanin miyake k'ullawaba taji bakinsa kawai cikin na>?+?..........
'





Nace, "Hummmm>?-?.




*_jiya wutarmuce tasamu matsala, har dare banyi posting ba, gashi angyara takuma gocewa, kumana addu'a agyara yau, inbahakaba typing zai gagareni kam_*.=??







=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?d'd'd'd'd'
[9/20, 3:26 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


1? 9?

Tsorone yakuma kama Aysha, dan ganin ya khaleel na Neman kauce hanya, tarik'e hannunsa dake yawo ajikinta, tsayawa yayi cak yadaina kissing d'inta, jin yadaina tafara k'ok'arin zame jikinta daga nasa.
Bai hanataba yabata dama tatashi zaune.
Kwanciyarsa ya gyara zuwa rigingine, yay filo da hannunsa yana kallonta ta k'asan ido, sotake tatafi wanka amma tanajin tsoron tafiya yad'auki wayar, ita duk zatonta yagantane.
Hijjab tad'auka tasaka, yad'an ta6e baki yana tashi daga kwancen dayake.
Gyara zamansa yayi sosai yana kallonta, itakam kanta Na k'asa takasa kallonsa.
"Ukkhhmm! Yay gyaran murya".
d'ago idanu Aysha tayi tana kallonsa, yad'age girarsa d'aya yana wani yatsina fuska.
Dariya yabama Aysha, Dan haka ta murmusa, shikuma yata6e baki yana jingina da gadon sosai.
"zoki zauna muyi mugana". 'Yay maganar batareda ya kalletaba'.
Bak'aramin fad'uwa gaban Aysha yayiba, tunaninta akan wayarne, haka tatafi jiki a sanyaye tazauna bakin gadon nesa dashi.
Jawota yayi tadawo saman gadon sosai, yad'ora kanta bisa cinyarsa, "miyasa kika kasa sakin jikine dani har yanzun?, nifa sonake mu shinfid'a k'yak'yk'yawar rayuwar aure, A'eesha aure hak'urine kawai acikinsa, bakomaine ake nema asamuba, duk abinda akace masa ibadane to tabbas yanada wahala, banmiki alk'awarin farinciki 100% ba a aurenmu, Dan zomu zauna zomu sa6a, ballantana mutum Irina da ayyuka sukama yawa, inafata zakiyi hak'uri dani lokacin sa6ani da lokacin farinciki, insha ALLAH zan kula dake iya iyawata, nima nabaki dukkan amanata, kirik'emin, Dan kece sirrina ayanzun".
Dad'i, farinciki, murna, duksun taru sun dabaibaye zuciyar Aysha, tarasa yanda zata musalta mitakeji, saidai Abu d'ayane ke ta6a zuciyar Aysha tawani 6angaren, har yanzu ya khaleel bai furata kalmar yana sontaba, shin kodai baya sontane? Itace keta shirmentane?".
Ganin tayi shiru yad'an girgiza k'afarsa, da sauri ta kalleshi, saikuma ta kauda kanta ganin yakafeta da idanu.
Lallausan hannunsa yasaka yamaido fuskarta, saita lumshe ido.
"Bud'e ido ki kallenimana, nifa sonake kisaki jiki dani, banason wannan nuk'u-nuk'u d'in, saikace wata matar k'auye, banson shariya, kice wani Abu".
Hannu tadaka tarufe fuskarta, "ALLAH inajin kunya".
bakinsa ya ta6e, yace, "kunya kuma aii tak'are A'eesha, tunda kinbiya kazar dakikaci bashi, kinzama Ibraheem, Ibraheem yazama A'eesha", yay maganar yana janye hannunta, tareda sunkuyowa ya sumbaci goshinta.
Dad'i Yakama Aysha, amma tanason ya khaleel yafurata mata kalmarso da bakinsa, dukda tagani a aikace bata gamsuba gaskiya, amma abinda talura dashi jin Kansa bazai bari yace yana sontaba, zatabishi su tafi ahaka itama.
K'ok'arin cire hijjab d'inta yafarayi, ta kallesa da dasauri zatayi magana, amma saitaga ya had'e fuska, dole tahak'ura yacire, hannunsa yad'ora saman cikinta, d'ayan kuma yana shafa kwantaccen gashin goshinta, muryarsa a tausashe yace, ''ina binki bashin maganar danayi, Duke kin wani maidani aku, kekuma kinyi tsit, nifa ustazancinki mamaki yake bani".
Ganin kamar da damuwa yake magana saita daure tace, "insha ALLAH zaka sameni mai biyayya agareka, saidai kayi hak'uri da dukkan kurakuraina idan nayi, koda kuskure, ko akan Sani saboda ajizancin Dan adam".
"Hummm". kawai yace, yasauka daga gadon yafita.
Da kallo tabisa haryakai k'ofa yajuyo yana kallonta, kiyi wankan zanje cikin gida Na gaisa dasu momy..
Kanta ta jinjina masa, ya ida ficewa.
Da Sauri taduk'a k'asan gadonta tad'auki wayar harta d'an tsage, kashewa tayi tatura can k'asan kayanta acikin wadrobe, sannan tashiga wanka.



_____________________________
Saida yafara shiga 6angaren baffah suka gaisa, sund'an dad'e suna tattaunawa, baffah yace, "yaushe matarka zata koma wajen aikintane? Banason asamu matsala, kagadai kusan watanni 6 kenan tana k'ok'ari, watanni 6 kawai yarage mata ta mammala NYSC d'inta, baikamata aimata wasa da damartaba".
"Insha ALLAH baffah zata koma ranar Monday insha ALLAH, nima ranar zan koma aiiki".
" to shikenan ALLAH ya kaimu lfy".
"Ameen".



******

Da sallama yashiga falon Momy, tana zaune ta rabga tagumi, itakad'ai tasan mike damunta, mufeedah Na wajen aiki, hakama hasnah da husnah sunje makaranta, Anty shukurah kam tana gidan surukanta, harya zauna kusada ita batasan ya shigoba, kansa ya d'ora saman kafad'arta, sai lokacin tayi firgigit tadawo hayyinta.
Ganin khaleel yasakata sakin ajiyar zuciya, " Ibraheem yaushe kashigo?", 'tayi maganar zuciyarta cikeda d'aci'.
d'agowa yayi yana kallonta, yamaida dukkan hankalinsa kanta, hannunsa rik'eda nata, "haba momyna miye damuwarkine? Kwana biyunnan bana ganin walwala taredake, shin miyyake faruwane?".
d'an murmushi tayi maikamada yafi kuka ciwo, tashafa fuskarsa tana had'iye yawu maikamada tafasashshem ruwa a mak'oshi".
Ganin tak'i cewa komai saiyaji babu dad'i, yazame ya kwantar da kansa bisa cinyarta, itadai Momy kallonsa kawai takeyi, hannayensa ya hard'e bisa k'irjinsa, yakafe Momy da kallo, gabad'aya hankalinsa ya tattara kanta, cikin muryar kwantar da hankali yace, " momyna damuwarki damuwar ibraheem khaleel ce, please & please my dear maah-maah, kifad'amin damuwarki, insha ALLAH zanmiki maganinta, inhar batafi k'arfinaba".
Wata ajiyar zuciya Momy tasaki, akankali takai hannu tana shafa sumar kansa, "Ibraheem konafad'a maka damuwata bazaka iya maganintaba".
" Momy miyasa zaki yanke hukuncin bazan iyaba da Sauri haka?, inason farincikinki Mamana, banta6a k'aunar wani mahalukiba fiyeda son danake miki.".
Sosai Momy taji dad'in kalamansa, Dan haka tad'an sake fuska kad'an, ''Ibraheem inason maganar aurenka tatashi kaida Aleeya".
Bak'aramin fad'uwa gaban ya khaleel yayiba, amma saiya dake, cikin taushin mirya yace, "to Momy, amma baiyi kusaba? koda yake yakikeson ayi?".
Dad'i Yakama Momy, takuma fad'ad'a fuskarta danganin alamomin nasara, ''kaima baffanku magana da kanka".
" OK karki damu Momy, zanmasa, ammafa ina Neman wata alfarma".
''Wace alfarma kenan?".
Muyi hak'uri nanda kamar wata shidda, sai ayi maganar, kinga inhar mukaima baffah maganar auren yanzun dawuya ya amince, zaice bandad'e dayin aureba, koya kika gani?".
"Na fahimceka yarona, amma kasamu lokaci kuyi maganar dashi, Aleeya zata shigo Nigeria next week, akwai wani aiki dazai kawota, kuma nan gidan zata sauka".
"Hummmm nifa Momy mamaki kike bani, wai ina kika sansu haka?".
" labarin mai tsawone, amma wataran zan baka".
Jinjina mata kai yayi yana lumshe idanu, daganan tasaki jiki sukahau hira.
Harsu hasnah suka dawo daga school, kallo suka rink'abin yayan Nasu dashi, aransu, suna fad'in yaukuma ta6arar ta tashi?.
Basuda damar zaman falon, Dan haka suna gaidasu suka shige d'akinsu.




____________________________
Aysha tagama komai tsaf, dukda bata girki har yanzu amma yaudai tad'anyi Abu mai sauk'i, Wanda mutanen gidan bazasuga tayi ba daidaiba, tunda sun bartane tayi hutun amarci.
Tana zaune afalo ya khaleel yadawo, sannu tamasa ya amsa babu yabo babu fallasa, maganar dasukayi da momyce take cizon zuciyarsa.
Batareda ya kalli Ayshanba yace, "zanyi wanka".
Tasan miyake nufi, danhaka ta amsa da to, tamik'e tabi bayansa.
Kanta ak'asa tashige bathroom d'in, dan harya fara cire kayansa.
Abakin gado ta iskeshi zaune shiru, da'alama yana duniyar tunanine.
Tace, " nahad'a ruwan".
Kansa ya jinjina mata sannan yamik'e yashige abinsa.
Aysha tabisa da kallo zuciyarta Na k'una, wai yazatayi ta canja ya khaleel ne?, idonta cikeda hawaye tabar d'akin.


Babu dad'ewa dafitowarta tajiyo ihun ifteehal, da gudu itama tafita suka rungume juna, kowa yana murnar ganin d'an uwansa.

Yana cikin wanka yajiyo ihunsu, Kansa kawai ya girgiza yamaida idonsa ya lumshe, yanamai jin dad'in yanda ruwan d'umin ke ratsa kowacce ga6a ta jikinsa.
Su Aysha kam sunacan sun kaure da murnar ganin junansu, Raudat Na hannunta tana cillata sama tana cafewa, itakam sai wangale baki takeyi.

Yadad'e a bayin kwance cikin ruwan, zuciyarsa amatuk'ar cinkushe, yarasa wane tunani zaiyi dankamo zaren lamuran Momy, badan yagaji da tunaninba ya d'auraye jikinsa yafito, shiri yayi cikin k'ananun kaya, bak'in wando da farar riga mai dogon hannu, yad'an fesa turare kad'an, yad'auki wayoyinsa da key d'in mota yafito.
Afalo yatsaya suka gaisa dasu Anty meerah, harya d'auki Raudat yamata wasa (nakula ya khaleel nason yara, tun akansu 'yan uku), mik'ama Aysha Raudat yayi, yana fad'in ''bara nad'an fita, zuwa yamma zan dawo".
Suduka suka had'a baki wajen yimasa adawo lafiya.
Kansa ya jinjina musu yajuya zai fita, da Sauri meerah ta zunguri Aysha, ta nuna mata tatashi tamasa rakiya, saida ta zum6ura baki sannan ta ajiye Raudat tatashi tabi bayansa.
Shi harma yafita, saida ta had'a da sauri sannan tacimmasa, kasancewar ahankali yake tafiya, tun maganar dasukayi da Momy d'azun ta haddasama dukkan jikinsa sanyi, jin kamar ana binsa abaya yasakashi juyowa.
Tsayawa yayi yana kallon yanda take tafiya cikin sassarfa harta k'araso inda yake.
"Lafiya dai ko?". 'Yay maganar cikin d'age gira sama'.
Kad'an ta turo bakinta tace, " rakkiyafa namaka".
"Uyimmm". 'Yafad'a yana ta6e baki da lumshe idanu'.
Haushine Yakama Aysha, dan ganin kamar da rainin wayo yay abin, sosai ta tunziro baki yanzu, shikuma ya hard'e hannayensa ak'irji yana kallonta.
Juyawa tayi zatabar wajen yarik'o hannunta, batareda yayi maganaba yajata har zuwa inda motarsa ke ajiye kusadata ya sultan, bud'ewa yayi da key d'in yashiga, har sannan yana rik'eda hannun Aysha, itadai kallon ikon ALLAH takeyi, saida ya zauna sosai sannan yajawota saman cinyarsa, idanu tazaro waje, " kai ya khaleel idan wani yagammufa?". "shiyaso". 'Yafad'a yana d'aga kafad'a sama da ta6e baki'.
Yunk'urawa Aysha yayi zata tashi yay saurin maidota jikinsa, " jimana madam!, haka akema miji rakkiya a garinku?".
Yanda yay maganar saiya bama Aysha dariya, tasaki dariya har hakwaranta suka bayyana, shidai kallonta kawai yakeyi, amma bak'aramin tafiya dashi dariyar tayiba, ya tattara hankalinsa wajen kallonta yaji tace, "wai ya khaleel anya kuwa kana dariya?".
Asama kawai yaji tambayar tata, wadda baita6a zatoba, saikawai yasamu Kansa dasakin k'aramar dariya, Dan wlhy tambayar tata dariya tabashi, ya rungumeta sosai tareda manna mata kiss agoshita, sannan yad'agota yana kallon fuskarta, haryanzu fuskarsa d'aukeda ragowar dariyar, " miyasa kikamin wannan tambayar?".
Cikin shagwa6a tace, "yoni banta6a ganin dariyarkaba, murmushima zan iya irga adadin Wanda naga kayi".
"umyimm, kinason naringa dariya kenan?". Yakai hannu zai d'alli bakinta, da sauri tasaka hannu tatare dantasan muguntar dayake shirinyi mata.
Nanma guntun murmushi yayi.
Itakuma tace, "inason naga kana dariya mana, Dan wlhy tana maka k'yau sosau".
Yad'an ta6e baki yana sosa girarsa da d'anyatsa d'aya, idonsa kyam akanta, " hummm nikuma kinga yawan dariya baya birgeni, hasalima ni bancika son mutum mai yawan dariya koyausheba, saikace wani mahaukaci".
Aysha ta jinjina kanta sannan tayunk'ura tatashi zaune sosai tace, "banga laifinkaba ya khaleel, domin kaid'in _Sadaukine_".
Tana gama fad'a tafice da sauri.
Kafin yayi yunk'urin rik'ota tabar jikin motar tana masa bey bey.

Da kallo yabita, yana wani sassanyan murmushi, jiyayi dukwata damuwar daya kwaso daga 6angaren Momy ta kwaranye, Aysha ta gogeta da shirmenta, ahankali ya maimaita sunan data kirashi dashi *_" Sadauki!"_*, yalumshe idanunsa ahankali, tareda kwantar da bayansa ajikin kujerar, kasala dajin k'yuyar fitar duksun saukar masa, (dama soyake yad'anje yasha iska, kozai samu nauyin zuciyarsa yaragu), saiga matarsama ta wanke 6acin ran nasa cikin sauk'i, saida yagaji dasak'awa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login