Showing 75001 words to 78000 words out of 155647 words

Chapter 26 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

476

ayshar saita sakar masa murmushi mai kashe zuciya.
Shima baisan sanda ya maida mata murtaniba.
Duk hakan nafaruwane akan idon momy da Aleeya.
Aikam bak'inciki tamkar zai karsu awajen.
Har suka tafi momy na antayama Aysha harara.
Itakam Aysha na sakarma momy murmushin k'ular da zuciya>?#?>?#?>?#?=?@?=?@?.
Sai bayan sallar isha'i wannan suka tafi, sukabar Aysha da kewa, ita dama akwai saurin Sabon tsiya da mutane, shiyyasa 'yan ciki da gaskiya fans suka maidata k'awarsu=??=??=??.




*_Monday morning_*

Around 11am ya khaleel yasaka aka kawo masa mai aikin hajia khaltum har office.

Daka ganta kasan a tsorace take, ya khaleel na zaune saman kujerarsa yana duba wasu files, Mahfouz yashigo da yarinyar, matsashiyar budurwace, bazata wuce shekaru 19 ba a duniya.
Cikin daka tsawa Mahfouz yanuna mata kujerar gaban table d'in ya khaleel, bai d'ago ya kallesuba, yana cigaba da aikinsa, Mahfouz yace, ''sir! Ga yarinyar".
Batareda yad'agoba yace, ''ok, zaka iya tafiya".
Saida yayi, salute nashi sannan yafita.
Kusan mintuna 10 yanata aikinsa, baisake bin takan yarinyarba daketa zare idanu, sosai tsoronsa ya shigeta, dan tsaf tagane ya khaleel d'in, tunda tana zuwa gidansu idan hajia khaltum ta aiketa, taga kuma hotunansa a jikin abubuwan bikinsa da hajia khaltum tabuga, suma har aka babbasu.
Fuskarsa a d'aure yad'ago yana kallonta, bayan yahad'a files d'in gabansa waje d'aya ya ajiye.
Bindiga ya nuna mata, kinsan wannan komiye aii=?+??".
Atsorace ta gyad'a kanta.
"Baki zaki bud'e kimin magana".
"Im.....Im..bindiga Ce".
"Minene aikinta?".
" harbi".
"Idan aka harbi mutum da ita a ciki ko kansa, ko k'ijinsa, mike faruwa?".
" idonta cikeda kwallah tace, "zai mutu yalla6ai".
" thanks god dakikasan aikinta, to inhar baki bani amsar tambayar dazan mikiba, saina tarwatsa kwalwar kanki da ita".
"Wlhy insha ALLAH zan fad'a maka komi kake buk'ata, inhar nasani".
"da k'yau 'yar gari".
"Miye sunanki?".
" sunana Sakina................
'



*_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_



*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


2? 8?

"Sakina kinsan miyasa aka d'akkoki aka ajiye anan harna tsawon kwanaki hud'u?".
"a'a yalla6ai".
"Inason wasu bayanai awajenkine, miye alak'arki da gidan Alhaji mustapha Adamawa?".
"ni mai aikice agidan yalla6ai".
"Aikinmi kikeyi?".
" sharan d'akunan masu gidan, saikuma falo dadai sauransu".
"Uhm, atunanina Wanda ka yarda dashi kake sakarwa shiga lungu da sak'o Na gidanka, danya gudanar da irin aikinki, da alama kema masu gidan sun amince dake kenan?".
Cikin in ina tace, "ha...hakane yalla6ai, amma nima duk sanda zanyi wannan aikin, musamman Na bedrooms nasu saiwani d'an gidan yatsaya akaina harna gama, sannan mu fito tare".
Shiru ya khaleel yayi yana kallonta, yakoma jikin kujera yana lilawa ahankali, hannunsa rik'eda bindiga yana sosata akan kwantaccen sajensa zuwa baki.
Sakina dai atsorace take sosai, tunda take bata ta6a ganin bindiga ido da ido hakaba, saidai ta 'yan sanda, itama daga nesane.
Kusan mintuna biyu baisake cewa komaiba, sai zuwa can yajeho mata tambayar data gama rikita dukkan illahirin halittar jikinta.
"Hakan yana nufin basu yarda dakeba kenan kema? Dukda tsawon shekaru Biyar dakika d'auka kina aiki agidan? Shin wacecema talatuwa agidan?".
Tsoro, razana, kad'awar ciki data zuciya duk suka riski sakina lokaci d'aya, takasa cewa komai, sai zufa dake keto mata takowacce ga6ar jikinta.
Cikin daka tsawa yace, "nace wacece talatuwa agidan dakike aiki?!!".
"yalla6ai fad'ata tamkar salwantar rayuwatane narantse maka, sannan bansan miyasa basu yarda dani d'inba".
Wani murmushin k'asaita yayi, tareda fad'in ''dak'yau yarinya, anzo wajen".
"Ki fad'amin, kokuma kafin ki koma wajensu su kasheki, ni zansaka alburushin bindigata acikin kanki, saidai akai musu gawarki su tambayeta".
Hawaye masu zafi suka fara zarya akumatun sakina, tace, " yalla6ai zan fad'a maka, amma Dan ALLAH karufamin asiri karkace nina fad'a".
Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanu, amma baice komaiba.
Tace, "shekaruna kusan biyar ina aiki agidan, lokacin da'aka kawoni banwuci 14 ba, kuma talatuwace ta d'akkoni daga k'auyenmu Na boza a fika Local Government, jihar yobe, mahaifina da hannunsa yabadani wajenta, bayan tabashi mak'udan kud'ad'e, ina kuka mahaifiyata Na kuka aka taho dani. Koda aka kawoni Abuja wani gida aka kaini, agidan akwai 'yan mata dayawa, k'anana da manya, kuma kowanne irin yare dake Nigerian zaka samu, hardama 'yan Niger dawasu k'asashe makwaftan Nigeria, banfahimci abinda yatara wad'annan mata agidanba aka d'akkoni aka dawo dani gidan Alhaji mustapha, nikaina bansan dalilin yin hakanba, amma daga nanne nacigaba da aiki agidan, Alhaji mustapha ba mazauni baneba, shiyyasa gidansa yazama k'ark'ashin mulkin matarsa, dukda dai nakanji masu gidan sukan tattauna akan hajia khaltum tanada kishiya, kuma alhaji mustapha yafi zama a can, yalla6ai satar amsa 1 zan baka, nasan kaid'in kwararrene Dan nakanji firarka awajen yaran gidan, suna yawan yabama kwazonka saboda soyayyar da baby take maka".
Da Sauri ya khaleel yataso daga jikin kujerar, ''kinga fad'amin wace satar amsace?, bar batun wancan shirmen".
Sakina ta jinjina kanta tace, " yalla6ai mafi yawancin masu zuwa gidan wajen hajia khaltum, namiji ko mace zaka samesu dawani tambarin hoton tarttu na >؂?kunama a damtsen hannunsu Na haggu, tabbas wannan shine tambarinsu, wannan kawai Na iya fahimta tartare dasu yalla6ai, wlhy iya gaskiyata nafad'a maka, Dan ALLAH karka kasheni, kuma karkace Nina fad'a".

Kwantar da hankalinki, zansa a maidaki yanda bazasu fahimci komaiba, da sauri yad'auki &waya yayi kiran office d'in Mahfouz da Basheer.
Babu dad'ewa saigasu sunzo kusan atare, saida suka k'ame, tareda salute nashi, sannan ya khaleel yace, "Mahfouz! Amaida yarinyarnan, amma yanda za'a iya fahimtar saceta akayi".
"OK sir"
"Kibishi kuje, inhar ina buk'atar k'arin bayani zansa akuma d'akkomin ke".
''To yalla6ai ngd, tayi maganar tana hawaye, Dan bata fatan akuma kawota wannan wajen".
Saida aka d'aure idonta kamar yanda aka kawota sannan aka fita da ita.
Ya khaleel yamaida hankalinsa akan Basheer dake zaune, ''Basheer ina buk'atar hotunan gawar David".
" OK sir!, bara na kawo, amma akwai Na binciken k'arshe da akayi suna hannun Oga Joseph ".
Jin jina kai khaleel yayi, yakira Joseph akan yakawo masa file d'in binciken mutuwar David.
Babu dad'ewa saiga Joseph ya iso, kar6a khaleel yayi yafara bincike, zuwa can yad'auki wani hoto da David ke shinfid'e a table doctors nata aikinsu akan gawar, damtsen =ت? Kar6ar picture d'in yayi yana kallo, sir! Inhar hasashena yayi dai-dai wannan kunama ce>؂?, dukada ba'a gani dak'yau".
Da sauri ya khaleel yamik'e yana fad'in Joseph inason ganin gawar David yanzunnan.
" OK sir!, idan ka shirya saimuje".

Cikin takunsa Na jarumta da isa yake tafiya, yanayinshi kawai zaka kalla kagane ransa a 6ace yake, sunshiga inda akan ajiye gawawwakin wad'anda wahala tasakasu mutuwa, ko aka kashesu, kokumadai Abu mai muhimmanci yasaka aka ajiye gawar tasu, Dan ayi bincike akanta.
Ma aikatan wajen sai k'amewa sukeyi, kasancewar suma police ne, amma likitoci.
Bakai tsaye su ya khaleel suka shiga wajenba, saida aka basu wata Riga suka saka, suka rufe dukkan jikinsu=?h? =؀?, har hannayensu da hanci sannan suka shiga, doctor Sadam mai bincike akan gawar David yabud'e abinda aka lullu6eshi, bayan anjawo gawar daga cikin wani glass, fitulu aka kunna saitin gawar David.
Doctor Sadam yabama khaleel wata fitila mai haske=?&?, suna haska damtsen hannun David Na haggu saiga hoton kunama>؂?.
Hoton wajen Joseph ya d'auka har sau biyu sannan suka fito.
Ahanya khaleel kecema Joseph, ''wato da muna aikine a birkice, ko kad'an mun Gaza samun bakin zaren matsalarmu sai a yau, tabbas akwai masu laifin dake da alak'a da juna a setetion d'innan, amma wad'anda suka kashe David basusan wannan sirrinba, mu kanmu bamusan da hakanba, wannan tambarin kunamar yana nufin tambarin wata k'ungiyane kenan?".
Maganarka gaskiyace sir, amma ya akayi kagane wannan tambarin kunamar?".
Ya khaleel bai bashi amsaba har suka k'arasa office d'insa, yacema Joseph kiramin Taheer, youseef. Adams, & Solomon".
&duk yagama kiransu cikin mintuna k'alilan.
Babu dad'ewa saigasu sunzo.
Yana shan shayin daya had'a suka shigo, kowa yazo saiyayi gaisuwa sannan ya zauna, kowa yayi shiru yana sauraren boss.
Khaleel yamik'e hannunsa d'aukeda mug d'in tea yanasha a hankali, idonsa a kansu, "kunsan dalilin kiranku?".
Atare sukace a'a sir!.
Remote yad'auka, ya danna TV d'in office d'in, saiga hoton kunamar dasuka d'akko ajikin gawar David, "wannan kunamarce, ita wannan kunamar takasance tambarin nawata k'ungiya, kuma nasameta ajikin David, ranar Taheer kasanarmin kana zargin alak'a tsakanin David da barau modibbo ko?, to yanzu inason abinciki wannan kunamar ajikinsa, bama shi kad'aiba, harda duk wasu criminal's da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi kamar David, sannan David yana safarar yara shima, kenan dukmai alak'a dashi akan bigire d'aya suke?".
"Zamu gudanar da aikinmu da lura, shiyyasa Na taraku kud'in amintattuna, bana buk'atar asaka wasu yara a aikin, dakanmu zamuyi, saboda akwai magoya bayan su David acikinmu, wannan ne yasakasu kasheshi dankar yafad'a mana komai".
Gaba d'ayansu suka jinjina kai.
Adams yace, " sir!, aikuwa akwai wannan hoton kunamar a hannun Moxies".
"Da gaske"?.
" am telling you sir".
"Kenan Moxies yanada alak'a da David?".
" zamu iya cewa hakan".
To inkuwa hakane, Ku bincikamin Ruth da aka kama da yara a air port zataje Dubai, sannan Solomon miye labari gameda bincike Dana sakaku akan email d'in sirri da'aka turo sunayen su Ruth aciki?".
Sorry sir, munata k'ok'ari, amma gaskiya mai email d'in mutumne mai wayo, Dan saida yabi matakan Kare kai daga binciken kwankwanto kafin yafara aikinsa, kuma tabbas yasan computer sosai, inhar ba k'arya zan makaba zan iya cewa bamu samo komai game dashiba, saidai kuma yin maganar kunama mai tambarin k'ungiya yatunamin dawani Abu, tabbas mai email d'in yasan wani Abu dangane da wannan k'ungiyar, domin duk sak'on dazai turo akwai hoton k'aramar kunama da bindiga kusada ita, bara kaganai". 'Solomon yay maganar yana bud'e laptop d'insa, mik'ewa yayi yay connecting da TV d'in office d'in, tana gama searching saiga jerin sakwannin mai email d'in sirri, acan gefe mak'ale kunamar take, >؂?=?+?, sannan an nuna kunamar da bindiga.
Huci mai zafi ya khaleel ya furzar daga bakinsa, ya ajiye kofin hannunsa tareda matsawa jikin tvn, nazarin komai yakeyi cikin kwarewar aiki, saikuma ya jinjina kansa, yajuyo yana kallonsu youseef, ajerin sunayen damai email d'in yaturo guda biyar, macece ta uku, kuma yabamu tabbacin zata sauka Nigeria aranar 17-ga watan 4, watan dazamu Shiga kenan, zata tasone daga k'asar Malawi, ta sauka Dar es salaam, babban birnin Tanzania, washe garine zata k'araso Nigeria. Jirginta zai sauka a Kano state ne, daganan yabamu za6in kamata a Kano, kokuma a Abuja, acewarsa wannan yarage namu, shi yagama nasa".
Gaba d'ayansu sunyi shiru, kowa da abinda yake tunani, ya khaleel yakatse shirunsu dafad'i "so ina jinjina kwakwalwar mai email d'innan, koda criminal ne shi tabbas yanada kwakwalwa, kamar yanda yabamu satar amsa akan kama Moxies haka yabamu akan wannan matar, saidai bazamu saki jiki kai tsaye da bayaninsaba, saboda tsaro".
Youseef, kaida taheer Ku tattaramin bayanin David, da Moxies awaje d'aya, tunda sunada alak'a da juna, Joseph kaida Faruk da Mahfouz kucigaba da bincikamin Duk wani mai wannan tambarin dake a setesion d'innan, Solomon kanemi su Kausar acigaba da bibiyar mai email d'in sirrinnan, nasan dolene watarana yayi kuskuren dazamu samu wani bayani akansa".
"Nida Adams da Samuel Zamu cigaba da farauta".
" komai yazama da kula, banason kuskure kuma kunsani, duk Wanda yamin wasa da hankali acikinku koyaci amanata wlhy dakaina zan fasa kwakwalwarsa da bullet, koda kuwa cikinsu youseef".
Ku kula da k'yau, Adams ina buk'atar Ak'ilu Abbas agabana yanzunnan, kukuma zaku iya tafiya".
Atare suka mik'e baki d'aya, duk sukayi salutes d'insa, murtani ya maida musu, sannan yakoma kujerarsa ya zauna, sukuma duk suka fice.



___________________________

"Aminiya agarin Yaya kikayi sakaci baici maganinnanba?, anya kuwa kinsan bala'in dake tinkaromu?, kekankifa kinama cikin saka idanun k'ungiya, dansu gano cewa Ibraheem d'ankine, kuma shine yake mana tsinci d'ai-d'ai, k'ungiya ta bada date d'in daza'ayi zama Na musamman domin Ibrahim kai tsaye, Alhmdllh munsami damar ku6tar da talatuwa daga hannun police, Dan munyi gamo da d,p,o kwad'ayayye, yanzu haka talatuwa Na gida".
"Alhmdllh, naji dad'in hakan, sannan karki damu aminiya rashin cinsa bashi yake nuna ya tsiraba, Dan nakafa masa wani tarkon ma, k'ungiya kuma zan fahimtar dakowa komai kai tsaye, Dan banason d'ana yafuskanci wani Abu daban, inasonsa fiyeda tunanin mai hakali".
" tsaki kawai hajia khaltum tayi, amma batace komaiba".
Hajia babba tace, "aminiya zan kashe matar Ibrahim".
" miyasa? aminiya, ita mitamiki?".
"Kinsani aii".
Dariya hajia khaltum tayi, tace, " bazan hanakiba aminiya, dama a k'ungiyance kisa yarinyar ya cancanta agareta, saboda gudun tonuwar asirinmu, dannasan wani daga cikin sirrinmu. Damacan ina shirya abubuwa akanta tuni, sonake sai mungano Inda meerah take, kisan Aysha tamkar munkashe macijine bamu sare kansaba, inhar meerah Na numfashi a duniya, wannan ne dalilin dayasa nabar Aysha bansake waiwayartaba".
"Shikenan aminiya nabar komai a hannunki".

Aysha dake bayan windown hajia babba tazaro ido, danjin maganar su momy, dasauri tabar wajan tana sauke numfashi, tabbas maganar su tadaki zuciyarta, amma bata tsorataba, haka takoma 6angarensu tana juya maganganunsu, takira Anty meerah ta zayyane mata komai.
" lil sholy kibani kwanaki biyu zanyi tunani, kema kiyi tunanin mafita saimu had'a tunaninmu waje d'aya muga miya dace muyi".
"Shikenan Anty meerah babu damuwa".
Yauwa ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH babu abinda zai cutar damu, kisa aranki *_CIKI DA GASKIYA..._* wuk'a bata hudashi da yardar ALLAH".
" To Anty meerah ngd".
"Aha saimunyi waya".

Bayan Aysha ta yanke wayar takwanta taci kukanta, da mamakin hatsabibanci irinna momy da hajia khaltum, lallai tasan zukatansu sun gama bushewa.
Dama dawowarta daga aiki kenan, driver ya ajiyeta saiga hajia khaltum, shinefa tabi bayanta ta mak'ale ta window hartajiyo abinda suke tattaunawa.
Saida tagaji da tunane-tunane sannan tatshi tayi wanka, kichin tashiga ta tanadarma ya khaleel abinci kafin yadawo, dukda batada tabbacin zai shigo gidan dawuri, tunda wani lokacin yakan kai 10 Na dare a office ma.


_______________________
A d'arare Ak'ilu Abbas yashigo office d'in, shima sanye yake da uniform na police Interpol, saida ya k'ame tareda salute d'in khaleel sannan yabashi izinin zama.
Ya khaleel yad'ago manyan idanunsa ya sauke akan Ak'ilu Abbas, shikuma saiyayi k'asa da nasa idon, Dan mara gaskiya baya iya kallon ya khaleel ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login