Showing 138001 words to 141000 words out of 155647 words

Chapter 47 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

469

musu da aljannah, sannan yana neman afuwar mama akan abinda yafaru alokacin daya saketa, hakan tafaru akan rashin Sani da ajizanci irinna d'an adam,.
Mama tace babu komai wlhy, dama tuni ta yafe masa, tunda tasan ba laifinsa baneba, kuma komai yawuce, tunda gashi har ALLAH ya k'addara zasu sake zama tare, gashima harda k'yautar 'ya'ya uku ya azurtasu dashi.
Itama tabasu hak'uri akan 6oyewar datayi, sannan tayima ummi amarya da gwaggo bintu godiya akan taimakonta dasukayi, takumayi addu'a da fatan alkairi ga family d'in baki d'aya, sannan tabama su Anty zuwairah hak'uri akan su gafarceta, batayi hakan domin cin zarafin mahaifiyarsuba, batada za6in daya wuce haka, saboda rayuwar yara mata dabasujiba basu ganiba dataketa salwanta, inhar irin wad'annan abubuwan zasu cigaba da faruwa muna zuba idanu saboda 'yan uwanmu na a ciki, to haka zamuyita rugujewa, watarana kuma 'ya'yanmu za'a d'auka asaka acikin irin wannan gararin rayuwar, danhaka kumin afuwa Dan ALLAH.

"Babu komai wlhy mama, muduka mun fahimceku, kuma hakan shine dai-dai, Dan gashi kuskuren momy harya shafi mufeedah, to watarana Kansu Najwa zai dawo, wlhy bazan ta6a bama momy goyen bayaba akan zama shugaba wajan yaryad'a mutuncinmu akan titiba, nasha damuwa dama akan amintakar dake tsakanin momy da hajia khaltum, amma kona nemijin ba'asin wani abunda sukayi dabai daceba sai momy tacemin sirrine, nadad'e inason Sanin wannan sirri nasu, Ashe bana alkairi baneba, khaleel Kaine kafi cancanta abama hak'uri, domin momy tayi walagigi da rayuwarka, ni nasan wannan tun ina yarinya, saidai zuciyata bata ta6a d'arsamin wani Abu dabanba, saboda nayi nisa wajen kwaikwayo da koyin halayen momy, Dan ALLAH kamin afuwa dagakai har Aysha, Dan itama nasaka hannu wajen k'untata."
Jin jina kai khaleel yayi, yace, "babu komai Anty zuwairah, komai yarigada yawuce, har gobe kuma momy nanan dakima a idona, saidai hakan bazai hananin hukuntata akan laifintaba, nima Ku gafarceni tawannan ga6ar, sannan mama ina godiya agareki, kece tushen komai, lallai da ace akwai irinki dayawa agidan aure da kowacce mace tabar kishin banza da wofi, an sace d'an kishiyarki, amma kullum idonki abud'e yake wajen Neman hanyar ku6tar dashi, lallai ked'in jarumace, maihalin dayakamata mata suyi koyi, suzama masu kishin junansu, bamasu kishin abinda zai iya kaisu wutaba, Dan kishin yanzu babu komai cikinsa sai shirme. Ummi amarya kema dolene a jinjina miki, Dan kema kintaka rawar gani irinta jaruman mata masu zuciya Saliha, ALLAH yabiyaki da alkairinsa, gwaggo bintu kece fitilar komai, Dan dabaki bayyana firar momy da hajia khaltum ba babu Wanda zaisan wannan sana'ar tasu, ALLAH yabiyaki da mafificin Alkairi, wannan abin alkairin naki. Yasakani biya miki saudia, sannan namiki alk'awarin siya miki gida a Kano madaidaici tunda bakida 'ya'ya, daga yanzu kuma duk kan buk'atunki dakikejin zaki iya fad'ama d'anki yamiki toki sanar dani su, karkiji nauyin hakan."
Kukan dad'i gwaggo bintu tafashe dashi, su Ammah Kuma suka shiga saka masa albarka, kowa kagani sai washe baki yakeyi saboda halaccin da khaleel yayi.
Yamaida kallonsa akan Aysha, cikin murmushi yace, "ngd matata, tabbas nagama dacewa, babu abinda zance ga Ammah saidai godiya, kinsha gwagwarmaya domin ganin kin ceto sauran mata 'yan uwanki, gakidai k'arama amma mai kwakwalwa da tunanin manya, irinku k'asarmu take nema, namiki alk'awarin cigaba da sonki daganan har k'arshen numfashina, sannan Na tanadi k'yaututtuka kashi-kashi agareki, amma dagani saike zan bayar, inama iyayena albishir dacewa damacan Aysha ce za6in raina, tunkan sumin tayin aurenta, tun sanda tazo gidannan tana 'Yar mililiyarta...............................................................kaf yakwashe labari yabasu.
Nanfa akaita masu dariya, Ammah tasakasu gaba da tsokana.
Farincinkin kowa yadawo, kaikace wani Abu bak'in ciki baishigo familie d'inba.
Daga k'arshe Anty Mamie tarufe taron da godiya mai yawa agaresu, tareda addu'oin fatan alkairi, sannan tace daga ranar tayima mama k'yautar ya khaleel gaba d'aya, Dan itace tafi cancanta da zama uwa agaresa, kodan wahalhalu datasha adalilinsa, dakuma sadaukar da d'iyarta jininta datayi wa duniya duk adaliln tushen abinda yafaru dashi, takumace daga wannan ranar Aysha ta zama daga cikin 'ya'yanta, dama tun sanda tafara ganinta saida taji hakan aranta.
Gaba d'aya aka d'auki kabbara, baffah da Ammah duk suka saka mata albarka, baffah yace, "tabbas nima randa nafara ganin Aysha saida naji fad'uwar gaba, amma narasa tamicece, tunkuma alokacin naga tsantsar kamarta da fad'ima, nayidai shirune kawai Dan banida tabbas, amma lallai Aysha tayi namijin k'ok'arin data cancanci yabo da jinjina ga kowa". ' yak'are maganar da tsokana'.
Yace.
"Koda yake, kuganefa Aysha gadon jarumta tayi fa".
Gaba d'aya aka saka dariya, Aysha ta saka tafin hannunta tarufe fuskarta saboda kunya.
Annanne baffah ya yanke hukunci akan hasnah da Husnah su fidda mijin aure, sannan mufeedah takoma gaba d'aya 6angaren Ammah har ALLAH ya sauketa lafiaya itama tasamu mijin aure, yace kuma ya yafe mata, danya d'auki hakan amatsayin k'addara, daganan yakumayin nasiha agaresu, danuna musu illolin hassada, Dason zama wane, dakuma burin Tara abin duniya, Wanda duk ta dalilin hakanne hajia babba ta tsinci kanta a wannan halin, Wanda hud'uba irinta uwa tayi tasiri aranta, amatsayinku Na iyaye kudinga nunama 'ya'yanku abinda zai zama alkairi arayuwarsu ba sharriba, sannan karku ringa zagin wasu agaban 'ya'yanku ko gulmar wani agabansu, koda kuwa mutuminnan yamuku ba daidaiba, hakan nasaka 'ya'ya sutashi da k'iyayyar wani azuciyarsu, harma da burin d'aukar fansa akan laifin dabasu akayimawaba, muzama masu k'yak'yk'yawar zuciya dason junanmu, muruk'e zuminci domin babban abune da ALLAH yamana albishir Na zuwa aljannah a sanadinsa, muzama masu yafiya wa juna alokacin dawani yayma d'an uwansa laifi, ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya, yasaka k'aunar juna da hak'uri azukatanku, ALLAH ka gafarta mana."


Gaba d'aya aka amsa da amin baffah, daganan dai kowa yanemi gafarar d'an uwansa, baffah yace, Anty zuwairah da Anty shikurah su shirya sukoma d'akunansu hakanan, tunda komai yalafa, sukuma cigaba dayima mahaifiyarsu addu'a.
Ammah ma tasakama kowa albarka sannan tarufe taron da addu'a kowa yakama gabansa...................
'



Jiya kunjini shiru, anguwa naje tareda Oga wlhy, nadawo kuma a late, babu damar typing a time d'in, ga gajiya kuma.






*_ALLAH ka gafarma mahaifanmu baki d'aya, dadukkan 'yan uwa musulmai=?-?=?-?=?-?>?? [10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


_d'ingimemiyar gaisuwa ta iso agareku_
*_pherty xarah (ALLAH yakaimu ranar aurenki muzo sokoto musha shagali my kakus=؃??8? @&) & Ummu Aysha (ALLAH ya kaimu ranar auren Aysha muyi rawar shaku-shaku=??>?8? @&)_*.

_ALLAH yak'aro muku haske a rubutunku kuma, ALLAH katsare k'ungiyar Haske dadukkan writers d'in dake cikinta >??


4? 8?


'Dakin taron tsit yake, da alama khaleel ake jira kawai, Dan kowa ya hallara, kayan hannunsa ya ajiye tareda had'e hannayensa waje d'aya alamar ban hak'uri da Lattin dayayi=?O? Duk manyansa ne awajen, shikad'aine k'aramima, kwazonsa da jajircewarsa akan aikice tasakasu shigo dashi cikin meeting d'in, Dan abinda za'a tattauna akai shine jigonsa.
Bayan bud'e taro da addu'oi suka fara abinda ya tarasu kai tsaye.
Jawabai sosai akayi, mafi yawa tashafi k'ungiyar su momyne kuma.
Khaleel aka bama damar tashi yayi jawabi akan nasarorin dasuka samu, dakuma abubuwan da aka kama k'ungiyar dasu.

Bayan khaleel yayi gaisuwar ban girma agaresu, yayi add'u'oi, sannan yafara jawabi cikin nutsuwa a harshen nasara ingilishi.

_"munkama mutane 57 dake cikin wannan k'ungiya, tareda bindugu 16, sai hodar ibilis (cocaine) datakai nauyin cg 1800,0 dawani abu, sannan akwai kwayoyi masu had'arin gaske suma masu yawa, saikuma yara 'yammata damuka ku6tar awani gida su 84, wasu acikinsu anyimusu viza za'abar k'asar dasu, akwai kuma 21 damuka samo a wasu k'asashe guda biyu"._
_har yanzun muna farautar kusan mutane 109 dake k'ashe daban-daban tareda yara kusan kimanin 800 da aka fitadasu tawasu hanyoyi daban-daban ak'asarnan. Akwai uku cikin wad'anda suke hannunmu suna kwance babu lfy acikin asibitinmu, saikuma 26 da suka mutu tawasu dalilai, wasu aciki mune muka harbesu, wasukuma sunmutune kawai, akwai mutum d'aya da aka bashi guba yamutu, Wanda munan muna bincike akan hakan, insha ALLAH kad'an garage mukawo sunayen masu hannu acikin kisan nashi."_
Saikuma mutun kusan 78 dawasu k'asashe suka samu kamawa 'yan Nigeria, wad'anda aka tabbatar sunada alak'a da k'ungiyar, suma munata k'ok'ari wajen ganin mun kar6osu, andawo dasu nan gida Nigeria ammusu hukunci dai-dai dalaifinsu. Da akwai mutane 13 ahannunmu dasuka fito daga k'ashen k'etare suma, wasu k'ashen suna buk'atar mubasu 'yan k'asarsu domin sumusu hukunci a k'ashensu, to badai muce musu komaiba har yanzu, munanan muna tattaunawa akan batun dai.
Saikuma jami'an tsaro dasuka fito a fannoni daban-daban guda 11 damuka samu cikin wad'an nan criminals, bincikenmu kuma ya tabbatar akwaima wad'ansu dabasu halarci wannan taronba aranar da'a kamasu, kuma gaskiya acikin manyane, dole saida had'inkan Ku za'a samu Damar kamasun, dukda akwai shirin damukeyi ta k'ark'ashin k'asa akansu.
Wannan shine bayanan da k'ungiyar tashafa, saikuma wad'anda basuda alak'a da k'ungiyar, muna shirin mik'a wasu kotu.
Suma d'in zamu shirya kaisu kotu acikin next week insha ALLAH.
AKWAI mutane uku dake hannun hukuma sss, d'aya d'an k'ungiyarne, biyu kuma laifinsu daban, munason suma subamusu danmu saka d'ayan cikin 'yan uwansa.
Yak'ame tareda salute Nasu Baki d'aya, sannan yadawo wajen zamansa ya zauna.

Gaba d'aya aka d'auki tafi, jikake raff raff raff!!!.

Lallai dolene hukumar police Interpol tamik'a gagarumin jinjina dayabo akan wannan gwarzon ma'aikaci nata, wannan hukuma da Nigeria harma da duniya baki d'aya bazasu ta6a mantawa da Ibraheem Abdallah ba, j! gwarzon ma'aikacine dayakamata ayi koyi dashi akowanne fanin d'ammara Na kaki, yakawomana nasarori masu yawan gaske, Wanda bamu kad'aibama duniya gaba d'aya dolene tayi alfahari dashi, yaje k'asashen duniya daban-daban yagudanar da aikinsa cikin nasarori, sannan wasu k'asashen sun gayyacesa domin taimakonsu duk Dan kwazonsane kuma, wannan k'ungiya damuke magana akanta ankai kusan shekaru 16 ana bincike akanta, amma bamu samu wani bakin zareba saida aikin yakoma hannun j!, jinjina agareka Ibraheem Abdallah, ALLAH yacigaba da haskaka rayuwarka kaji, ALLAH yasa ka d'ore ahaka kar watarana ka canja.
Gaba d'aya aka amsa da ameen.
Yacigaba da fad'in akwai ganawa da shugaban k'asa daza'ayi gobe a fadarsa, kowanne hukuma taza6i mutane uku dazasu wakilceta, sannan annad'a Wanda zaizama kwamitin shugabancin wannan zama baki d'aya.
Mudai anan J! Yana ciki, sannan kuma shine shugaban wannan kwamiti gaba d'aya dazai jagoranci wannan zama har fadar shugaban k'asa.

Nanma aka d'auki tafi gaba d'aya, kowa yayi na'am da hakan, saidai fuskar mutum biyu babu alamar sun amshi zancen, kuma koda khaleel yake bayani babu alamun jindad'in bayanan nasa, babu Wanda yakula da hakan sai khaleel da hankalinsa ke akan kowa, tunda dama yana zargin wasu manyansu acikin k'ungiyar, akwai guns kusan 6 acikin wad'anda suka kar6a duk Na jami'an tsarone, sannan ankama wasu acikinsu masu kaki.

Haka sukaita tattaunawa, kowa yana kawo albarkacin bakinsa, da hanyoyin dazasubi domin dak'ile ta addacin da'akeyi acikin gida da k'asashen k'etare ana zubarma da Nigeria mutuncinta.
Har 1:30pm suka kai ad'akin taron sannan aka tashi, amma khaleel yariga kowa fitowa, bama arufe taron dashiba yanemi excuse saboda time d'in sallah yayi, wad'anda suke musilmai awajen sai kunya Takamasu, dansu ko alamar tunawa da za'a shiga time d'in ibadarsu basu nunaba, saima k'ara 6ararrajewa suke suna sakin bayanai.
Shi dai khaleel yamusu sallam yafito, akan idan basu kammalaba har aka idar da sallah to zai dawo, idankuma sun tashi shikenan.


=?B?=?M?
(Bawai ta addanci bane addini, Adinin musilinci ba addinin 'yan ta'adda baneba kamar yanda duniya take fad'a ahalin yanzun, duk Wanda kagani musilmi d'an ta adda to tabbas baya cikinmu, yana amfani dahakanne kawai domin kansa, sannan shid'in ru6a66en musulmine, mukuma maba d'aukarsa d'aya daga cikinmu, addininmu zaman lafiya da adalcin k'yautatawa junanmu yakoyar damu, yanunamana muhimmancin adalci gawad'anda bama addinimu d'ayaba, addinin musilinci adalin addinine, dake koyar damu k'yawawan ayyuka, sannan addinine mai sauk'i, danhaka duk wani d'an ta'adda dazai kira kansa musilmi munce k'aryane, shiba mabiyin addininmu baneba, ISLAM IS THE BEST RELIGION=ت?=?-?.

Wlhy iyaye Ku kula sosai akan films da 'ya'yanmu suke kallo, musamman wad'anda ake nuna Muslim's amatsayin 'yan ta'adda, yaranmu kwakwalwarsu k'aramace, komai suka gani zasu iya d'auka hakane dai-dai, ALLAH yasa mugane.>??


_____________

Koda aka fito sallah yaga sunfito saiya wuce office, zamansa babu dad'ewa youseef yay knocking d'in k'ofar, izinin shigowa yabashi.
Ya k'ame tareda yin salute Na ya khaleel.
Kansa ya jinjina masa sannan yamasa alamar ya zauna, bayan ya zauna khaleel yamik'o masa hannu sukayi musabaha>?? Takardun dake hannunsa yamik'a masa, sir! ga wad'annan bayanan, mun tattarasu duka, insha ALLAH komai zaka samu. Maganar Munner kuma munata bibiyarsa ta number d'insa, haryanzu kuma yana cikin abujarnan. Saidai yayi wata waya damukayi recording ". 'Yay maganar yana mik'a masa k'aramar wayarsa.'
Kar6a khaleel yayi yakunna record d'in yana saurara. bayan yagama saurare yamik'ama youseef wayar yana furzar da isaka.
" naji youseef, shima zaibi jirgin 6:30pm ne zuwa Kano, kiramin Adams".
''OK sir".
Babu dad'ewa saiga Adams, cikin girmamawa yace, "gani sir".
''Ok, uhm dama inason naji katanadar mana jirginne?".
" yes sir!".

"Uhm Na k'arfe nawa?".
" 6:30pm".
"OK, bama saimunje kanoba, zamu kamashi a airport kawai. youseef kiramin Joseph, kace yayi shiri kune zakuje kama Munner, zuwa 6pm kaidashi Ku tabbatar kunzagaye airport, kaga insha ALLAH kafin akira sallar magriba kun gama da matsalar".
" babu damuwa sir, barama naje nasamu Joseph d'in a office, amma sir danazone please akan hajia, kadaure muje ka ganta, kullum saita ambaci sunank.........
Kasa k'arasawa youseef yayi, saboda wani mugun kallo da khaleel ya watsa masa.
=?O? Khaleel baice komaiba ya kauda kansa daga kallon youseef d'in.
Jiki a sanyaye youseef yamik'e, yay salute nashi sannan yafice.
Adams natsaye baice komaiba dai, amma shima yanason yarok'eshi akan yaje d'in, saidai yana shakka.
d'ago ido khaleel yay ya kalleshi, "akwai damuwane". 'Ya tambayi Adams yana maida idonsa a kan computer dayake latsawa'.
" a'a sir!, amma........
......Amman mi? Indai akantane karkacemin komai".
Yak'atseshi da Sauri.
Wani yawu Adams ya had'iye tareda girgiza kansa, shima saiyayi salute nashi yafice.

Binsa da kallo khaleel yayi, ya sauke numfashi tareda dafe kansa, ahankali yafurta momy kingama da rayuwata, ALLAH ne kawai kerik'e da zuciyata, amma datuni ta tarwatse9&
'

Agurguje inji Perty=? ?

********
Alhmdlh aranar su Youseef sunsami nasarar cafke Munner, kuma cikin sauk'i da nasarori.


****

Kusan 8pm khaleel yakoma gida, saida yafara shiga cikin gidan, Dan yanaso su gaisa dasu Anty Mamie, yau yafita da wuri basu gaisaba.
K'annensa suna falon, harsu Hasnah, fira suketayi, su Affan naganin khaleel suka taso da gudu sukamasa oyoyo, rungumesu yayi shima yana farincikin ganinsu, d'ai-d'ai yabisu ya sumbaci kumatunsu, shima duk haka suka sumbaceshi.
Manyan kuma suka gaidashi. Da 'Yar sakin fuska ya amsa, yabisu da kallo d'ai-d'ai amma babu Aysha.
"Su mamafa?". 'Yay maganar idonsa akansu'.

" mama sunfita itada baffah, ummi Amarya kuma kanta ke ciwo ta kwanta, Anty Mamie tana d'aki itama."
Batareda yace komaiba yanufi d'akin Anty Mamie, saida yay knocking tabashi izinin Shiga sannan yatura k'ofar yashiga da sallama.
Da Aysha yafara cin karo zaune kusada Anty Mamie tana bata dambu abaki.
Suduka idonsu nakansa, duk suka masa sannu da zuwa.
A sanyaye ya amsa yanamaijin k'aunar mahaifiyarsa har cikin ransa. K'arasowa yayi ya zauna d'ayan gefen Anty Mamie shima.
"Babana andawo?".
Kansa ya jinjina mata, ya d'ora kan nasa agefen kafad'arta yana kallon Aysha, yace, " Mamie kidaina shagwa6a yarinyarnan, jiyafa ta6ara taitamin iri-iri."
Aysha tad'an murgud'a masa baki, tana fad'in "jealousy kawai".
Anty Mamie kam 'Yar dariya tayi, " babana aidolene Na shagwa6ata, bakaga ba ita kad'ai baceba, yanzu hakama abinci taci tayi amansa, shine matar zunnurain tayi dambu takawo mata, inad'an lalla6atane tanaci".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login