Showing 114001 words to 117000 words out of 155647 words

Chapter 39 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

477

hakan tafarune? Miyasaka Momy aikata haka?, babu Wanda yata6a kawowa aransa hatsabibancin Momy yakai koda quarter d'in hakama, kowa ya d'auka masiface dai tazafin kishi da yanayin halitta kawai, Ashe lamarin Na Momy yagama gawurta.
Babu maibasu amsoshinsu, saidai sukaita juyasu da tattaunawa a zukata, dukkansu fatansu ayanzu bai wuce farkawar su khaleel ba gaba d'aya.
Ganin yanda lokacin yatafi, har 8 Na dare baffah yace suje gida hakanan, subarshi shidasu Mujahedeen, idan suka farka za'a sanar musu.
Gara suje su nemama yara abinci, dansu khaleefa sai kukan yunwa sukeyi, saidai asayi biscuit abasu, yara babu hak'uri, biscuit baya d'aukarsu suka fara k'ananun kuka.
Badan sun soba suka tattara suka tafi, Zunnurain da Musleem suka tafi kaisu gida.
Akabar baffah, Ramadan, sultan, Muhseen, mujahedeen, hafiz anan.

Haka kowa yashiga gidan tamkar anmusu mutuwa, jikin kowa a sanyaye, duk da abinci dasuka Tatar 'yan aikin sunyi hakan baisa wani yadamu da Neman abincinba, yara kawai sukaci su Affan, dakuma yaransu ya Sultan, sai Ummunoor da Nuriddin.
Amma irinsu tasleem ai duk haka kowa yanemi guri yazauna, suka d'ora tunaninsu daga Inda suka tsaya.
Abindama Yakuma basu mamaki shine uban matakan tsaro dasuka Tatar agidan, tako ina anguwar da gidansu zagaye yake da ainahin police dakuma police Interpol, hakama asibiti dasuka baro, ko'ina matakan tsarone, musamman d'akinda khaleel da Aysha ke kwance, babu kuma Wanda ya Isa yashiga d'akin sai doctor Faisal kawai, ko nurse d'aya ba'a amince da itaba, shikansa doctor Faisal d'in akwai sa'idon ma'aikata akansa yake shiga.


_______________________

Su Momy yaukam za'ayi kwanan sel, gashi ba'a had'ata da aminiyar tataba, kowa d'akin da'aka ajiyeshi daban.
Kallon inda zata kwana tayi kawai saita fashe da kuka>?#?.
Akan dindinyar sumintine, ga uban zarnin toilet d'in dake d'akin da wari, ga d'an karen sanyi daya fara busawa alokacin, k'afarka kawai kasaka a Simintin sai tsigar jikinka tatashi bare kuma kwanciya, sauk'inma da sauk'in sauro, saboda sanyine sauro baya zama, amma akwai Baban sauro awajen, shine kud'in cizo, irin 6ula-6ula d'innan, wad'anda dasunji kamshin mutum zasu fara gudun fanfakak'e Na k'ok'arin isowa gareshi susha jini, su sanyinma bai koresuba.
Kasa kwanciya hajia babba tayi, ko rayuwar yarinta datayi gidansu 'yan gatane, bare kuma rayuwar gidan mijinta Alhaji Abdallah daba'a cewa komai.
Zarya taitayi ad'akin, ta zauna, ta kwanta, tamik'e tsaye, babu style d'in dabatayiba ranar, gashi tanata fama da toshe hanci sabida wari, daga k'arshe dole tahak'ura da toshen hancin tafara damuwa da inda zata kwanta tasamu barci, dukda d'umbin damuwa da juya abinda yafaru d'azu da zuciyarta keta mafan yi, towai yama akayi bata ta6a d'ago shirinsu mamaba?, kenan batayi aiki da hankalintaba? kokad'an bata ta6a kawoma ranta wani agidan zaisan tana cikin wata k'ungiyaba, Dan sosai takeyin taka tsan-tsan ko 'ya'yanta bata basu fuska tananba balle su fahimci wani Abu, Ashe ita tana shukane a idon makwarwa bata saniba.
"Kai!! Jama'a>?&?
@&, miya faru danine haka?".
Hajia babba tafad'a tana dafe kai, batada mai bata amsa, danhaka tashare kwallar data cika mata ido, wlhy datasan wannan ranar zatazo mata da hakaba, datun khaleel yana jinjiri zata kasheshi, datayi dukma yanda zatayi kar wata mata tasake nak'udar haihuwa agidan.
Haka taita k'ullawa da kwance wasik'ar jaki maicikeda dak'ik'anci=?@?=?9? har garin ALLAH ya waye.


____________________________
Dole da dare yayi su baffah duk suka tafi gida, Dan su khaleel sun samun tsaro wajen yaransa.
Saida baffah yashiga ya tofeau da addu'oi sannan suka tafi.
Gwaggo bintu kawai aka bari wajen Ammah, saboda ita tafarka tun wajen????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
9:30.
Har washe gari dai su khaleel babu Wanda yafarka acikinsu.

******
A can gidama bakowanne yay barcin kirkiba, Anty Mamie ma asaman sallaya ta kwana, hakama baffah da mama, kowa da nau'in addu'ar dayakeyi, mama tana mik'a godiyarta ga ALLAH dayaja ranta har zuwa wannan lokaci tafesar da abinda ke ranta, Anty Mamie da baffah kam duk addu'arsu akan mamace, sunma rasa irin rokon dazasu mata kasancewar itace silar komai daya faru, saikuma addu'oin samun lafiya da saukayi akan Ammah da khaleel da Aysha.=?M?
Hakanan badan wasu sunsoba sukaje suka lallek'a su ya khaleel suka wuce wajen aiki, da ammah kawai suke samun damar gaisawa, amma su Aysha basu farkaba.
Baffah dai you jingine aiki yayi, aka barsa shida mama da Anty Mamie, sai surukansu matansu Ya Sultan, saikuma Anty zuwairah data tattara tafiya ta jingine gefe, Anty shikurah ma tazo bayan Anty zuwairah takirata awaya ta shaida mata komai tana kuka.
Baiwar ALLAH mufeedah takasa zuwama asibitin, tanacan kwance agida sai aikin kuka kawai takeyi, Dan ayanzune tasamo zaren dalilin abinda ya tarwatsa mata rayuwa, halin momyne, tanacan tana kacaccala rayuwar wasu, taya za'ayi mutuncin 'ya'yanta yatsira?, baga mamaba, dayake zuciyarta a tsarkake take dason ceto rayuwar 'ya'yan wasu, sai ALLAH yamata alfarmar kare mata tata d'iyar, dukda taje cikin manyan tantirai da yakamata ace ta lalaced'in.
Lallai yakamata d'an Adam yayi k'yak'yk'yawan nazari awannan ga6ar, babu yanda za'ayi kazama sanadin tarwatsa rayuwar wani kai d'in kazauna lafiya, ko zuri'arka ta zauna lafiya, shiyyasa kullum tarbiyya keta kuma ta6ar6arewa aii.
Yo kana majalissa kana antayama 'ya'yan jama'a zagi da aibantasu, hakama gulmar matan mutane da zind'ensu, budurwa zata wuce kaji har tushen uwarta sai an bada labari, so Dan ALLAH kana nufin naka zasu zauna lfy kenan?.
Wlhy bazai ta6a yuwuwaba kuwa, lokacin dakake tozarci gawata zuri'a, sai ALLAH ya jarabci taka zuri'ar yaga yazakayi, tunda ga abin zagi da zund'e agidanka aisaikayi ko. basai kawahalar da kankaba wajen hangen gidajen wasuba=?D?.

*_wlhy nasan wani mutum agarinmu, kullum bashida aiki sai aibanta 'ya'yan jama'a, zagi da gugar zana akan iyayensu basa kulada tarbiyyarsu, kullum shi d'an kiran wane tsinanne, wane d'an iska, wane d'an shaye-shaye yake, ko hutawa bayayi mai bakin >؆?agwagwar, aikam rana d'aya saigayi anwayi gari d'ansa nutsatstse dakowa ke yabo yafad'a shaye-shaye, wlhy yanzu idan kukaga yaron saikun tausaya masa, saboda shaye-shaye Yakoma mahaukacin k'arfi dayaji. Shin wannan aikunga bakin mahaifinsane dabai fad'in alkairi akan 'ya'yan wasune yaja masa?.>?7? @&_*
_please yakamata iyaye mu gyara harshenmu, karya zama takobi wajen yankan naman jikin 'ya'yanmu batareda munsaniba, aibanta wani bashida k'yau, ko Abu mara k'yau kaga yanayi kace kawai ALLAH ya shiryeshi, tafi sauk'i akan kaci naman jikinsa agefe. Barakuji illar gulma._
=?G?
*_"Masuyin gheeba (gulma) zasu shiga wuta ranar lahira, za'a dinga fincike naman jikinsu ana basu suna cinyewa, suna murtuke fuska tareda kurma ihu, kamar yanda aka nunama ANNABI su ranar isra'i yagansu awannan hali, har aka gayamasa cewa sune masu aibanta mutane, tareda yimusu nune. Duba hadisin Abu sa'id alkbudry (Abu dawud da Ahmad da ibnu abidduniya) kuma ya inganta"._*

*_gheeba (gulma) k'azantace, saboda manzon ALLAH (SAW) ya kwatantata da cin mushen jaki a hadisin Abu huraira, (Abu dawud da ibnu hibba)._*
*_dakuma mushen alfadari a hadisin Amru d'an Ass, (Adabul mufrad da ibnu hibba)._*

Shin yakai bawa miye ribarka a gulmar mutum?, kazama mai gaskiya kawai, idan wani ya 6ata maka nemarsa kasanar dashi, yabaka hak'uri koku fahimci juna kawai, amma Dan ALLAH muringa tsare harshenmu daga cin naman 'yan uwanmu, kundaiji hukuncin mai aikatawa nan, ALLAH ka shiryemu.


______________________________
Sai kusan 11 Na safe ya khaleel yafara farkawa, ahankali yabud'e manyan idanunsa dasuka masa jingin da nauyi, yabud'esu jajur abin tsaro.
Kalle-kalle yafarayi ad'akin, har idanunsa suka sauka akan aysha daketa barci, shiru yayi tsawon mintuna 2 yana kallonta, soyakeyi yatuna abinda yafaru jiya, amma kwalwarsa takasa tariyo masa komai, kusan mintuna 10 yana ahaka sannan ahankali komai yadawo masa sabo fil, tamkar mafarki kokuwa film, wai Momy ba mahaifiyarsa baceba>??, shiyyasa take masa duk abinda tagadama kenan?, kai wannan lamari akwai d'aurewar kai, ya tsurama Aysha idanu tamkar ajikinta yakeson gano gaskiya maganar.
Yaja mintuna masu tsayo sannan yatashi ahankali zaune, cire k'arin ruwan da'aka saka masa yayi, k'afafunsa yaziro k'asa ya sakko ahankali, dabin bango ya iso gadonda Aysha take kwance, yaja kujerar plastic fara yazauna, awahalce ya feso iska daga bakinsa, sannan yad'ora Kansa asaman shafaffen cikinta, maikama da babu wata halittar mutum acikinsa, ahankali yasaki kuka mai ta6a zuciya da ruhin mai sauraro, shikansa baisan dalilin kukan nasaba, bashida wani za6in daya wuce yayi kukad'in, Dan hakan shine mafi sauk'i agaresa, kwakwalwarsa takasa d'aukar abinda yafaru, Ajiyakam yamanta shikansa wane jinsine, namiji kokuwa mace?, Dan bashida wata aba jarumta ahalin dayake yanzun.
Acikin barci Aysha taringa jiyo kuka sama-sama, ahankali tabud'e idanunta tasauke akan d'an kufan gashin sumarsa, gabantane yashiga fad'uwa ganin ya khaleel yana kuka, saidai batada wani kuzarin tambayarsa kokuwa matsawa jikinsa, saikawai tazuba masa idanu tana kallonsa.

Da k'yar ta iya d'aga hannunta Na dama dababu k'arin ruwan tad'ora saman kansa, ahankali take shafa kwantacciyar sumar dabatada yawa, saboda askewa dayakeyi, itama hawayenne take zirararwa, tausayin ya khaleel yakamata, wannan wace iriyar rayuwace? Mi hajia laurah kenema itakuwa aduniyarnan? Miye dalilinta naraba d'a da mahaifiyarsa aranar datagama shan nak'udar haihuwarsa, bayan watanni Tara data d'auka Na azabar rainon cikinsa, amma saboda rashin tausayi atsige matashi batareda ta ko kallishiba taji sanyi aranta.
Yanzu da ALLAH baisa hankali ajikin khaleel ba, dahaka kullum zaita cin zarafin mahaifiyarsa amatsayin kishiyar uwa? Wanda hakan hajia babba taso yakasance, takan takali Anty mamie tsiya kodan khaleel yaci mutincin Anty mamie, Amma ubangiji gafurun rahimun saiya dakatar dahakan, yasaka kunya daganin mutuncin juna tsakaninsu, tareda k'arfin soyayya irinta uwa da d'anta.
Dr Faisal ne yaturo k'ofar, dasauri yak'arso inda suke, tausayinsu yakamashi, dukda baisan miya faruba, yafahimci tun ajiya family d'in suna cikin tashin hankali, yadad'e tare dasu, har ankai matsayin dazai iya sanin farincikinsu ko akasin hakan.
Dabaya yakoma, yakira baffah.
Jin sun farka yasaka su mama ma mik'ewa da sauri, saidai dole su suka tsaya ajikin window, baffah kad'ai yashigo.
Jiyayi kwalla tacika masa idanu, jarumin d'ansa mai k'ok'ari da dakakkiyar zuciyar tunkarar kowanne irin had'ari shine ke kuka, shikansa sometimes yakan jinjina jarumtar Mu'azzam, saboda mutumne shi mara tsoro, komai girman mulkinka zai fad'amaka gaskiyane awuce wajen, shiyace bashida lokacin zaman gulmar wani, amma kalla yaushine ke kuka, kuka ajikin mace, kuka irin Wanda Duk Wanda yagani zaisan kukan bak'incikine da k'unar zuciya.
Bayansa baffah yadafa shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa nasa idon.
Jin k'amshin turaren baffah yasaka khaleel d'ago kansa, dasauri yafad'a jikin baffah yakuma sakin kukan.
Huci babbafa yafurzar daga bakinsa, yana shafa bayan khaleel da hannayensa, alamar lallashi.
Aysha kallonsu takeyi cikeda tausayawa, itama har sannan kukan takeyi.
Anty mamie tashigo itama, inda Aysha take kwance tak'arasa, ta zauna bakin gadon tareda d'aukar kanta tad'ora bisa cinyarta, tasaka hannayenta tana share mata hawayen.
"Ya Isa kinji d'iyata, daina kukan hakanan, kinga bake kad'ai baceba, ba'a son mai juna biyu da 6acinrai kinji.
Jinjina kai kawai Aysha ta iya yi, amma batace komaiba.
Shima baffah yanata lallashin khaleel, saida yasamu yayi shiru sanan, saman gadon baffah yamaidashi ya zaunar, yasaka masa filo yajingina da bango.
Dr Faisal yad'an duddubasu yace, " Alhmdllh. Yanzudai jikinsu normal, sai abasu abinci suci, ga magani susha, idanma ALLAH yataimaka k'ila mu sallamesu zuwa dare.
Hamdala duk sukayi taredama Dr Faisal godiya.

Mama da Anty zuwairah da Anty shikurah suka shigo, duk jikinsu asanyaye yake, sannu sukai musu, khaleel yad'ago ido ya kafe Anty zuwairah dasu, kallonta yakeyi tamkar Momy, Dan ita tana kama da ita sosai.
Jikin Anty zuwairah saiya kuma yin sanyi, Dan ganin kallon da khaleel kemata, kusadashi tak'arasa, takama hannunsa ta rumtse anata, hawaye masu zafi suka ziraro akumatunta.
Takasa magana, Dan batasan mizata cema khaleel d'inba, batada bakin furta komai, harshenta yamata nauyi.
Ya khaleel yasaka hannunsa ahankaki yashiga share mata hawayen.
Baffah dake kallonsu cikeda tausayi yayi murmushi, hakama mama da Anty Mamie.
Mamace tazo ta janyeta tana lallashi, ya isa haka zuwairah, kukan ya isa haka, tunjiya aketa Abu d'aya, dolene muyi hak'uri, bamuda dalilin canja k'addara, abinda yafaru yarigada yafarun, saidai mu kiyaye Wanda zai faru anan gaba kuma.
Ku sakama zukatanku hak'uri, muyimasu addu'ar samun lafiya kawai kunji.
Duk Kansu suka d'aga mata.

Anty shikurah tahad'amusu shayi, tamik'ama Anty Mamie dake tareda Aysha, Anty zuwairah kuma takar6i na khaleel, dakanta taringa bashi, baiyi musuba yakar6a tamkar wani k'aramin yaro=?:?.
Aysha dai dafarko tace bazata shaba, saida Anty Mamie da baffah sukaita lalla6ata sannan tad'ansha, kur6artama baifi hud'uba tafara yunk'urin amai, da sauri Dr Faisal yakawo wata tasa, aikam saida ta amayar dashi tas sannan aka samu sassauci, dukta gama galabaita, sai numfashi take fitarwa da k'yar.
Ya khaleel jiyakeyi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, laulayin ciki yana bata wahala, gashi yazo ga6ar tashin hankalin dasuka tsinci Kansu aciki, duk Aysha tagama canja kamanni, tarame sosai, sai uban haske datayi, ko mak'iyinta dolene ya tausaya mata.
Shima daganan daina shan tea d'in yayi, duk lallashinsa da Anty zuwairah keyi itada mama k'insha yayi, hankalinsa gaba d'aya yanakan Aysha.
Bayan Anty Mamie ta taimakama Aysha ta wanke bakinta ta rungumeta ajikinta, saida tad'an huta sannan tashiga tambayarta mitake sha'awar ci yanzun?.
Shiru nad'an wani lokaci, sannan Aysha tace, "Anty Mamie zan iya samun fura".
" da guduma kuwa d'iyata, furama abu mai sauk'i".
Anty shikurah tace, "bara naje nasiya miki kinji sholyn khaleel". 'Tayi maganar cikin 'Yar tsokana'.
Saida kowa yayi murmushi kuwa, har khaleel d'inma, Aysha kam kanta ta 6oye ajikin Anty Mamie.

Bayan Anty Shikurah tasayo furarne a Shop d'in dake cikin asibitin tadawo tagamu dasu meerah sunzo dubasu.
Atare suka rankayo d'akin.
Nanfa aka shiga gaishe-gaishe da tambayar masu jiki, harda Aleeya akazo.
Sosai Aysha tasha furarnan, ALLAH kuma yataimaka ta zauna, batayi amanba.
Babu dad'ewa kuma saigasu Amal amare, Adams yakawota, saikuma gasu Hamdiyya, kowa mijinta yakawota yatafi, bayan sunshigo sun duba masu jiki, har Ammah, Adams dai anan aka barsa, Dan baigama hutun amarciba, amma yanaji aransa dolene yakoma aiki kam.
Bayan sun gaisa da kowa saisuka ragu, wasu suka tafi d'akin Ammah jar wuya, aikam tiryan-tiryan saida Ammah tabama su Shahuda labarin duk abinda yafaru ajiya, sunsha kuka kuwa, da tausayin khaleel da Anty Mamie, tareda jinjinama k'ok'arin mama da ummi amarya da gwaggo bintu, badai suce komai Akan momyba, kowa yabar tsinuwar dayake mata azuciyarsa.

************

Kowa yayi shiru, d'akin tsit idonsu akan TV suna kallon labarai a tashar NTA da ake maimaitawa Na jiya, labaran kamasu hajia babba dasu khaleel sukayine afarko.
An nuna inda aka kamasu, dakuma makamai dawasu abubuwa irinsu kwayoyi da cocaine da'aka kamasu da'ita, sai yara kusan 64 da'aka samo awani gida, wad'anda an ajiyesune ana shirin kaisu wasu k'asashe.
Saikuma aka nuno youseef yana tattaunawa da 'yan jarida. Yace.
"Kwarai da gaske, mundad'e Muna musu tsinci d'ai-d'ai, saidai bamusan gawurtarsu hartakai hakaba, abin bak'incikinma shine samun manya-manyan mutane masu fad'a aji ak'asarnan, wad'anda al'umma suka d'auki ragamar Kansu da d'aukarsu iyayen k'asa, amma sukaci amanarmu da k'asarsu wajen aikata wanann ta'addaci, wannan k'ungiya tanada k'arfin gaske, danba'a Nigeria kawai takeba, akwaisu ak'ashe daban-daban Na duniya, babbar illar dasuke mana itace d'aukar yaranmu mata suna kaiwa karuwanci, dashigo mana da miyagun kwayoyi".

*_'yan jarida:-_* "to amma yalla6ai, wane mataki kuka d'auka domin ruguza wannan k'ungiya mai k'arfin iko? Sannan zaku iya dawo da yaran dasuka salwanta tasanadin wannan k'ungiya?".

" insha ALLAH munakan yin hakan kam, Dan zuwa yanzun sauran ma'aikatanmu dake k'asashe daban-daban sun duk'ufa akan aikin zak'ulo dukwani mai alak'a dawannan k'ungiya. Sannan zamu dawo da sauran yaranmu gida da'aka kai wasu k'asashe".


*_'yan jarida:-_* "yalla6ai ance akwai jami'an tsaro dayawa ta fannonin kowanne aiki dake cikin wannan k'ungiya, kuma manya-manya masu fad'a aji, shin gaskiyane kuwa?".

" hakane, akwaisu, kuma insha ALLAH nangaba kad'an duk za'aji sunayensu, bayan mun kammala aikin cikin gida".

*_'yan jarida:-_* "yalla6ai dagaskene rad'e rad'in daketa fad'a cewar ankashe babban jami'in tsaronnan mai jarumtar aiki dakan tsorata 'yan ta'adda saboda rashin tsoronsa awannan gumurzu, Ibraheem Abdallah Jigawa, Wanda kowa yafi saninsa dasuna j!".

" hummm", youseef yafad'a yana murmushi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login