Showing 30001 words to 33000 words out of 155647 words

Chapter 11 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

453

akanta, amma zuciyarsa tak'i amince masa, tana nuna masa hatsabibancin yarinyar baikai nanba, to amma wacece? Yasha bibiyar Ayshar amma baiga wani abun rashin gaskiya tattare da itaba, yafurzo zazzafar iska daga bakinsa, Kokuwa badaga 6angarensa mai tura massage d'in takeba?, yakamata yabinciki Joseph Taheer youseef, alokacin dazasuje kama barau modibbo awaccan ranar suna inane?.
Da wannan tunanin yacigaba da aikinsa.
Aysha tagama gyara komai tsaf tafito, dama babu wani datti.
A inda tabarsa anan ta iskesa, yakuma maida hankalimsa gaba d'aya akan aikinsa, itama saikawai tamaida hankalinta ga TV.
Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta, yamaida kansa, ahaka har aka kira sallar magriba, yarufe lap-top d'insa yamik'e danyin alwala yana "fad'in kidafamin shayi kafin nadawo".
Aysha ta amsa da ''to tana mik'ewa itama".


______________________________
Yauma abinda yafaru adaren jiya shiyya faru, bayan dawowar ya khaleel daga sallar isha'i kaitsaye d'akin Aysha yashiga, gama wayarta da Anty meerah kenan tafad'a mata komai akan zuwansu kubrah da tuhumar da ya khaleel yamata, sunk'ullah hanyar dazasuyi aikin sirri da ya khaleel batareda ya fahimci suneba.
Khamshin turarensane yasaka Aysha d'agowa, Dan ciki-ciki yay sallama, cikin hanzari tafara Neman hijjab d'inta ta sanya, Dan k'ananun kayane ajikinta, sunkuma kama jikinta sosai amma sunmata k'yau.
Jiyayi wani Abu yadaki zuciyarsa yay azamar kauda kai daga kallonta, itama cikin in ina take masa sannu da zuwa.
Kansa kawai ya gyad'a mata yajuya zai fita yana fad'in zoki bani tea.
Aysha batajin dad'in yanda yake mata wlhy, amma yazatayi, insha ALLAH zata canjashi kamar yanda Anty Mamie tasanar da ita, (mace takan canja namiji duk a yanayin datakeso, cikin hikima da ilimin da ALLAH ya bata irinna y'a mace mai daraja), ajiyar zuciya tasauke, afili tace hakane Anty Mamie, insha ALLAH nima zan gwada.

Saida ta zumbula hijjab sannan tafito, zaune ta iskeshi da remote ahannu yana Neman tasha, tabi tabayan kujerar dayake zaune tanufi kicin, babu dad'ewa tafito d'aukeda tire k'arami Wanda tad'ora k'aramin filas da mug, taja table gabansa ta d'ora, tana k'ok'arin fara zubawa yace, "cire wannan hijjabin".
Da sauri Aysha tad'ago ta kalleshi.
Ya harareta, ''miye kikawani tsareni da wannan kwala-kwalan idanun? karfa zuciyarki tafad'a miki shirme, danbakida abinda zan kallah ajikinki, mtsoww".
Maganarsa ta 6ata mata rai, ta janye idanunta daga kansa tana murgud'a baki.
Ganinta kawai tayi a cinyarsa, amma batasan tayaya ta hauba.........
'



Kuyi manage da wannan jikin babu kwari=??.



*_ina tayamu murnar shiga sabuwar shekarar musulinci, alkairin dake cikinsa ALLAH ya sadamu dashi, shirrinkuwa ALLAH ya nisantamu dashi, ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan y'an uwa musulmai baki d'aya, muma ALLAH ka gafarta mana, kacika zuciyarmu da tsoronka da soyayyar ANNABINMU (SAW), ameen._*=?O?

_ngd da addu'oinku gareni, masu kirana daturomin sak'o dukna gode, ALLAH yak'ara mana lfy baki d'aya ameen._=?O???







d'd'd'd'd'=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?.
[9/13, 7:32 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


1? 3?

Yayi mugun had'e fuska, tsoro da fargaba suka mamye zuciyar Aysha, yasaka yatsunsa biyu yamatse bakinta, hawaye kawai tafara zirararwa amma babu damar kuka.
Jin yana Neman tsinke mata la66a takama tsintsiyar hannunsa tarik'e kam, yay tsaki tareda watsa mata wani mugun kallo, "ni sa'ankine ko? Miyasa raini keneman shiga tsakanina dakene?", yakuma matse bakin "zaki kuma murgud'amin wannan bakin naki maikama dana tsuntsu?".
Aysha Na kuka da k'ok'arin janye hannunsa tashiga girgiza masa kai.
Saida ya tabbatar taji ajikinta sannan yasaki bakin yana fad'in " fitsararriya kawai".
Aikam saita fashe da kuka tana k'okarin tashi daga jikinsa, maidata yayi ya kwantar bisa k'irjinsa yana jan k'aramin tsaki,  ki tsaidamin wannan kukan kafin nakuma hukuntaki .
Da k'yar ta had'iye kukan, shikuma yatsura mata idanu yana dariya a cank'asan ransa, yajanye hannunta data dafe bakinta dashi yana fad'in,  o, sholyn Anty meerah naga le6en baicireba dai ko? .
Sosai Aysha tarazana da sunan daya kirata dashi.
Shikam baima nuna yasan miya fad'a d'inba, saima zagaya yatsansa dayakeyi bisa la66anta, Aysha tabud'e baki danufin tambayarsa ina yasan wannan sunan?. Saikawai taji bakinsa cikin nata.
Ya salam tafad'a acikin ranta, jikinta yafara rawar mazari, yaune rana ta farko da'aka ta6a kissing nata, shikansa jikinsa tsuma yakeyi, danbai ta6a tsintar kansa a wannan yanayinba, tuni zuciyoyinsu suka k'ara k'arfin gudu, wannan yak'arama khaleel k'aimi a sabuwar duniyar daya tsinci Kansa.
Aysha kam hawaye sunjik'e fuskarta, tsoro kuwa yazama shike tafiya da gudun jininta, sai k'ok'arin tureshi rakeyi amma takasa, mamaki yacika zuciyarta, dama haka ya khaleel yake shima?, shi baima San tanayiba, danya tsinci kansa aduniyar dabaisan haka takeba, saida ya dirji bakin Aysha San ransa sannan yacire bakinsa yana sauke numfashi, rungumeta yayi tsam ajikinsa yana shafa bayanta alamar lallashi, saboda kukan datake rera masa.
Bayan shid'ewar wasu y'an mintuna yad'agota, tadaina kukan saidai shashsheka, kunya dukta lullu6eta, jitake kamar ta tsaga k'asa tashige, ta rumtse idanunta GAM danta kasa kallonsa..
Murmushi yayi, yasunkuya ya sumbaci la66anta dasukayi jajur saboda punishment dasuka fuskanta a hannun boss, muryarsa can k'asan mak'oshi yace,  bud'e idonki kona k'ara........".
Baima rufe bakiba Aysha tabud'e idonta da Sauri suka had'a ido, tayi saurin janye nata, Dan ganin yanda nashi suka canja kala, lallausan hannunsa yasaka ya tallafo fuskarta data maida gefe. Zata rufe ido yace,  bud'esu ki kalleni! .
Da sairi tabud'e danjin yanda yay magana adake.
Jikin Aysha yafara rawa, harga ALLAH bazata jure kallon kwayar idanun ya khaleel ba, shima lura dahakan yasakashi sakin guntun murmushi, yajanye idanunsa daga cikin natan,  daga yau zaki kuma murgud'amin baki? .
Da Sauri ta girgiza kanta tana matso kwalla, gaba d'aya tsoronsa Yakuma kamata, tundaga john take tsoron maza arayuwarta.
 dabakinki zakimin magana, banason raini .
Kafinma yak'arasa tace,  kayi hak'uri ya khaleel wlhy bazan sakeba, wancanma kuskurene .
Yanda ta marairaice fuska tana masa magana saita bashi dariya, amma ya gimtse fuska yace,  idan kika sakefa? .
"Wlhy ka d'auki kowane mataki".
 kowanne matakifa kikace? .
 eh, wlhy Na amince .

"OK to shikenan, tashi ki had'amin shayin".
Dasauri tamik'e tafara cika umarnin Oga, saidai duk kunya ta isheta saboda kayan jikinta.
Shikam Yakuma jikin kujera ya lafe yana kallonta k'asa-k'asa, saika d'auka idanunsa arufe suke, amma duk wani motsinta akan idonsa yake, tagama tamik'a MASA mug d'in tea d'in.
Raba hankalinsa yayi gida biyu, rabi a kallon labarai, rabi akan Aysha, yana shan shayi yayinda k'asan zuciyarsa ke shirya masa wani Abu daban.
Aysha dai Baki yamutu, tanacan lafe cikin kujera 1seat abin duniya dukya isheta, dama duk maza haka suke da halinnan?, tana kallon ya khaleel kamar babu ruwansa Ashe Bahaka baneba, shi ko kunyama bayaji Yakama tsotse bakinta, tashafa la66anta da har yanzu suke mata zogi, hawayene Yakuma cika idonta, amma tahanasu zubowa.

Ring d'in wayarsace tasakata juyawa ta kalleshi, wayar na aljihunsa yana k'ok'arin cirowa, ahankali yafurta "Momy kuma? Badai jikinba?" Dan da yamma daya shiga ya tarar da ita tanama Anty zuwairah complen cikinta da k'irjinta sun fara ciwo, saida yace, "suje asibiti" amma tace, "ad'an bari zuwa anjima tunda tasha magani, idana baidenaba saisu jed'in".
Cikin damuwa yad'aga wayar, "ya khaleel jikin momyfa yayi tsanani", 'cewar mufeeda datayi kiran wayar'.
Yanke wayar yayi batareda yace komaiba zai fice, Dan hankalinsa a tashe yake.
Aysha kamar zatayi kuka tace, " jikin momynne?".
Baiyi maganaba, amma ya jinjina mata kai yafita da hanzari..
Kuka Aysha tafashe dashi, Dan wlhy tsoro takeji, tasan kuma tashiga cikin gida yanzu fad'a za'a mata miyasa zata baro d'akinta, batada damar shiga 6angarensu Anty Aymana kuma, dan duk mazajensu nanan, tana mamakin mugun k'udiri irinnan Momy, tarasa mita tsare mata aduniyarnan, tasan tanayin hakane Dan k'untata rayuwarsu, amma babu komai ALLAH nanan.
Tashi tayi ta kulle k'ofar falon, tadawo ta kwanta saman doguwar kujera, kallo takeyi a tsorace dajiran dawowar ya khaleel, amma har 2pm babu alamarsa, kashe TVn tayi dama bata fahimtar komai, takwashi wayoyinsa da lap-top tanufi d'akinta, bata yarda yau tayi zaman wahala da tsoro irinna jiyaba, saita d'auro alwala tazo taita sallah da karatun alkur'ani, wannan yad'auke hankalinta har tayi sallar asubahi sannan tazame a wajen ta kwanta.

Su ya khaleel yauma kwana sukayi akan Momy, Dan jikinma yafi jiya tsanani, dukkan y'ay'anta Na gewaye da ita, harsu hasnah sunanan, Tanana a kira kowa, har baffah, haka suka kwana azaune zubur.
Ya khaleel baidawoba saida gari yayi haske bayan yayi sallar asubahi, saida yalek'a d'akin Aysha sannan, akan abin sallah yaganta kudundune cikin hijjabinta, ga alk'ur'ani a gefenta, tabashi tausayi, ya d'auketa tamkar wata babe ya kwantar a kan gadon, cikin dabara yazame mata hijjab d'in ya lullu6eta da bargo, sannan yamik'e yafice daga d'akin.
Bai kwantaba yau, Dan akwai aikin dayakeson yi ayaud'in, dukda yana cikin hutun angwanci, shirinsa yayi cikin uniform d'in aiki, masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, yashiga d'akin Aysha yana d'aura agogo, haryanzu tanata barcinta, yad'auki lap-top d'insa da wayoyinsa yazuba a jaka, sannan yad'anyi short not ya ajiye mata kan madubi yafice su Adams na jiransa awaje.
Ta gate d'insu yafita, Dan haka babu Wanda yasan fitarsa acikin gidan.
Atare sukayi salute nashi, yad'aga musu hannu damusu godiya akan hidimar bikinsa dasuka tsaya tsayin daka aka kammala lfy.
Adams yabud'e masa motar yashiga, sannan suma duk suka shiga.


___________________________
Aysha bata farkaba sai around 10, ta tashi d'aukeda addu'ar barci abakinta, tayi mamakin Wanda ya maidota saman gadon, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne".
A gaggauce ta k'imtsa kanta, saida tazo gyaran d'akin sannan talura babu wayoyinsa da laptop, d'aukar y'ar takardar daya ajiye tayi, written d'in yamata k'yau.

_ Nad'an fita wani aiki, amma insha ALLAH bazan dad'eba zan dawo. _
_ ki kula da kanki. _

Aysha tayi murmushi, tareda maimaita _ki kula da kanki_ sau babu adadi, kalmar Tamata dad'i sosai, aganinta wannan kalmace dake nuna kulawa akan abinda kadamu dashi, "kenan ya khaleel yadamu da ita?", takai hannunta tana shafa la66anta datuna abinda yamata jiya da daddare, ta sumbaci takardar tanamai lumshe idanunta, ahankali tafurta ina k'aunarka sosai ya khaleel, Dan ALLAH Nima kasoni fiyeda yanda nake sonka, (Dan bazaka ta6a Sanin inasonkaba harsai kafuta soyayyata da bakinka), zan rayu dakai, zankuma mutu da sonka, Abadan inafatan mukasance tare har mutuwa, dukda mugayen dake zagaye da rayuwar aurenmu, amma ALLAH zaimana maganinsu da k'arfin ikonsa.
Haka taita sambatun begensa ita kad'ai, tanayi tana aikinta, tsaf tagyara gidan, ko ina yad'auki k'amshi, har d'akinsa saida takuma gyarawa, dukda babu wani datti, tunda baikwana acikiba.


____________________________

Su ya khaleel kam suna can sunyi fakon Lazarus, babban yaron Ahaji bishasha, Wanda suka sami damar kamashi a babban shagon saida kayan masarufi dake kasuwar suleja, yazo sayen kayan abinci dasukan saya duk k'arshen watanni uku zaikai mafakarsu, ankamashi bisa had'inkai damai shagon yabasu, saboda shima yagaji da cutar dasuke masa, sometimes sukan d'ibi kayan masarufi amma basa biyanshi, idan yay magana sumasa barazana da mutuwa, yanason Barin kasuwar kuma sun hanashi saboda zalunci, since yana Barin wajen zasu kasheshi shida iyalansa.
Abinciken su ya khaleel ne suka gano nanne shagon dash Lazarus kezuwa siyen kaya aduk bayan watanni uku, shiyyasa suka nemi had'inkan mai shagon, dukda daga farko yaso musu k'arya saboda tsoron abinda zaije yadawo, saida ya khaleel ya tabbatar masa zai sassa6a masa kamanni sannan yabada bayanan gaskiya.


Aysha nacikin aiki saiga tasleem dakayan break fast, ita ta taimaka mata suka kammala komai, sannan tagudu, Dan azatonta ya khaleel nanan, dukda kuwa Aysha ta tabbatar mata dabaya gidan, amma tak'i tsayawa.
Aysha tazauna tayi break d'inta, bayan ta kammala takira Ummah suka gaisa, tak'ara mata nasiha. sannan takira mama, tana mata shagwa6ar yaushe zata dawo? Itafa Tayi missing na sosai.
Mama tace, "to daba'a gidan kuka zaunabafa? Kijimin yarinya da iyayi, INA mijin naki kike addabata da safiyarnan?".
" kai mama, wannanne Safiya, 11 fa tawuce".
"Eh duk da hakan, ainasan mijinki nagidan ba aiki yake fitaba shiyyasa".
" to aii mama barci yakeyi bai tashiba, mama kamarma kin daina sonafa?".
Dariya Maman tayi tace, "keni bazan iya da fitinarkiba Aysha, kinga sai anjima, ki gaida mutan gidan".
Kafin Aysha tayi magana mama ta Yanke wayar.
Dira k'afafu tafarayi irinnan shagwa6a tana fad'in kai mama! kai mama!, saikace tana gabanta, a haka mufeedah tashigo tasameta, ta ta6e Baki da sakin tsak'i, tawuce d'akin ya khaleel batareda tayima Aysha maganaba.
Itama ayshan ko kallo mufeeda bata ishetaba, saima fad'i take aranta, "" inama yananan yacimin uwarki, shegiya karuwar gida, lokaci kad'an yaragemin namiki tonon silili, tsohuwar guzuma kawai, badolema kiyi karuwanciba shekara kusan 28 babu mijin aure".
Tana cikin gulma da zuciyarta mufeedah tafito tana cikada batsewa, "k! INA ya khaleel?".
Yatsina fuska ayshan tayi tana kauda fuska, tamkarma batasan dawata halitta awajenba.
Hakan Yakuma tunzura mufeeda kuwa tace, "k! Dan uwarki bak'ya jinane? ALLAH saina lakad'a miki dukan tsiya".
Idanu Aysha tazaro tana fad'in "Kuttt dukafa? Ina matsayin matar yayan taki? Lallai Ashe kuwa zaimiki dukan mutuwa agidannan, aiko Momy tadakeni banyi tunanin zai d'aga mata k'afaba bare ked'in, idankuma zaki gwada bismillah".
Duk maganarnan da Aysha keyi a tsorace take, dantasan mufeeda zata ita zaneta d'in, gashi gida babu kowa, amma Dan k'arfin hali irinnan Aysha saita dake, harda wani girgiza jiki.
Bak'inciki yakume mufeeda takasa magana, sai zuwacan tayi kwafa tareda Nuna Aysha da yatsa, ai wlhy sainaci ubanki agidannan naga mai d'aure miki gindi, dagake har uwarki sai zaman gidannan ya gagareku.
Aysha tarik'e k'ugu tana fad'in tofa babbar magana, wai d'ansanda yaga gawar soja, zaman gida bai gagari karuwar dareba, dakuma dillaliyar kai yara karuwanci k'asashen duniya saimu?, a dai kula kar'a kwaso mana ciwon sida, a6ata sunan gidan dattijo mai mutunci irin baffah.
Shiru mufeeda tayi, Dan maganar Aysha ta birkita kwalwarta, sai kawai ta6ige da borin kunya tana zagin Aysha, saita fad'ama Momy tazo taji dasu ubanda take, a can k'asan zuciyarta kuwa sai luguden Daka yakeyi, tana mamakin a INA Aysha tasan tana fitar dare? Saidai idan d'an gwari mai gadi yafad'a mata, aiko aikinsa yak'are agidannan, gwamma tamai kutu-kutun daza'a koresa kafin ya tona mata asiri, sosai maganar ta daketa, dukkan ga66an jikinta rawa sukeyi.
Tana fita Aysha ta ta6e baki tareda Jan tsaki, tafara laluben number yaya fadeela dansu gaisa.


Mufeeda kam k'arya da gaskiya taje ta zayyanema Momy, amma ita babu zancen ance mata karuwar gida, saidai tafad'i na Momy dillaliyar kai yara karuwanci kasashen duniya.
Anty shukurah tace, "k! Mufeeda kiji tsoron ALLAH, y'ar yarinyarnance zata fad'i haka? Wlhy babu k'yau tada musifa, keda aka aikekima kiran khaleel miye ya had'aki da ita?.
Mufeeda ta turo baki gaba, "kai kajimin Anty shukarah d'innan, bata fad'aba zance tafad'a".
Momy kam takasa cewa k'ala, danba k'aramin dukan zuciyarta Aiken na Aysha yayiba, Anty zuwairah tamik'e tana hucin bala'i, " bara naje naci uban yarinyarnan da kaina, saita fad'i waye dillalin kai yara karuwancin?. Momy tanason dakatar da Anty zuwairah amma bakinta yamata nauyi.
Anty shukrah ta harari mufeeda tana fad'in "hankalinki ya kwanta kin had'a saikijira kuma sakamako daga khaleel, dannasan ba k'yaleki zaiyiba wlhy.
Mufeeda ta tunzuro baki gaba tana k'unk'unin fad'in "yo basai Momy tabarsaba sannan zai dakeni".
Aysha nacikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login