Showing 93001 words to 96000 words out of 155647 words

Chapter 32 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

483

alamun sanyi takeji, jikinta ringim yake da zazza6i, yariga yazame mata jiki, haka take wuni dashi takwana dashi.
Idonsa akanta yasunkuya ya sumbaci goshinta da la66anta, sannan yagyara mata bargon sosai yajuya yafice.
Ko sallama baima Ammah ba yafice, bata damuba, dantasan zuciyar 'yan mazan tana kusa yau.
Itama Tisa k'eyar mufeedah tayi suka shiga bedroom d'in, suduka a gadon suka kwanta, Dan gadon Ammah babbane, zaima iya cin mutum 6.

Yauma haka ya khaleel ya kwana babu dad'i, da k'yar barci yad'aukesa wajen 2:30, bayan yayi nafilfilinsa yamik'a kukansa wajen ubangiji.

**********
A 6angaren Momy kam, tunda Ammah tafita da ya khaleel da mufeedah hankalinta yakuma tashi, inna jummai kuwa Dan munafunci kuka tasanya, wai za'a rabata da jikokinta.
Babu Wanda yabi takanta, Dan kowa damuwarsa ta isheshi>??.


*_Bayan kwana uku_*.
Kowa ka kalla agidan kasan akwai damuwa, Dan kowa sukuku yake, duk abinda yafaru adaren ranar yagama karad'e gidan, harara da tsaki da habaicin yaran gidan yasaka inna jummai tattara inata-inata dole tabar gidan, dansu Tasleem sungama tasota gaba, dasu Nureedin Ummu noor babu mai raga mata agidan, musammanma matansu ya Sultan, basa yimata agaban mutane, saisun ganta itakad'ai.
Ita kanta Anty Zuwairah da Anty Shikurah bawani shiga sabgarta sukeyiba, Aleeya kam kwana biyu ma bata gidan, waitaje aiki wani asibiti Na sati 1, dama haka takeyi, takanje tayi kwanaki saikuma yadawo, babu Wanda yata6a damuwa dahakan, Dan a zatonsu aikin daya kawota take zuwayi.


Nidai nace hummm.


Akwanaki ukunnan kuwa ya khaleel ba'a magana, dukya wani birkita kansa, duk binciken daya dace akan Aysha yayishi, amma baikamata dawani kuskureba, saidai hakan baisa yagama yarda da itaba, hakama Anty Mamie yasaka mata idanu itada Momy.
Shida Momy yanzu kam gaisuwace kawai, itama sama-sama take amsashi, baidamuba, baikuma ta6a nuna mata yadamunba.
Aysha kam sosai takeshan wahalar cikinnan, gadamuwar rage kulawar da ya khaleel ke nuna mata, ita harma mamakin mufeedah takeyi, kokad'an nata cikin baya bata wahala, amma ita kullum tamkar kurar wasa haka take yini agidannan.
Mama nazuwa da safe da dare kawai dubata,, Anty Mamie kuwa aii koda yaushe tana zaryar tambayar mi Aysha zataci adafa mata ko a siyi mata?.
Data fad'ane zataje ta dafo matashi, kokuma tabada asiyo, Ummie Amaryama tana bakin k'ok'arinta, kafin tatafi aiki satazo dubata, idan tadawoma haka, kuma zakiga tasayo mata 'yan abubuwan kwalama namasu ciki.
Yaran gidanma kwai da kwarkwata dasafe saisunzo gaisheta, masu schools sutafi masu aiki su tafi, Anty zuwairah madai anad'an lek'owa sau 1 saboda gori da Ammah tamata, to gobema suke shirin komawa Lagos, dama yaran tuni sun koma saboda makaranta, Anty Amatullah kuwa tatafi jiya, Anty shikurah dai tana nan tukkuna, mijin take jira, Dan INA k'yautata zaton sundawo Baki d'aya, yanzu hakama gyaran gidansu akeyi.
Matansu Sultan kam yanzu sunmaida 6angaren Ammah wajen hirarsu, harda amare suma, duksun saki jikinsu anata harkokin arzik'i dasu.
Gwaggo bintu itama kulawa ta musamman Aysha kesamu saga gareta, ita har mamaki abin kebatama

**********

Ya khaleel dasu Joseph zaune ad'akin bincike, su Solomon duksun duk'ufa akan computers, har shima ya khaleel d'in, suna bincikene akan wani dasuke harin kamawa, kusan awanni biyu suka d'auka, bayan sun kammala suka fito.
Ya khaleel yakalli Taheer dake gefen haggunsa.
" Tafeer inason ganawa da kubrah".
"OK sir, babu damuwa, idan ka shirya saimuje".

"Eh, muyi sallah first amma, tunda naga time yayi", yay naganar yana kallon bak'in agogon hannunsa".
"Atare sukace to".
Wad'anda zabasuyi sallan ba suka koma office, sukuma suka nufi massalacin dake cikin setetion d'in.

Suna idar da sallar la'asar suka fito, ak'ofar massalacin suka iske Joseph, basabon abu bane hakan awajensu, Indai zasu shiga sallah yakan tsaya yajirasu awaje.
Musabuha>?? Sund'an ta6a hira akan abinda ya shafesu, akuma k'arshen watannan zasu bud'e k'ungiyar matasansu dasuka kafa.
Daganan su youseef suka tafi office, taheer kuma shida ya khaleel suka tafi Inda kubrah take a gark'ame. .......
'

Kubra one Luv>?#?>?8? @&



*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


3? 5?

Dogon d'akine, saidai anyi kananun d'akuna aciki tamkar na prison, yawancin d'akunnan dukda mutane aciki, matane kuma zallah awajen.
d'akin dake can k'arshe suka k'arasa, kubrah Na zaune tacusa kanta tsakanin cinyoyinta, sai kuka takeyi, bata ta6a tunanin shiga wanga haliba, musamman yanda ta'iya takunta.
K'arar bud'e k'ofarce tasanyata d'agowa da sauri dukta fita hayyacinta, kamar wata sabuwar kamu a hauka.
Ganin khaleel yasakata mik'ewa zumbur zata nufosa, wata uwar tsawa Taheer yadaka mata, babu shiri tayi baya ta zauna da6ar.
Lumshe ido khaleel yayi yana girgiza kansa, Samuel dake binsu abaya ya ajiyema ya khaleel kujera, zama yayi idonsa akan kubrah data koma jikin bango ta raku6e.
Saida yamata kallon minti 2 sannan yajuyo yakalli Sam... Da Taheer batareda yayi maganaba.
Ficewa sukayi, Dan sungane miyake nufi.
Suna fita yadawo da kallonsa kanta, itama dataga daga ita saishi saita fashe da kuka, tana fad'in "Dan ALLAH khaleel kafitar dani, wlhy bammusu komaiba, zalincine yasakasu kamani".
K'asaitaccen murmushi ya khaleel yayi, Wanda yadad'e baiyi irinsaba saboda damuwa, cikin turo iska daga hancinsa yace, " nima abinda yakawoni kenan kubrah, nasan ked'in mutuniyar kirkice, banta6a ganinki kina aikata Abu mara k'yauba, zan ku6tar dake ammafa saikin bani had'inkai".
Har taune harshe takeyi wajen fad'in "wane irin had'inkai?".
Nanma murmushin yasaki, muryarsa can k'asa yace, "kwantar min da hankalinki mana my Sweet".
Wani dad'i yaratsa kubrah, khaleel yacemata Sweet.
Shima murmushin yayi danya hango matakan nasara.
" kubrah wanne kasuwanci kikeyi ak'asashe daban-daban Na duniya?, dannaga bak'ya kulla watanni biyu a Nigeria ".
Tashin hankali, jikin kubrah ne yafara 6ari. Khaleel yace, " yahaka kuma da rawar jiki? Tambayacefa bawani abuba, saikace wata mara gaskiya?".
"A...a'a wlhy, inada gaskiya khaleel, dama dai tambayarce tazomin a bazata, shi....shin...shinefa kawai".
"Uhyimm, Sorry fa kinji".>?(?
Khaleel yay maganar yana d'age gira d'aya sama.
" ina jiran amsarki".
"To khaleel mizance maka, kasan ina business ne aii".
" Nasan business kikeyi, amma wane iri nufina?".
Gumin da keta tsatstsafo mata ajiki tashare da hannun doguwar rigar atanfarta, amma takasa furta komai.
Shikam khaleel yayi masifar tsura mata idanu, zuwacan yace "shikenan, shikenan, barma waccan tambayar Nagano amsarta, miye alak'arki da hajia khaltum?".
"Kamar Yaya take a wajena".
"OK".
" akwai wadda kuka ta6a zuwa gidanmu da ita, lokacin bikina, itakuma wacece? A INA kuma take?".
"Kamar zata fasa kuka tace k'awatace".
"Tana ina yanzun?".
" kwanaki tayi had'arin mota tama rasu".
"Ayya, lalai ta iya mutuwa, amma nikuma naganta kwanakin baya a Lagos, zataje America".
Afirgice kubrah tace, "glory d'in?, itafa a Islands UK takema".
K'aramar dariya ya khaleel yasaki, danya samo amsar tambayarsa, yace, "kwarai kuwa, saidai inaga bayan dawowarta tamutu ko?, waccan dai kamar sunanta glory Zamani, koba ita baceba?".
Kubrah tasaki ajiyar zuciya, "A'a ba ita baceba, k'awata sunanta glory maba".
" dak'yau 'Yar gari, kin gamamin komai, tabbas ba ita baceba, amma ina jajanta miki mutuwar k'awarki, zanje muyi magana da habeeb dan yazo ya kar6eki, idan ni nanemi haka baza'a baniba, za'aga kamar munhad'a bakine".
Godiya kubrah tamasa, dad'i yakamata baigano komaiba, gashima har yana shirin k'ubtar da ita.
Harya mik'e Yakoma ya zauna, af kinga kuma Na manta, a INA zan samu habeeb?, Dan inaso yazo gobe, jibi inada tafiya zuwa London ".
"Ito habeeb d'inne sai a slow, amma hanya mafi sauk'i kaje Cinema, yau za'a haska film, Na tabbatar zaije".
"OK thanks, angama, gobe ki saurari sakamako, bye my Sweet=? ?".
Dad'i kamar yakashe kubrah, haka Sam...yashigo ya d'auki kujera yafice, aransa yace banza, bakisan halin boss bane, dagani wayo yamiki.



______________________________
Tunda ya khaleel yadawo office yaketa tunane-tunane, ta hanyar dazaibi yaje Cinema yau, ga tunanin binciken glory, ta inama zai fara?, kiran wayarsa da'akayi yakatse masa tunani.
Wayar ya d'auka yaga Aysha Ce.
Guntun murmushin yayi, danya kula kwana biyunnan tashiga damuwa da sharetan dayakeyi, saida takatse yakirata, bugu biyu kuwa ta d'aga.
Muryarta can k'asa akuma galabaice tayi sallama, komawa yayi yajingina da kujera, shima murya can k'asa ya amsa mata, yace, " gimbiya yajikinne?".
"Ga shinandai, ya aikin?". 'Duk a shagwa6e take maganar'.
Saida ya furzar da huci sannan ya amsa mata da Alhmdllh, yaudai babu zazza6in ko?".
" akwai mana, yanzuma nagama amai".
"Wannan amai bazai tausayaminba, yabarki kid'anyi k'ibama, mikikaci to?".
"Kunun gyad'ane".
" sannu kinji sholyna, babies suna wahalarmin dake, dolene idan sunzo duniya namusu bulala, Saboda wahalarmin dake dasukayi, kona dawo gidane?".
'Yar dariya tayi, wadda tadad'e batayiba, tace, _''A'a Sadauki, gara kazauna a office, kullum burina bai wuce kakawo k'arshen azalumaiba, idan kayi hak'an 'ya'yankama zasuyi alfahari dakai, hakan zaikuma tabbatar musu mahaifinsu jarumin jarumaine, 100% nimai k'arfafakace, bamai raunanakaba, koda yaushe addu'ata nanan biye dakai, nidai Burina kada kabar Azzalumai suyi barci mai dad'i, kahanasu dariya da farinciki, ALLAH ya dafa maka mijina abin alfaharina nida al'umma=؋?=؋?._
d'ifff takashe wayar.
Zabura ya khaleel yayi daga kwancen dayake yana saurarenta, "please karki kash......"
Ina harta kashe, cikin hanzari yake dialing d'in number, amma ance switch up, yagwada yakai sau hud'u amma maganar d'ayace akashe take. Maida akalar Kiran yayi kan Ammah, cikin kwakwazonta ta amsa, dama Amman bata iya waya ahankaliba>?#?.
Kowacce Lamba da alamar datama mutum yanda zata gane, Dan haka khaleel Na kira taganeshi, iro!! Kaine da rana tsakarnan? toya ofishin nakune?".
Dafe Kansa yayi, afili yace, ''wayyo nafa kira uwar kwarmato, yanzun saita had'amin mutanene gidan duka".
"Wai iro Baka jinane?! Allo iro!, nifa banajinka, inaga natuwok ne, kasake kirana kawai ta ajiye batareada ta Yanke wayarba.
tsaki yaja ya Yanke wayar, afili yace, " kai tsohuwarnan akwai kwakwazo, zubaina kenan, tuni Ammah zata saka kwalwar mutum harmutsewa, shi kawai inda yake sonta akwai tsage gaskiya".
Komawa yayi Yakuma lafewa jikin kujerar, kalaman Aysha sai kai kawo suke a zuciyarsa, yarasa mitake nufi? Yakuma kasa fassarasu? Amma tabbas kalaman NATA sunfi kama dana mai gugar zana.
"O my god, waimike faruwane?".>?&? B&

*********
Gaba d'aya yau haka yaraba hankalinsa biyu a office, rabi kan aiki rabi wajen FASA kalaman Aysha Dason fassarasu, amma har kusan 11 Na dare dayakai baisamu fashin bak'i ko d'ayaba.



____________________________

Wajen k'arfe d'aya Na rana saiga hajia khaltum tazo yima Momy barka da tashin bak'i, batasan abinda yafaruba ita, saboda tayi tafiya zuwa Benue state tun washe garin bikinsu mufeedah, wani aikin k'ungiyane yakaita.
Tunda tashigo falon taga sauyin fuska ga aminiyar tata, bata damuba tazauna suka gaisa, Momy tajata suka tafi k'uryar d'aki kamar yanda suka saba, saboda bataso yaranta su fahimci komai, babuma kowa daga ita sai zuwairah da mashi'a mai aiki, ganinma tayi bak'uwa Anty zuwairah tad'auki gyalenta tafita nan makwaftansu gidan wata k'awarta Tamata sallama.
Mashi'a ce kawai a kichin, itama ganin Anty zuwairah tafita sukuma shunshige bedroom saita turama Aysha message akan tazo.
Aysha nakwance ciwon ciki ya isheta taga message d'in mashi'a, amma dan k'arfin hali haka tasato jiki tafito.

Hajia babba da hajia khaltum na shiga d'aki suka zauna a bakin gado, hajia khaltum ta kalleta, "umm aminiya barka da tashin bak'i fa, Ashe 'yan biki duksun kama gabansu?, kai Alhmdllh, daganan kuma sainasu babie na, kisan kuwa yanda aiki yayi k'yau a Benue? Yara kusan 13 nasamo mana, kuma zagad'a-zagad'a, wannan karon kubrah ce zata tafi dashu UK, munsami sabon dila ma bayan john, hhhhh aikifa na k'yau aminiya, kud'i sai k'ara zama sukeyi, shiyyasa ban damu da account d'ina da Ibrahim yarufeba, saboda k'aramine, nidama bana zuba zunzurutun kud'i a banki aii."
Itadai Momy batace k'alaba, duk uban surutunnan da hajia khaltum kezubawa, bata kula Momy tayi kicin-kicin da fuskaba, saida takusa kai k'arshen aya sannan talura.
" a'a aminiya waishin lafiya kuwa?".
"Da sauk'i dai khaltum".
"Mike faruwa to?".
" mufeeda tadawo gida tun kwana biyar dasuka wuce".
Wata zabura hajia khaltum tayi, tagyara zamanta sosai tana fuskantar hajiya babba, "ki min dallah-dallah mana yanda zan fahimta".
Afad'ace hajia babba tace, " aii dolene namiki dallah-dallah kuwa khaltum, domin tasilar habibu aka sakkomin d'iya, habibu ya yaudare Mufeedah ya d'irka mata ciki, wannan ne dalilin dawowarta gida harda saki".
"Habibu kuma? Habibuna daine ya yaudari mufeeda da girmanta? Shekarun mufeeda nawa aduniya hajia laurah? Ince 27? Yanzu mai shekaru 27 ne aduniya za'ace an yaudareshi?, please babu wannan tsakaninmu, idan har cikin ya bayyana jikin mufeeda, kuma yakasance Na habibune to tabbas da had'in kanta, amma babu batun ya yaudareta anan, idanma gaskiya kikeso kawai mu jingina laifin Kansu su duka, amma bawai shikad'aiba......."
"K!!! Hajia khaltum!, wlhy ki iya bakinki, zan d'auki komai arayuwa amma banda wulak'anta rayuwar 'ya'yana, ya ina gaya miki magana zakina gayamin babu dad'i? Kema kinsan wanene bunsurun k'aninki aii........
" laurah!! Maza sakama bakinki linzami wlhy, inhar habibu bunsurune aii mufeeda ma akuyace, tunda ba har ciki gida yazo yamata fyad'eba, kum.........

Aysha data shigo d'akin da sauri tace, "kai Sirikata kuyi ahabkali, kuna d'aga murya dayawafa, gashi ya khaleel yana gida, kuyi maganar k'asa-k'asa surukata>?-?. Saikuma Aysha ta shek'e da dariya.>?#?
Daga hajia khaltum har hajia babba mutuwar tsaye sukayi, suma kasa cema Aysha uffan Dan mamakinta.
Hajia babba ce ta harzuk'o zata shak'e Aysha, da sauri Aysha tad'aga mata hannu tanaja da baya, " A'a fa Surukata, karkiyi wannan kuskuren, akwai jikanki anan", tanuna cikinta, "sannan ta6ani babban kuskurene dazai iya 6allo ruwafa, nidama shawara nazo Baku, aganina daku zauna tada jijiyoyin wuya kan k'yautar jika da ALLAH yabaku, gamma kulura da abinda ke tunkaroku fa, kuyi azamar bincika ina Kubrah? yau tsawon kwanaki 3, itada tace zataje Lagos tayi kwana 1".
" sannan kekuma k'awar surukata kibar tada jijiyar wuya akan beeb guy, >?#?>?#?kema yasama miki jika kuma d'a ajikin 'yarki babie>?*?".
"Please & please aminan juna, abar fad'a fa, kusan masu iya magana nacewa *_SHARRI 'DAN AIKENE, DUK KUMA INDA KA AIKASHI SAIYA DAWO YASANAR MAKA YAJE=? ?_*.
Bye, har Aysha tafita tadawo, "o, wlhy Na manta suruka, dama inason fad'a mikine idan za'a siyama mufeeda kayan haihuwa atuna da d'an jikalle>?(?, tayi maganar tana nuna cikinta>?#?>?#?, tafice tana 'Yar dariyar mugunta.

Rasa wanda zai iya motsawa acikinsu akayi, maganganun Aysha sungama dukan zukatansu, kowanne arikice yake, hajia khaltum ta kalli hajia babba, itama kallonta takeyi, " Aminiya da gaske yarinyarnan keyi? Habibu yayima babie ciki, kuma ankama kubrah?".
Cikin marairaicewa hajia babba tace aminiya ban saniba, amma ina mamakin rashin dawowar kubrah dama, Dan kwana d'aya tace zatayi, gashi tunda tatafi bata kiraniba", hajia babba tayi maganar tana zama agado ja6ar'.
Itama hajia khaltum zubewa tayi, sai zufa sukeyi kamar babu fanka ad'akin, jiki Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login