Showing 111001 words to 114000 words out of 155647 words

Chapter 38 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

478

kwanakin mijinta 5 kacal da rasuwa, gaisuwama naje mata.
Atake anan Yaya fad'ima tacemin muyi amfani da Aysha d'iyarta kawai.
Wannan magana bak'aramin razanani tayiba, nacema Yaya fad'ima hakan bazai yuwuba, yaza'ayi musaka rayuwar Aysha ahad'ari, tunda bamuda tabbas akan zata iya baro wajennan ba'a 6ata rayuwartaba.
Bud'ar bakin Yaya fad'ima saitace hakane, kuma tayarda da zancena, amma ita bazata saka rayuwar d'an kowa ahad'ariba, itakuma nata 'ya'yan a killace, ta sadaukar da Aysha danta ceto rayuwar yara masu d'unbin yawa daga gararin rayuwa, inhar rayuwar Aysha ta lalace awajennan tad'auki hakan amatsayin k'addara, amma tana rok'on ALLAH yama tsare mata ita, kodan darajar maraicinta dakuma sadaukarwa datayi amatsayinta Na uwa agareta.
Hummm Na jinjinama k'ok'rin Yaya fad'ima awannan lokacin, Dan masu irin zuciyarta k'alilanne aduniya, bakowane keda irin wannan k'yak'yk'yawar zuciyarba, kuma duk akan kishiya, wadda mutane dayawa suke d'auka amatsayin abin k'yama, (wlhy hakan datayi yakuma sakama zuciyata salama akan wani Abu waishi kishin banza, tabbas kishin taimakon juna shine kishi, ba kishin hauka Na wannan zamaninba), awannan lokacin naji araina ina addu'ar son dawowar Yaya fad'ima d'akinta Na asali.
Haka nadawo Abuja cikeda al'ajabin jarumtar mace irin Yaya fad'ima.

Kwanakina biyu da dawowa kacal saiga bintu d'ukeda Aysha kuwa.
Aysha bata sanniba, saboda duk sanda zanje gidansu saida nik'af nake zuwa, ko Ummah abokiyar zaman Yaya fad'ima bazata ta6a shaida fuskataba bare yaran gidan, bama koyaushe nake zuwa gidanba, saidai Yaya fad'ima tafito muhad'u awani waje.
Hummm wani al'amarin ubangiji hajia laurah naganin Aysha kuwa saita tanka, dama nasan dawuya hakan bata faruba, saboda Aysha tanada k'yau da tsarin halitta irinta mata, dukda alokacin yarinyace ita k'arama.
Wannan tankawa datayi kuwa bintu ta sallama mata bisa yanda muka tsara.
Hajia laurah suka d'auki mak'udan kud'i suka bama bintu, duk Na kar6ar Aysha.
Dukda yarinyar tana bani tausayi, amma haka muka kauda kai nida bintu aka tafi da ita, da taimakon wata mai dillacin yara muka samu akabama kubrah Aysha kamar yanda muka tsara, ita kuma waccan mai dillacin ba 'Yar k'ungiyar baceba, suna amfani da itane batareda tasaniba, saisu sakata samo yara daga k'auye amatsayin za'a sakasu aikatau, data basu shikenan sai'a rarrabasu k'asashen duniya batareda sanin iyayenauba da ita kanta wannan mata.
Alhmdllh Aysha taje islands UK, inda matashiyar budurwar nan take, kuma ana kaita ta ganeta, Dan nasanar mata komai akanta ta waya.
Hummm kuyi hak'uri, bakowa baceba budurwa nan face meerah!!...

Arazane Aysha tamik'e cikin dafe k'irji, tace, "Ummu amarya kina nufin Anty meerah ta?."

"Yes lil sholyna haka zancen yake".
Meerah tafad'a daga k'ofar part d'in Ummu amarya.
Kowa saida yajuya ya kalli meerah dake takowa cikin falon inda kowa yake.
" lil sholyna kiyi hak'uri, kuma kimin afuwa, banida za6in d'aya wuce hakan, saboda ceton d'inbin yara mata dake fuskantar mulkin mallaka irinnan k'ungiyar su hajia laurah, wadda akema lak'abi da saunan *('ya'yan kunama)*, tabbas sud'in 'ya'yan kunamane masu amsa sunan 'ya'yan sharri, Dan adalilinsu ALLAH kad'ai yasan yara nawa suka salwanta da matasanmu. Nadad'e ina neman hanyar ku6tar da 'yan uwana, amma babu mai taimakona, sai had'uwata da wanan baiwar ALLAH hajia saudah, itace ta k'arfafamin guywa da yak'inin zamu iya tarwatsa wanan k'ungiya da ire-irenta, amma saida k'arfin addu'a da taimakon juna.
Aysha shugowarki rayuwata itace mataki nabiyu danagane ubangijina ya amshi addu'ata danakeyi adare darana, akan ALLAH ya canjamin rayuwa, dukda sanadin kwad'ayin mahaufiyata Na tsinci kaina, tabbas kece kika canjani, dukda kasancewarki k'aramar yarinyar akaina.
Aysha nina shiga nafita nasamu aka sakaki makaranta, saboda ALLAH ya taimakeni john yanuna yana sonki, nasan kuma hakan daga ALLAH ne kawai, (maybi ALLAH yadubi sadaukarwar mahaifiyarkine, kokuma maraicinki, dakuma yawan ibadarki) yacusa soyayyarki a zuciyar john, harya kasa keta miki mutunci aranar daya fara ganinki, bayan kuma hakan baita6a faruwaba, Dan tunda nake banta6a ganin john yad'agama wata yarinyar da'aka kawo k'afaba komin k'ank'antarta kuwa, amma ke sai ubangiji yahanashi cutar dake.
Nasarar dana samu tasilar abokinsa kika shiga makaranta shine yazama matakin nasararmu tafarko akan k'ok'arin mahaifiyarki da kuma hajia saudah.
Alhmdllh saikema kika maida hankalinki, gakuma kwazo da ALLAH yabaki.
Ya Naufal shine mutum na biyu damuka k'ara samun ha6akar nasarori ta silarshi.
Dukda naso fahimtar kamar akan aiki yake bibiyarmu, amma yata 6oyemin hakan, nima saina tattara Na hak'ura saboda nakasa gano komai.
ALLAH sarki Aysha aranar da kad'an yarage john ya keta miki mutunci bakiyi mamakin zuwan period d'inkiba?.
Bata jira amsar ayshaba tacigaba dafad'in, nina baki magani dasafe saboda jininki yazo, nayi hakanne dalilin jin firar glory da kubrah awannan daren, suna labarin washe gari kema john zai d'and'anaki, hankalina yatashi ainun Aysha, adaren ranar saida Na nemo maganinan da k'yar, saboda komai Na turai akwai tsari da k'a'idoji.
Hankalina yatashi sosai ganin har John yazo gidan banga alamar jininki yazoba, alokacin haka naita kuka, danna sadak'ar john zaici galaba akanmu, amma alhmdllh Shi ubangiji baya barci, kuma yanjin kukan bayinsa da taimakonsu, saiga jininki yazo, Wanda hakanne matakin nasara Na uku, john bai keta haddin mutuncin marainiyar ALLAH ba, wadda tafito daga tsatson uwa mai tsarkakakkiyar zuciya.
ALLAH gafurun rahimun yabama ya Naufal damar ku6tar damu, bayan Na tattaro mafi yawa daga cikin sirrin k'ungiyar su hajia laurah, batareda yayi la'akari damu suwayeba.
Mijina ngd sosai akan rawar daka taka arayuwarmu.

Murmushi ya Naufal yayi, ya ida takowa ahankali zuwa cikin falon.
Hajia babba da hajia khaltum dai jikinsu yagama yin sanyi dajin wannan gagarumin k'ulli Na Mama, wanda zasu iya kiransa kai tsaye da suna (takun sauro, mai kwana inda ake nemansa>?*?)

Maganar ya Naufal ce tasaka kowa maida hanakali kansa, yace.
Nima an d'orani akan aikine, gaban ya khaleel yaje yay salute nashi tareda k'amewa, sannan yaja da baya.
Bisa umarnin khaleel Na bibiyeku, har ALLAH ya k'addara soyayya tsakanina da Ameerah, Ashe 'Yar uwatace ma.
Kamar yanda kowa yasani khaleel oganane awajen aiki, dukda nawa reshen aikin Na k'asar Canada, sannan kuma abokineshi tun Na yarinta.
Yasamenine akan yanason namasa aikin bibiyar wata yarinya da'aka tura karatu islands UK, shi yana tsoron asamu akasi ta lalace a zamanta Na turai, kuma yagamsu da tarbiyyar yarinyar 100%, alokacin nayi dariya, harna dinga damunsa akan kodai budurwarsace, amma saiya nunamin bahaka baneba, k'anwarsace, sukda bawai Na gamsu dashi baneba, amma Na kar6i aikin nahad'a dawani na office.
Tabbas nadad'e ina bibiyar rayuwarku keda Aysha batareda kunsaniba, abinda ya tada hankalina shine ganin irin rayuwar dakuke ciki, kuma nafahimci ko kad'an khaleel baisan da wanannba, shi duk azatonsa karatu Aysha takeyi, saboda dawanan akai amfani wajen yimata visa, banyi yunk'urin sanar masaba, Na duk'ufa addu'a dabin dukkan hanyoyin daya dace naku6tar damu daga wannan gur6a tacciyar rayuwa, Alhmdllh nasamu nasarar yin hakan, kukanku yakamata kuyi mamakin yanda nasamu visa d'in fiddaku awannan k'asar mai matakan tsaron tsiya cikin sauk'i.
Gabda zaku baro UK khaleel yabani wani sak'one nabama Aysha<؁?, dukda bansan minene cikiba, bankuma dubaba, harna tabbatar sak'on ya iso gareta ta hanyar Ariana k'awarki ta school, wadda nine nahad'ata da Aysha batareda Aysha tasaniba, nayi hakane danta taimaka mata ta hanyar karatunta.
Har ALLAH yasa muka dawo Canada da zama, khaleel ne yacigaba da d'aukar nauyin karatun Aysha, kuma har sanan bansan manufarsa akan ayshaba, Dan baita6a nunamin wani abuba dake tsakaninsa da ita face dangan takar k'anwa da Yaya.
Ban fahimci akwai alak'ar soyayyaba sai lokacin da meerah ta nunamin wani ring da tambayata yawan kud'insa, takuma tabbatarmin Aysha aka kawomawa cikin wani sak'o=???.
To daga wannan lokacinne zuciyata tafara hasashen Kodai khaleel son Aysha yakeyi?.
Ban gaskataba sai alokacin dayazo Canada wani aiki, yabuk'aci ganin Aysha, dukda dama yakanzo ganinta lokaci-lokaci, amma baya yarda suhad'u, ko alokacin dakuke UK yazo sau d'aya, saidai makarantarku kawai yaje yaganki batareda kin saniba yajuya yatafi.
Amma a Canada yazo kusan 3times.
Ahad'uwarku ta k'arshene kika masa rashin kunya=??.
Alhmdllh nasamu damar maidoku cikin ahalinku, bisa umarnin Khaleel, tareda iyayena.
Wannan shine abinda nasani kawai.

Aysha dai kanta yagama d'aukar charge, raba idanu kawai takeyi wajen kallon ya khaleel da Naufal, amma har yanzun khaleel Kansa Na a duk'e, bai iya koda d'ago ido ya kalletaba bare sauran mutamene dake falon, shikad'ai yasan cikin irin azabar rud'anin dayake aciki a yau d'inan


Umme amarya tace, masha ALLAH, tabbas aikinmu yatafi cikin nasarori akan turbar taimakon ubangiji, Dan bayanan da meerah tasamu damar kwaso mana daga wajensu glory, da kuma wasu sirrika dasuka Sani itada ayshane suka cigaba da taimakonmu, saikuma kaifin basira da hazak'a Na Aysha, Wanda daga baya duksai muka zama 'yan kallo nida bintu da Yaya fad'ima.
Dalilina nafad'in haka kuwa shine yanda Aysha tatashi da ak'idar tarwatsa k'arfin k'ungiyarsu hajia laurah, gata k'aramar yarinya amma sai kwazo da baiwar ilhama daga ubangiji.
Dukda mund'an taimaketa batareda tasaniba, amma gaskiya itace k'arfin aikin nan.
Aysha tanemi had'in kan meerah wajen bama khaleel bayanan sirri akan k'ungiyar su hajia laurah, saboda samuwar salwantar da yara dasukeyi, Wanda k'ank'antar Aysha da k'arancin shekarunta bai hanata son jagorantar taimakoba.
Aysha tabi hanyoyi dayawa naganin tasamu damar sanarma khaleel amma bata samuba, nina ringa amfani da hankalinta bisa ilimin aikina Na lauya, Na 6oye number tareda nuna mata wasu hanyoyi masu sauk'i, sune internet, yanar gizo, Alhmdllh kuma Aysha ta amince dani, nasan hakan yanada nasaba da k'arancin shekarunta, har alokacin akwai wautar k'uruciya tareda ita, Dan datafi haka girma kaitsaye baidace ta yarda daniba, tunda zan iya kasancewa cikin criminals, nayi amfani da hankalinta Na zumrata rami.
To saikuma ALLAH yadubi k'yak'yk'yawar zuciyarta yabata basira.
Dakanta tasamo wani masanin computer, yataimaka mata wajen bama khaleel bayanan sirri.
Ganin aikin yamata yawane muka sakko Aleeya aciki, Dan bamu ta6a tunanin aure zai shiga tsakanin khaleel d'in da Aysha ba, Dan wannan aure nasu kawai daga ALLAH ne, wata ayace ubangiji ya saukar akan hakan, ba wayonmu baneba, bakuma tsarinmu baneba, Dan babu hakan acikin tsare-tsarenmu kam.
Afarkoma somukayi Aleeya ta auri khaleel, Dan tabbas munda yak'inin inhar mukayi yunk'urin nunama khaleel asalin mahaifiyarsa to tabbas dolene laurah tayi yunk'urin salwantar da rayuwarsa, ilai kuwa hakance ta faru, Dan karo uku laura Na harin rayuwar khaleel, ALLAH ne kawai ya k'addara kwanakinsa agaba shida Aysha.
Yunk'urin kashe Aysha Na farko a kwanaki ukun farko datayi ad'akin mijinta khaleel, bayan laura tata pretending akan hana khaleel kwana tareda Aysha,, ganin kwa6arsu zatayi ruwa suka aika su gwaska su sato Aysha, ALLAH mai iko saiya nuna musu ikonsa, aranar sai shukurah ta sanarma Ammah abinda ke faruwa, amma kuma tad'auki matakin gaggawa wajen saka doctor Faisal yima laurah allurar barci, ALLAH kuma ya k'addara khaleel ya kwana a 6angaren nasu.
Dalilin hakanne yasakamu kawo Aleeya ta zauna da hajia laurah amatsayin wadda tazo aiki, tunda tace mata itad'in likitace.
Saidai nida yaya fad'ima mundad'e da fuskantar khaleel yana zargin Aysha, bisaga wasu abubuwa data ringayi agabansa, alhalin ita kanta batasanma tanayin wani abunba, har masu aiki yakawo gidannan su biyu, cikin wad'anda akayi canji bayan mama ta bayyana bintu amatsayin 'Yar uwarta.
Zeenatu tadad'e tanabin kwaf-kwaf d'in Aysha, amma ALLAH baisa tafiskanci komaiba, saboda Aysha Nada wayo, irin Wanda sai an tona d'inan, saikuma Zaliha, itama tadad'e tana bibiyar Aysha har wajen aiki, hakama Afrah, amma basu ta6a samun komaiba agareta.
Wayon Aysha ne yasakata cusa mashi'a jikin hajia laurah batareda itad'in tasaniba.
Kuma tabbas mashia tayi rawar gani, Dan itace tahana khaleel cin alkubus da laurah tabashi ayunk'urinta Na kasheshi alokacin.

Da Sauri khaleel yad'ago yana kallon aysha.
Ba k'aramin tsorone yashigi ayshaba, saboda ganin idon khaleel yazama tamkar garwashin wuta saboda jaa, gashi duk fuskarsa tawani birkice.
Batareda cewa komaiba yajanye idanunsa yamaidasu k'asa kamar yanda suke ada.
Mama tacigaba dafad'in, ko meatpia da Aysha tahana khaleel ci ranar Masha'a ce ta turo mata massage akan karsuci, anzuba guba aciki, rud'ewar da Aysha tayine yasakata kasa control d'in kanta, harta ambaci sunan Laurah, rud'ewa dajin maganar Asama tasaka khaleel Marin Aysha. Wannan shine abinda nadad'e ina 6oyewa samada shekaru 30, Dan haka ina Neman afuwar Wanda Na 6atamawa acikin wannan aikin nawa, bankuma San dalilin laurah Na aikata dukkan wad'anan abubuwanba, tundaga kan sace khaleel har zuwa yunk'urin salwantar da rayuwar yaron, abinda nasani shikad'ai nafad'a.
Yawancin duk Wanda yake falon kuka yakeyi, musamman Anty Mamie data rungume mama da Ummu amarya, shikansa baffah kwalla tacika masa ido, ya khaleel kam babu mai iya fassara halin dayake aciki, Dan tunda yad'ago ido ya kallo Aysha baisake d'agiwaba.
Dukkan hankalin Aysha kuwa yana kansa, batada k'arfin tashi taje gareshine kawai.....
Tunaninta baije k'arsheba khaleel yafad'o daga kujerar dayake zaune.
Kaf falon kansa akayi kuwa, saidai babu ko alamar numfashi a tartare dashi.
Da gaggawa aka d'aukeshi sai asibiti, harda Ammah dake fama da k'afa, danma tasamu taimako daga doctor Abraham, Ayshama ciwo sabo fil yadawo, Dan sanadin fad'uwar khaleel itama ta yanke jikin tafad'i alokacin da tajiyo Anty Mamie nafad'in karka mutu kabarni Dan ALLAH babana.
Wannan kalmata ta daki Aysha kuwa sosai.
Haka aka kwashesu akai asibiti dasu, sukuma su hajia babba su taheer suka tafi setetion dasu.
Tana kuka da kallon 'ya'yanta suma suna kuka, da bak'incikin mugun halinta da dukkaninsu suke k'yamata, musamman Anty zuwairah dataji dukta tsani wanan rayuwa ta Momy maicikeda gallafiri da son zuciya.
Agidan babu Wanda yadamu da tafiya da momy, hankalinsu duk yanakan khaleel...........
'





Amin afuwa>?8? @&, kaina bai daina ciwoba, Na daurene kawai namuku, Dan anzo ga6ar dabazaku juri hak'uriba nasani, muhad'u gobe idan ALLAH ya kaimu, Dan dolene musan dalilin Momy Na aikata dukkan wannan mumunan rayuwar, komai daka Sani d'an Adam yanayinsa bisa jagorancin dalili.
To yakamata musan dalilin hajia babba, dakuma halinda khaleel yake ciki ayanzun=?"?.
Wlhy inajin tausayin khaleel da Aysha, sunfi kowa shan wahala da jigata=?-?=?-?=?-?.

Karku k'osa da kasancewa dani, Dan aski yafara zuwa gaban goshi=?L?





*_ya ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'aya._*=?-?=?-?=?O?

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_

4? 1?

Alhmdllh su khaleel sun sami taimakon gaggawa a asibitin general hospital, dukda su taheer sunso awuce da khaleel d'in Na station nasu, amma baffah yanuna musu Subari akaisa wannan d'in tunda bashi kad'ai baneba.
Shida Aysha d'aki d'aya aka kwantar dasu, gadonsu kusada juna.
Ammah jar wuya kam itakad'ai>?#?.

Kowa kagani a familie d"in yana cikin wani yanayi, kowa da sak'e-sak'en da zuciyarsa kemasa akan abubuwan mamaki dasuka faru yau, Wanda tunani ko hasashen su baffah baita6a kaisu nanba, balle irinsu Sultan dabasu San komaiba.
Ko Anty zuwairah bazata iya dogon labari akan haihuwar khaleel ba, Dan gaba d'aya batafi 6years ba lokacin, to bare kuma Anty Shikurah.>?7? @&
Anty Mamie kam ita kanta daza'a bata gadon kwanciya zatayi, harma a zurara mata ledojin jini dana ruwa, ko'a mata allurar barci tasami Hutu Na wucin gadi, k'ila tunaninta zai dawo dai-dai, ayanzu kam kallon komai takeyi tamkar mafarki zuwa anjima zata farka taga ba hakaba=?E?
@&.
Bawan ALLAH baffah, shiruma maganace gamai hankali, shikansa dauriyace kawai da juriya, amma kallon komai yakeyi tamkar acikin barci ko shirin film, kokuma labarin hik'ayoyi Na marubuta, zuwa anjima komai zai tsaya yaga dukba hakabane.

Haka sukaita zaman asibitin suna dakon jiran farkawarsu suduka ukun, babu mai damuwa da yunwar cikinsa acikinsu, Dan babu Wanda yake a cikin duniyar mutane balle yatuna akwai ci da sha, kowa ya lula cikin gajimaren tunani, masu kukan zuci nayi, masu hawayen fili nayi, masu rad'ad'i da k'unar zuciya nayi, kowa tambayar zuciyarsa yakeyi miyasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login