Showing 117001 words to 120000 words out of 155647 words

Chapter 40 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

480

"Gaskiya bahaka baneba, yalla6ai j! Yananan daransa, ko harbin bullet d'aya baishiga jikinsaba, Dan haka mutane su kwantar da hankalinsu, Ibraheem Abdallah bai mutuba".

*_'yan jarida:-_* ''to amma miyasa yak'i yarda kowa yagansa har zuwa yanzun? Ko hakan yana cikin sirrin aikine?".

Dariya.
" kokad'an Bahaka baneba, bai 6oye Kansa dan bayason agansaba, saidai wasu 'yan dalilai, amma insha ALLAH nanda kwanaki kad'an za'a iya jin bayanaima kaitsaye daga bakinsa".


*_'yan jarida:-_* "to ALLAH yasa hakan takasance, nasan kowa zaiyi murna da hakan, Dan zuciyar 'yan k'asarnan tana cikin jimamai dafargaba kam sosai, basuda burin daya wuce suka j! Darai ayanzu.
Duka duka anan muka kawo k'arshen rahoton namu, jama'a kuma yakamata su kwantar da hankalinsu, kundaiji yalla6ai j yananan daransa, saidai wani daliline ya6oyesa.
Munyi-munyi Nason jin dalilin 6uyar tasa hakan bai faruba, hakama munso jin tabakin shugaban wannan hukuma amma hakan yaci tura, munkira wayarsa har kusan sou hud'u bai d'agaba k'arfin had'a wannan rahoton.
ALLAH ka zaunar dak'asarmu lafiya, kamana maganin 'yan ta'adda.

Kowa ajiyar zuciya yasauke ad'akin, ya khaleel kam saiya lumshe idanunsama gaba d'aya...........
'


*_Happy juma'at Mubarak my sweet fans_*=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=??=??=??=??=??=??=??=??=?K? @&=?K? @&=?K? @&.



Duk wanda yaga yamin magana ta PC ban amsashiba yamin afuwa, mura nakeyi, typing d'in kawai nake dauriyar yi, amma zan duba. ngd sosai.=؋?=؋?


*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_

>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&
*_yau ranarkuce masoya, kumarmatso kusa, ngd da k'auna da k'ok'arin bibiyata, inasonku irin trillions d'innan, kunanan manne azuciyar bilyn Abdul, bazan ta6a mantawa dakuba kona dak'ik'a d'aya=?M?
Zainan umar, Mmn khadija, Hawwa, Aysha admin, Mmn siyama, Ummu hanan, Kbbello87, Amina isah n, Mycm, Zeeharuna, Mss calm, Maryam, mamu, Amina aliyu, Hanan yusuf, Haleema s adam, Ummu'assisdiq, Umar ruqaiyah, Precious, Hajara, Mmn fatima, Mmn beauty, Falmi k aliyu, Mariam a umar, Billy A A, Ummu barakat, Hajara isma'il, Fatima (zarah), Ummu Ahmad, Mommyn iman, Juwairi, Maryam Haruna, Mom muhaseen, Zubby Abdullahi, Maryam sulaiman, Mmn ihsan, Ummin sayeed, Nafisa salis, Amina musa, Aunty baraka, Mmn sanah,
Mmn fkyht, Marnona, Aneesah Abubakar Rimi=??(=?M?
_ina mik'o gaisuwar ban girma da fatan alkairi_
=?M?

4? 2?

Alhmdllh jikinsu yayi sauk'i sosai, maganar 'yan dubiya kam ba'a cewa komai, manyan ogannin ya khaleel Sai zuwa sukeyi dubashi, hakama wad'anda suke k'asansa, abokan baffah ma da matansu, koda yaushe asibitin FAM da mutane, saidafa idon securitys nakan kowa, gudun kar a cutar da ogansu.
Ammah ma tanata samun lfy, Dan bakinnan yana nan rad'am>?#?bai mutuba.

Nagafa gayyar fans dadama awajen sunzo gaisuwa, su o'e akaita washemin hakwara=??, naganoki to=??, kunjifa su madam son gulma anbaza kunne aji wacece, to nak'i fad'a d'in=??.

Da safe aka sallami su ya khaleel, amma banda Ammah, aikam tasaka rigima akan bazata zaunaba, aii k'afarta k'afar ironta, itafa baza'a barta a wannan asibitiba babu iro wani yabiyo dare yasakata abuhu.
Anta lallashinta, aka nuna mata akwai securitys za'a bari suna tsaronta.

"Yo duk tsaron mutum yakai ALLAH ne?, nidaifa bazan zaunaba, duk wad'annan dakake gani iro yafisu jarumta, ganinsa yasakasu wannan zazzare idanun, dasunga yatafi gida gyangyad'i zasu farama mutane, har aje asaceni basu saniba."=??
Babu Wanda bai daraba awajennan.
Ya khaleel yataka ahankali gaban Ammah, hannunta yakama tasakko daga gadon batareda yayi maganaba, shiya taimaka mata takama sandunan dazatayi tafiya.
Saida tarik'e da k'yau sannan suka fara tafiya ahankali, tana d'an d'ingisawa, suka fice.
Kowa da kallo yabisu, baffah yay murmishi tareda kallonasu, " to tsayuwar mi mukeyine? Saimu tafi aii, Dan mu'azzam sunyi gaba da Ammah, muskilancin nakusa har yanzu, shiyyasa baza'a mana maganaba".
Duk d'an darawa sukayi, sannan suka tattara komai suka tafi.
Amotar Sultan suka iske Ammah da khaleel.
Kowa saiya shiga mota, Anty zuwairah tabud'e kusada khaleel tazaunar da Aysha, sannan takoma gaba ta zauna kusada Ya Sultan dazaiyi tuk'i.
Juyowa ya khaleel yayi yakalli Aysha data raku6e jikin murfin motar, talumshe idanunta.
Tausayintane yakashi, ahankali yasak'alo hannunsa tabayan k'ugunta ya kwantota jikinsa.
d'ago idanunta tayi ta kallesa, shima idonsa nakanta, ya d'age gira d'aya tareda k'anne idonsa d'aya.
'Dan murmushi Aysha tayi, tamaida kanta gefen hannunsa ta kwantar.
Yad'anyi murmushi, tareda sumbatar kanta ahankaki.
Duk abinda sukeyi Anty zuwairah da ya Sultan Na kallonsu, murmushi kawai sukayi, amma babu Wanda yace komai.
Ammah dai batasan wainar da'ake toyawaba, hankalinta nakan danna wayarta, Wai tana neman number uncle ma'aruff.=?9?
Bawata tafiya mai nisace takaisu gidaba.
Suna zuwa mama tace Aysha da khaleel suwuce 6angarensu kawai.
Babu Wanda yace komai, khaleel yakama hannunta suka tafi.
Tsaf suka tadda ko ina, da'alama kullum sai'an gyara ko ina.
Aysha tazube saman gadon tana sauke numfashi, Dan har yanzu jikinta babu wani k'arfi.
Kallo khaleel yabita dashi kawai, baice komaiba yafara k'ok'arin cire kayan jikinsa.
Aysha nadaga kwance take kallonsa, harya gama, yad'auki towel ya d'aurama k'ugunsa, sosai Aysha taga ramar da ya khaleel yayi akwana ukunnan.
Ruwan wanka maid'an zafi yahad'a, sannan yafito.
Idon Aysha alumshe taji and'uketa cak.
Da sauri taware idonta akansa, yad'age girarsa duka yana kallonta, bazata juri kallonba, sai kawai ta lumshe idanunta.

Atare sukayi wankan, konace yamusu, Dan duk khaleel ne k'arfin komai, Aysha duk batada wani kuzari ajikinta.
Dakansa yadawo da'ita cikin d'akin, yad'an Mirza mai, yasaka jallabiyya milk color mai gajeren hannu. Ayshama tad'an dage ta shafa man, amma duk awahalce, burinta kawai ta kwanta.
Tana gamawa khaleel ya taimaka mata ta sanya doguwar rigar daya ajiye mata mara nauyi sosai, fara mai adon bak'ak'en furanni, batada hannu, sannan anmata d'inkinne kamar Na yara, rigar tamata k'yau, iyakarta kwaurinta, batakai k'asaba=?W?.
Ita kanta saikuma kallon kanta takeyi amadubin, tasan rigar tagama amsar jikinta, kaikace saida aka gwadata aka d'inka, danma tad'an rame, tana mamakin a ina ya khaleel keta zak'ulo kayanan d'ai-d'ai hakane?.
Bata samu amsarba, saima ajiyar zuciya data sauke, sakamakon jin hannun ya khaleel acikin sumar kanta yana warwareta, dukta cirkud'e saboda rashin samun gyara Na kwana biyu.
Sai matse baki da rik'e hannunsa Aysha keyi, zafi takeji sosai, amma baice komaiba yad'auki cumb yana taje mata, bayan yasaka mai sosai, dukda haka zafi Aysha keji, sai shiii take fabaki tana rirrik'e hannunsa, amma muguntar khaleel saida yaga gashin ya warware sannan yamaida ribbon d'in ya d'aure mata a tsakkiya.
Sai tunzura baki Aysha take gaba, wai ita zafi.
Yatsansa yasaka ya d'alli bakin.
Da sauri tadafe da hannayenta sabida zafi, tuni idonta sun cika da kwalla kuwa, murmushi yayi, yaduk'o ahankali yasumbaci bakin bayan ya janye hannunta akai.
Harya cire bakin amma saiya maida.

Hummmm lallai masoyanann sunyi missing juna kam, Dan Ayshama a wannan karon tabada gudunmawa>?+?.
Saida sukaji ana knock d'in k'ofa sannan khaleel yazare bakinsa awahalce .
Jingina yad'anyi da madubin, yagama sauke numfashi Na Seconds sannan yanufi k'ofar fita.
Itadai Aysha kunyarsace takamata, kanta Na k'asa takasa kallonsama.
Yana fita tamik'e ta haye gado ta kwanta.
Hasnah ya iske a bakin k'ofar falon bayan ya bud'e, sannu tamasa cikin ladabi, ya jinjina mata Kansa.
Itakuma tamik'a masa basket k'arami dake d'aukeda kuloli, tace inji Ummu amarya, kar6a yay yakoma ciki, itakuma tajuya tatafi.
Bin Aysha yayi dake kwance akan gado da kallo, aransa yace yarinyarnan dukta zama ragguwa wlhy.
Saman sofa yazauna, yad'ora basket d'in abincin saman k'aramin table Na glass dake gaban kujerar.
Ahankali ya furta "A'eesha".
Tunda abinnan yafaru sai yanzu taji muryarsa, ko'a asibiti akazo dubasa bayama kowa magana, saidai d'aga kai ko girgizawa yayinda aka masa magana ko tambaya.
Aysha tad'an d'ago idanunta dasuka fara shanyewa saboda barci, ta amsa da " na'am".
Yace, "sakko kici abinci, saiki kwanta".
Kanta ta girgiza masa alamar ta k'oshi, tana yatsine fuskarta.
Baice komaiba yashiga bud'e abincin, jallof d'in macaroni ce dataji kayan vegetables da busashshen kifi, sai k'amshi takeyi kuwa.
d'ago ido yayi yasake kallon Aysha, yace.
" kingafa macaroni ce".
Kallon abincin Aysha tayi, haka kawai taji tana sha'awar taci.
Saita sakko tanufoshi.
Zama tayi kusadashi, ta jingina ajikinsa, dukta koyi son jikin tsiya.
Baice komaiba yad'auki fleet d'aya yazuba abincin, cokali d'aya yasaka yagyara zamnsa sosai, saida yafaraci sannan yad'iba yakai bakin Aysha.
Bakin tabud'e bayan tayi bismillah.
Haka sukaci abincin a tsanake, yanaci yana bata, har suka kusa cinyewa, amai Aysha tafaraji.
Tsayawa yayi dabata abincin, yay saurin zuba ruwan lemon cittan a cup yabata.
Kad'an tasha, ALLAH ya taimaka aman yatsaya batayiba, saikawai yadaina bata abincin, ya jinginata da kujera, tareda tartare kayan yafita dasu.
Mintuna kad'an yadawo, akwance ya isketa saman sofa, tashinta yayi yana fad'in, "kibari mana abincin yad'an narke, babie yasamu cikin salama shima".
Itadai batace masa komaiba, sai kallonsa datad'anyi, tamaida kanta gefen kafad'arsa ta kwantar tareda lumshe idanu.
Shima ajiyar zuciya ya sauke, yajingina kansa da kujera ya Lula suniyar tunani daya zame masa aboki ahalin yanzu.9&
Bayajin dad'in komai sama da tunani, shikad'ai yakeyi yaji d'an sanyi aransa.
Sun d'auki tsawon lokaci ahaka, hardai Aysha tafara isarsa da mutsu-mutsu saboda tagaji da zaman, gashi barci takeyi k'ak'as abinta.
Bud'e idanunsa yayi akanta, ganin barcinta taketasha ya girgiza kansa, d'aukarta yayi suka koma saman gadon, bayan yakai dubansa ga agogon dake d'akin, ganin da sauran lokacin sallah shima saiya kwanta, yagyarama Aysha kwanciya ajikinsa.
Hannunsa d'aya Na saman cikinta yana shafawa, tareda tunanin wai mutumne anan ciki?, yagadai randa cikin Aysha zaiyi girma=?
?.
Itakam bama tasan yanayiba, tuni barci yakuma yin gaba da'ita.
Shikam yakasa barcin kwata-kwata, abubuwane dayawa akan Momy suketa dawo masa, har yanzun zuciyarsa takasa fassara wasu abubuwan....
Shigewa jikinsa da Aysha takumayine yasakashi maida idonsa kanta, tausayinta yakamashi, k'aramar yarinya da ita amma tasha gwagwarmayar da wani namijinma bazai iyaba, yakai hannunsa d'aya saman kanta yana shafawa ahankali, wata k'aunarta da soyayyarta tana kuma ha6aka a zuciyarsa, murmushi yad'an su6uce masa daya tuna ranar daya fara ganinta, ahankali yakai bakinsa saman goshinta yasumbata, har yanzu fuskarsa d'aukeda sauran murmushin, shikad'ai yasan miyakeji a zuciyarsa, kuma k'ank'ameta yayi tamkar za'a kwace masa ita, har saida tad'an motsa sannan ya sassauta mata.
Haka yacinye lokacin barcin NASA da tunani iri-iri, wad'anda suka shafi al'amuran rayuwarsa daban-daban.
Kiran sallah ne yasakashi tashi, ahankali yazare Aysha daga jikinsa, danya lura tanajin dad'in barcin nata, filos yad'an sakamata sannan yashiga toilet ya d'auro alwala.
Bai tashi Ayshaba yafice masallaci bayan ya kulleta tabaya, dukda akwai securitys zagaye dagidan, hakan baisashi jin yarda da kowaba, inhar matum irin Momy zata iya aikata abinda ta aikata, tokuwa baikamata zuciyarsa aminta daduk wani makusancinsaba ahalin yanzu, har yanzu baigama farkawa daga magagin barcinsaba, Dan maganar gaskiya har yaud'inna tunaninsa a birkice yake, yakasa samun nutsuwar warware komai dake dank'are a zuciyarsa ballantana ya fahimci komai dalla-dallah, saidai yana kamanta rashin fahimtar tasa da neman son dalilin momy Na aikata wad'annan abubuwan masukama da labarai kokuma tatsuniyoyi.

Har yadawo daga massallaci Aysha nata barcinta, zama yayi gefen gadon saitin face d'inta, yakai hannusa saman sumar kanta yana kwantar daduk wadda tad'an tashi, d'ayan hannun kuma yanajan hancinta dashi.
Bud'e idanunta tayi akansa, tad'an lumshe sannan takuma bud'ewa.
"Sorry, nakatse miki barci ko? Daure kitashi kiyi sallah time Na tafiya kingani".
Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka, "please sadauki, ALLAH barcin bai ishenibafa".
Yad'an zaro manyan idanunsa tareda d'ora hannunsa saman bakinsa, "kai, bakiji minaceba kenan? anfayi sallar zuhur, duba 1:35pm".
Batace komaiba kuma, ta yunk'ura dak'yar tatashi zaune, shine ya taimaka mata ta sakko k'asa, zai rakata toilet tace zata iya.
K'yaleta yayi, yajingina da fuskar gadon yana kallonta yanda takebin bango ahankali, aransa yace ALLAH yarabaki lfy matana, yakaimu randa zanga kin haifamin baby girl ko boy d'ina, nasan dai zansha raki a d'akin haihuwa=?
?.


_____________________________

Bak'aramar azabar wahala hajia babba tashaba akan cizon da kud'in cizo yayata mata adaren jiyaba, haka tatashi jiki dukyayi burd'ai-burd'ai, Dan kokad'an fatarta batason kwari dama, koyaya wani Abu yata6ata saikaga ya lalata mata fata.
Duktayi wani iri da'ita, ga azabar sanyi da ciwon kai dake damunta.
Kwana d'aya kacal amma dukta fita hayyacinta, sai soshe-soshen jiki takeyi, jitayi wata wutar k'iyayyar mama nak'ara zafafa zuciyarta, wlhy da ace zata samu damar fita awajennan saita tarwatsa kan mama da d'iyarta Aysha da bullet, hakama khaleel, tatsani shegen yaronnan, sannan tayi bak'inciki da takaicin rainon abinda yazama mata masifa arayuwa, inda har tasan haka Ibrahim zai zamema rayuwarta masifa datun yana jinjiri tagama murd'e kansa anwuce wajen, ta zabga kwafa tana zirar da hawayen bak'incikin barin Ibrahim aduniya.



Nikam nace, "to Momy, zakaranfa da ALLAH yanufa da cara, ko'ana mazuru ana shaho saiya kai, khaleel yazama kainuwa dashen ALLAH, shifa mai arzik'i ko a kwara ya saida ruwa, sannan mairabon ganin bad'i........=??=?L?
>?*?garama ki rungumi k'addara, danta k'are miki keda muk'arrabank.
Saima Anfara muku sassafar gero a turmi>?#?, sannan ne zakiji tsanar tasa mai dalili=??=?9?=?9?>?7? @&.


____________________________

Wuni guda haka yau suka kasance manne da juna, dukda babu wata fira dake shiga tsakaninsu, Dan gaba d'aya ya khaleel yamaida hankalinsa kacokan a duniyar tunani, saima Aysha tad'an gaji da shirunne take zungurarsa.
Yakan juyo ya kalleta, wani lokacin yakan mata alamar tambayar miyafaru?, kokuma yamata murmushi.
Bayanda Aysha ta iya dashi, haka tahak'ura suka taru sukai jugum-jugum, saidaifa Aysha nacikin tsananin farincikin kawo k'arshen Momy, tana kannewane kawai saboda kunyar khaleel, dantasan koyayane akwai shak'uwa tsakaninsa da Momy mai k'arfi, baidace takuma assasa damuwa aransaba, danta kula kokad'an bayason jin dukwani Abu daya shafi Momy, wannan yasaka Aysha kame kanta, tacigaba da ririta jikintama.
Bayan yayo sallar isha'i suna zaune afalo, kan Aysha saman cinyarsa tana kwance a doguwar kujera, hannunsa Na cikin gashinta yana wasa dashi, idonsa kam akan TV yana kallon labaran ait.
Kallonsa Aysha tayi, murya ashak'e tace, "ya Sadauki!".
" uhhm".
Yafad'a yana maido idonsa kanta.
Shiru tayi itama tana kallonsa.
Yace, ''ina jinki, akwai matsalane?".
Kanta ta girgiza masa tana shagwa6e fuska.
Ya tattaro dukkan hankalimsa akanta, fuskardai babu walwala, wannan yasaka Aysha jin Shankar masa tambayar dake ranta, dantasan halin kayanta sarai.
Ganin tayi shiru saiya d'alli la66anta da d'anyatsa, baki taturo masa, ashagwa6e kuma ido cikeda kwallah tace, "kai ya khaleel, ALLAH mugunta babu k'yaudai".
"uyimmm hakanefa, bara Na daina miki karfa nima ama d'iyata wataran".
Kunya takama Aysha data tuna lokacin data fad'a masa maganar, hannu tasaka ta rufe fuskarta.
Bakinsa yad'an ta6e yana guntun murmushi.
Har yanzu idonta arufe yake, tace, " inban takurakaba, kafad'amin miyasa kayita bibiyata har k'asar Islands?".

'Dan murmusawa yayi, Dan dama tun d'azun yalura da abinda takeson tambayarsa kenan, danyaga kallon tuhuma datake jifansa dashi tun suna asibiti, ya lumshe idanunsa yanamai tariyo komai tamkar yanzun yake faruwa.
Itakuma ta tsuramasa idanu tana sauraren amsarsa.
Kusan mintuna 5 sannan yabud'e idon akanta, cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login