Showing 21001 words to 24000 words out of 155647 words

Chapter 8 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

451

ya khaleel yayi, amma baice komaiba.
"Oga Asokoro zamuje kokuwa mai tama?".
"Adams muje mai tama tukun, zanyi magana da baffah, kuma zand'an k'imtsa ko, saiku barni a can kukoma d'aukar su Sameer d'in, zuwa dare zan k'arasa can gidan".
"OK sir, hakan yayi aii".

'Dan gwari yabud'e musu gate suka shiga, nanma gidan akwai jama'a sosai, y'an uwan mahaifin hajia babba sunzo sosai, hakama 6angaren mahaifiyarta Wanda sukazama dangin gidan, tunda da Ammah da mamanta uwarsu d'aya uba d'aya, danhaka sai dangin sukazama d'aya, wasukuma suna kano sai an d'aura aure gobe su k'araso abujar.
Najwa d'iyar Anty zuwaira tazo da gudu kamar zata rungumeshi, amma saitaja birki, Dan wargima waje yaka samu, "uncle oyoyo".
Murmushi yamata tareda fad'in "dota ank'araso kenan?".
"Lah uncle yau kwananmu 6 fa a Abuja".
"Eye kunsha Abuja abinku, muje ciki to".
Kar6ar jakarsa tayi suka k'arasa ciki, tun afalo suka fara gaisawa da jama'a, wasu nad'an tsokanarsa da ango kasha k'amshi, amsarsa d'ayace murmishi.
Saida yashiga 6angaren Momy suka gaggaisa da jama'a sosai, itama momyn sun gaisa a tsaitsaye saboda bak'i, yafito zuwa 6angarensu.
Duk samarin gidan sunan hardama k'arin bak'i, sunbaje afalo kowa na harkar gabansa, wasu kallo wasu gugar kayansu na kwalliyar biki, masu danna waya nayi, masu hira nayi.
Duk suka Shiga masa sannu da zuwa da gaisheshi.
Ya amsa fusakarsa d'aukeda murmushi.
Saida yashige sannan "Hafiz yace a lallai Yaya nason aurenan, irin wannan fara'a haka".
Ramadan yace, "dagedai yajika, dawani kankan like kwakwa".
Dariya sukayi gaba d'aya.
So rayuwar families d'in tana burgeni gaskiya, komai nasu cikin mutunta juna.
Bayan kamar awanni biyu yafito, ya tambayi su Musleem Anty Mamie fa? Yaga baigantaba da sauran yaran?.
"Ya khaleel ai wad'annan sun tsufa a kano, tuda asuba suka tafi, dagamu sai baffa da umme amaryar saikuma Momy dasu Anty zuwairah aka bari"..
Jinjina kansa yayi sannan yafita, yana nazarin hidimar bikin nasa.
Yaje sun gaisa da baffa, Wanda shima yana tareda bak'i abokansa dasukazo daga Turkey, dakuma dad d'insu ya Naufal.
Baffa yajashi gefe suka tattauna sosai, akan d'aurin auren na gobe, dakuma walima da aka shirya bayan d'aurin aure, wadda aka gayyaci manyan malamai dazasuyi lectures awajen, sannan baffah yabashi akwati guda na d'unkunan biki dayamasa.
Godiya sosai yayma mahaifin nasa sannan ya sallamesu yatafi inda bokansa suke.
bayan Momy takar6i kud'ad'e masu yawa a hannunsa.
Acewarta sisinta bazaiyi kuka a bikinba, shida ya yarda sai dai ayi da gumimsa.
Bai nemi ba'asiba yamata transfer yatafi.
Yana shigowa abokansa suka saka ihun ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu sosai, wasu andad'e ba'a had'uba, tun'a schools, harda wad'anda sukayi Secondary dakuma University, abokan aiki dakuma na kasuwa, y'an uwa da abokan arzik'i, nanfa akashiga hirar yaushe gamo da firar abokan ango dakowa yasani.
Abdul'azeez yace, "wlhy mamaki nakeyi wai J! Da mata?".
"Aii bakai kad'aiba cewar Nawaff, kasanfa wasanmu na k'arshe a k'asar Argentina damuka had'u nake masa maganar aure, cemin yayi babu rana".
Mahmud yace, "aii mutumin namu akwai taku, amma dai bahaka zakajema yarinyar mutane kana mazuraiba?".
Hararsa j yayi, "kai banason iskancinkufa, kai ince mazuran karingama Noor da billy, kaikuma Nawaff saboda jarabarka dafad'a kuka fara da Yasmeen ahad'uwar farko, su mai mata uku Abdul'azeez (Dady) kam aiba'a magana".
Harara Dady ya wullah masa, "kai Malam yanzu matata d'aya my Munnerah kaji".
Dariya suka shek'e da ita, Sultan yace, "wlhy auren mata biyu da dad'i, Juwairiyya takula dani, itada ikram d'ina haka, uncle G dake gefe yace kai malam my sopy ma ba bayaba, auredai dacene kawai". Mus'aff yace, "wannan gaskiyane, idan INA gaban My Nazeefa tamkar kwai a cokali nake". "Muzzaffar ya kar6e dafad'in wlhy haka Ameedah na take, tauraruwata kenan".
Isma'il yace, "kukefad'a anaji, aii soyayya sai Iman d'ita wlhy". hummm kowa nasa yasani, kuje gidana kuga yanda Rahma ke riritani Cewar Abdulmaleek bobo. Umar Fharuk yashek'e da dariya, "amma sanda aka aura maka ita kanata wani dojewa kai na Ni'ima, hakanayi a lokacin aurena da Asma'u, amma yanzu kam babu kamarta". "kana nufin har Uwargida Lubna?".
"Daga baya kenan malam".
Shureim ya shek'e da dariya, "aiini nida my badar sai mutuwa".
Khaleel da sauran abokan daketa binsu da kallo suka shek'e da dariya, "to iyayen soyayya, sannunku da k'ok'ari".
"Yauwa Wanda bai iya soyayyaba, kaima aii zaka shiga layinmune, daga gobenefa".
Sameer yace, "ALLAH kasadamu da matan kwarai, bilyn Abdull nimafa yakamata labarina yashigo layi gaskiya".=??=?M?

Babu damu Sameer, kaine next insha ALLAH=??=? ?>??

Haka sukaita shafta d'insu, ranardai k'alilanne acikinsu sukayi barci, washe gari tunda 7:30 suka d'auki hanyar kano a motoci.

Sun Isa lafiya, yayinda suka sauka a hotel, annan suka cigaba da shagalinsu har zuwa 12, daganan akafara shirin tafiya d'aurin aure.


Gidansu Aysha.

Cike gidan yake, da k'yar nake kutsawa cikin mutane, har Na isa inda su Aysha suke, a d'akin abbansu marigayi, y'anmatan da amare sunata kwalliya dacin gayu, amma banda Aysha, kwance take kangado tanata kallonsu, dukda d'unbin son datakema ya khaleel sai jikinta yay sanyi k'alau yau, tun d'azun takeson tayi kuka takasa, sunata rk'onta tatashi tayi wanka amma tak'i k'oda motsawa daga inda take kwance, hak'ura sukayi suka barta.


*_RANA BATA K'ARYA...._*
K'ofar gidansu Aysha dank'am yake da al'ummar annabi, kasancewar d'aurin aure biyar za'ayi, y'ay'an kawu bilyamin biyu. Sai Rufaida da Sadiya, sai Aysha.
Dole kasancewata mace natsaya daga gefe har liman yafara sanar da d'aurin auren Rufaida, kasancewar itace babba, sai Aysha, etc...., gaba d'ayansu sadakinsu dubu 30 30 ne kacal.
Ana gama d'aurin aure police Interpol da ainahin police, da sauran masu d'ammara daban-daban dasuka halarci d'aurin Auren, suka d'ana kunamun bindugunsu atare, kamar yanda suka shirya aka saki harbi lokaci d'aya, gabad'aya wajen ya hargitse, saboda abin yazoma jama'a babu zato, >?#?>?#?zokaga gudu wajan jama'a @& @& @& B& B& B& B& B& B& B& B&, Dan harbinne na bindingu kusan 50+, kuttt idan bakayi bani guru, k'afa minaci banbakiba.
Kanawafa sunzata bomb ne zai tarwatse dasu>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?=??=??.
Aradu harsu baffah sun tsorata=??.
Saida kowa yafuskanci wasan manyane domin girmama Ango sannan aka koma cin dariya datuna gudun da'akasha>?#?>?#?>?#?.
Canna hango muku xoxo da buje a hannu, mom of 12 kam filet d'in shinkafa tasaki ak'asa, su Aysha Umar anacan mamuke da Manshat data kusan sakin Zunnurain a k'asa.
Hadiza muktar harda fitsari a kayan ankonta, tab danbakuga halinda Maman Khaleed da Zarah maigari sukashigaba da kdeey=??, jamila zozo da mamybmj ana can bayan durom, kuttt kunga nasiba a bokitin ruwan datti kuwa,>?#?, Uwargida can Na hangota tasaka kai a drom d'in ruwa, y'an group d'in cikin da gaskiya kam ba'a magana, duk zumud'in tafiya bikin ya khaleel da ankon dasukeyi baihanasu kwasa agujeba, wasu takalma ahannu wasu d'ankwali, harda masu zani a hannu>?#?, kuttmelesi kunga y'an taskar littafan Hausa kuwa, tashin hankali=? ?>?#?>?#?>?#?, wasu harsunkai k'arshen layi, anasu dawo ga kaji suna fad'in sun yafe wlhy>?#?>?#?>?#?, radu sunga mutuwa yau babu kwad'ayi.
Falfala kenan wai Malam bud'e mana littafi, yaukam naga gudun gayu aradu, abin ba'a cewa komai, Na hauwa'un Janu yafi nakowa, idan nafad'a saikun toshe kunnuwa>?#?, su d'an mom kuwa tuni aka baza babbar riga aka ranta cikin Na kare,.
Hakama abokan Ango su Nawaff dabasusan da shirinba kowa yanemi ma6oya>?#?>?#?>?#?.
Abin yabirge ya khaleel, Dan baisan da wannan shirinba, aikam saigashi yana tuntsura uwar dariya=??, ya khaleel an iya dariyar mugunta=??.
Damma baiga mata acikin gida baneba, dayayi wadda tafi wannan=??.
Fans d'in ciki da gaskiya wlhy kun iya gudu zazuuuuuu>?#?>?#?>?#?>?#?=?M?
Lokacin da zance yashigo cikin gida and'aura aure sai Aysha ta rushe da kuka, Dan sai yanzu tasamu damar yin kukan datakesonyi tun d'azun.
Nanfa dangi suka rufu akanta dasonjin ba'asi, kasa cewa komai tayi tacigaba da kukanta, (dolene duk macen da akace and'aura aurenta saitaji wani iri tareda ita=?%?, bawai Aysha kawaiba).
Ganin tak'i yin shiru ifteehal takira Anty meerah.
Babu dad'ewa tashigo d'akin, ita ta lallashi ayshar har tasakata tayi wanka, dak'yar tayarda aka mata simple makeup, tasaka doguwar rigar farar shadda kamar yanda sauran y'an uwanta suka saka.
Bayan d'aurin aure aka zauna yin saukar alkur'ani, domin nemawa amare tabarraki, bayan ankammala saukane su Anty Mamie suka shirya tafiya, Dan tarbar amaryarsu gobe idan ALLAH ya kaimu.

Sai lokacin nagano muku ya khaleel dayaci kwalliya cikin farar shadda d'inkin babbar riga, Wanda yasha adon golden d'in surfani, hular kansa golden, hakama agogo da takalmansa sau ciki, fuskarnan washar da annurin angwaci, said baza kamshi yakeyi, Dan kusan kwalbar turare Taheer ya zazzage masa ajiki Dan shak'iyanci.=?? kwarjininsa da sihirtaccen k'yawu sunk'ara fitowa, babudai dariya, amma anama jama'a murmushi=?
?.
Yanata gaisawa da abokansa, dakuma manyansa a wajen aiki dasuka halarci d'aurin auren.
Saida komai yanatsa sannan suka tafi wajen waleemar da aka shirya, manyan malami sunyi lectures mai ratsa jiki, anci ansha kam alhmdllh.
Bayan antashi baffah da gayayyarsa suka tafi, su ya khaleel kam sai washe gari zasu tafi da amarya Aysha.
Dan haka da daddare suka shirya d'an biki a hotel d'in dasuke iyasu kad'ai abinsu, wajen ya k'ayatar sosai, sunyi nishad'i Alhamdllh.

Adaren akakai su Rufaida, Aysha duk saida taje gidan kowa batareda ansan tabi y'ankai amarya ba=??.
Bayan dawowarsu kam mama takirata, itama dangi suka sakata tsakkiya anata mata nasiha, tasha kuka kam, ranar tareda mama takwana.

Washe gari...........
'




*_kowa ya shirya, yau sai abuja=??_*

=ؗ?=ؕ?=ؙ?=،?=؎?=ؘ?=ؓ?=ؔ?=ؖ?






=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?
[9/8, 1:56 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


1? 0?

Jama'a sunata shirye-shiryen tafiya Abuja, domin rakkiya ga Aysha.
Itakam tanacan k'uryar d'aki sai zuba kuka takeyi, gabad'a tausayin kanta takeyi, tasan tana son ya khaleel, amma shi takula baidamu da itaba ko kad'an, jibafa tunda aka d'aura aurennan bataga idanunsaba, ahaka za'ayi rayuwar aure kenan?.
Hayaniyar jama tafara jiyowa suna fad'in mitocin d'aukar amarya sunzo, gabantane yacigaba da fad'uwa, kukanta yak'aru, har rawa jikinta keyi saboda tashin hankali.
Ahaka gwaggo Asma'u tashigo ta sameta, "haba Aysha, kekuwa bazaki daina kukannan bane hakanan? Kowafa dahaka yafara, yanzu y'an uwanki basun kwana gidan nasu mazajen ba, kinsandai tafiya babu fashi aii, kikamaje wata k'asar kikayi hak'uri zama babu mu bare nan gaki ga Yaya fad'ima, kinga tashi ki saka wannan hijjab d'in da nik'af kinji, yihak'uri bar kukan hakanan?".
Haka taita lallashin Aysha harta kuma sakata ta k'imtsa, ankai Aysha tayi sallama da dangin mahaifinta tsofaffi maza da mata, aka kaita wajen Umma wadda takasa magana sai kuka itama, dak'yar aka 6an6are Aysha daga jikin Ummah, mama ankaita tayi sallama da ita, (ita sai zuwa jibi zata koma abujan).
Haka akafita da Aysha tana 6arzar kuka, sanye take cikin atanfa ruwan zuma mai duhu da ratsin ruwan shanshanbale mai haske, hijjab d'intama ruwan Zuma, sai bak'in nik'af, tana kallon kowa tacikin nik'af d'inta, dukda har yanzun tanata kwarar da hawaye kuwa.
Gabanta yafad'i lokacinda idonta ya sauna akan ya khaleel dake jingine da wata farar mota, rabonda taganshi harta mantama ita, sanye yake cikin shadda galila ruwan sararin samaniya, (sky blue) ya murza hula kalarta, hakama takalmansa, agogonsane kawai bak'i, yayi masifar yin k'yau, mayun idonsa k'yam akan Aysha da fuskarta ke lillu6e da Nik'af, dukda baya ganin fuskartata hakan baihanashi cigaba da kallontaba, baka Isa gane wane yanayi yake cikiba.
Gwaggo Asma'u tace, "wainikam ko wancanne angon? Naga yakafe d'iyar tawa da idanu?".
Dariya meerah tayi, tace, "gwaggo shine kuwa wlhy".
Kai masha ALLAH, "ALLAH yabada zaman lfy dai".
"Ameen ya rabbi gwaggo".
Duk Aysha najinsu.
Zungurinsa Sameer yayi, da sauri yamaido kallonsa ga Sameer d'in, yad'an sauke siririyar ajiyar zuciya.
Sameer yace, " haba alhaji, gidankafa zataje, irin wannan kallo haka?".
Baki ya khaleel yad'an ta6e, "kai nifa karkamin Sheri, ba kallonta nakeba, kawai tunanin yatafi wani wajene daban".
"Hhhh j!, J! Ikon ALLAH, Na Aysha bada kanka asare kajegida kace yafad'i, d'ad'ina dakai komai naka akwai tsari, kana tunanin shan angwancine kenan?".
"Hhmm wlhy Sameer kaima ka canja, yakamata Papa yamaka aure gaskiya".
Dariya Sameer yasaka, hakan yayi dai-dai da isowar Joseph wajen, j! Zaka shiga motar amaryane? Kozaka tafi daban?.
"Haba saikace wani kai, mubaha akeyiba, bakagama da y'an uwanta suka shigaba?".
"Aii nazata zaka zauna agabane?".
"A'a".
Tom saiku tafi kaida su Sameer ko?.
"Nifa karka had'ani da wad'annan, kasan zasu takuramin da surunsune wlhy".
Dariya sukayi, Sameer yace, ''aikam zamu barka a kano wlhy".



___________
Kowa yagama shiga, motocin sun wadata alhamdllh, y'an anguwa anata d'agama amarya Aysha hannu, wadda tacusa kanta akan cinyoyinta tana kuka.
To Aysha ALLAH yabada sa'ar zaman aure.

Kunsan miya faru?.
Harmun fara tafiya saiga gayyar motocin y'an CIKI DA GASKIYA...FANS, group 1,2,3,4, wai daga baya zasu tsaya kada abokan ya khaleel suk'ara irin najiya>?#?>?#?.
Ammafa antara matsota=??.



*_Abuja_*
Sun Isa Abuja 2:pm dai-dai, saboda babu laifi sund'anyi gudu, kasancewar harabar gidan akwai mutane motocin suka tsaya ak'ofar gida, ta amaryace kawai tashiga cikin gida.
Anty Mamie dakanta tazo tafiddo Aysha, Wanda ganin Anty Mamie yasakata kuma rushewa da kuka, lalashinta tashigayi.
Anma bak'i tarbar mutunci, amma hajia babba da Anty zuwairah ko lek'owa basuyiba, Anty shikurah komai itakam tana aciki, ankai amarya Aysha d'akin Anty Mamie, kafin da daddare amaidata 6angarenta.
Daga ita sai ifteehal a d'akin, saikuma wasu y'an uwansu su uku, zee da Saleema da Mimi. Hirarsu sukeyi cikin nutsuwa, amma Aysha batacewa uffan, tana kwance kangado tana saurarensu dabinsu da ido.
Amal takawo musu abinci.
Sukad'ai sukaci, amma Aysha ko saukama tak'iyi daga gadon Anty Mamie.

Gayyar ciki da gaskiya fans kuwa aii dole aka bud'e musu d'aki guda agidan, dukda hakama yamusu kad'an, sundaiyi manege ne kawai, Dan kowa yasan hidimar biki yanda take, Baka Neman komai kasamu yanda kakeso.

Haka akaciga da y'an hidimomi har zuwa 8 Na dare.
Kowa yafara shirin dinner da abokan ango suka shirya, wadda shima baisan da itaba saida suka dawo daga Kano, babu yanda zaiyi tunda sunriga sungama komai, amma baiso hakanba gsky.


_________________
Amarya Aysha ansha kwalliya, Hamdiyya tamata danta iya sosai, tasaka popul d'in doguwar riga, aka nad'a mata farin ashoke, tayi k'yau harta gaji, kowa fad'i yakeyi masha ALLAH, itakam gabanta sai fad'uwa yakeyi, tana tunani had'uwarta da ya khaleel, tunda tasan dolene amota d'aya zasu tafi.
Isowar Anty shikurah ce ta katse tunaninta, ''Aysha tashi muje Yaya Na jiranki".
Cikin marairaicewar murya Aysha tace, "wlhy Anty Ama kamarma afasa".
Dariya Anty Ama tayi, " kiyi hak'uri kinji Aysha, shima ya khaleel d'in bada son ransa baneba, abokansa Na wajen aikine suka shirya batareda saninsaba, kinga kuma babu damar yace bazakujeba yasakasu asara". Kinga tashi muje karsuyita jira.
Dole Aysha tamik'e, Anty Ama tarik'e hann???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?unta, saima yanzu talura duk mutane sungama tafiya, gidan yayi shiru, Dan harsu hajia babba duk anacan=??.

Anty Ama tabud'ema Aysha motar dake gabansu, zuciyar Aysha sai harbawa takeyi, ahaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login