Showing 54001 words to 57000 words out of 155647 words

Chapter 19 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

462

abinda ke faruwa agidan.


Ho sholyn sadaukinta, kina aljannah ina binki da addu'ar fatan alkairi nida fans>?#?=?M?



Har wajen 12 su baffah duk suna asibiti, amma jikin momy da sauk'i, barcima takeyi an saka mata k'arin ruwa.
Baffah yace, "duk suje gida su karya, idan sukaje saisu Shukurah su taho shima yaje gida ya shirya".
Suduka suka amsa da to.
Ya khaleel yace, " baffah kabisu kuje, idan su Anty shukurah sukazo nisana tafi".
"A'a mu'azzam kuje kawai, karka damu".
Badan yasoba ya amsa dato.


Aysha na kwance afalo saman doguwar kujera, hankalinta a kwance take buga game a waya, k'arar bud'e k'ofane yasakata saurin kashewa ta gyara fuskarta takoma kalar damuwa, sannu dazuwa tamasa, murya a sanyaye tace, ''yajikin momyn? Nida harzamu taho aii".
Huci ya furzar yana sauke numfashi, "da sauk'i tana barcine".
" amma to wakuka baro a wajenta?".
"Baffah nacan, zanyi wankane saina koma, gasu Anty shukurah can zasuje su kar6esa shima yazo ya karya".
" ALLAH yabata lafiya to".
"Ameen, had'amin ruwan wanka".

Dad'an d'umi tahad'a masa ruwan, tana niyyar fitowa yashigo toilet d'in, harda saka key a k'ofar.
Aysha ta marairaice fuska tana rok'onsa akan yabud'e mata.
Kauda kansa yayi, fuskarnan babu walwala yace, "wanka zakimin".
"eyeee! Tafad'a da zaro ido waje=?(?".
Baice da ita komaiba, yad'auki shawa=ؿ? yakunna, kafin Aysha tayi yunk'urin guduwa yafara zuba mata ruwan ajiki.
Tsalle-tsalle tafarayi dan gujema ruwan, wayyo ya khaleel, please kabari, ALLAH nayi wankafa.
Uffan baice da itaba, saida yaga tayi sharkaf da ruwan yanda dole tasake wanka sannan yak'yaleta.
Babu yanda ta iya, haka tabiye masa suka sake wanka, awajen shafa maima haka ta shafa masa dole, Dan yayi kicin-kicin da fuska babu damar turjewa.

Tsaf suka fito falo, tahad'a masa abinci, baiwanima ci sosaiba yamik'e, hankalinsa ta lura yana asibitin gaba d'aya.


Duk 'yan gidan suka shirya suka tafi asibiti, harsu Aysha, masu aiki kawai aka bari..............
'





*_Nagafa kamar kuna neman rikicewa, kutuna ba hajia babba takira barau modibbo ba aranar, hajia babba takira hajia khaltum ne tasanar mata taji ya khaleel zaije kama barau modibbo, itakuma hajia khaltum takira barau modibbo bata bai d'agaba, shine ta tura masa message. Wanda bai ganeba yakoma page 40 k'arshen part 1 yaduba kuma._*
Ngd sosai da k'aunar dakuke nunama buk d'inan, Nina wlhy ina k'aunarku irin Trillions d'innan, ga diamond k'yauta=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=??=?M?








=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?
[9/22, 3:10 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


2? 1?

Wajajen 1 Momy tafarka, duk suka shiga suka dubata, kanta kawai take iya d'aga musu amma babu magana, ya khaleel dakansa yabata abinci abaki, Aysha Na mamakin irinson da ya khaleel kema mahaifiyarsa.
Baffah yace, duk sutashi su koma gida, itamad'in an sallamesu.
Kaya suka shiga harhad'awa, sai gida.


Tunda suka dawo ya khaleel Na 6angaren Momy, yana zaune kusada ita yanzuma a bedroom d'inta, itakuma tana kwance, tarik'o hannunsa tana magana ahankali, "Ibraheem inaso aiima mufeedah aure, kazaunar da ita tafad'ama Wanda takeso kaimasa magana yafito, saika sanarma baffanku".
" amma Momy miya faru haka? Lokaci d'aya ace ta fidda miji?".
"Ninasan minagani Ibraheem, mufeedah Neman zubar mana da mutunci takeyi agidannan, gaban kishiyoyi da 'yan uba, mufeedah sotake amin dariya da eho agidannan", nan Momy takwashe duk abinda yafaru jiya tasanar masa.
Sosai ransa ya6aci, amma Momy tace yay shiru Dan ALLAH, fitowar maganar tamkar tonon asirinsune, kawai yasaka mufeedah ta fidda mijin aure, su aurar da ita kawai ahuta.
" shikenan Momy zan mata magana, Dan ALLAH kema kicire komai aranki, kingafa jiya ALLAH ne ya kiyaye fad'uwar dakikayi, bawuya saikiga ansamu matsalar ciwon 6arin jiki, kisama zuciyarki hak'uri".
''To ibaraheem ngd".
Ya jinjina mata kai, cikin hikimar iya zance yayta bata labari mai dad'i da kwantar da hankali, itama saitaita sakin jikinta, saida yaga tasamu 'Yar nutsuwa sannan yabarta.



_______________________________

Kusan kwanaki biyu Momy Na jiyya, Alhmdllh sauk'i yasamu.
Kulawa dai sosai tana samu wajen 'ya'yanta, musamman Anty shukurah da ya khaleel.
Anty zuwairah dai babu damar zuwa, saidai waya takira Tamata sannu.

Ayau kuma Aleeya zata iso daga England.
Sosai Momy tasaka akema zuwan NATA shiri Na musamman, d'aki guda tasa aka gyarama Aleeya a 6angarenta, komai Na buk'ata aka tanada mata aciki, kaikace wata sarauniyar bak'uwa zasuyi, (lallai Momy nason Aleeya kam).


************

"Nikam dakinbar shayinnan natafi kawai, inada aiki sosai a office wlhy".
" please yafa huce, wlhy nasan katafi zaka mance da yunwar cikinka ne kawai, gashima ya huce aii".
Kar6an mug d'in yayi yana girgiza kai kawai, yay bismillah yafara sha, "rigimarki yawane da ita Sholy".
" nidai kadaina cemin wata sholy, wai a inama kasan sunan?".
"Bakinsa yata6e, yana shan tea d'in da dankali ad'an hanzarce, saboda saurin dayakeyi yafita, yajuyo yana kallonta, kinsan a ina asan sunan?".
Girgiza masa kai tayi, batareda tayi maganaba.
Ya maida kansa kan abincin, ''wajen meerah naji, nikuma sunan yamin dad'i, Dan haka dole abarni nake kira".
"uhm, Aysha tafad'a tana tunzuro baki".
Mik'ewa yayi yana gyara belt d'in wandonsa, danharya shirya cikin uniform d'insa masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, "idan Baki maida wannan bakinba yanzu zanyi maganinsa".
Da Sauri Aysha ta gyara bakinta, danta San sauran sarai.
Yad'auki jakkar laptop d'insa da wayoyi da hula zai fita, ya kalli Aysha "bazaki rakaniba?".
Da sauri tamik'e dantaji kunya, takar6i jakar suka fito, babu mai magana harsuka fito tsakar gidan, tom bani kayana ki koma ciki, su Adams najirana awaje.
Mik'a masa tayi, tanamasa addu'a. Saida ya kar6a sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshinta da la66anta.
Kunya yabata, tasaka hannunta tarufe fuskarta, kai Yaya, ko kunya bakaji?".
" Yaya ko?".
Da Sauri tamatsa bays o sorry sadauki, tayi maganar a shagwa6e".
Lallausan murmushi yasaki, sannan yajuya yatafi.
Saida yaje k'ofar gate dannan yajuyo ya kashe mata ido d'aya tareda d'aga mata hannu yafice gaba d'aya.
Dariya abin yabama Aysha, ta juya cikin gida tana mamakin ya khaleel da halayensa, yanzu takuma tabbatarwa ya khaleel murd'ad'd'en mutumne, Dan har yanzu yana nan yanda tasanshi, kwanakinta Tara kenan taredashi, amma kaf halayrnsa suna nan Tatare dashi, babu wani canji, wani lokacin kigansa mutum mai sauk'i, wani lokacin kuma amurd'e, dariya abuce mai tsada awajensa, hakama bashida yawan surutu, Alhmdllh tana samun kulawa bakin gwargwado daga wajensa, dukda har yanzu bai furta yana sontaba, bata damuba, aganinta watarana shima zai fad'ane, Abu mafi burgeta agareshi shine tsafta, ya khaleel akwai tsafta da gwalli tamkar mace, yamafi wata macen. Komai nasa k'al-k'al yake sonshi, shiyyasa tadage da bada himma wajen gyara kanta da muhallinsu, bata yarda tabar wata 6araka dazaiga gazawartaba, iya k'ok'arinta tanayi Dan ganin tak'ara daraja da kima a idonsa, halayensa kuma basu dametaba, insha ALLAH zata iya zama dashi a aduk yanda yake, kuma su zauna lfy.
Agurguje itama ta shirya driver yad'auketa zuwa Inda take aiiki.


Yana fita Adams yak'araso da hanzari yakar6i kayan hannunsa, atare sukayi salute nashi, ya maida musu da murtani cikin sanin darajar d'an Adam.
Adams yabud'e masa Mora yashiga, Ema... sarkin mota yafara aikinsa Na tuk'i, yayinda sauran mota biyu ta securitys nashi kebinsu abaya.
Shiru ya kwanta jikin kujera, tunaninsa gaba d'aya yatafi akan aysha da shirmrnta, yana mamakin yanda take komanta cikeda k'uruciya, saidai kasancewarta mai tsafta da yanda take girmamashi yakan sakashi cikin farinciki da annashuwa, yarinyar tanada mafi yawan halayen dayake buk'atar matarsa dasu, Abu da kedamun zuciyarsa shine aurennan da Momy tatasoshi gaba akansa, yanzu haka yauma saida tace yaje ya d'akko Aleeya idan ta sauka a airport, da to kawai ya amsa mata, amma bayajin akwai yarinyar data Isa ya6ata lokacinsa wajen wani tarbarta, yaja siririn tsaki Wanda har saida Adams yajuyo ya kalleshi, yana mamakin miya saka boss tsaki haka?.
Babu dad'ewa suka iso setetion d'in nasu, nanfa aka Shiga gaisheshi damasa murnar aure, shikuma yana musu godiya da halartar dasukayi.
Duk saida yashiga office's d'in oganninsa yakai gaisuwa, sannan yadawo nashi, shima wad'anda suke k'asa dashi suka shiga zaryar zuwa gaidashi, dakawo masa aiyukan dasukayi bayan baya nan.
Aiki kam ya iskeshi jingim, damma su youseef nayin wad'ansu.
Su Joseph ma sunshigo sunyi gaisuwa amatsayinsa Na ogansu.
Kowanne yakawo masa aikin dayayi dawanda suke kai, sosai yau aiki ya rinca6e masa, gaba d'aya yagaza samun kansa.
Wajen 12:30mp yaji shigowar sak'o a familie phone nasa, baibi takan massage d'inba, saboda aikin dake gabansa.
Zuwacan kuma sai kira yashigo, nanma bai d'agaba, saida aka kira kusan 3times bai d'aukaba, daganan aka daina kira.
Nock d'in k'ofar office d'in akayi. Yabada izinin shigowa, Basheer ne wani ma'aikacinsu, ya k'ame tareda salute Na khaleel.
Kansa ya jinjina masa sannan yanuna masa kujera alamun ya zauna.
Basheer ya zauna a kujerar dake kallon ya khaleel, sannan yamik'a masa wasu files dake hannunsa.
"Sir ga bayanan damuka samu akansu, wannan kuma sunayen mutane 17 ne damuka kama acikinsu, akwai 13 anan setetion d'in, saikuma 3 a hannun police, 1 yana hannun hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi".
"OK, yakar6i files d'in yana dubawa, saida yagama tsaf yad'ago yana kallon basheer, "wanene Dr Sageer!?".
"shine likitan da aka kama Na Osun d'innan, Wanda ake zarginsa da saida kwayoyi ta asibintinsa, amma ya tabbatar mana bashi kad'ai baneba a bayanansa, hukuma sha da fataucin miyagun kwayoyi tana bincike akan sauran mutanensa".
"Kukuma kuna aikinmi? Kuna zaune kawai kuna jiran su kawo muku bayanai kenan?".
" a...a'a sir, Bahaka baneba".
"To yayane? Bansan miyasa kuke sakaci akan aikinkuba, kunada damar kwatar cases a hannun kowace hukuma idan kukaga tanada rauni wajen hukunta mai laifi, amma saiku zuba idanu yayinda aikin had'aka yashiga hannunku, ni narasa mike damun tunaninku?, shin kunada tabbacin za'a hukuntasu yanda yakamata acand'in? Shiyyasa kullum muna aiki amma bamu samun alk'aluman cigaban wahalarmu, idan muka toshe can saikaga can ya 6alle, sakacinkune kuma kejamana wannan fad'uwar tasar".
Sorry sir, insha ALLAH za'a gyara".
" zancen kenan kullum, za'a gyara za'a gyara, amma haryanzun gyaran baizoba, haka za'a gama yayinmu bamukawo wani sauyiba a k'asarmu kan 'yan ta'adda, muwuce wasuma suzo Suyi tsarinsu suwuce, haka-hakadai kullum k'asa nak'ara ta6ar6arewa da lalacewa, mtsoowww aikin banza kawai".
"Basheer dai yanata bada hak'uri".
files biyu ya khaleel yamik'a masa bayan yasaka hannun, kakai wad'annan office d'in Taheer, wad'annan kuma yasaka hannu kakaima Mahfouz su".
" OK sir, thanks you sir".
Kansa kawai ya jinjina masa, yajanyolaptop d'insa yacigaba da aiki, shikuma basheer yafice, yanamai jin k'auna da sha'awar halayen Ibraheem Abdallah j!, yana addu'ar ALLAH yabashi ikon yin koyi dashi..
Dan bakowa keda makamancin k'yak'k'yawan hali irin nasaba, nason a gyara k'asa, musamman masu girman matsayi irin nasa, da Wanda suka fishi, harma da wad'anda basu kaishiba.


*******
Kiran wayarsa da'aka k'arayine yasakashi yin k'aramin tsaki, batareda yaduba mai kiranba ya d'auka yasaka a kunne yanayin sallama, yayinda hankalinsa kenan aiki a laptop.

"Ibraheem Aleeya ta saukafa, tace tanata kiran wayarka Baka amsaba".
" wlhy Momy aiki yamin yawa a office, please ki aika driver ya d'akkota mana, kokuma cikinsu Muhseen idan wani yana gida yaje ya d'akkota".
''ni babu wasu su muhseen dazan saka, dadai zaka daure saikaje ka d'akkota minti nawane kwata-kwata".
"Hummm Momy bazaki baneba wlhy, kinganni kuwa a office?, yanzu haka sallah nakeson natashi nayi nadawo kan aikina, kisankusa kwanaki goma bana office, please amin afuwa Dan ALLAH driver ya d'akkota".
Shikenan bara nama driver magana, sai suje da 'yan biyu".
OK saina shigoto, baijira cewartaba ya yanke wayar yana mita.
"kajiminfa Momy dawani zance, ita hartakai Isar dazanje airport d'aukarta, haba saikace wani lusari, mtsoww, wlhy kemafa Momy kinada matsala, haba kullum zance d'aya, yay maganar yana mik'ewa saboda Kiran sallah da akayi Na azhur.
Wayar yad'auka yaduba number data kirasan, saiyaga harda miss call d'in Aysha, itacema tafara kira, saikuma Na Aleeya guda biyu.
Kansa yadafe, Dan baiyi tunanin kiran nataba, yama manta yanada number ta, yakar6ane wajen mama tun lokacin gabatowar bikinsu data tafi Kano, tunda yakar6i number ma baita6a kirantaba, ita kanta ayshan batasan yanada number d'intaba.
Massage d'in da'aka turo yaduba Dan ganin number ayshane.

_"Sadaukina ya aikin?, kakasance cikin farinciki da kwazon aiki irinnan gwarazan sadaukai mijina"._
*_Sholynka Ce_*=??

Murmushin dabai niyyaba ya su6uce masa, yakuma maimaita massege d'in, aransa yana jinjina baiwar Aysha, gata 'Yar k'arama sai wayon tsiya.
Masallaci yafice Dan gabatar da sallah.

Bayan idar da sallah suka had'u dasu taheer. Cikin tsokana Taheer yace, "kai alhaji kaga kuwa k'yawun daka k'ara? Lallai ango kana kwasar amarci yasin".
" mtsooww! ALLAH ya shiryeka Taheer, kaidai bazaka ta6a canjawaba ko? To dan k'aniyarka muni kakeso Na k'ara saboda nayi aure?".
Cikin dariyar shak'iyanci youseef yace, "A'a bak'inciki yakeson maka, k'ilan soyay kadawo aiki wujiga-wujiga ko? Katina lokacin daya dawo hutun angwanci, ALLAH Taheer harwani yallew-yallew yakeyi saboda gara daya kwas.........."
.......Bai k'arasaba taheer yakai masa rankwanshi.......
Youseef yamatsa yana dariya. "Kai Malam ALLAH ka rankwasheni ramawa zanyi, koka manta Na girmeka tunda narigaka aure?".
"To uban 'yansan girma, munji karigamu aure saime to? abinda kake tak'amar kasani mumadai yanzu mun sanshi koko Taheer?".
" A'a j bakada bakin maganama kaikam, tunda kaine auta acikinmu".
"Kuttt ammafa ka sameni, d'an iska zan ramane, nakula tonon silili zakamin cikin yara, bara nawuce office aiki nacan jingim yana jirana, ni dama banje wannan hutuba".
" hhhh tab wlhy ganganne, muzaka saka a kwali, kagama dirzar amarci da young girl d'inka kazo kanawani daddojewa>?#?".
"Banza d'an iska banida lokacinka, kagama tafiyata", 'ya khaleel yay maganar yana barin wajen, fuskarsa d'aukeda murmushin iskancin da youseef kemasa'.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login