Showing 90001 words to 93000 words out of 155647 words

Chapter 31 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

475

kwana biyu rak da kaita gidan, sannan amaye gurbin gidan da jinin Bilkeesu, wlhy impossible, wannan wane irin rikitaccen tunanine?, ko ance muku idan mufeedah ta haihu bazata koma d'akinta baneba?".
Mik'ewa tsaye baffah yayi yana guntun murmushi, yace, "Laurah Baku Isa hanani abinda nayi niyyaba, Ammah datai sanadin kawoni duniyama ta amince, hakama d'an uwana ya amince, Ameenudden ya amince, ahakama iyayen yarinyar, banida abinda zan sakama Ameenudden dashi saboda zalincin da ballagar 'yarki tamasa, adalilin sakacinki, babu abinda zai saka aurennan fasuwa saidai mutuwa, idanma zaku kwantar da hankalinki Ku kwantar, idan bazaku kwantarba kune awahale, narigada Na zartar da hukunci babu mai canjashi, wlhy da'ace akwai budurwar danake da ita bayansu Tasleem saina aura masa, bazankuma aura masa Hasnah ko Husnah ba, saboda suma hankalina bai kwanta dasuba, ki kiyayeni kuma".
Yajuya zai fice abinsa.........
Cikin k'araji hajia babba tace, kayan kicin aida kud'ina nasiya, Dan haka sai an kwasomin kayana, kuma zargin dakama sauran 'ya'yana ban yafeba, dama cin zarafina kazoyi gaban 'ya'yana ba dubaniba, dama aii tuni nagama sanin Bilkisu ta shanyeka, kayi nisa bakajin kira, ALLAH saiya mana hisabi tsakanina daku".
Juyowa baffah yayi yana kallonta. Yasaki guntun murmushi, kiyima kayan kichin d'in kud'i konawane zan biya, sauran maganarki kuma kisameni zan baki amsarsu, amma ba'a nanba, yanagama fad'a ya ficewarsa abinsa.
Kuka rurus momy takeyi, sai zage-zage da zabgama mufeedah ALLAH ya isa takeyi, wai itace taja ake cin zarafinta.
Inna jummai tashigo tana mata fad'a.
Dak'yar suka samu yayi shuru kuwa.


___________________
Har bayan isha'i ya khaleel bai dawo gidanba, Aysha Na kwance bisa doguwar kujerar ammah, lullu6e take cikin bargo saboda sanyi datakeji, ga zazza6i mai zafi ajikinta, tun d'azun tunanine da damuwa suka to she kwalwar kanta, duk yau bataga ya khaleel ba, dukda tana zargin yatafi aiikine, amma yakamata yakirata yaji yajikinta, ganin bai kira d'inba takirashi har kusan 4times amma bai d'agaba, hawaye masu zafi suka zubo akan kumatunta, tun d'azun take kukannan, saboda lullu6a datayi da bargo har fuskarta yasa ba'a ganin.
Ammah dabatasan abinda ke faruwaba, suna zaune da inna jummai suna hirarsu irinta zuminci, sai Tasleem da maleekah dake can gefe zaune kowacce suna chatting, inbakama saniba zaka zata suna falonba.

Sallamar ya khaleel tasakasu d'agowa suduka, amma da inna jummai suka masa sannu da zuwa, suma su Tasleem suka gaidashi.
Ya amsa awani yanayi, Ammah sai binsa da kallo takeyi, Dan taga Alamar yana tareda damuwa.
Inna jummai tamik'e tafita, waizata duba jikin Momy tadawo.
Ko kallo bata ishi ya khaleel ba, danshi bayason wanda bai sonsa, tana fitama k'amin tsaki yaja, ammah datajisa batace dashi komaiba, Dan tuni take fuskantar 'Yar tsamar dake tsakanin Khaleel da kakarsa tawajen uwa, kuma k'anwar kakarsa ciki d'aya.
Zama yayi saman hannun kujerar da Aysha ke kwance, wadda tunda taji sallamarsa tashare hawayenta.
Hannu yakai ya yaye bargon, hucin zafin zazza6in yasakashi fad'in ''ya salam, wannan zazza6in har yanzu bai saukabane Ammah?".
"Yana sauka yadawone iro, aii saidai hak'uri kuma, idan ba kwari yayiba haka za'aita fama".
" ALLAH ya k'ara lfy, yay maganar yana lek'a face d'in Aysha data lumshe ido, saika d'auka da gaske barci takeyi, ammashi tuni yagano idonta biyu.
K'aramin hannun rigarta ya janye, babu komai a damtsen hannunta, aransa yace k'ila d'ayan hannun tane kunamar take?, saikuma yace amma banta6a ganiba?".
Aysha dai batako motsaba, yamaida bargon ya lullu6eta yana mak'ewa, ammah bara nad'an watsa ruwa, shigowata kenan gidan.
".
A to yakamata aje a kimtsa, kazo ga abincinka Bilkeesu ta aiko dashi".
Kansa kawai ya iya jinjina mata yafice, Aysha tabishi da kallo asace, tabbas akwai abinda ke damun mijin nata gaskiya, to minene?".
Batada amsa, babu kuma mai bata, wannan yasakata tsuke bakinta tayi shiru. Tana binsa da addu'a a zuciyarta................
'







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?O?

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


3? 4?

Bai shiga 6angaren Momy ba, kai tsaye 6angarensu yawuce, yad'an watsa ruwa sannan yadawo falo yazauna, komai akashe yake, babu haske Afalon, yana zaune cikin duhune. Sai tunani yakeyi, yarasa yanda zai fassara abubuwan dake tunkaro rayuwarsa, kallon komai yakeyi abaibai, miyasa abubuwa suketa rikid'ar hawainiyane acikin gidansu?, muyasa baita6a kawo tunanin komaiba dangane da wasu abubuwa sai yanzu?.
Guntun tsaki yaja, yazame ya kwanta a doguwa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r kujerar, hakai yayta tunane-tunane har kusan 10, ring d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yad'auki wayar yana kallon mai kiran, baffah ne, harta katse bai d'agaba, kamar bazai kiraba saikuma yay k'ok'arin dailing d'in number, gamo yayi da miss call d'in mimy har uku, ya furzar da huci, Dan kokad'an baiji kiranba, baikai karshen tunaninsaba kiran baffah yasake shigowa.
'Dagawa yayi, cikin ladabi yagaida baffah tamkar yana gabansa.
"Mu'azzama kana inane?".
''Ina gida baffah".
" kazo to ina nemanka, amma yanaji muryarka haka?".
"Babu komai baffah, barcine yad'an figeni, ganinan zuwa dai".


***********
Baffah kad'ai ya tarar zaune afalo yana kallom labarai a NTA, harma sunkusa gabawa, zama yayi yagaidashi.
Baffah ya amsa idonsa akansa, danya hango damuwa tartare da d'an nasa, baidai cemasa komaiba dangane da damuwar tasa, Dan yasan bazai wuce awajen aikibane.
baffah yafara magana " dama nakirakane akan shawarar damuka yanke nidasu Ammah, saboda kafita tunda safe yau, akan maganar Ameenudden ne, da cikinsu tasleem zance yaza6a, amma sai Ammah takecemin Tasleem tana tareda k'anin Naufal ne, Maleeka kuma yaron Alhaji musa batsari, kuma duk takula mu'amullar tasu tayi k'arfi, wannan yasa na janye batun akansu, saida bazan bashi Hasnah ko husnah ba, saboda mahaifiyarku bazata barsu su zauna lafiyaba, akwai yarinyar Hameesu, k'anin Bilkeesu, Nafisa, tazo bikinnan, Tanama gidannan bata tafiba, kawai mun yanke shawarar maidama Ameenu ita a madadin mufeedah."
Jin baffah yayi shiru, ya khaleel yagane yagama, zamansa yagyara shima.
"Baffah shawararku tayi dai-dai, kuma ALLAH yasanya alkairi aciki".
"To ameen, saikuma batun mufeeda, da nace takoma 6angaren Ammah, Dan asamu jinin ita momyn taku yasauka, tokuma saitace tafison tabi innah jigawa, idan tahaihu wai saita dawo".
" karka yarda da wannan batun baffah, kasandai halin inna jummai, wlhy dakanta zata 6arar dacikin jikin mufeedar".
Hakama Ammah tacemin d'azun.
"Tokagani baffah, kawaima tatattara adarennan takoma 6angaren Ammah, barama dakaina zanje".
" shikenan Mu'azzam, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, yajikin matar taka?".
"Ameen baffah, jiki Alhmdllh".
" ALLAH yak'ara afuwa to, tashi kawai kaje".
Sallama ya khaleel yayma baffah yafice.
6angaren Momy yanufa. Afalo ya iske su suna hira, inna jummai Na tsakkiyarsu, Duk suka gaidashi, sama-sama ya amsa yashige, innah jummai tarakashi da harara. dariya Anty Zuwairah tayi, tace, "nifa 'Yar tsamar innah da khaleel tana bani dariya, waimi kika masane haka innah?".
Kunyace takama innah jummai, saita fara 'yan kame-kame, tarasa abinda zata fad'a domin Kate kanta.

Daga Momy har ya khaleel da Anty shukurah suna jiyosu daga d'aki, saidai hankalin Momy nakan khaleel, sosai taga damuwa afuskarsa.
"Ibraheem mike damunkane?".
" murmushin yak'e yayi, babu komai Momy, ciwonkune mana keda A'eesha, waini momya bammaji kinmin maganar A'eesha ba, kobakisan batada lfy ba?, kinsamu jika Momy, amma banga kin nunamin farincikiba ko sau d'aya".
Cikin daburcewa Momy tace, "ba....bahaka baneba Ibrahim, in...I..ina farin ciki mana sosai, Kasan tashin hankalin mufeedar nanne yadanne komai azuciyata. Amma yanzu ya jikin nata?".
" Alhmdllh, saidai tana shan wahala".
Baki hajia babba tad'an ta6e, amma khaleel bai ganiba, afili kuma tace, "ayya Allah Yakawo afuwa, dama ciki saida hak'uri, barema cikin fari".
"Hakane Momy".
" naga kema aii jikin naki Alhmdllh".
"Uhm da sauk'i kam sosai, saidai abinda ba'a rasaba, kaji wai mi baffanku suke son k'ullawa?".
" naji, Indai akan Auren Nafisa da Ameenu ne".
"To mikace musu?".
" mizance Momy, Addu'ar fatan alkairi namusu mana, ai hakan shine dai-dai kodan halaccin da Ameenu sukamana shida iyayrnsa".
Fuska Momy tahad'e, "wai Ibraheem nikam mikakeson maida kankane?, Kaine babba acikin yara mazan gidannan, amma kokad'an bakada wata jarumtar kwato mana 'yancinmu nida 'yan uwanka, katunafa kaikad'ai ALLAH yabani namiji".
''Hakane Momy. Amma inason kiringa fahimta abinda yazo akan turbar gaskiya. Kasan cewata wakilinku agidan nan, bashine zaisa nayita danne gaskiyaba saboda farincikin Ku, itafa gaskiya D'ayace, daga k'inta sai 6ata, shin bakiji masu iya magana nacewa *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI BA_*, wannanfa zancen gaskiyane wlhy, idan zaka kasance mai gaskiya abuga-abuga, dole abarka momy, Idan Abu yazo a turbar gaskiya yakamata kudinga kar6arsafa".
" naji shashasha, tashi ka6acemin anan, sallamamme kawai, basaikaje kaita goyon bayansunba".
Khaleel baice komaiba yatashi yafice, afalo yace INA mufeedah?.
Hasnah tace, "tana d'akinta ya khaleel".
Baice komaiba yashiga d'akin muferdah, tararwa yayi tana 6alle magunguna zatasha, jikinta sai rawa yakeyi bataso kowa ya ganta, shiyyasa taketa waige-waige.
Shigowarsa yasaka jikimta k'ara k'arfin rawa, tasaki magungunan hannunta a k'asa yanayinta kawai ya tabbatar masa batada gaskiya, cikin takunsa Na jarumta yak'arasa gareta, tsugunawa yayi yad'ibi kwalayen maganin yana dubawa.
Fuskarsa amatuk'ar d'aure yad'ago manyan idanunsa da suka koma jajaye gabad'aya yinin yau yad'orasu akanta, (humm todama Yaya lafiyar giwa) idon ya khaleel Na a daidaima ya'aka k'are ballantana yau dayake cikin 6acin rai, fitsari kawai mufeeda tasaki atsaye, jikake tsululululu!!=??.
Lafiyayyun Marika hud'u yasakar mata, cikin daka tsawa mai firgitarwa yace, " ubanwa yabaki maganin zubar da ciki?!!! Nace ubanwaye yabakishi agidannan?!! Wlhy koki fad'amin koma 6a66allaki, dagake har cikin kutafi barzahun 'Yar iska maikama da dabba. Wlhy bak'aramin asarar kud'in Tara akayiba wajen biya miki kud'in makaranta, mai kwakwalwar kifi kawai, bazaki fad'amin Wanda yabakibane saina miki dukan mutuwa?".
"Wlhy ya khaleel innah Ce, narantse bani nasiyaba..."
Bata rude bakiba innah jummai tafad'o d'akin, saiwani cika da batsewa takeyi, Dan duk abinda ke faruwa sunaji afalo.
Cikin masifa tace, "kai wallhi kafita idona in rufe, kafara shigarmin hancifa, yanzunnan saina fyatoka".
kallon samada k'asa yamata, kamar ba kakarsaba, Dan Ransa amatuk'ar 6ace yake, idonsa yarufe baima tantance wadda yake agabansa, yace.
"Dan ALLAH karki fasa fyatonin, ya da girmanki da shekarunki zaki d'auki abinda zai cutar da yarinya kibata?, anya kuwa ked'in kakarmuce? Nifa INA kokwanto wlhy, dan tuni nakula da rashin k'auna dakike nunamin tun INA k'aramina, yanzu kuma shine zakibama yarinya magani wai danta Barar da ciki?, shiyyasa kika nemi abaki ita kutafi Jigawa?, shin idan ita batada hankali kema bakida shine?, wlhy tuni dama nakula ked'in tsohuwar......
Bai k'arasheba yaji saukar mari akumatunsa, shiru yayi yaduk'ar da kansa, Dan yaga k'afafun Momy, karo Na farko data mareshi dawayonsa, bama itaba, zai iya rantsuwa da hankalinsa wani baita6a marinsaba sai yau.
"Ibraheem bakada hankaline?, uwar tawa katasa gaba kakema fitsara? Shin INA hankalinka yatafine?, koka fara shan giyane wai?".
Shiru yayi bai tankaba.
Cikin daka tsawa Momy tace, "ibraheem kobaka jinane!!!!?".
Nanma shiru yamata, har yanzu kuma hannunsa Na dafe da kuncinsa, idanunnan sunkuma rinewa jajur.
" yaza'ayi yabaki amsa, dukdai kece kika jamana bala'innan, tunda kece kika dage wajen.......
"Haba innah mikikeson fad'ane haka?"......
Adai-dai nan baffah da Ammah suka shigo.
Anty Zuwairah Na kuka tasanar musu abinda ke faruwa, Dan yau tausayin d'an uwan nata yashigeta, tadad'e da fahimtar tsangwama da k'yara da innah jummai ke nunama khaleel, ita kanta tana mamakin hakan, amma bata ta6a kawo komai arantaba, Dan innah nacewa saboda miskilancin sane da taurin zuciya, itakuma batason mai wannan halayyar, dukda dai wannan bai Isa abin gamsarwa ba haka Anty zuwairah tashare bata maida hankaliba.....
Baffah baice komaiba, sai Jan khaleel yayi ajikinsa, yana buga bayansa ahankali, wannan ne ya karya zuciyar ya khaleel, dama ga damuwar dake cunkushe da zuciyarsa tunda safe, saikawai hawaye suka fara zirara a kumatunsa.
Karo Na farko danaga ya khaleel yana kuka=?3?.

" Jummai iro yanada hujjar fad'a miki duk kalamin dayazo bakinsa, shin amatsayinki Na babba yadace kifita kinema maganin zubar da ciki kibama mufeedah?, shiyyasa kai tsaye nace banyarda kitafi Jigawa da itaba, saboda nasan halinki, nasan mizaki iyayi, wato hanawata tasakaki canja salo?, kika bata maganin dantasha yazube ayanzu? Wlhy jummai kinji kunya, tunda ke bazaki ta6a zama mai hankaliba, da ALLAH bai kawoshi d'akinba dashikenan
........
Haba yaya, wai yazaki tasani gaba kina gayamin maganganu agaban yara? Naga yanda kikeda iko da mufeeda nima inada iko da ita aii.
Tabbas kinada iko da ita jummai, amma ikon bashi zaisa abarki ki cutar da itaba.....
"Ammah kiyi shirunki kawai, kidaina 6ata ranki, aiiduk abinda kashuka saika girbeshi watarana".
Hannu Innah jummai tad'aga zata mari ya khaleel dake magana, da sauri yarik'e hannun, ido cikin ido suka kalli juna, (wani irin tsoron khaleel ne yashigi inna jummai, mugun kwarjininsa da baiwar rikita Mara gaskiya da ALLAH yayma kwayar idonsa yasaka dukkan sassan jikin inna jummai fidda zufa) yace, "daga yau banida kaka ta 6angaren uwa, nashafeki acikin tarihina, danhaka jummai, wlhy kikayi kuskuren marina saikinyi nadamar haiguwata dakika bari akayi, Dan saikinji inama Momy kika bama maganinnan tasha lokacin tanada cikina, Na radaddage aciki kuka watsani a gotta......"
Baffah ne yazo ya janyeshi yana masa fad'a, Momy kuwa da innah jummai kuka suka Sanya, itakam Ammah ko'a kwalar rigarta, dantaji dad'in abinda ironta yayma k'anwar tata, taja hannun khaleel da mufeedah tafice.
Baffah ma bayanta yabi.
Anty zuwairah madai yau bataji dad'in lamarinnanba, kuma zuciyarta tafi karkata ga khaleel, Dan ganin gaba d'aya yanda aka tozartashi, tamkar ba jinin momyba, tomi khaleel ya tsarema innah haka? Miyay mata dazafi haka? Kowa yasan tun suna yara batajan khaleel ajikinta, "why?".



___________________________
Tunda suka shigo idon Aysha nakan ya khaleel, tun d'azun itama take rabzar kuka, Dan komai akan idonta yafaru, tunda Hasnah tazo arikice tafad'ama Ammah abinda ke faruwa itama ta tak'ark'ara tabi bayan Ammah batareda ta saniba, la6ewa tayi tajikin window, komai akan idonta yafaru, (Mashi'a kuma tafad'a mata sauran) tausayin ya khaleel d'inta Yakuma kamata, tabbas zarginta yana Neman zama gaskiya.
Shima hankalinsa Na kanta, kunyar baffah kawai tahanashi matsawa kusada ita.
Baffah ya masa fad'a akan abinda yayma inna jummai yamusu sallama yafita, saboda dare yayi, 11 yawuce sosai.
Baffah Na fita ya khaleel yakoma inda Aysha take zaune, muryarsa a sanyaye yace, "mike faruwa? Ko wani guri kemiki ciwo?".
Girgiza masa kai tayi, tana share kwallah. Shima baice komaiba yajawota jikinsa ya rungume, yamaida kansa yajingina da kujera ya lumshe idanu.
Tausayinsu yakama Ammah, ita kanta mufeedah taji tausayin yayan nata, yaune rana ta farko data farajin nadamar abinda ta aikata, gashi ta silarta sa6ani Na k'ok'arin shiga familie d'insu, tashare hawayen fuskarta tana satar kallon miji datar cikeda sha'awa.

Saida Ammah taga barci ya suri ya khaleel ahaka, itama Aysha barcin ya d'auketa, tadashi tayi, " iro tashi katafi ka kwanta, kaga dare tayi, gashi zakaje aiki gobe idan ALLAH ya kaimu".
Kansa ya jinjinama Ammah, ahankali yad'auki Aysha dankar ta tashi, yakaita bedroom d'in Ammah, ya kwantar agado, zama yayi kusada ita yamata addu'oi ya tofeta, yaja bargo ya lullu6eta saboda yaga tanata takurewa waje d'aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login