Showing 72001 words to 75000 words out of 155647 words

Chapter 25 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

455

9am ya khaleel yashiga gaida momy, Momy kad'ai da husnah yatarar afalon yazauna yana gaida momy cikin girmamawa, husnah ma ta gaidashi.
Momy ta kalli ya khaleel tace, "aikam kazo a dai-dai, ALLAH yasadai baka karyaba?".
" tofa momyna uwa mai dad'i, miya farune? ban karyaba kuwa, tashina kenan daga barcima nayi brosh nafito gaidaku".
Momy tayi masifar washe baki kuwa, Alhmdllh, yau saboda kai nashiga kichin da kaina, mutuminka nayi Alkubus, Mashi'a!!.
takwalama mai aikinta kira, wadda taware cikin 'yan aikin gidan.
Murmushi ya khaleel yayi, "wayyo momyna ALLAH yak'ara yawancin kwana, yanzunan saboda ni kika wahalar da kanki?".
Dariya kawai momy tayi amma batace komaiba, saboda zuwan Mashi'ah.
''Yauwa mashi'ah, ina abincin khaleel danace ki ajiye min?".
"Yana kicin hajia".
" to d'akko masa".

Babu dad'ewa mashi'ah tazo ta shirya abinci gaban ya khaleel, takoma kichin, tana shiga ta rushe da kuka, nashiga uku ni mashi'ah, yanzunan ina kallo za'ayi kisan kai?".
"Kai. Bazai yuwuba, dolene Na ku6tar da bawan ALLAH nan, mutumin kirki dashi, kodai nafad'ama momy maganin kashe d'anta hajia khaltum tabata, kai fad'ar hakan matsalane".
Gabanta yay mummunar fad'uwa data tuna zaifa iya faracin abincin yanzunnan, da sauri tafito daga kichin d'in zuwa falo................
'







*_tofa masu karatu, yaya zata kasance idan ya khaleel yaci abincinnan?, miyasa hajia khaltum tabama momy guba amatsayin maganin gusarma ya khaleel hankali akansu? Shin momy tasan gubace kokuwa?._*

Kucigaba da kasancewa da d'iyar baba iro danjin cakwakiyar dazata cigaba da faruwa, Dan alamomin tonuwar asirifa sun fara bayyana>?8? @&>?8? @&>?8? @&.





=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?=ؔ?


*_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_



*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


2? 7?

Da gudu mashi'ah tafito daga kichin d'in, hakan yayi dai-dai da k'ok'arin saka laumar alkubus da ya khaleel keyi cikin bakinsa, gaba d'aya suka mik'e suna tambayar ta miya faru?, ina mashi'ah bata saurari kowaba, burinta ta isa inda ya khaleel yake, Dan d'ago ido kawai yayi ya kalleta yacigaba da k'ok'arin saka abincin abakinsa, tirjewa tayi tafad'i, k'afarta ta bigi table d'in gabansa yakife, komai yazube k'asa har laumar hannunsa daya jefar yay saurin tashi saboda yanda ta hankad'o abincin jikinsa.
Bak'aramin 6acin raine yaziyarci momy da ya khaleel ba, yadaka mata tsawar data tadasu Aleeya daga barci.
"K wacce iriyar dabbar yarinyacene? Shin wani Abu yashiga kwakwalwarkine Dan ubanki?".
Kanta yayo zai daka momy tarik'eshi, "barni da ita Ibrahe???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?em, karma ka 6ata ranka abanza".....
Husnah dake kusada ita tayi wani uban ball da mashi'ah tafara dukanta, daga ya khaleel har momy babu wanda yahana husnah, harsu Mufeedah suka fito suma, da k'yar mashi'ah ta kwaci kanta, zata gudu 6angaren masu aiki Aleeya tadaka mata tsawa, ''k ubankine zai gyara wajennan?".
Dawowa mashi'ah tayi, jikinta sai rawa yakeyi, kokad'an bataji zafin dukan da husnah tamataba, hakama zagin dasuke mata bai 6ata rantaba, saima godiya takema ALLAH azuciyarta data samu damar hanashi cin abincin, gyaran wajen tashigayi.
Ya khaleel kuma yafice ransa a6ace, jallabiyarsa dukta 6aci da miya.


***********
Aysha Na shirya abinci a tsakkiyar falo yashigo, cikin mamaki take kallinsa, shikam ko kallonta baiyiba yashige d'akinsa. bin bayansa tayi da sauri, gaban madubi ta iskeshi yana cire rigar yana Jan tagwayen tsaki.
Taimaka masa tayi yacire rigar, tana rik'e ahannunta sai duba miyar takeyi, tace, " sadauki miya 6ata maka jiki hakane?".
"Mtsoww wlhy wawuyar mai aikincan Ce ta momy mana, tawani fito daga kichin kamar mahaukaciya kawai ta6aramin abincin da momy tamin".
"wai kana nufin mashi'ah?".
K'in tanka mata yayi, sai tsaki dayaja yashige toilet, tabishi da kallo itama, aranta tana raya miyakai mashi'ah aikata hakan?, tasan halinta, yarinyar batada damuwa, tabbas akwaidai dalilin yin hakan, shin miyema yasaka momy girkama ya khaleel abinci? alhalin ita bata ta6a ganin hakanba?.
Bakinta tata6e tana d'age kafad'a, ">?7? @&komadai miye susuka Sani, d'antane dai". 'Aysha tafad'a tana ficewa d'akinta darigar a hannu'.
Jik'ata tayi a boket sannan tadawo d'akinsa, bai fitoba, kaya marasa nauyi ta fiddo masa, ta fesa turare ta ajiye a bakin gado, tadawo falo tazauna tana jiran fitowarsa.
Kusan mintuna 25 saigashi tafito sanye cikin kayan data fiddo masa, saidai fuskarnan babu walwala ko kad'an.
Bata damuba ta sauka k'asa ta zuba musu abincin, saida tamasa magana kusan sau biyu sannan ya sauka k'asa.
Hakadai sukaci abincin kamar wasu kurame, babu mai cewa uffan, garama Aysha tana kallo tanacin abincin.
Hardai suka kammala.
Wajen ta gyara tsaf.

Batareda ya kalletaba yace, "yau su Joseph zasuzo da matansu, saikima su Amal magana da zeenatu su tayaki had'a musu abinci", baijira cewartaba yamik'e yafice.
Kanta kawai ta girgiza, ahankali tace, " ALLAH ya canjaka ya khaleel".
Koda tafito domin zuwa cikin gida saita taraddashi a barandarsu zaune bisa kujerun wajen, yanata danne-danne awaya.
Batace komaiba tawuceshi, shima ko d'ago kai baiyiba ya kalleta, amma yaji alamun wucewarta.

Maimakon tashiga 6angaren masu gidan kai tsaye, saita wuce 6angaren 'yan aiki, cikin sa'a ta taras babu kowa afalon nasu, tasan suna cikin gida, saboda yau weekend kowa zaici abinci agida.
saida ta lallek'a sauran d'akunan taga babu kowa aciki sannan talek'a d'akinsu mashi'ah, akwance ta hangota tana kuka, ta k'arasa da sairi inda take, "mashi'ah tashi".
Da sauri mashi'ah tamik'e zaune danjin muryar Aysha, saikawai tafashe da kuka, "Anty wlhy zasu kasheshi?".
"Mashi'ah waye zasu kash?". 'Aysha tayi maganar ahankali'.
"Anty ya khaleel mana".
" ya khaleel kuma?, mashi'ah miyasa kikace haka?".
"Anty shekaran jiyane hajia khaltum takawo wani magani wai abama ya khaleel yaci acikin abinci, abinda yasa nima nasani naje kaima momy fura da yamma d'akinta, harzan shiga sainaji magana k'asa-k'asa, hajia khaltum nafad'a mata cewar maganin inhar ya khaleel yacishi zai manta da komai, wannan ne zaisa su zauna lfy karya kamasu wai, cikin farinciki momy takar6a, tace insha ALLAH yau da safe zata yimasa alkubus da kanta, saboda yana masifar sonshi".
"Inajin haka saina koma baya, saida hajia khaltum suka gama sanan nakaima momy furar, nadawo tsakar gida zan komo nan saiga hajia khaltum tafito itama tana surutai cikin harshen futanci, nikuma batasan inajintaba, hummm wai zatayi maganin ya khaleel, Dan babu wani maganin manta komai data bashi, gubace tabashi, zatayi awa 48ne ajikinsa kafin tafara aiki, kinga kwanki biyu kenan, batareda an zargesuba saidai ya mutu, kuma gubar bata nuna wata alamar daza'a gane guba yaci, saidai idan binciken likitoci".
"Wlhy jiya banyi barciba Anty, sau kusan uku ina zuwa 6angarenki saina samu ya khaleel na nan, shiyyasa Na hak'ura, yau da safe bayan nagama taya momy yin alkubus shine ta aikeni babban kichin d'aukar Abu, harna fita namak'e ina lek'enta ta kafar makulli Dan nasan maganin jiya zata zuba, shiyyasa ta aikeni, ilai kuwa Na hangota tafiddo kullun maganin cikin zaninta ta barbad'a amiyar ya khaleel".
"Bayan yazo gaidata aka sakani kawo masa abincin, to banida mafitar dazan hanashi cin abincin, shine nayi pretending harna samu nasarrar zubarwa, shinefa Anty husnah ta dakeni, bayan tafiyar ya khaleel sai momy ma ta mammareni=?-?".
Lallashinta Aysha tashigayi, tabata hak'uri sosai, saida taga tayi dariya sanan tafito.



____________________

Girki sukeyi amma hankalin Aysha nakan juya zancen guba da akaso bama ya khaleel d'azun da safe, wanan lamarin yana buk'atar k'yak'yk'yawan nazari, haka kawai Aysha taji tana zargin wani Abu, musamman da zuciyarta ta waiwayi tarinhin baya akan lamarin gidan, kafin samuwar yara da bayan samuwarsu, har zuwa yanzun, amma tabarma zuciyarta, kuma lokaci yayi dazata fara bincike awannan fannin kam...
Hummm saidai kuma ta ina zata fara?, tana buk'atar shawarar wani kenan? To kuma wannan sirrintane all, ko Anty meerah batason tasan dashi, wacce mafitace da ita kenan?.........
Girgizatan da Shahudah tayi yasakata juyowa da sauri, antynmu miya faru haka? Kiketa tunani?".
Ajiyar zuciya Aysha tayi, ''kibari Anty shahudah, wlhy ina tunanin zuwan bak'innan ne kawai".
Dariya sukayi su duka, harsu Amal, daganan kuma akacigaba da hira.
Cikin awanni 2 suka gama kammala girgi masu dad'i da d'and'ano, aka zuba a sabbin kuloli, Dan yaune rana ta farko da aka fara girka abinci a kichin d'in ayshar, shayine kawai take dafama boss.
Saida suka taimaka mata ta mammala komai tsaf, sanan suka koma cikin gida, har lokacin ya khaleel yana baranda zaune.
Saida su Amal suka fita sannan yashigo shima, Aysha nacikin wanka taji ambud'eta, juyowa tayi saitaga ya khaleel, maida kanta tayi k'asa, Dan har yanzun kunyarshi takeji, batawani gama sakin jikinta dashiba gaba d'aya (aganina ko shekaru ashin kukayi da mijinki yakamata kiringa irin wannan 'Yar kunyar, Dan tana saka miji nishad'i dajinshi sabo awajenki).

"Wayyo sadauki, zanmaka ihufa inbaka rufeniba".
Yanda tayi maganar a shagwa6e tana kuma k'ank'ame jiki Dan karya ganta, said abin yabashi dariya, baiyiba amma yayi murmushi yamaida k'ofar yarufe. gadonta yadawo ya kwanta, yana jiran fitowarta.
Ita a zatonta tama yafito, danhaka ta d'auro guntun towel tafito kanta tsaye, saida tafito tsakkiyar falon sosai sannan taganshi kwance yana danna wayarta.
Da Sauri taja baya zata koma yace, " kina komawa saina hukuntaki, garama kizo ki shirya".
Babu yanda ta iya tak'araso, sai k'unk'uni takeyi, yanajinta amma ya shareta, yacigaba da buga game d'insa a wayarta.
Atakure dai tayi shirin, tasaka atanfa d'inkin zani da Riga, kayan sun mata k'yau, ta gyara gashinta, tana cikin d'aurewa maganar ya khaleel tasaka juyowa ta kalleshi".
"Kishirya gobe idan ALLAH ya kaimu nakaiki kitso, nakula in barinki za'ayi wannan kan naki saiya shekara a haka babu kitso".
Baki ta tunzuro gaba, ''nidai banason kitso ALLAH sadauki, bakasan akwai zafi baneba?".
Wayar hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba d'aya kanta, "rantse kitso yanada zafi?".
Saida ta kammala d'aurin d'an kwalinta, da yay mugun zama yay k'yau sannan tataso gaba d'aya tadawo bakin gadon, " ALLAH sadauki kitso akwai zafi, nifa Na manta tsawon lokacin Dana zauna amin kitso wlhy".
"Miyasa to?".
" haka kawai nidai damacan banason kitso ALLAH kuwa".
Girarsa d'aya yad'age sama, yana kallonta, kinga nikuma inason kiyi kitso, harda wannan lallin da'aka miki irin Na biki, ko kad'an banso ya gogeba ni".
Nima inason lalli, ammafa banda kitso, tayi maganar da turo baki.
Jawota yayi saman gadon sosai, sadauki bak'ifa na hanya, please kabari kada kayana suyi S.....bai bari takai karshen zancenba ya >?+?.

ALLAH ya k'yauta nafad'a ina d'akko d'an alk'alamina da takarda nayo waje>???
@&.


___________________________
Wajajen 12:30pm saiga su Youseef, kowanne yakawo matarsa.
Tarba ta mutunci Aysha tamusu, dukda duk sun girmeta gaskiya sosaima kuwa, dandanan Aysha tacika gabansu da kayan ciye-ciye, duk saida sukayi mamakin ganin k'aramar yarinyar da ya khaleel ya aura, dukda sun ganta a wajen dinner, amma lokacin tasaka hill, kuma gown d'in data saka bubu Ce, amma babu Wanda yace komai, garama matar Joseph tama mijinta gulma ahankali, my sweet! Dama j! K'aramar yarinyar nan ya aura haka? Amma awajen dinner kamar ba itabafa?".
Mintsininta Joseph yayi, taja bakinta tayi shiru kuwa.
Bayan an gaggaisa Aysha taja Matan suka koma wani k'aramin falo da akayishi Dan hutawa kawai.
Ananne sukai mata introduces d'in kansu.
"Amaryarmu Aysha ko?".
Aysha ta gyad'a kai cikin jin kunyarsu, dan tana ganin dunsun girmeta, dariya mai tambayar tayi, takama hannun Aysha tana fad'in "kisaki jikin damu, munzama k'awaye yanzun aii, ni sunana Haneefa, nice matar taheer".
Kai Aysha ta gyad'a, tace, " ngd Anty haneefa".
Dariya duk sukayi, "nikuma sunana Joy, matar Joseph".
"Thanks you Anty joy".
"Nikuma Hafeezah, matar Youseef".
"Anty Hafeezah thanks".
"Hhhhh duk kin maidamu Anty, haba Aysha mud'in friends nakine aii".
" dukda hakadai Anty joy ".
Tun Aysha na d'ari-d'ari dasu harta saki jiki, sukasha hira, dandanan sabo yashiga tsakaninsu kuwa, saika rantse sun dad'e da sanin juna, musamman ma joy datakeda yawan tsokana.

Afaloma abokan hud'u sun had'e kai suna tattauna zance bud'e k'ungiyarsu ta taimakon matasa, kowa yana kawo shawararsa.
Kiran sallar azhur ne ya tashesu, hakama matan, akabar Joseph da joy kawai.
Duk sai sukaji babu dad'i, abin yata6a zuciyarsu, joy tace, "Sweet! dan ALLAH basu birgeka ba?".
Murmushi yamata, amma baice komaiba, tun tuni idan suna zaune da abokan nasa aka kira sallah suka tashi, saiyaji wani iri babu dad'i, abin na cizon zuciyarsa sosai.
Itama joy shiru tayi. Saitayi tagumi.
Suna nan zaune shiru, har duk suka dawo, Aysha tanufi kichin domin shirya abinci, su Hafeezah duk sai suka bita suka taimaka mata, a falon aka shinfid'a ledar cin abinci, suka shirya abincin akai.
Kowa yana kusada matarsa, sukaci abincinsu, itadai Aysha takasa sakewa taci, dan kunyarsu Taheer takeji.
Ya khaleel na lura da ita sosai, saida yagama cin nasa sannan yamaida hankalinsa kanta, kar6a cokalin yayi ahannunta, Babu musu tabashi, dan batasan mizaiyi dashiba.
Sai kawai taga yad'ebo yanufi bakinta dashi, idanu tazaro waje, "na k'oshi ALLAH sadauki, tayi maganar a hankali".
"Naji kin k'oshi, amma kar6a dai".
rok'onshi zata farayi yadakar da ita, "infa baki kar6aba, ninasan mizan miki yanzu awajennan, dan saina sakaki jin kunyarsu fiye da wadda kikeji yanz....
Bata bari ya k'arasaba tabud'e bakin da sauri ya zuba mata.
Gaba d'aya suka kwashe da dariya, ashe duk suna kallo dajin abinda ke faruwa.
Sinne kai aysha tayi jikin ya khaleel, yayinda shikuma yake murmushi.
Haka sukaci sukasha cikin nishad'i, bayan sun kammala suka taimaka mata wajen gyara wajen tsaf.
Saida akayi sallar la'asar sannan aysha tamusu rakkiya cikin gida, suk saida sukaje suka gaida kowa agidan, saboda aysha ta k'ular da momy saita bar 6angarenta yazama k'arshe.
Aikam sak'on aysha ya isa ga momy. Dan zuciyarta tayi k'unci sosai, aganinta ita ya cancanta sufara zuwa su gaida.
Su Mufeeda sai antayama aysha harara sukeyi, itako ko'a jikinta, su sukaga zasu iya wai sautin mahaukaciya.
Basu wani dad'eba aysha tace sutafi.
Momy kasa hak'uri tayi, tace, ''to isashshiya bazasu tafi d'inba, kedai tafi ga hanya nan, ko akwai Wanda ya rik'ekin........
Shigowar su ya khaleel ya katsema momy bayaninta, sarai kuma ya khaleel yaji da Aysha momy take, amma koda suka had'a ido da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login