Showing 81001 words to 84000 words out of 155647 words

Chapter 28 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

491

har 6angarensu dayake anan 'yammatan amare suke, 6angaren ya sultan, danshi yad'anfi sauk'in kai, mujahedeen ma halinsa d'aya da ya khaleel, shiyyasa basu cika sakewa a wajensaba, balle yau yana gida.
Babu wacce ta isheshi kallo yashige 6angarensa, su Rufaidah suna bedroom d'in Aysha, wasu na sallah wasu na gyara kwalliyarsu.
Aysha na falo tana barci, Dan basu tada itaba, tunda sunga tanajin dad'in barcin.
Harya wuce zai shiga d'akinsa ya hango Aysha na Neman fad'owa daga kujera.
Da sauri yak'araso cikin falon, ahankali ya d'auketa gudun karya tada ita, yana jiyo hayaniyarsu maleekah ad'akin Aysha, saikawai yawuce d'akinsa da ita, ya shinfid'e agado yana mai kallon face nata, mamakin irin kyawu da farin da ayshan tak'ara yakeyi, yakai hannu yana shafa sumar kanta ahankali, gashin gaban goshinta kwance luf-luf, cikin tsanaki yakebin dukkan illahirin jikinta da kallo, shi saiyagama kamar tad'an k'ara k'iba, ga fatarta harwani k'yalli takeyi, gashi gazar-gazar duksun fito taciki k'ofofi dasuka k'awata shek'in fatarta.
"Sholyna wane irin k'yawune haka?, ga jikinki akwai d'umi kamar bakida lafiya". 'yay maganar yana sumbatar goshinta'.
Kusan mintuna 12 ya lalata wajen k'arema Aysha kallo, sannan yamik'e ya canja kayansa zuwa k'ananun kaya, wani d'an aiki yakeson fita shi kad'ai.
Harya gama kimtsawa yafice tanata barcinta.

Sai wajen 5 Aysha ta farka, sai zubama su Rufaidah masifa takeyi wai basu tasheta tayi sallah ba.
" yo aii bamu kad'ai zakiyima jarabarba, saiki bari ya khaleel ma yadawo ki had'a dashi, tunda shiyya d'aukeki daga falon yamaida bedroom, amma bai tadakiba, kujimin yarinya kai, kodanmu kin gama rainamune?".
Banza Aysha tama sadiyan, tasan inta biye mata bazata huta da surutuba.

____

Zuwa 9pm duk angama kai amare d'akunansu, ankawo nasu Ramadan 6angarenda su ya khaleel suke, suma anan aka musu gininsu.
Babu inda Aysha taje, Dan ya khaleel yahana, yana gida yakasa ya tsare, dole ta hak'ura, Dan itama batajinma dad'in jikinta sosai.


*_ABINDA KA SHUKA........._*
(sabon buk d'ina mai zuwa insha ALLAH)=? ?.

Masu iya magana kance abinda ka shuka shizaka girba.
(Wannan batu haka yake)
Asafiyar litinin misalin 11:30am bak'i wasu duksun tafima, wasu kuma na haramar tafiya kamardai mutanen Kano, dake shirin tafiya amma amai da Aysha tawayi gari tana shek'awa yasakasu dakatawa.
Ana tararrabin ciwon na Aysha wadda yasaka ya khaleel rikicewa saiga mufeedah da 'yan rakkiya har mutum uku, tana rusarkuka.
Cirko-cirko kowa yayi, a tsakar gidan, Dan ya khaleel ne d'aukeda Aysha zai saka amota zasu tafi asibiti, yunk'urin amai datakeyine yasakashi sauketa k'asa, yana rik'e da ita tana tsaka da kwara a man m
ne motar 'yan rakiyar mufeedah tashigo gidan, ananne wasu suka raba hankalinsu biyu lokacinda akaga mufeedah tafito a motar tana sharar kwalla>??...................
'





*_"yaro bari murnar karenka Yakama zaki"._*=?I?

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


_hummm kunata yad'a jita-jita feedohm tarasu, inaga wataran sai wata tace agabanta aka saka gawar wata writer a kabari, to da ranta, haka kawai kudinga jamata bala'i, wai tayi had'arin mota, please mana, haka babu k'yau, duk masoyinka Na kwarai bazai gizganya masifa a kankaba, mutuwa dolece, kokun fad'a kobaku fad'aba zamu mutu aii, amma adaina jamana masifa please._
*duk wadda ta rubuta kuma ALLAH ya shiryeta, ammafa jakace wlhy tunda ta d'auki alhakin mutane, mtsoow.*


3? 0?

Ya khaleel baisan hidimar da akeyiba, shi gaba d'aya hankalinsa nakan Aysha, ya kar6i ruwan da Anty Amatullah ke basa ya wankema Aysha baki, duk jikinta ya saki, sai langa6e masa ajiki takeyi, (kunsan dai yanda amai ke saurin galabaitar da mutum), bare Aysha datakeyi tunda daddare.
Anty Mamie ce tayi azamar k'arasawa garesu, ''hajia Atine lfy dai ko? Naga d'iyata Na kuka?".
"Hajia Bilkisu mudai shiga daga ciki wajen Alhaji Abdallah, lfy naganku waje tsaitsaye?".
" wlhy Aysha ce matar babana khaleel babu lfy, shine zamuje asibiti, amma kumuje ciki, alhajin yana nan aii".
Wajen Ammah datun d'azun itama idonta nakan mufeedar Anty Mamie ta k'arasa, saida ta rissina sannan tasanar mata sunzo wajen baffane.
Ammah ta ta6e baki, ''to Bilkeesu, kiyi musu iso, nasandai lalatacciyar nan ta tafka halin uwartane gidan mutane".
Anty Mamie dai batace komaiba, tamusu jagoranci zuwa 6angaren baffah. Saida tafara Shiga ta sanar masa sannan tabasu izini suma.
Dukda daga baya ya khaleel yaga mufeedah amma bai maida hankalinsa kantaba, yashige mota da matarsa Na jikinsa, Hafez nagaba zai tuk'asu. Harya tada motar mama tak'araso wajen.
"Babanmu inaga kabar su Amatullah saisuje da Ayshan asibiti, kaga ga mufeedah dabak'i, ba'asan mike faruwaba, nasan kuma dolene anemeka amatsayinka Na babba".
Marairaicema mama fuska yayi, please mama kibarmu mutafi, wlhy Aysha ta galabaita, aii su Sultan suna nan, kuma uncle ma'aruff ma yana nan, mama Dan ALLAH jikinta k'ara zafi yakeyi".
Tamkar mama tayi dariya, amma saita danne, tace, " shikenan, kuje, amma idan kaga da sauk'i kudawo gida".
"To mama".
Hafiz yaja mota suka fice, Amatullah na agaba, shikuma yana baya rungume da Aysha.
Anty shukurah ma batabi takan abinda yadawo da mufeedah ba tashiga mota itada Ramadan sukabi bayansu.

Duk rugund'imin da akeyi agidan akan ciwon Aysha hajia babba naji amma kota kula, sunatama shan hirarsu da sauran bak'inta, hakama Anty zuwairah tanaji amma tayi kunnen uwar shegu, saima k'ok'arin had'a sauran kayan mufeedah takeyi wai su najwa suje su kaimata. Fitowar su Najwa zasuje gidan mufeedah ne sukaji k'ananun magana Na tashi akan dawowar mufeedar, dasauri suka koma suka gayarama hajia babba.
Da Sauri tamik'e tana fad'in, " ke shashasha mikike fad'ane?".
Baki najwa ta zun6uro gaba, "Niba shashasha baceba, kajimin momynnan, bajinayi ana gulmaba awaje, wai tana 6angaren baffah Anty mufeeyn".
Da sauri Momy da zuwairah suka nufi 6angaren baffa, kotakan jama'ar tsakar gidan basubiba.
Mufeedah Na k'asa, 'yan rakiyarta da baffa da ammah Na zaune.
Wayace a hannun baffa yana kiran Ameenudden, Dan yafison ayi komai a gabanshi.
Babu dad'ewa ameenudden yad'aga, cikin ladabi ya gaida baffa. Baffah ma ya amsa cikin kulawa, yace, " yarona Ameenu kana inane?".
"Baffah ina gida".
''gidanka konan gidanku?".
" a'a gidana".
"Idan ban takurakaba kazo INA nemanka".
" to baffah inazuwa".
Dama ashirye Ameenu yake, yasan dolenen anemeshi, tunda mahaifiyarsa da yayyensa biyu kawai sukasan miya faru, wad'anda suka raka Mufeedah kuwa Yayar babansace da k'anwar mamansa.
Babu dad'ewa saiga aminudden.
Cikin girmamawa ya gaida kowa dake falon, Yakoma kusada mufeeda k'ad'an ya zauna.
Baffah ya kalli Anty Mamie, "Bilkeesu ina Mu'azzam da Sultan?".
" babana yatafi kai Aysha asibiti, saboda tanata amai, saidai akira Sultan d'in".
''Ya salam, shine ba'a sanar daniba, yaushe abin yafaru".
"Kayi hak'uri baffansu, wlhy dukmun rud'ene".
''To ALLAH yabata lfy, bara agama da wannan matsalar saimu bisu, kiramin sultan da Mujahedeen awaya........
Shigowar hajia babbane yasaka kowa waigawa ya kalleta, mufeeda tatafi da gudu tafad'a jikinta tana kuka.
Tsawa baffa yadakama mufeedah, ''Dan ubanki dawo ki zauna, kafin Na sassa6a miki kamanni".
" tofa zaka raba 'ya da uwane?".
Banza baffah yayma Momy, kuma babu Wanda yasake tankawa, dukda surutai da Momy ke saki marasa dad'i, wai ba'a kirataba, amma ancika mak'iyanta da falo sun saka mata 'ya tsakkiya.
Cik'in 'yan rakkiyar mufeeda hajia Altine tace a lallai, Ashe da dalili shiyyasa matarka babu tarbiyya Aminu?".
Kowa dai yay shiru ba'ace komaiba, harsu ya Sultan suka shigo.
Ananne baffah yay gyaran murya, tareda sallama, yace, "aminuddin mike faruwane?".
Kafin yayi magana hajia babba ta kar6e, wlhy bazai yuwuba, saidai kowa yafice yafad'a dagani saikai da mufeeda, amma baza'a fad'i komai gaban kishiyoyinaba".
Tsaki baffa yayi, yad'auki waya yakira mama da umme amarya, yace suzo yana nemansu.
Cikin k'uluwa hajia babba tafara zuba jaraba.
Amman Ce ta taka mata birki, Laure wlhy inbakiyi shiruba yanzu zakibar falonnan, kokuma nasaki nadama.
Saida Momy ta gatsina baki sannan tayi shiru, tasandai wacece ammah, bata d'aukar raini.

Su mama suna isowa kowa ya zauna, sannan baffah yasake maimaitawa Aminu tambayar.
Kan aminuddin ak'asa yace, "baffa ka gafarceni da abinda zan fad'a, nasan wannan ba tarbiyyar gidanka baceba, Dan kamalarka data yaran gidannan yasakani kwad'ayin auren mufeeda, wlhy koda hakan ya bayyana ban zargekaba, shiyyasama namik'a zancen ga magabatana".
"Tunda aka kai mufeeda gidana ranar asabar da zazza6i taje jikinta, ni duk Na d'auka gajiyar bikice tasakata zazza6in, haka muka kwana babu dad'i dai har safiyar jiya lahadi, shine nakira family doctor namu ya dubata, yay mata text yace zaije ya bincika yau zai kawo mana sakamako, ganin yanda takejin jiki sosai ajiyan, kuma maganin da doctor yabata zazza6in yak'i sauka, harma tana ganin jiri, gashi tak'i cin abinci har 4 Na yamma, shine nasake kiransa, hak'uri yabani akan bara ya bincika text d'in daya mata, saiyazo da sakamakon, dakuma maganin daya dace tasha.
Nacemasa shikenan ngd.
Wajen misalin 8:30 saigashi yazo, saidai duk yanayinsa ya nuna a sanyaye jikinsa yake, kirana gefe yayi yabani result d'in. wlhy baffa Dana bud'e saida juwa ta kwasheni, saida doctor Ameer yarik'eni saboda tashin hankalin abinda ke ciki.
Dana dawo dai-dai nahaushi da masifa akan baisan aikinsaba, yanata bani hak'uri dason fahimtar dani amma nak'i saurarensa, saina d'auketa mukaje Rahma especial hospital, amma bayan gama dubata result d'in duk d'ayane dana doctor ameer, saidai saboda bushewar zuciya irinna mufeeda ta dage akan k'aryane wlhy, tun a asibiti muka fara fad'a, ganin abin zaiyi tsamari karnaje Na daketa Na illatata nakira ummi Na Na sanarmata komai, tun a Daren sukaje suka taho da mufeeda nan maitama, anan gidanmu takwana".
"Humm mi result d'in ya nunane Aminu?".
Farar takarda Aminu yamik'ama baffah kansa ak'asa.
Baffah ya kar6a zuciyarsa Na harbawa, jikinsa a sanyaye yamik'ama Ya sultan, Dan bazaiso yafara ganiba, gudun karyaga abinda zai saka zuciyarsa bugawa.
Ya Sultan yabud'e takardar yafara dubawa, saida yamik'e tsaye Dan tashin hankali, har zufa saida tafito kan goshinsa, murya Na rawa yace, " mufeeda kin 6ata sunan gidanmu, da girmanki kije wani yamiki cikin shege harna tsawon watanni uku, kuma kinssan da hakan amma kika bari aka d'aura miki aure dawani?".
Duk falon kowa sallallami ya d'auka, baffah kam yakasa koda motsi, hajia babba kanta ture mufeeda tayi daga jikinta, ta fisge takardar daga hannun ya Sultan tana dubawa, jikinta sai 6ari yakeyi kuwa, aii batakai k'arsheba tazube awajen.
Zuwaira da ya sultan dasu mama duk sukai kanta, ya mujahedeen kam sarkin zuciya aii kan mufeedah kawai yayi yahau duka kamar ALLAH ya aikoshi.
Da k'yar Aminuddin ya kwaceta a hannunsa, please ya mujahedeen kayi hak'uri kasan ba ita kad'ai baceba, kar dukan yajawo wata matsalar".
"Kabarni Ameenu, sainama yarinyarnan dukan mutuwa tafad'i yanda akayi, munafuka afuska kamar bazata iyaba, idanma ka hanani dukanta wlhy ya khaleel yadawo saiya kusan kasheta agidannan".
Duk da hakadai kayi hak'uri Dan ALLAH, nima danya zama dolene asani shiyyasa nafad'a wlhy".
Ammah da hankalinta nakan d'anta baffah tace Ameenu kabarsa yadaka fitsararriyarnan, Mujahed kiramin Babanku Ma'aruff awaya.
Ya mujahedeen yana huci yakira uncle Ma'aruff dayaje gidan wani abokinsa.


____________________________

Lokacin da ake bak'incikin cikin dake jikin Mufeey baby>?#?, ya khaleel nacan Na farincikin result d'in kazarsa da Aysha taci tabiya a asibiti.
Gwajin farko doctor Faisal ya tabbatar musu Aysha ta harbu, cikin watanni biyu da sati =?F? Wayyo zokaga bidiri wajensu anty Shukurah da Ama...
Oga kwata-kwata kam rungume Aysha yayi dukda tana barci ansaka mata k'arin ruwa, hawayen farincikine ke zirara a kumatunsa, wai yau shine za'a haifama d'a, gudan jininsa, wanda dole akakira sunan d'an ahad'a da nasa sunan, duk inda 'yar ko d'an yaje za'ace d'an/'yar Ibraheem khaleel ce, wayyo ya ubangijina, kaike bada k'yautar da kud'i ko mulki bazasu sayaba, kaike bada abinda babu wani mahaluki aduniya dake ikon bama mutum ko hanashi sai kai kad'ai ubangijin talikai, ngd maka godiya mara adadin k'ididdiga, godiya irin wadda tafi k'arfin harshe, saidai zuciya taita ayyanawa.
Duk su Hafiz cirko-cirko sukayi suna kallonsa, kowa fuska d'aukeda murmushi, yau sunga farincikin d'an uwansu.
Cikin tsokana hafiz ya kirashi, "ya khaleel tunda nina kawota asibiti idan ta haifi namiji sunana za'a samasa".
Dariya duk sukayi, harda ya khaleel da idanunsa ke a lumshe, ya kwantar Aysha ahankali yana kallon Hafiz, " Hafiz ko sunan 'yan gidanmune duka zan iya sanya masa ko mata kaji".
Nanma duk dariya sukayi, Hafiz yaciro waya zai kira gida yayi kwarmato Anty shikurah ta dakatar dashi, "A'a Hafiz dakata, dolenefa mufad'a yanda za'a bamu goron Albishir, wayakamata afara kira?".
"Anty!, baffah ko Ammah".
" yes akirah Ammah, tunda itace tushen kowa".
Hafiz ne yakira Ammah, dukda yanda ta amsa sallamarsa bai damuba, Dan zumud'i baisa yagane muryar tata da damuwaba, "Ammah Albishirinki".
Cikin dakewa amma ta amsa da goro, Dan batason katsema Hafiz farincikinsa, dantaga azumud'i yakirata".
" mizaki bani to?".
"Duk abinda kakeso bayan kafad'amin kaza6a".
" anzo wajen, Anty Ayshan ya khaleel tanada ciki".
Da sauri Ammah tamik'e tsaye tana fad'in Alhmdllh, yanzu kuna inane?".
"Muna asibitin doctor Faisal, ansaka mata k'arin ruwa tana barci".
Duk jama'ar falon suna kallon Ammah ne, jira kawai suke tagama wayar ta sanar dasu abinda yasakata farinciki, dukda suna cikin bak'inciki.
Tana yanke wayar kuwa tayi gud'a, dafad'in "Alhmdllh. Dama wani Na haddasa maka damuwa wani yana yaye maka, matar iroce da ciki".
kowa saida yafurta Alhamdllh, banda hajia babba data farfad'o yanzu, hakama Anty zuwairah bak'inciki kamar zai karta.
Tuni kowa yadaina damuwa da cikin mufeedah yakoma murnar Na Aysha, mama dai batace komaiba itama, saboda kara.
Bayan uncle ma'aruff ya iso akabama dangin Aminu hak'uri, aka kuma sanar dasu za'azo har gida ak'ara bada hak'urin.
Annakuma take Aminuddin cikin jin kunya yabama mufeedah saki d'aya.
Babu Wanda yaji haushi, saidai mufeedarce ta rushe da kuka, momyma kukan zuci takeyi.
Sudai su Aminu sukayi sallama suka tafi, bayan sunmusu murnar cikin Aysha.
Babu wanda yasake bi takan mufeedah, Dan hukunci kuma sai'an zauna, baffah ya sallami kowa, suka d'unguma zuwa asibiti.
Momy dai da Anty zuwaira basubiba.>?#?.lol.


********

Labarin cikin Aysha dana mufeeda yakarad'e gida, harda result d'in saki d'aya.
Kowa saidai yace ALLAH ya k'yauta, Na Aysha kam sai murna sukeyi, musammanma 'yan Kano.
Amma da baffah dawasu cikin 'yan Kano da uncle ma'aruff dasu Sultan, Anty Mamie duk suka d'unguma zuwa asibitin.
Har lokacin dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login