Showing 63001 words to 66000 words out of 155647 words

Chapter 22 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

467

ba'a ganin k'ok'arinmu, saikaji wasu nacewa ana musu Jan ajiaji ko wulak'anci ko yanga, humm kumana adalci mana, tun farkofa mu muka saka kammu, babu Wanda yasamu, wataranfa idan mutum yaga yana free har 2pages yi yakeyi arana, amma dukda haka inbakayi washe gariba sai anmaka maganar dazata sosa ranka, dukda dai nasan soyayyar dakuke manace take sakaku zumud'in son posting d'inmu._*
_To ALLAH yabar k'auna, muna godiya. Amma please & please aringa amana uzuri_.=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?d'd'd'>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&.


2? 4?

Iya dai gurzuwa bakin Aysha ya gurzu wajen ya khaleel, Dan harda bak'ar mugunta yahad'a wajen kissing nata, saida ya tabbatar ta jigatu sannan yasaketa, cikin balla mata harara yabar wajen.
Kuka Aysha tafashe dashi, "ALLAH saina had'aka da baffa nace giya kakesha, wataranama Baka kwana agida".
Wandonsa ya ida cirewa, sannan yad'ago idanu ya kalleta, "k! Bakinki baya mutuwa ko?, aikam yau zaki tabbatar giyar nakesha d'in", zuwa yayi yasakama k'ofar key, baibi takantaba yashige toilet.
Aysha tak'arasa jikin k'ofar tana jijjigawa, wai nufinta tagudu kafin yafito, amma ina ya kulle k'ofar ya cire key d'in, dawowatayi tana Neman key d'in, bata ganiba.
Rasa yanda zatayi tai, sai kwarar da hawaye takeyi, tasan inhar yafito kashinta yabushe, dukda akan gaskiyarta take, aiba k'arya tayiba, warin giyar yakeyi.
Tana nan tsaye tana sak'a wasik'ar jakai yafito sanye da rigar wanka, kallo d'aya yamata tana tsaye ya d'auke kai, babu ko kunya yacire rigar wankan yazauna zir dashi.
Da sauri Aysha tasaka hannu tarufe fuskarta gaba d'aya, bakinsa yata6e, yad'auki body spry ya fesa yasaka doguwar farar riga, sallar asuba yarama.
Saida Aysha taji alamun ya kabbara sallah tabud'e idonta, idanu tazaro waje, batareda tasan maganar ta su6uce mataba take, la'ila, harma sallah bakayiba?, tab lallai giya takai maka, hu'im, aikam tamkar agaban baffah akayi, saina fad'i komai=?o?
@&.

Atsanake yay sallarsa, yay addu'oi da azkar kamar yanda yasaba, tareda rok'on ubangiji gafara akan taushe hak'in lokacin sallah dayayi, bayan ya shafa yamik'e yanad'e abin sallar.
Itadai Aysha tana tsaye kanta ak'asa, la66anta sai uban zugin azabar zafi sukeyi mata.
Tana cikin tunaninta taji kawai anyi sama da ita, wutsil-wutsil tafara da k'afafu tana fad'in "wlhy nidai ka saukeni, ni ka saukine nace".
Bai kulataba yajefata agado, shima ya haye, nauyin rabin jikinsa yasaki ajikinta, >?#?dak'yar Aysha ke numfashi, cikin huttai tace, " please ya khaleel wlhy kanada nauyi, karka fasamin ciki ALLAH kuwa".
"Uhhm, mikike fad'a ina sallah d'azun". 'Yay maganar cikin d'aure face'.
"nifa ALLAH bance komaiba, please wlhy zaka fasamin ciki".
"yafashe mana ina ruwana, kedai bakinki bazebar rashin kunyaba ko? Wai miyasa bak'yajin maganane?".
Tunzuro baki tayi gaba, " yo aidai kaima kasan gaskiya nafad'a, wlhy sanda kashigo warin giya kakeyi, kuma ba jiya kwalliya kaci kafitaba? ina kaje to?".
"Kishinsa yagani k'uru-k'uru a cikin idanun Aysha, tana bashi mamaki yarinyarnan, ko kad'an bata tsoronsa, baisan miyasaba?".
Ya dungure goshinta, tareda saka yatsansa ya d'alli bakinta, da sauri tadafe bakin tana zubar da kwallah.
" shikenan, bakince zaki fad'ama baffah ba?, bara nahad'a da punishing d'inki saiki had'a duk kifad'a masa yamin hukunci".
Kafin Aysha tayi wani yunk'uri ya janye hannunta...........>?+?kundai san sauran basai an fad'aba.



(Wlhy ya khaleel yacika wayo, shidai kawai yace yakwaso damuwarsa a club zai sauke kan Aysha, amma yake dojewa=??).



______________________________

*_Islands uk_*

Hankali tashe Anty glory keta safa da marwa da waya a hannu, su Lola sunyi cirko-cirko kowanne fuska da damuwa, Lyn tayi k'arfin halin cewa, "shin wai Anty glo..... Mima yakai Moxies 9ja yanzu?, bayan kuma anfad'a masa anakama Anty Ruth a 9ja cikin wannan week d'in".
" hum Lyn bakisan taurin kai da izza irinna moxies ba, shi yad'auki kowa wawa, ranar Saturday fa saida nasanar masa yahak'ura da zuwa 9ja, saboda jami'an tsaro suna farautarmu, ankama Alhaji bishasha da yaransa, hardama Lazarus, yanzu hakama Neman alhaji barau modibbo sukeyi, amma sai cemin yayi su sukaso, shifa birthday d'in joy k'awarsa zaije, nabashi shawara yabi mata kud'in jirgi tazo nan saimuyi amma dayake munafukine saiya zare jiki yatafi bansaniba, yamin k'aryan zaije America ".
" yanzu haka cocaine yasiya yatafi da ita a6oye dankar musani, mai kwakwalwar kifi kawai".
"Happy tace, " ALLAH ya k'ara masa, ni dama su tarwatsa Kansa da bullet jaki kawai".
"Besi tayi dariya tana fad'in amma happy ked'in muguwace".
Serah da Queen dai basuce komaiba.
Anty glo ta zabga tsaki, " nifa Inda zasu kasheshin daidai kenan, kunsan bakin Moxies tamkar bututun mai yake, dayaji wahala wlhy tonamana asiri zaiyi".
Sudukansu kallonta sukeyi a tsorace, Lola tace Mo.....ka cucemu wlhy, Anty yakamata kikira ko Anty kubra kisanarma, kokuma Anty Grass".
"Hakane Lola kema kinzo da shawara".
Grass tafara kira amma baijeba, tamaida akalar kiran kan kubra, bugu biyu tad'aga, bayan sun gaisa ta kwashe komai ta sanarma kubra.
Hankalin kubra yayi masifar tashi, Dan itama jiya dak'yar tasha, wata mota taita binta abaya, shin wanene kemusu tsinci d'ai-d'aine haka?, kiran hajia khaltum tayi itama ta fad'a mata".
''Duk hatsabibancin hajia khaltum matsoraciyace, dandanan tagama rikicewa, tasaka driver yakaita gidansu ya khaleel, Dan aganinta zancen yawuce Na wayama....


>?8? @&>?8? @&>?8? @&muje zuwa guys>?'?.


___________________________
Ido sha6e-sha6e da hawaye Aysha tashiga wanka, bak'aramar mugunta ya khaleel yamataba wajen kusantarta, saida tayi nadamar yimasa maganar shan giyarnan, (tasan baikamata ta tambayeshi ta wannan sigarba, amma tanada dalilinta itama nayimasa wad'annan abubuwan), haka tahad'a ruwa a toilet d'insa tagasa jikinta, Dan yahanata key d'in bare taje d'akinta ta kimtsa.
Shikam yana kwance akan gado idonsa a lumshe, zuciyarsa fal da tunanin Aysha da k'uruciyarta, akwai rashin kunya kuma akwai tsoro, saidai dauriyarta wajen k'ar6arsa yana sakashi jin tana burgeshi, sosai yake jinjinama k'ok'arinta wajen kar6ar uzurinsa aduk yanda yazo mata, yakanji tausayinta over, saboda tayi k'arama dayawa, shigarta bayi yasakashi bud'e lumsassun idanunsa.
Ya furzar da iska abakinsa sannan yasakko daga gadon shima, toilet d'in yashiga, tana kwance cikin ruwa ta rufe idanunta, kallonta kawai yatsayayi, tabashi tausayi yanda take zubar da hawaye har yanzun, yasaki guntun murmushi sannan yashiga cikin ruwa.
Da sauri tabud'e idanu tareda zabura zata tashi, yamaidata cikin ruwan, amma baice komaiba, itama shiru tayi takasa fitar, takoma ta lafe a k'irjinsa saboda rungumota dayayi, ahankali yake shafa gashin kanta idonsa a lumshe, duk suna cikin ruwan, d'uminsa na ratsa dukkan wata ga6a ta jikinsu.
Kusan mimtuna 40 suka d'auka cikin ruwan, sanan sukayi wanka da taimakon ya khaleel, yanad'o Aysha a towel yafito, itadai tama kasa kallonsa saboda kunyakunya.

(Nima nakasa kallonku saboda kunya gaskiya=?H?).

Dakansa ya shiryata cikin wata doguwar riga brown, mai kwalliyar fari d'ishi-d'ishi, tamata k'yau, har yanzun tana mamakin yanda yake zak'ulo kaya iri-iri yana bata tana sakawa, badai tayi maganaba saboda tsaro ba tsoroba=??.

Bayan sungama kimtsawa yabud'e k'ofar, aii Aysha tarigashi fitowama, ta tarar zeenatu tafita, amma ankawo break fast an jera a dinning table.
Tana cikin bud'e abincin yafito, dining d'in yak'araso, yaja kujera ya zauna, batareda ya kalletaba yace, "had'amin abinci yunwa nakeji".
Yanda yay maganar yana wani cin d'aci sai abin yabama Aysha dariya, tasaki murmushin daya bayyana jerarrun hakwaranta farare tas, batace dashi komaiba tanufi kichin.
Bin bayanta yayi da kallo shima yana murmushi, yana kallon sanda tasaki murmushin d'azun, bayansa ya jingina da kujerar yajawo wayarsa yakira Taheer.
Babu dad'ewa yad'aga, suka gaisa.
" hummm sannufa da k'ok'ari j!, kace jiya operation d'in dare kafita?, nakulafa mai email d'in sirrin nan dagaske yake taimakonmu zaiyi".
"Hakane taheer, dama nace inhar muka kama mutum uku acikin sunayen biyar daya jero, tom tabbas da gaske yakeyi, amma ina mamakin waneneshi? Miyasa kuma ya 6oye mana kansa?".
" hakane j, wlhy nima tambayar dakemin yawo kenan kullum arai, amma ko wayema insha ALLAH zai bayyana mana kansa k'ila anan gaba kad'an".
"To ALLAH yasa".
" Ameen to, kana inane?".
"Ina gida wlhy, sallar asubahice ta kwacemin shine nakoma gida nayi wanka nayi, amma zuwa kamar 1 zanzo office, akwai wasu files dana sakama hannu please kad'auka ka kaima Oga, kaima Na ajiye wasu takaddu kad'aga k'ark'ashin files d'in da youseef yakawomin ranar Friday Na d'ora kwalin pen akansu, saika d'auka kadubasu, idan kagama kabama Solomon".
"Ok, shikena saika shigo".
"Ok".
Duk agaban Aysha yayi wayar, jitake wani uban dad'i Na ratsata, tamkar ta taka rawa Dan murnar ganin aikinsu Na tafiya dai-dai, lallai bud'e email d'in sirrinnan bak'aramin sauk'ak'a musu aiki yayiba, ALLAH mungode maka, kubrah kece next=??, insha ALLAH". 'Tayi maganar tana dariya a zuciyarta'.

Abincin tahad'a masa, yanda take komanta cikin nutsuwa da Jan aji sai ta burge ya khaleel, harya shagala da kallonta tun yana waya da taheer, harga ALLAH yanson mace mai nutsuwa, kai shi harma namijin, yanason mu'amulla da nutsatstsun mutane.......
Sai magana take masa, tagama, amma yana wata duniyar, cikin mamaki Aysha tace, "naga ta kaina, mikuma ya khaleel yake tunani? Ko har yanzun giyar bata gama sakinsa bane?".
Karaf sai a kunnensa, ya fesar da iskar bakinsa, sannan yakamo hannunta ya zaunar kan kujerar dake kusadashi, "A'eesha! Kalleni nan".
Babu musu Aysha ta kallesa, amma bazata iya jure kallon tsakkiyar idonsaba, saboda kwarjinin dake cikinsu Na kamala da nutsuwa, tajanye idanunta akansa, amma dukkan hankalinta na kansa.
" miyasa kika rainani wai?".
"Lah nifa ba rainaka nayiba".
" uyim to miye? Inba rainiba".
"Shikenan to, kayi hak'uri bazan sakeba".
Idanunsa ya lumshe, batareda da sake tankawaba yagyara zamansa, abincin yad'iba yakai bakinsa, lumshe ido yayi Dan dad'i, yasandai wannan girkin kodai mama kokuma Anty Mamie, Dan sune keciyar dasu bbinci mai dad'i da gamsarwa.
Yad'iba yakai bakin Aysha, bata bud'e bakinba, saidai d'ago ido tayi ta kallesa, ya harareta, babu shiri tabud'e bakin azuba mata.

Sallamar su mufeeda ne yasakasu d'ago ido suka kallesu, Aleeya da mufeedah ne, wadda Aleeya tamatsa sai an rakota wajen ya khaleel d'in sun gaisa, shine momy tasaka mufeeda ta rakota.
Ya khaleel kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa, yad'ibi abinci Yakai bakin Aysha, itako Dan kawai ta k'ulal da mufeeda takar6a a yangance.
Aikam ba mufeeda kawaiba har Aleeya sak'on Aysha ya iso gareta, mufeeda falo taje ta zauna, bayan ta gaida ya khaleel da ko kallonta baiyiba, itakam Aleeya dining d'in tak'araso, taja kujera tazauna.
Da mamaki Aysha take kallonta, ya khaleel baima nuna yasan da zamantaba.
"my boo... Good morning".
Maimakon shi ya amsa sai Aysha ce tace, " tofa, kajimin wani sabon salo, boo...kuma? Babbar magana, su gwaggo daga ina? Dan nikam kin wucemin Anty saidai gwaggo, Dan nakula kinkai haihuwar kamata".
Bak'aramar dariya Aysha tabama ya khaleel ba, amma yadake bai yiba, sai guntun murmushi, yakula yarinyarna akwai rainin wayon tsiya, Ashe rainashin datayima k'aramin alhakine, inbanda wulak'anci dai yaza'ayi takalli Aleeya tace mata wau tama haifeta, kajifa iskanci, hardama kiranta gwaggo......
Tea d'in da Aleeya tad'auka agabansa tana sha wanda Aysha ta had'a masa yasakashi juyowa ya kalleta, tamasa fari da idanu.
Janye idanunsa yayi yamaida kan Aysha, wadda tacika tayi fam daboda rainin wayon Aleeya, gashi Aleeya tak'i tanka maganar da Aysha tamata.
Amma itama sai cakud'a maganar ayshan takeyi cikin zuciya, tarasa abin da zata cema Aysha ne shiyyasa taza6i yin shiru tashare maganar, batareda ta maida murtaniba, saidai tunani takeyi akan badai Aysha bace matar khaleel?.
Wani tea d'in Aysha tahad'ama ya khaleel, batareda takuma kallon ko Aleeyar ba, yauce rana ta farko da Aysha tamasa Abu mafi mamaki, Wanda baita6a zaton tsaurin idonta yakai nanba, dukda hakan yasaka takuma birgeshi da k'ara kima a idonsa, domin ta nuna martabarta ta d'iya mace mai aure.
Humm. Koda Aysha tagama had'a tea saita kar6i cokalin hannunsa, bai hanataba, yabata yanamai kallonta da mamaki fes a fuskarsa, soyake yaga mizatayi....
Baikai k'arshen tunaninsaba yaji lallausan tafin hannunta a face d'insa, kuma fuskarta d'aukeda murmushi, tad'age gira d'aya sama kamar yanda yakeyi sannan tazuba masa abinci abaki.
Shikansa batareda yasaniba yabud'e bakin=??, Dan salon Aysha yagama kashe masa jiki murus.
Aleeya dai da mufeeda kallonsu sukeyi cikeda bak'in ciki, har Aysha tagama ciyar da ya khaleel abinci, shima kuma yaciyar da ita dariya kuwa nata cinsa azuciya, wai wannan 'yar yarinyar tasan kishi.
Kamar wasa aleeya takamo hannun ya khaleel, cikin shagwa6a tace, "haba my boo...wajenkafa Nazo mu gaisa, tunda kagama break fast d'in saika juyo aii muyi hira".
"Kambu tak'ashin ubankiiii Aysha tafad'a azuciya, tayi kwafa aziciyarta tana fad'in yau zan nuna miki Na haddace karatun Anty glory Ashe, sannan inasamun ilimi wajansu Lola da Lyn.
Kawai ya khaleel nashirin juyawa yama Aleeya tatas saikawai yaga Aysha bisa cinyarsa, kutttt>?%?, baikai k'arshen mamakinsaba tafara shafa fuskarsa tana fad'in cool dawn Sadauki na, kasanfa 'ya'yan tasha ako ina sai sun nuna hali, naga ranka zai 6aci abanza akan shakatafin gwaggon nan, kwantarmin da hankalinka mana sadauki na", 'tayi maganar tana shafa k'irjinsa'.
>?#?su ya khaleel an suma alkur'an.
Lallausan murmushi yasakar mata Wanda bai shirya yinsaba, saidai kawai birgeshi datayi, ita kuwa Aysha ganin tasamu goyon bayansa saita kashe masa ido d'aya, zuciyarta Na dukan uku-ukun tsoron tahad'e bakinsa danata".=?@?
Sassanyar Ajiyar zuciya kawai ya khaleel yasaki, aransa yace ya salam zata kasheni>?#?.
Kawai saiya bada kai bori yahau, yakuma tallafota da k'yau jikinsa suka cigaba da faranta ran juna=??.
Mamaki yakama mufeeda dakecan falo tana hangosu, dama yarinyarnan haka take?.
Aleeya kam aii mutuwar zaune tayi, tuni zuciyarta tafara tafarfasa kamar talgen tuwon dawa, dak'arfi tabuga table d'in dining waidan su tuna akwaifa mutane a falon, amma ina ko gezau basuyiba, su ya khaleel anyi nisan kiwo.>?-?
Da sauri mufeeda tataso tazo takama hannun aleeya dake hawaye sukabar falon>?#?>?#?>?#?.


(ho Aleeya kinyi gamo da sholyn sadauki=?9?)


Suna fita Aysha tacire bakinta dagana ya khaleel tana sauke numfashi, yunk'urin tashi tayi daga jikinsa, yay saurin janyota yamatse, murya awahalce yace, "aibaki isaba yarinya, zaki tadamin hanakiline abanza kigudu, kinci bulus kenan?".
Hawaye Aysha tafarayi, "please ya khaleel wlhy bakina yakusa daina aiki, kaji kuwa zugin dayakemin, kaima baka iya con kwan makauniyaba, daga tayi saika nemi zarmewa acinye dakai".
" koma miye kekika Sani, wayace ki kawo kanki". 'Yay maganar yana d'aukarta cak yanufi d'akinta'.
Wutsil-wutsul taketayi da k'afafu da kukan bashi hak'uri, amma ko'a kwalar rigarsa.


(Nikam bilynku dariya kamar ta karni>?#?>?#?>?#?>?#?, maganin sholy kenan aii, waya gaya mata barno gabas takene?, ta6o su ya khaleel aiba wasan yara baneba>?#?>?#?>?#?, gashinan wajen maganin aleeya, ita ya khaleel zaiyi maganinta=??.
gobema tak'ara aii.>?#?
su ya khaleel ba'a gayyacesu bama sunzo>?'?, bare ankawo musu goro>??.


______________________________

Da kuka aleeya tashiga 6angaren Momy, babu kowa saisu kad'ai, Dan su husna suntafi makaranta, Momy kuma tatafi aiki bayan fitarsu.
Lallashin Aleeya mufeeda taitayi.
"Humm bazaki ganeba mufeey, waini yau wannan 'Yar yarinyar zatama bariki?, tasan koni wacece kuwa mufeey?, shi yarasa wadda zai aura sai wannan tatsitsiyar abar, miyagani to ajikinta? Ko farar fatar da wad'an nan kwala-kwalan idanun nata uwa Na mujiya?".>؉?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login