Showing 99001 words to 102000 words out of 155647 words

Chapter 34 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

481

Sumbatar gefen wuyanta yayi, cikin kunnenta yace, " idan naje aikennan nikuma miye tukuycina?, hannu tasaka ta shafo kumatunsa, sannan tad'aga masa gira>?(?, saika dawo zaka gani".
"Wata sassanyar dariya yasaki acikin kunnenta, yana shinshinar wuyanta yace, ''yanzu kuwa zan samo abinci, kuma duk kukanki saina kar6i tukuycina".
Baijira cewarta ba yasaketa yafice.
Murmushi Aysha tayi tana binsa da kallo ta madubi, akan la66anta tafirta I love you so much sadaukina, kabani farinci yau d'innan, bakuma zanta6a mantawa da hakanba=?
?".
Shima abinda yake ayyanawa aransa kenan, fuskarsa d'aukeda murmushi sukayi karo da Momy afalo zaune.
" Momy kece?".
Juyowa tayi ta kalleshi, bak'incikin ganin fusakarsa a farinciki yadaki zuciyarta, amma saita dake, "nine my lovely son, zonan mana, kwana biyu ana fushi da Momy ko?".
Murmushi yayi, yak'arasa gefenta ya zauna tareda d'ora kansa a kafad'arta, yace, ''I miss you momyna".
" miss you 2 my dealing, ykk?".
"Alhmdllh momyn, saidai missing naki danayi, kiyi hak'uri kidaina fushi dani, ranarma sharrin shaid'anne, kinsan banida kamarki duk duniyarnan".
"Karka damu kaji Ibrahim, komai ya wuce, ina d'iyata d'in Aysha".
Kunyace takamashi, yad'an Sosa kansa yana murmushi, da hannu yanuna mata d'aki.
Murmushin yak'e Momy tayi.
Khaleel yace, ''dama zanje cikin gidane samo mata abinci, wai yunwa takeji".
" ayya gama meat pia na kawo muku, dama itace tacemin tanaso jiya, shine nayishi yau, kamaji da zafinsa saika kaimata taci, ni bara naje, Dan zuwairah na shirin tafiya".
Dad'ine ya lullu6e khaleel Dan ganin momy tafara basu kulawa shida matarsa, yamata godiya tafice, shikuma yanufi d'akinsa, tararwa yayi Aysha kwance bakin gado, yunwa tahanata ta6uka komai.
Kwanon tangaran d'in kawai yamika mata, jikinta har rawa yakeyi tatshi zaune, kusan tare suka d'auka, amma tarigashi gutsura, harta fara taunawa tatsaya, waini Sadauki inama kasamo meat pia ne haka? da zafinsa.
Harzai gutsura yatsaya bata amsa, momyce takawoshi yanzu, tace dama jiya kikace mata tamiki". (Acikin d'oki yake gaya mata).
Da sauri Aysha ta furzar dana bakinta, shima tayi saurin ka6e na hannunsa daya gutsura, bayi dasauri, fuskarsa a murtike yace, "k miye haka?".
Hankad'a kwanon Aysha tayi yafad'o k'asa ya tarwatse, Aysha tayi azamar tura hannu cikin bakin khaleel tana kwakulo Wanda ya 6allah, dama ko taunawa bayyiba.
Hankad'ata yayi tabigi gado, bata damuba, tunda tasami nasarar Ciro na bakin nasa.
" waike wane irin iskancine sannan? Uwatafa nace takawo ba uban waniba!!!".
Itama Aysha a tsawace tace, "ko itad'ince takawo bazakacishiba, kasan miye cikinsa?!!! To gubace ta kasheka inbaka sanib...........
Bai bari ta k'arasaba ya d'auketa da mari, ''k!!! Karfa kiga ina wasa dake kiringa kawomin iskanci, kina nufin uwata data tsugunna ta haifenice zata kawo guba tabani naci na mutu!!!!!?".
Hannun Aysha dafe da kuncinta tana kuka tace, " wlhy koda zaka kasheni saina fad'a, nace gubace aciki, bai dameni da matsayin Momy agarekaba, inma bakai tayi nufin kashewaba nitazo kashew........
Da sauri yamatsota, itakuma tamatsa baya, duka takuma kaimata ta kauce, ya wawurita tafice da gudu, shima binta yayi har cikin gida.
Basu zame ko inaba sai 6angaren Ammah, yanda Aysha tashigo aguje yasaka kowa mik'ewa, saiga ya khaleel shima, Ammah ce tayi jarumtar tareshi, sai huci yakeyi tamkar kurar daji.
Aysha da bakinta bai mutuba, saboda rud'ewar datayi, cikin kuka takuma fad'in wlhy koda zaka kasheni yau agidannan saina fad'a, gubace Momy tabamu muci a meat pia muci mu mutu, idankuma bahaka baneba tazo ta gardama mana.......
Kuma yunk'urowa yayi kanta, baffah daya shigo yanzu yay saurin rik'eshi, dandanan 6angaren Ammah yacika daduk Ahalin gidan.
Daga Aysha har ya khaleel sunkasa nutsuwar da za'a tambayesu, sai Aysha daketa fad'in ko khaleel zai kasheta saita fad'a guba Momy tabasu suci su mutu, kuma inba haka bane tazo ta Musa zancen.
Shikuma ya khaleel sai fisgewa yakeyi daga rik'on baffah, burinsa kawai Yakama Aysha yamata dukan mutuwa, tunda har tsaurin idonta yakai taringa yima mahaifiyarsa sharri haka.
"Tsawa baffah yadakamusu, yace, " kai duk banason rashin hankali, minene yahad'aku?".
Aysha zatayi magana ya khaleel yay saurin tareta ta hanyar fara fad'e.............
'





Hummm sannu-sannu bata


*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_

3? 7?

Tunda ya khaleel yafara bayani kowa yay tsirmai-tsirmai da idanu, dankuwa duk Wanda yake a 6angaren Ammah yaci meatpia d'in, Dan Tasleem ma sarkin tsoro hawaye takeyi, tasandai sungama aiki sukam, yau sai mutuwa>?#?.
Mama ce tadakama Aysha tsawa, tayo kanta zata daka, Ammah ta dakatar da ita.
"Fad'ima kema bakida hankalin kamar iro, waishin kun mantane yarinyarnan k'aramin cikine da ita?, sokuke cikin yazube saboda rashin hankalinku..........?
Maganar Ammah takatse yayinda sukaga Aysha nalayi, tamkar wadda tasha giya, dak'yar numfashinta ke fita, duk kanta sukayi suna kiran sunanta.
Yarab Aysha tazube ak'asa asume, sallalami kowa yafara, Muhseen yafita da Sauri d'akko key d'in mota.
Jikin ya khaleel ne yayi sanyi, dukda bai k'arasa inda Aysha takeba, amma idonsa Na kanta, gashi gaba d'aya mutan gidan sun rud'e, mamace kawai take tsaye agefe kamar ya khaleel, saidai itama hankalin nata amatuk'ar tashe yake.
Baffah ya dakama ya khaleel tsawa akan yazo yad'auki Aysha yakaita mota.
K'arasawa yayi ya d'auketa, koda yasakata mota bai shigaba, sai Anty Mamie ce tashiga tarik'e Aysha, babu Wanda yadamu dashi motocin biyu suka fice aguje.

>??wai inama momyne?.

Tunda hajia babba tabama khaleel meatpia tabar gidan, sai gidan Aminiyarta, cikin farinciki take sanar mata komai ya kammala, yau damuwarsu tak'are.
Atare suka shak'e da dariya, suka tafa, hajia khaltum tace aminiya nasan dolene k'ungiya tabaki k'arin girma wlhy, dama abin yazo a dai-dai, jibine za'ayi gagarimin taron k'ungiya.
K'yak'yal suka saka dariya.
"Amma aminiya wani hanzari ba guduba, shin kinsaka Wanda zai kwashe meat pia d'in idan sunci?".
"A, Aminiya daguduma kuwa, nasaka yarinyarnan Dije mai aiki, babu Wanda yasan yarinyar tanamin aiki ta k'ark'ashin k'asa aii, barama nakirata naji mike wakana agidan?".
Kiran Dije momy tayi, babu dad'ewa dije ta d'auka, jikin dije har rawa yakeyi tace, " hajia akwaifa Matsala".
Zumbur hajia babba tamik'e tsaye, ke banason mummunan labari kinfa sani".
"Hakane hajia amma dolene nafad'a miki, ................kaf dije ta sanarma hajia abinda yafaru, tad'ora dafad'in amma hajia ki kwantar da hankalinki, yanzu haka naje nakwashe meatpia d'in dakika basu, Na canja dawani mai k'yau, koda d'auka akayi danyin bincike bazasuga komaiba, itakuma matarsa dazasu sami bayanai tasuma, bansan miya sametaba, yanzu haka suntafi asibiti. Kinga sauran aiki nakine, saikiyi azamar samun Wanda zai ida miki ita a asibitin".
Ajiyar zuciya Momy tasaki, tace, " shikenan dije, ki kula da komai, yanzunnan zanzo gidan nima".
A gaggauce Momy tayima hajia khaltum bayani, dukda a rud'e suke hakan baihanasu Neman yanda zasu salwantar da rayuwar Ayshaba, sungama shirya hajia khaltum zataje asibiti, Momy kuma tanufo gida.



***********
Suna tafiya asibiti ya khaleel yanufi 6angarensu, meatpia d'in nanan inda suka barsa, tattarashi yayi yazuba aleda, yad'auki key d'in mota da sauri yafito. Aharabar gidan sukaci karo da Momy, kallon-kallo aka tsaya yi, amma dayake Momy A ce, saita wayance, tak'araso gun ya khaleel tana fad'in Ibraheem! Lafiyarka Kuwa? Naganka wani iri?".
Hawayen dasuka mak'ale a idonsa suka ziraro, Momy tak'araso kusadashi sosai tana share masa, 'yan gidan wad'anda basubiba asibitin duk suna tsaye suna kallon ikon ALLAH.
kad'an ya khaleel yazame jikinsa daga kusada Momy, yabi sauran 'yan gidan da kallo, yace, "duk Wanda yasan yaci meatpia d'in yashiga mota muje asibiti".
Cikin dukan k'irji da zare ido Momy tace, " meatpia kuma? miyafaru dashi?".
Bai bata amsartaba, sai cewa yayi "kedai Momy Shiga mota kawai muje asibiti".
"Wane irin nashiga mota muje asibiti? Waimike faruwane? Ninasan ninayi meatpia agidannan yau, kuma anacewa duk Wanda yaci yashiga mota aje asibiti, Ibraheem banason kwana-kwana fad'amin miya faru!?".
Tayi maganar ad'an tsawace.
Rintse idanu ya khaleel yayi, bai cema Momy uffanba yara6a ta gefenta zai wuce, wata razananniyar tsawa ta Dana masa, "kai!!! Ibrahim, banason iskancifa, Dan ubanka inamaka magana amatsayina Na mahaifiyarka shine kake shareni?".
Ransa amatuk'ar 6ace yake, amma cikin sanyin murya yace, " Momy mikeso nace mikine, kefa kika bada meatpia d'innan, kuma kinfi kowa sanin mikika zuba acik........
Baikai k'arsheba ta tari numfashinsa, " minazuba Dan ubanka?".
"Momy A'eesha tace kinzuba guba aciki, kuma dabata ganiba bazata fad'aba, dukda zuciyata bawai ta amince baneba, amma inason Sanin mike tsakaninki da matar d'anki? tabbas akwai wani Abu 6oyayye tsakaninki da A'eesha, yazamemin dolene naje abincika duk Wanda yaci meatpia d'in agidannan".
" yanzu nan Ibrahim harni kake zargi akwai wani Abu tsakanina da matarka??, harma zargina kakeyi nazuba wani Abu aciki nabaku kuci Ku mutu ko? To aii Alhmdllh tunda Baku kad'aine kukaciba, su Ammah ma sunci. shikenan naji, muje asibitin abincikasu".
Babu Wanda yace komai duk suka Shiga mota, harda ita momyn.


________________
A asibiti kar6ar gaggawa akaima Aysha, harsu khaleel sukaje doctors basu fitoba daga kan Aysha.
Cirko-cirko suka iske su baffa, kowa da sak'e-sak'en dake ransa, musammanma baffah daya rasa wane kalar tunani zaiyi, koda Momy sukazo itadasu khaleel bai kalli inda takeba, tabbas zuciyarsa Na raya masa akwaidai abinda basu saniba, Dan haka kawai Aysha bazatace Momy tabasu guba suciba, ya salam, wannan wane irin lamarine haka? idan zancen Aysha gaskiyane miye ribar hajia laura Na kashesu?, Mu'azzamfa d'antane nacikinta, Wanda tafiso duk cikin 'ya'yanta, dan tasha fad'a masa hakan, ya ALLAH ka warwaremana wannan lamari cikin sauk'i".

Nace amin baffah.

Ya khaleel office d'in babban likitan yaje gaba d'aya, yafad'a masa aikin dayakeso amasa yanzun cikin gaggawa, Dan gudun kar gubar tafara aiki ajikin wad'anda sukaci, inhar gaskiya Ayshan takeyi.
Babu kuwa 6ata lokaci aka kira duk Wanda yaci meatpia d'in, likitoci dayawane suka maida hankali Kansu, harda meat pia d'in da ya khaleel yad'akko a Leda.
Yini guda zubur a asibitin sukayishi, Dan har zuwa bayan isha'i anata bincike, Aysha kuma ta farka, amma sun mata allurar barci.
Ganin dare yayi aka sallamesu akan sukoma gida, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu komai zai kammala, amma dukkan wanda yaci meatpia d'in anmasa allurar rigakafi, dukda dai doctors d'in sunga alamun babu guba ajikinsu.
Ya khaleel da baffah sai anty mamie gwaggo bintu kawai aka bari a asibitin, sauran duk baffa yace su koma gida, tuni ya khaleel yabaza ma'aikata a asibitin.
Dukda hakan bai hanasu hajia babba k'ule-k'ullensuba akan Aysha, saidai har yanzun basu sami nasarar aiwatarwa bane.



*****"*****
Daren ranar gaba d'aya hajia babba bata rintsaba, tasan wanene khaleel akan bin k'wak'wk'wafi, dukda babu wata hanyar daza'a gane tabasu meatpia mai guba, tunda sauran 'yan gidan Wanda babu gubane tabasu, kuma dije tayi saurin canja Wanda tabama Ayshar.
Haka taita safa da marwa a d'akinta, takasa zaune takasa tsaye.


******

Kusan dukkan ahalin gidan atsorace suka kwana jiya, musamman ma yara=? ?.


*WASHE GARI*

Washe gari takama lahadi, salla ce kawai ta fidda ya khaleel daga jikin d'akin da aka kwantar da Aysha, garama baffah bayan sallar asuba yaje gida ya kimtsa yadawo.
Aysha har sannan barci takeyi sosai, tafiyar baffah babu dad'ewa saiga Momy.
Ya khaleel ya gaidata, ta tambayi jikin Aysha yace da sauk'i badai ta farkaba har yanzun.
Dad'i sosai Momy taji.
Tace, "to aii dakunje gida kaidasu Bilkeesu, nisaina tsaya wajenta kafin kudawo".
" A'a Momy, saidai su Anty Mamie suje su, amma ni barin asibitinnan bai kama niba yanzun".
Shiru Momy tamasa bata tankaba, Dan yazama dole tayi yanda zatayi subar asibitin, dansu sami damar aiwatar da shirinsu, zuwacan wani tunani yafad'o mata, tabbas baikamata ta matsa akan saisun tafinba, Dan zai iya zargar wani abun.
Suna nan zaune awaje su duka Dan ba'a buk'atar yima Aysha hayaniya, wata nurse ce tazo tashiga d'akin da Aysha take kwance, kusan mintuna 30 tafice, fitarta dakamar minti 10 saiga watama, kamar ya khaleel zaiyi magana amma saiyayi shiru, yakoma yasake jingina da bango.
Kusan mintuna 20 nurse d'in ta d'auka ad'akin Aysha, sannan tafito ad'an hanzarce, harta gotasu ya khaleel ya tsaidata dafad'in jimana".
Idanu tarintse, gabanta Na fad'uwa tadawo baya.
Ya khaleel yace, "mike faruwane sai shigi da fici kukeyi?, kunk'i kuce mana komai, tafarkane naga kin fito jikinki Na rawa?".
Gabantane yakuma fad'uwa, muryarta Na rawa tace, " sorry Alhaji, zankira doctor, naga kamar tana motsawa".
Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, da hannu yamata alamar taje to.
Da saurinta kuwa tayi gaba.
Saida ta6acema ganinsa kuma saiyaji zuciyarsa takasa nutsuwa, da sauri yatura k'ofar d'akin da Aysha ke kwance yashiga, idanu yazaro waje=?3?, Dan ganin halin da Aysha take ciki, sai juye-juye takeyi kumfa Na fita ta bakinta.
Aguje yafito, su baffah Na tambayarsa lfy, INA bai sauraresuba yashige sashin offices d'in doctors d'in asibitin.
Ganin haka suma suka afaka d'akin da gusu.
Sallallami kowa yakamayi, Anty Mamie da Momy suka fashe da kuka, gwaggo bintu ce tayi k'arfin halin rik'e Aysha daketa fisge-fisge, harta fincike k'arin ruwan da aka saka mata.
Da doctors uku ya khaleel yashigo, cikin hanzari suka kori su baffah waje, sukuma suka duk'ufa kan aikinsu, duk yanda sukaso ya khaleel yafita yak'i fita, yanzukan hankalinsa atashe yake, yadafe kai yana jujjuyawa, waimike faruwane haka a gudundune? Wlhy kwalwar kansafa Na neman tarwatsewa daga jiya zuwa yau.
Ganin halin dayake ciki doctor Faisal ya lalla6ashi da k'yar yakaishi waje.

Yana zama kiran youseef yashigo wayarsa, tamkar zai fasa kuka yad'aga wayar.
Daga can youseef ya sanar masa cewar sunfa sauka Nigeria dasu glory, babu wani Neman bayani yace, sukaisu su ajiye.
Cikin mamaki youseef yace, "j! Kana lfy kuwa?".
Huci ya khaleel ya furzo kawai, amma yakasa cema youseef komai.
" j! Kayi shiru, kana inane wai?".
"Asibiti".
Abinda ya iya fad'a kenan ya yanke wayar.
Youseef ya sanarma su Samuel da Taheer, gaba d'ayansu suka furta asibiti kuma? Atare.
''Haka kawai yace ya yanke wayar".
Taheer yace, " tabbas babu lafiya, nidama tun a jiya dana kirashi yak'i d'aga waya kusan 18 call nacemuku badai lfy ba, tunda yasan irin aikin damukaje yi mai had'arine".
Gaskiyane, yanzu dai kawai munemi asibitin dayake, wani yakira mana Emanuel.
OK.
Bayan sun kira Emanuel yamusu bayanin abinda yasani shima, yace suna babban asibiti.
Cikin mintuna 40 saigasu kuwa.
Bak'aramin tashin hankali suka shigaba daganin abokin nasu, kuma ogansu ta fannin aiki, gaba d'aya yafita hayyacinsa, gawata uwar rama ta kwana biyu dayayi.
Basu nemi ba'asi awajensaba, sai baffah ne yamusi bayanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login